Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ta riƙe suka fita.
Shafi'i ya rufe hancinshi yace.
"Umma Dauda wari yake yi kamar yayi kashin wando" Carab Amina tace.
"Ni shi yasa ma naƙi zama a kusa dashi" Ni dai ina zaune jigum na rasa abinda yake yi mun
daɗi a rayuwata, nasan ba lalle bane in kwana da igiyar aure a kaina. Ina ganin rayuwa fitintinu
daga wannan sai in faɗa wannan, ya Allah kafi ni sanin abinda ke jawo wannan matsalar kai
mun zaɓin alkhairi, in Kaila ya sake ni Allah kai mun mafita, bani da kowa sai kai ya Allah. Ita
kuma Hajiyayye sharrin da take nema na dashi Allah ka mayar mata abinta. Duk wannan
magana a zuchiyata nake yi. Ga abinci a gabana na kasa ci sam. A inda su Yaya Use suka fita
suka barni a haka suka dawo suka same ni."
"Kun yi sallar isha ne?" Sani yace.
"Mun yi Mama. Mama amman ba'a katifarmu Dauda zai kwana ba ko?" Yaya Use ta dubeni,
kana ta dubi Sani tace.
"Anan zai kwanta ɗan uwanku ne fa Sani, wanka ne" Baki Sani ya turo gaba yace.
"Wallahi wani abune a jikinshi yake wari sosai, mu gaskiya bazai kwanta mana a katifa ba. Zata
yi magana na katseta da cewa.
"A kusa dani zai kwanta, katifar ai ba zata isheku ba." Shine fa su kai shiru, da ƙyar Yaya Use ta
dinga rarrashina sannan na samu na tuttura abincin. Ina zaune cikin zulumi na jiyo tsaiwar lifan
ɗin Kaila a ƙofar gida. Tun daga ƙofar gida ina jiyoshi yana ta faman jaraba, kamar tare da Isa
abokinshi yake. "Shanono, Shanono zo nan?" Na jiyo muryarshi a cikin zauren, a zabure na miƙe, Yaya Use ta
ce.
"Jira bari in je in mishi bayani na fahimta tukunna" Tana kaiwa nan ta fita da Hijabinta a hannu.
"Kaila sannunku" Wani irin haɗe rai yayi yace.
"Ita shanonon bata ji ina kiranta ne? Ko nima kin fito ki dake ni ne, tunda ba'a koya muku
tarbiyya ba? To ina ma aka nutsu da za'a koya muku tarbiyya? A kwararo fa....."
"Kai Kaila dakata kaji ko, kul ka kawo wannan zancan. Ni ba sa'arka bace, ka sani ba ƙanwar
Tani bace ni, yarta ce ko ince uwarta ce ni. Dan ina da mai shekarunta a gidan miji"
Maganganun Kaila yayi dai dai da saukar aradu a kaina. Ji nayi wani abu ya tokare mun
maƙoshi, sai lokacin na samu zarafin yin kuka, kukane ya turniƙeni mai ɗacin gaske. Ina jiyo
muryar Yaya Use da Kaila a sama.
"To Use bari kiji, ni na fiki tashanci wallahi, a kwararrafa na girma, har za'a nuna ma ɗan
kwararrafa iya shege ne? Iyayen Hajiyayye sunce ba zasu yarda da abinda ku kai ma ƴarsu ba,
zasu shigar da kararku, wallahi babu abinda ya dameni tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan
doka. Kuma ki fice mun daga gida kar ki kuma zuwan mun, tunda zuwan naki ba alkhairi bane."
Muryar Isa naji yana faɗin.
"Kaila baka kyauta ba. Tun a asibiti ina faɗa maka kabi komai a sannu kaƙi. Kayi haƙuri mana,
abinda ya faru ya riga daya faru. Allah ya ƙaddari Yaya Use ita zata kashe yaron dake cikin
Hajiyayye.Use gaskiya kema kin yi kuskure, ai ko Hajiyayye ce ta cakaleki da faɗa kya ɗaga
mata ƙafa. To sakamakon dukan cikinta da kika yi, yaron ya mutu mata a ciki, an yi tiyata an ciro
mata shi ba rai, kin ganshi a kwali. Danginta sunce bazasu taɓa yarda ba ƙara zasu shigar. Nayi
iya yina ma a kashe maganar a gida, wallahi basu yarda ba..............✍
MRS BUKHARI
Sai jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya "NA FAƊO DAGA BENE......
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 14
*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*
*INA Marubuta da masu business*
*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin
farashi me sauki*
Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu
Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776
*All netwk Data is available*
*ASIBITI*
HAJIYAYYE:
Tana kwance a asibitin dake babban masallacin juma'a mai suna MATANMI. ƙarin ruwa ne jone
a hannunta. Gefenta kishiyar mamansu ce a zaune ita ke jinyarta. Tunda Hajiyayye ta dawo
gayyacinta aka sanar mata mutuwar da yaro yayi mata a ciki ta shiga ruɗani. Take ta sake
rikirkicewa amman fa makircine zallah. Dan har fiffisga ta dinga yi, sai da akayi mata alkurar
bacci. Ganin haka ne yasa ƴan uwanta cewar su fa ba zasu yarda ba sam. Dole a ƙwatarma
Hajiyayye ƴancinta kisan ɗan mutum ba wasa ba, kuma su kotu suke son a tura kes ɗin. Dan
har Yaya Ta bizaro mijinta ya kawo lauya yayi ma Hajiyayye tambayoyi domin sanin makamar
aiki da kuma yanda zai tunkari kes ɗin dan ganin yayi nasarar ganin Shanono da Yaya Use a
ƙasa.
Shigowar su Ta Bizaro da kamar awa guda sai ga Kaila shi da ɗanyan gwal Kaila ya kawota ta
duba Hajiyayye. Wani irin material ne mai stone sunfi dubu a jiki ta saka, mai santsin gaske, fari
ne jikin material ɗin da baƙi, takalmi da jakarta, da mayafinta baƙaƙe ta saka masu tsada, harda
ɗankunne da sarka na gwal saudi. Shamwila na biye dasu a baya da basket cike da kayan
abinci da Bilkisa ta sa ta girka ma Hajiyayye. Hajiyayye na ganinsu ta yi saurin kawar da kanta,
tana fatan Allah ya kawo ranar da Bilkisa zata faɗa tarkonta. Ta san ta riga ta gama da
Shanono, babu makawa a halin Kaila data sani bazai iya ci gaba da zama da Shanono ba. A
tunaninta saura Bilkisa itace target ɗinta na biyu, dogon tsaki mai sauti ta ja.
"Sannu Mama yaya mai jikin?" Cewar Bilkisa kenan. Baba Tumba tace.
"Jiki da sauƙi zamu ce dai. Kaila wannan itace Amaryar?" Dariya Kaila yayi harda gyara tsaiwa
yace.
"Itace Tumba Bilkisa kenan. Kin ganta likita ce itama mai zaman kanta, unguwar zoma ce dan
da naso in haihuwar ita Hajiyayyen ya zo ta karɓi haihuwar, amfanin ilimin mace ta yi aiki dashi
a gidanta kafin ta fitar dashi waje dama. A babban asibiti take aiki a Zaria. Yanzu haka ma da ta
gama kwanakin amarci zata ci gaba da aiki a babban asibitin juth na can lamingo." Hajiyayye ta
juyo ta dubi Kaila ta dubi Bilkisa, zuchiyarta kamar zata fashe, harara ta sakar ma Bilkisa Kaila
yace.
"Yaya jikin naki iya rigima?
Bata tanka ba. Bilkisa ta gaishe da su Ta Bizaro, suka amsa babu yabo babu fallasa dai.
Shamwila kuma ta dire basket ɗin abincin a gefe. Agogo Bilkisa ta kalla tace.
"To Gwanda ina ganin mu koma gida ko, mun gaishe da mai jiki ai" Jakarta ta zuge ta ƙirgo
dubu biyar ta ajjiye a gefen fulon da Hajiyayye take kwance.
"Ga wannan ko ayaba a siya ma mai jikin. Hajiyayye Allah ya ƙara sauƙi sai kun dawo gida
kuma" Ficewarta tayi waje ita da Shamwila, Kaila kuma ya tsaya yana tambayar babu matsala
dai ko? Daga ƙarshe yai musu sallama a gurguje ya fice. Da Amadudu da Hindatu suka ci karo
a wani ɗan dogon falo da zai sadaka da da waje. Dan daga bakin ƙofar ana hango titi kai tsaye. "Amadudu kun samu ƙarasowa kenan?" Cewar Kaila, Amadudu ya shagala sosai wajan kallon
shamwila, take ran Kaila ya ɓaci yace.
"Kai me kake kallo haka ne, meye haka wai?" Sai lokacin Amadudu ya dawo nutsuwarshi, ya
ɗanyi tsaki yace.
"Yaya wallahi yaron da Tani ta tawo dashi daga ƙauye baka ji yanda ya ɗume gidan da wari ba.
Yanzu haka mun fito mun tarar yana wanka a tsakar gida, wata ƴar budurwar yarinya na kulawa
da su Sani. A gaskiya bazai yiwu mu zauna da wannan yaro a gida ɗaya ba. Wannan ai sai
wata cutar ta kama mu ko ta kama namu yaran." Duk maganganunnan da Amadudu yake yi,
idanunshi na kan Shamwila, ita kuwa sai ƙasa take yi da fararen idanunta. Ganin haka Kaila ya
miƙa ma Bilkisa keyn motar Isa daya aro yace.
"Ku je mota Ɗanyan gwal ku jirani" Bilkisa tayi gaba ba tare data karɓi keyn motar ba, sai
daddanna wayarta take yi.
"Shamwila karɓo car key ɗin mu je" Tace a gadarance, tare da yin wucewarta tana taku ɗaiɗai.
Hindatu ta taɓe baki ta yi shigewarta cikin ɗakin da Hajiyayye take kwance. Dan ko gaisawa
basa yi da Bilkisa, ba ma wani fitowa tsakar gidan take yi ba sam, in ma ta fito Bilkisa ba
ubanda take kulawa, bata ma nuna ta san da mutane a tsakar gidan. Shamwila tasa hannu ta
amshi key a hannun Kaila. Fatar hannunta da fatar hannunshi suka samu haɗuwa, ɗumi da
laushin fatar Shamwila ya jijjiga tunanin Kaila. Kusan mutuwar tsaye yayi a wajan, tare da bin
bayan Shamwila da idanu. A yau ne yayi mata kallon ƙurulla har ya gano lallai akwai sirri tattare
da'ita. Ita kuwa Shamwila sai kaɗa mazaunanta take yi suna wani irin rawa tamkar an ƙulle ruwa
a leda. Gata gwanar iya tafiya tamkar mage, takunta a harɗe take yi. Ajjiyar zuchiya ce ta kubce
ma Kaila da Amadudu. Harara Kaila ya doka ma Amadudu kafin yace.
"Shanono ai bata da hankali. Ashe ɗanta ne dake ƙauye ta tawo dashi, tunda ta zaci Ni ɗin ɗan
mahaukaciya ne, ko dan ta ga na aureta ina saurayi ita kuma bazawara mai aure huɗu, ko shi
yasa tayi tunanin lusarine ni ohon mata. Zata bar gidan daga ita har yaron ka sha kuruminka.
Yanzu dai bari muje kar in bar su Shamwila suita jirana kaga babu daɗi. Sannan zan yi ma
gargaɗi ka ɗauke idanunka akan Shamwila in kana son kan ka da arziki. Kar ka kuma yi mata
irin wannan mayunwacin kallon" A wajan ya bar Amadudu. Yana shiga mota ya ja fuu suka
koma gida, a lokacin har azahar tayi"
Caji office:
Shanono:
Muna zaune sama da awa uku ni da Yaya Use babu wanda yace da ɗan uwanshi wani abu, sai
tubka da warwara nake yi. Babban damuwata ƙunzugun dake jikina ya jiƙe sharkab da jini,
bansan yaya zanyi in sake wani ba. Ga tunanin Dauda, da sauran yaran, duk da nasan Sabira
zata kula min dasu, amman ba lallai ta iya jure wari da tsutsotsin jikin Dauda ba. Ina cikin taɗin
zuchi wata ƴar duma dumar ƴar doka ta shigo ɗakin da muke.
"Ku taso kuna da baƙi a kanta" Zungui_zungui muka fice tare da ɗaura ƙafafunmu a inda ta
ɗaga. Habiba Bala na hango tare da Sabira a zaune a binci. Tana ganina ta miƙe tsaye tare da
ƙaremun kallo.
"Shanono meya same ki haka, kaddai dukan ki suka yi Shanono?" Murmushin ƙarfin hali nayi
mata nace.
Babu wanda ya dake ni Habiba Bala. Nagode da kika amsa kirana a lokacin da bamu da kowa
sai ke." Ajjiyar zuchiya Habiba Bala ta sauke tace.
"Oficer a fito mun dasu kamar yadda dpo yace. Ni kuma da kaina zan dinga kawo muku ita a
duk sanda ake da buƙatarta" Wanda ta kira officer yace.
"Sa mana hannu a wannan takaddar Hajiya. Kuma duk sanda kotu ta buƙaci ganinsu ba'a same
su ba. Ki sani ke zamu kama. Dan mika kes ɗin za'ayi gaban kotu kamar yadda masu kes ɗin
suka buƙata. Kuɗin beli kuma ko wacce dubu goma_goma, sai dubu biyu kuɗin biro da takarda.
Jaka Habiba Bala ta zuge ta ciro damin kuɗi ta ƙirga ta basu dubu ashirin da biyu kamar yadda
suka buƙata. Ta kuma kaɗa hannunta a kan takaddar. Mayafinmu suka miƙa mana kana suka
bamu hanya muka fito. Sai lokacin naji salama. A motar Habiba Bala muka wuce.
"Habiba Bala ni kam ba zani gidan Tani ba. Dan mijinta yace in na kuma zuwa kotu ce zata raba
mu. In ji da wannan sharrin da Hajiyayye tayi mun ma
Kinga in na kuma taka ƙafata na shigar mishi gida, da laifin maita ƙila za'a kamani, ace na
lashe kurwar Amaryar Tani" Sabira tace.
"Yanzu yaya Use shi Baban Sulaiman ɗinne ya hana ki zuwar mishi gida, bacin ƙanwarki yake
aure?" Yaya Use tace.
"Ke dai bari Sabira ai sha'anin mijin Tani sai adda'a zamu ce. Nima tsautsayine yasa na daki
Hajiyayye da ciki. Amman wallahi da ba ciki a jikinta saina karairayata." Ni dai ina zaune jigum.
Habiba Bala sai girgiza kanta take yi kawai. Nan yaya Use tayi mata kwatancen gidanta muka
ɗauki hanya. A ƙofar gida muka haɗu da Baban yara mijin yaya Use. Da halama fita zai yi
kasuwa. Motar da muke ciki ya ƙurama idanu, bai ƙibta ba har sai da yaga fitowarmu daga
motar. Duk yanda yaso ɓoye farin cikin ganin an sakomu kasa boyuwa yayi, sai ga Murmushi
shinfiɗe a fuskarshi, har yana tararmu.
"Use an sako ku? Kin ganni a tsaye a nan nafi awa uku ina tubka da warwara. Malam zailani
nake jira ma ya fito mu je can caji office ɗin mu dubo ku. Malamai sannunku da zuwa. Tani
dukan ki su ka yi a caji office ɗinne?" Kai kawai na girgiza mishi halamar a'a. Bayan mun
gaggaisa muka shiga cikin gidan muka bar yaya Use a tsaye da mijinta. Muna shiga yara na
ganinmu sai murna suna faɗin.
"Sun dawo, sun dawo, sun dawo" Murmushi nayi musu domin in ƙarfafi murnarsu. Inno ƙarama
na kalla nace.
Inno ɗaura mun ruwan zafi dan Allah. Habiba Bala, Sabira mu shiga daga ciki." Ɗakin Yaya Use
muka shiga, muna zama sai gata ta shigo. A dofane Habiba Bala ta zauna a gefen tarin tulin
tsummokin kayan wanki. Ɗakin da kaɗan yafi nawa fasali. Sai dai baya zarni sam dan yaranta
sun girma, sai dai warin dauɗa, da warin jinin kuɗin cizo. Inno ƙarama ce ta lego bayan ta
gaishemu tace dani.
"Umman Sulaiman na kai miki ruwan ban ɗaki. Yaya Use tace.
"Ki gargasa jikin ki da kyau Tani dan dole ki sha fanado ma. Ni dai to kawai nace. Ban jima ba
na fito, illahirin jikina ciwo yake yi, duk inda na watsa ruwan zafi sai in ji kamar an watsa mun
wuta. Da zafin ya isheni sai na haƙura da wankan na wanke tsumman jinin dake jikina, da ɗan
diras ɗins, na shanya a langa_langar data kewaye bayan gidan. Na ɗaura zani na fito. Ɗakin
kwanan su Inno ƙarama na shiga. Kayanta na saka, ta bani ɗan diras ɗinta da tsumma na yi
sabon ƙunzugu kafin na koma ɗakin Yaya Use, Habiba Bala na kalla itama ni take kallo.
"To Yaya mu kam zamu gudu zan saukesu a gida, ni kuma zan koma Bauchi yau. Amman zan
ɗaukar muku lauya da zai kareku. Dan na fahimci so suke Shanono ta wulaƙanta, in sha Allah
muddin ina da rai Shanono tafi ƙarfin wani yai mata wulaƙanci ko cin zarafi. Ku kwantar da
hankulanku ina tare da ku, ga Sabira da mijinta ma. Dan Sabira ta tsokata mun kaɗan daga
cikin irin zaman da Shanono take yi a gidan kaila" Yaya Use tace.
"Mun gode Habiba Bala, da ace du ƙawaye irinku ne ke da Sabira da kawance yayi daɗi sosai.
Allah ya saka muku da Alkhairinshi" Da "Ameen" Muka amsa dukkanmu. Har bakin mota yaya
Use ta raka mu, sai da taga tashin motarmu kana ta koma ciki. Kai tsaye Habiba Bala naga ta
nufi Nalele pharmacy dake Bauchi road "Bari in shiga in siyo magani, dan kina buƙatar magani da wadataccen bacci." Bata jima a cikin
Nalele ba sai gata da ledar magunguna. Kasuwa ta wuce, nan ma tayo mun siyayya ni da
jaririna, Sabira kuma ina ganinta ta fita . Na dai ganta a teburin mai nama amman bansan
abinda ta siya ba. Daga nan muka wuce gida kai tsaye. Da sallama muka shiga gidan. Zurub
sai ga Hindatu ta leƙo zauren ganina yasa ta riƙe bakinta.
"An sako ku ne Umman Sulaiman?" Murmushi nayi nace.
Allah ya nufa Hindatu" A wajan na barta muka shige ɗakina. Habiba Bala ta toshe hancinta
tace.
"Meye haka shanono, wannan ai iskanci ne. Wannan warin na meye kuma haka, ɗakin yara ne
amman nan?" Tsuru_tsuru nayi, na bisu da kallo, Sabira ma hancinta a toshe yake. Kuka na
fashe musu dashi kamar ƙaramar yarinya. Ganin hakan yasa duk suka saki hancinsu, Habiba
Bala ta kama ni ta zaunar dani. Itama ta zauna a gefena. Da sauri ta miƙe tana duba
mazaunanta, fitsarine sharkab ya jiƙe mata tsadaddiyar rigarta. Sabira tace.
"Habiba Bala. Inaga mu je gidana mu tattauna, amman kafinnan bari in fitar da komai na ɗakin a
samu ɗakin ya sarara."
"A'a Sabira babu damuwa. Mu fitar da kayan tare. Shanono ga kujerar tsugunno ki zauna"
Cewar Habiba Bala. Zama nayi jiki ba kuzari, Sabira ta kunto mun jaririna ta samun shi a
cinyata. Nono na zura mishi a baki, su kuma suka fita da katifu suna yararin ruwan fitsari. Harda
kayayyakin wankinmu dukka Habiba Bala ta janye buhun zuwa tsakar gida. "Ki fito waje Tani ki zauna, a samu a wanke ɗakin."
To Sabira na fa gode." Fitowa nayi na nemi inuwa na zauna. Habiba Bala na ciki tana wanke
mun ɗaki. Sabira kuma tana haɗa gawayi a kurfo, naga ta cika tukunya da naman kan saniya.
Hindatu da jin kaya_kaya sai gata ta ɗakko kujera ta dasa a bakin ƙofarta. Wannan ƴar
kyakkyawar budurwarce ta fito daga turakar Kaila hannunta rike da bokiti mai cike da kayan
wanki. Kayan Bilkisa ta soma shanyawa, su bireziya da ɗan diras, da wasu rigunan baccin da
kallansu suka sani na ji kunya. Yanzu ta yaya mace zata sa irin kayannan ta tsaya a gaban miji?
Kayan Kaila naga tana shanyawa,