Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 24

15K to 18K   out of 70.8K words

son tara mata da kula mata, da
zantuttukan batsa marasa daɗin ji. Ka rasa ina matsalar take laifin mazan ne, ko laifin ƴan
matan ne, ko kuwa laifin matan cikin gidane, a'a ko kuwa laifi na iyayene?"
"Shanono....." Wannan tunani haka lafiya meke damunki ne haka?" Cewar Habiba Bala kenan.
Har motar ta tsaya ashe ni ban sani ba ina can duniyar tunani.
"Ki yi iya ƙoƙarinki wajan ganin ɗa namiji bai sa zuchiyarki tayi bindiga ba, yaranki ne zasu yi
maraici shi kuwa bashi da asara." Idanu na zuba mata ƙur ban da zarafin iya furta komai. Fitowa
nayi ina ƙarema haɗaɗɗen gidan kallo. Muna baya tana jagorantarmu har zuwa cikin
matsakaicin falo mai kyau mara shirgi da hayaniya. Setin kujerune dak blue a falon irin ƴan
ƙanana na zamani. Sai tv na bango dake ajjiye akan t v sitan, sai kafet na tsakar ɗaki wanda ya
dace da kujerun, haka ma labulen falon ya dace da kujerun. Sai wani guntun firji a gefe da
disfensa ta shan ruwan sanyi ko tea iyakar abunda ke cikin falon kenan ya fito yayi ƙwasƙwas
sai sheƙi tayil ɗin falon yake yi. Zama nayi a kujera ina kallon Habiba Bala da maɗaukakin farin
ciki yalwacce akan fuskata .......✍
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU. 5





Cikin fara'a nace
Masha Allah rayuwa tayi albarka Habiba Bala. Irin wannan daula da kike ciki haka. Ah abun yayi
kyau" Murmushi ta sakar mun kawai ta nemi ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna. Muma
zama mu ka yi. Halima Bawa tace.
"Ni banji motsin kowa ba a gidan, kaddai baki samu rabo bane Habiba Bala?" Wani murmushi
tayi mana irin na manyan mata kana tace.
"Na samu rabo yarana uku dukka maza" Tare muka haɗe baki wajan cewa.
Masha Allah." Halima Bawa tace.
"Ismaliyya suka tafi ne, ko gidan kakanninsu nasan dai ana hutun Sallah?"
"Halima Bawa kina nan a ƴar bin diddiginnan dana sani, aikin jarida zai fi dacewa dake. To
yara suna Jigawa gidan Babansu. Bani da Aure a halin yanzu. Ni kaɗai nake zama a gidannan
sai Iya mai taya ni gyaran gida da jire mun gidan, ni kuma ina zuwa asibiti kamar yadda na faɗa
muku a cikin taro" Jijjukannanmu gabaki ɗaya sai yayi sanyi laƙwas. Wato wannan
mace_macen auren ya karaɗe Arewa sosai? Ada ƙabilar Hausa an san mazansu da riƙon Aure
da haƙuri. Kamar yadda matan suke da kunya, kawaici, gami da yakana. Ni dai na rasa gane a

inda matsalar take. Furucin Halima Bawa ne ya dawo dani daga zancen zuchin da ya jima da
aurena.
"Hmm mazan ƙabilar Hausa na wannan ƙarnin sun maida saki tamkar ya da ledar fiya wata.
Nakan yi mamaki da tunanin mai ya taɓa malam bahaushe ne haka, wannan aure da sakin yayi
yawa, yawan zawarawa a ko da yaushe sake hauhawa yake yi a ƙasar Hausa, hakan yasa
zinace_zinace yai yawa, duk da zina yanzu ta zama ruwan dare game duniya. Su kuma
al'ummar Hausawa basa yi ma bazawara kallon tausayi, sai kallon maras tarbiyya, maras
haƙuri. A cikin gidanku ma sai mahaifanka su kasa yi ma uziri, ai ta hantararka, in Aure ya mutu
to fa macen itace mai lafi. Da tayi aure ɗaya biyu sai a sa mata suna, wata ma taƙi auruwa.
Amman shi Namiji a kan dukkan abinda yake a kai ƙarfafa mishi guiwa jinsinshi suke, in aure
goma zai yi, ij yaje nema za'a wanke a bashi. Haka Namiji da mace zasu aikata zina, ita macen
ya zame mata masifa, taƙi auruwa aita goranta mata. Shi kuwa namiji sai ace mishi duk abinda
yayi adone. Zina ashe zata iya zamewa ado? Wa'iyazubillah. Nima na ɗanɗani wannan rayuwar,
sai da na shekara takwas ina zawarci. Duk wanda yazo wajena da iskanci yake zuwar mun. Ko
ku ga da girmana yara ƙanana masu soyayyar shan minti suna zuwa. Wannan dalilin yasa na yi
fatali da surutun iyaye da dangi, sai na koma makaranta na yi karatun jami'a, ban yi aure ba sai
da na dafi aikina mai kyau a hannunna. Ko yau aka sake koroka a ƙalla ba zaka tagaiyara ba,
kana da abun yi, ba zaka bada jikinka dan ka biya buƙatar kan ka na yau da kullum ba"
Idanuwanta take suka ciko da ruwan hawayen tuno da wasu ƙunci da suka shuɗe mata a baya.
Ni kuma leɓe nake cijewa kawai, irin azabar da rijalu suka ɗanɗana ma ruhina bana wasa bane.
Hmmm Allah ya kyauta" Shine abun da na iya cewa, amman tabbas Halima Bawa ta taɓo inda
yake mana ƙaiƙayi ainun.
"Halima Bawa kenan. Ke aure ɗaya ma kika yi kika fito a ɗan labarin da kika bamu. Kin ganni
mazaje uku na aura amman zaman yana ƙin yiwuwa. Ku dai mu shiga daga ciki ku ɗan watsa
ruwa ku huta. In muka nutsa zan dan baku a taƙaice, amman naci wuya. Jagora tayi mana i
zuwa cikin ɗakinta wanda ya kasance haɗaɗɗe. Ga takalma a jajjere sunfi sawu talatin,
jakunkuna suma gasu nan kaya guda a rarrataye a abun rataye jaka. Ɗakin sai wani irin
ni'imtaccen turaren wuta ke tashi wanda ban taɓa jin ƙamshi turare mai sanyi irin wannan ba. (
In kina son ɗakin ki ke ma ya dinga ƙamshin gidan sarakai ki neme ni, zaki samu dukkannin
nau'ikan turaruka masu sanyin daɗi 08179523215) A 3sitter dake uwar ɗakin na zauna. Hauwa
na sinto a baya na na shinfiɗeta a gefe baccinta take ta shantakawa. Halima Bawa kuma
mayafinta ta yaye ta yi zamanta akan gadon Habiba Bala wanda yasha shinfiɗa lallausa."
"Ga bayan gida nan akwai ruwan zafi a ciki. Ku yi wanka, sai ku yi Sallah. Bari in samu Iya a
kitchin inga mai take dafawa yau ina da manyan baƙi" A haka ta fita ta barmu hatta Halima
Bawa kallon sha'awa take yi mata ballantana kuma ni tukururu. Wanka mu ka yi dukkanmu tare
da ɗauro alwala. Kayan jikina ni dai na mayar na yafa mayafina ina tunanin to ina ne gabas ina
son gabatar da sallar la'asar wacce aka jima da yin ta. Dan yanzu ƙarfe biyar ma ta gota,
amman har yanzu lokacin sallar bai wuce ba. Ina cikin wannan tunanin Habiba Bala ta shigo da
ƙaton tire shaƙe da kayan abinci.
Nuna mana gabas mu yi sallah Habiba Bala." Gabas ta nuna mun, da mamaki ta dube ni tace.
"Wai da ki ka yi wankan kayan jikin ki kika mayar Shanono, har yanzu kina nan da halinki na
adankiya ko? Wannan fa ƙazantace, kin sako kaya tun daga gida, kin ciyo uwar tafiya yanzu
kinyi wanka kin sake mayarwa jikin ki, to meye ma amfanin wankan naki in banda abinki, baki

zo da wasu kaya masu sauƙi bane na shan iska haka?"
Gaskiya banzo da kayan shan iska ba." Dariya tayi tace.
"To yi sallar bari in kawo miki ƴar doguwar riga ta shan iska ko kema kya ji dama_dama.
Bauchi ana zafi ba kamar Jos bane da zaki ji sanyi kamar a masko." Dariya mu ka yi dukka.
Bayan mun idar da Sallah, muna zaune, Halima Bawa tana saye da ƴar doguwar riga ta shan
iska mai kyau. Habiba Bala ta shigo rike da riga ta miƙo mun. Na saka rigarnan ɗas dani
gwanin sha'awa ga cikina ya sake fitowa sosai a kayan. Soyayyar shinkafa da pepper chicken
Habiba Bala tasa ayi mana shinkafar taji kayan lambu da yankakkun hanta ƙananu, ga masar
Bauchi da ƙuli_ƙuli shima, sai lemon kwali na tatacciyar abarba mai shegen sanyi. Ni dai sai
cika bakina nake yi. Har ga Allah tunda nake ban taɓa cin shinkafa mai daɗin wannan ba.
Lemon tatacciyar abarba na kora dashi. Habiba Bala tace.
""Shanono watan yarinyarki nawa ne, naga cikin naki tsoho shima ga yarinya ƙarama?" Sai da
na haɗiye naman kazan dana yaga nace.
Watan ta dai to tara zance kawai duk da bata ƙarashe ba shi kuma cikin wata takwas zance.
Dan Allah a matsayinki na likitar mata wacce hanya zanbi dan ganin na kauce ma samuwar ciki
ina shayarwa? Ke ni yaran ma sun isheni haka inason in huta ma rayuwata, Kaila sabon Aure
ma zai kuma zai sake samun sababbin ƴaƴa ƴan gaban goshi, tunda iyayen nasu suma ƴan
gaban goshin ne" Tataccen ruwan abarba ta kora kafin tace.
"Akwai hanyoyi da dama da mace zata yi tsarin iyali, domun jikin mace yana da buƙatar hutu
da hakanne komaɗar mace zai dawo. Amman ta yaya ma zaki zama ƴar gaban goshi a wajan
miji. Kullum cikin ciki da goyo, yau ƙarnin jinin biki, gobe ƙarnin nono haba. Akwai allura ta tsarin
iyali, akwai wanda ake sawa, sannan akwai ƙwayoyin da ake haɗiya, duk in ba wannan ba
akwai hanyar da zaki iya yin tsarin iyali ta hanyar ƙirgen kwanaki, ina nufin kwanakin sakkowar
ƙwai, in muka ƙirga kwanakin al'adarki zan ɗauraki a kan hanya in wannan ɗin kike so. Kinsan
mutane da dama na gudun matsalolin da tsarin iyali suke haifarwa ga lafiya. Amman yana da
kyau tsarin iyali musamman a wannan ƙarnin da muke ciki na yawan mace_macen aure, da
kuma yanda a wannan zamanin mazanmu na Hausawa basu cika tsaiwa akan ƴaƴa ba, hakan
shi ya jefa Arewa a cikin musibu iri daban_daban." Gaskiya ne dukkan maganganun Habiba
Bala, a raina naji na gamsu zan yi tsarin iyali ko dan nima jinin jikina ya dawo, so nake in daure
in zama ƴar kallo a tsakankanin Kaila da abokan zamana. Duk da dama ƴar kallon ce. Hakan
zai yiwu ne in na dakatar da haihuwa zuwa wani lokacin, suma su miƙe ƙafa suita zubo yaran,
wala Allah su ya kula dasu da kyau, ni kuma in ci gaba da kulawa da nawa yaran." Halima
Bawa tace.
"Wallahi hakane maganarki Dr Habiba Bala. Ni kaina daga wannan haihuwar dai in sha Allah
ni na dena haihuwar baki ɗaya ma, wallahi da da hali ma mahaifar zan juya, wadanda na samu
ma Allah ya raya mana su da imani. Yanzu mazan mu basa iya sauke ratayayyen hakkunan
iyalansu daya rataya a wuyansu, mafi yawancinsu duk haka mazan suke, ɗaiɗaikune na kirki.
Babban abinda yake bani tsoro shine ba ga gidan mai sani ba, ba ga gidan jahili ba, mata kuka
suke ta ko ta ina kawai. Allah dai ya iyar mana kawai." Habiba Bala tace.
"Ni zan faɗa miki wannan Halima Bawa. Kun ganni aurena na fari malami na aura, wanda yake
da sani sosai ta ɓangaren addini. Ni abinda ya fara jan hankalina a game dashi ma kenan.
Sabida a tsari da zubinshi bai yi mun ba har ga Allah. Tunanin samun kwanciyar hankali, da
kwaɗayin gurje soyayya yasa na shiga wannan gidan, dan kunsan ance ustazai akwaisu akwai

iya soyayya da kwantar da hankalin mace" Dariya muka kwashe dashi ni ko har da
tuntsurawata. Sai da mu ka yi mai isarmu sannan ta ɗaura da cewa.
"Amman dana shiga gidan nashi abun mamaki ashe ni nawa kallon kitse naima rogo (na
ɗauka irin dacen da Mrs Bukhari tayi nima irinshi nayi. Dan nata ustaz ɗin sune mayun soyayya
da tsantsar sanin darajar mace irin na ustazan asali) Wata na farko dana biyu duk lafiya. Daga
wata na uku muka soma samun saɓani. In kwananane sai yayi ƙundumbala ya faɗa ɗakin uwar
gidana, ni kuma babu haƙuri dan wannan ai rainin hankaline tsantsa, kuma duk macen da
akaima haka tabbas sai ta zargi kanta da cewar ANYA NI CIKAKKIYAR MACACE KUWA? In
na shiga na same shi yana cin abinci a ɗakin uwar gidanshi, da nayi mishi magana cewar
kwanan nawa ne fa, sai yace ya sha'afa amman in yi haƙuri tunda yaci abincinta gobe ya shigo
ɗakina. Daga haka matsala ta soma tun yana shigowa ɗakina wallahi har ta kai ta kawo ko iya
ɗaga ido ya kalleni bayayi. Da nayi magana sai zagi da hantara, har ya dinga ce mun shi
aurena bai amfaneshi da komai ba tunda ni ba haihuwa nake yi ba. Bazai dinga asarar ruwan
jikinshi ta hanyar yin mu'amular Aure dani ba, ina mai asarar ruwa a banza yana bin rariya. Sai
da na shekara biyu cib a gidanshi baya ko ɗaga labulen ɗakina. Abinci sai Babanmu ke aiko su
Mansura su kawo mini. Dana je gida, sai su dawo dani raɓe_raɓe tare da faɗar wannan kalmar
ta gadon mata (ko wacce mace zaman haƙuri take yi a gidanta. Amman duk macen da kika
ganta a gidan mijinta akwai wani abun da mijinta yake yi mata wanda bata so) haka za'a tusoni
gaba in dawo. Daga ƙarshe dai yai mun sakin tozarci. Yaronshi ɗan shekara uku ya aiko mun da
takaddar sakina saki uku. Sai na dawo gida. Nan ƴan uwa da dangi suka dira a kaina. Biki ko
suna sai da suka gagareni shiga. Mahaifiyata kuwa wallahi kamar sauyamun ita akayi, wani irin
tsanata tayi, ko gaisuwata bata amsawa. Shekara guda nayi a gida sai na samu bazawari.
Sakamakon tsangwama da son barin gaban iyayena yasa na auri wannan miji daya nuna yana
sona. Dan ko bincike ba'aiba aka wankeni aka kaini gidan miji. Ashe madokine shi kuma. Ga
matanshi tamkar karnuka kullum cikin haushi suke. Daya zo sai ya haɗa mu yaita labta tamkar
Allah ne ya aiko shi. Ba dama kuyi magana ta arziki. To watan aurennan biyar ya mutu mus.
Hmmmm" Hawaye ne ya gangaro a kumatun Habiba Bala, ni kuma nayi jigum ina saurarenta
dan ko kwatan kwatan azabar da nasha a hannu maza bata ci ba sam, ni bana ma ƙaunar tuno
da baya, banga abinda zai sa in zauna ba da labarin aurarrakin da nayi a baya ba. Na tabbatar
labarin zai karya zukatan al'umma da dama, mata zasu zubar mun da hawaye sosai, maza da
suke tunanin matsalar a mata ne, zasu sama ma mata lafiya. Habiba Bala ta share hawayenta
taci gaba"
"Dana koma gida, na miƙa ma mahaifiyata takaddar sakina. Sai ta fashe da kuka, ni kaina
kukan nake yi, shikenan na dawo gidan jiya. Ni ba mutuwar auren bane yafi ɗaga mun hankali
ba, a'a irin zaman da zanyi da mahaifiyata da ƙannena shi nake tunani, dan hatta maƙota in
suka shigo gidanmu sai sun yada mun habaici kafin su fita. Mahaifina a ranar ko runtsawa ya
kasa yi, ni dai haka naci gaba da rayuwa a cikin gidanmu. Rana tsaka mahaifiyata take sanar
dani mahaifina ya janye duk wani taimako da yake mun. Dangin su sabulu, man shafa, abinci,
suttura. A ranar nayi kuka ainun, amman ya zanyi, sai na nemi mai gidan wani abinci ina mata
wanke_wanke tana biyana ɗari biyu da abinci dafaffe. Da ɗari biyunnan zan sai sabulun wanki,
dashi nake wanka, da ɗan man kaɗanya ko man alaiyadi su nake shafawa. Ina cikin wannan
halin kwatsam wan mahaifina yazo daga ƙauye can Jigawa. Anan ya samu labarin mutuwar
aurena na biyu. Ni dai bansan yanda suka ƙareba, bayan kwana biyu da tafiyarshi, sai ga

Asabahu ɗanshi wai an turoshi ne ya ganni, in nayi mishi sai mu sasanta, in ban yi mishi ba to"
hmmm Asabahu yace banyi mishi ba, wallahi mahaifiyata ta zaunar dashi ta dinga cewa ya rufa
mata asiri, dangi sun sata a gaba ita kaza_ita kaza. Da haka ta jawo hankalin Asabahu ya
amince da aurena. Ni ina gefe kamar yajin ƙosai, bani da bakin furta komai. Haka aka sa rana,
aka kawo kayan aure a cikin baƙar leda viva. Ranar wata asabar aka ɗaura aure. Babanmu da
kanshi ya kaini har wannan ƙauye. Dama nasan ƙauyen ni ba baƙuwa bace a ƙauyan. Nayi
kuka sosai ganin yanda mahaifana suke neman kai dani. Ina cikin maraya haifaffiyar maraya
sabida kawai ba sa son a zagesu ace sun kasa bani tarbiyyar da zanyi zaman Aure, shine suka
kawoni ƙauye suka juye. Iya wuya naci wuya nice daka, nice zuwa gona, nice_nice_nice dai, ga
ƙauye da gori wannan tambarin aure biyu fa yana nan anata yaɓa mini magana. Ni dai nasa
audiga na toshe kunnena. Ta ɓangaren Asabahu babu daɗi, ta ɓangaren abokan zamana kuwa
lafiya muke zaune dasu sosai. Shi kuwa babu dama yayi ba dai_dai ba in yi magana sai yace
shifa dole akayi mishi alfarma yayi mun. Haka naita wannan zama na alfarma harna haihu.
Sannan iyayena suka sake dani a bisa doron fishi da suke yi dani. Akayi suna ƴan uwa da suka
zo daga Bauchi suka koma. Ni kuma naci gaba da shayar da Sani. Watan sani huɗu na samu
wani cikin. Laulayi da raino ya haɗe mun. Hmm karfa ku mance a lokacin ni har ma nafi ƴan
ƙauyannan munin kama wallahi, sabida rayuwar babu daɗi. Wata tara na haifi Auwal. Daga nan
kishiyoyi suka sani gaba, wai na haifi maza biyu, nazo ina baƙuwa inason kwace dukiyar
Asabahu. Hmm gashi shi kuma ya ɗauki son duniya ya ɗaurama Sani da Auwalu. Ni dai dama
bani da wata daraja a wajanshi, bani kaɗaiba irin dai wannan ɗab'ar ta da yawan maza ta raina
ƴaƴa mata, gani suke amfaninmu shine su huta damu suyi mana ciki, mu renan musu ƴaƴa.
Daga lokacin da abokan zamana suka sauya mun, sai matsatsin gidan ya takureni, dan su suke
debe mun kewa, mu yi daka tare, mu je roro tare. Sani da da shekara biyar na sake haihuwar
ɗa Namiji ranar suna yaci sunan mahaifina Tasi'u ( Bala) Aifa nan komai ya caɓe mun. Ai mun ai
ma yarana, yara babu damar su fita tsakar gida dan bala'i fa. Shi kanshi Asabahun bashi da aiki
sai zaginsu da dukansu, da hantara kuma duk wannan son su da yake ya dena. Kullum a cikin
kuka da lallaminsu nake.

6 / 24