Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
rataye jakata.
To maza ku yi ku gama mana. Ku je gidan su Mustapha ku yi wasanku, in lokacin islamiyya yayi
sai ku je tare. Sani banda zuwa wanka rafi, dan Mustapha ya faɗa mun kana bin yaran gidan
Rahilu. Ni zan je makaranta ku yi mun adda'ar samun nasara." Adda'a su kai ta mun. Raina fes
na fito zauren, dai_dai Hajiyayye ta rako ƴan uwanta zaure. Turus Hajiyayye tayi kawai tana
kallona. Ni ko da ganinsu gabana ya yanke ya faɗi. Dan banso nayo arba da kowa ba. Da sauri
na ɗauke kaina, ina rufe ɗakina na jefa ɗan mabuɗin a jakata na fice. Yara su ka bi bayana. Da
sallama mu ka shigarma Sabira. Tana ganina ta soma tafa hannaye.
"Ga ƴar makaranta, ga ƴar makaranta" Dani da yara duka muka tuntsire da dariya.
Sabira baki da dama. Ga yarannan. Sabida in na barsu a gida ba lallai suje islamiyyar ba."
Sabira tace.
"Yau bana nan na fita, sai da na dawo Abban Mustapha yake faɗa mun irin dukan da Abban
Sulaiman yayi ma Sani. Gashi idanunshi sun tara jini." Na ƙwafe wannan dukan sosai a raina.
Sosai nake jin zafin dukan, har bana so ayi zancan. Bagarar da hirar nayi ta hanyar juyawa da
gudu_gudu. Sai a zaure mu kai sallama na kama hanyar makaranta. Aji ya cika bundin, ni dai
bancin ƙarshen aji na samu, mu biyu ne a bincin ni da wata dattijuwa. Mata sai hira suke yi ana
tafi. Malami bai shigo ajin ba, shewa kawai kike ji yana tashi. Ni kuma sai kallonsu nake yi, ina
mamakin wai yau nice a zaune a aji a karo na biyu. Bayan haihuwa ta takwas, Allah mai iko,
Allah ya bani nasarar karatu. Ina cikin tunanin nan sai naji ajin ya yi tsit, ashe malamine ya
shigo.
"Sababbin zuwan mu su je ajin ƴan B su mayar da form dinsu da fasfo, za'a rubuta sunansu a
rijista. Ni dai na taso amman sai harɗewa nake yi. Duk inda na walga kallona mata suke yi
kamar wata baƙuwar halitta. Har na fita na jiyo Muryar wata mata na faɗin.
"Baiwar Allah kuɗin cizo suna bin hijabinki ta baya" Da sauri na waiga bayan nawa ai kuwa na
gansu har uku, yatsana manuniya nasa a baki na dangwalo yawu na kamo kuɗaɗen cizonnan
na kashesu a ƙasa. Kab ajin ni suke kallo. Ni kuma ina ɗagowa nabi ayarin mata biyun da suka
nufi B likas dan mayar da fom. Muka mayar da fom sunanmu ya shiga rijista. Da darasin lissafi
muka soma ( maths) Nan dai na shiga rubutu hannuna na kakkarwa, har wani zufa hannuna ke
yi dan tsoro. Abubbuwan dai gasu nan ga kamarsu gani nake tamkar ban taɓa shiga aji ba. Ko
malamin turanci daya shigo ni dai ina zaune dunkum kawai. Gashi sai aikin gida suke bamu (
home work) Ni dai kwafewa kawai nake yi, wasu abun dai nakan haɗa in furta kamar mai koyon
magana. Ana cikin yin darasin gona, agiric Salis ya soma kuka.
"Wacece ɗanta yake kuka? Ta fita waje in ma ta shayar dashi, ko ta rarrasheshi. Ya kamata ku
dinga zuwa da mataimaka da zasu dinga kula muku da yaranku, iyakarku dasu ku fita ku basu
Mama ko ruwa" Da sauri na fita, dama fitsari nake ji. Sai da na nemi ban ɗakin makaranta, ashe
basu da banɗaki sai na malamai, ɗalibai sai dai su shiga maƙota. Nima maƙotan na shiga na
soma yo fitsarin. Ina dawowa makaranta ana buga ƙararrawar yin hutu. Gefe na samu na yaye
hijabina na dumbulama Salis nono. Yayi maza ya cabka ya shigo tsotso yana sauke ajjiyar
zuchiya. hutun minti talatin muka yi. Ina gani mata sai siyayyar ƙwalam suke yi, ni kam inaa. Aji
muka koma muka ci gaba da ɗaukar darasi, wallahi ji nayi bana iya fahimta, ƙwaƙwalwata ta
toshe sosai. Har ƙwalla sai da na tsiyayar dana tuno ƙoƙarina wajan karatu da naci. Duk abinda
ya gagari su Habiba Bala da su Halima Bawa, ni ake kawo ma, har mayya suke ce mun. Dan
ina da ƙwaƙwa ko darasi akayi mana komawa ɗaki nake in ta bitar karatunnan, ko kuma in
shiga ɗakin karatu na cikin makatanta wanda aka tanada domin ɗaliba, ni dai ku barni da
ƙazanta kawai. Kuma ni ban ɗauka abinda nake yi ƙazanta bane, dan a haka na taso na tarar
da mahaifana, da yayyena. Amman yau gani a aji bana ko gane komai. Dattijuwar dake gefena
ta taɓoni.
"Baiwar Allah an tashi fa, bani wuri in wuce" jakata na raruma na matsa mata, nan na shiga
kiciniyar goyon Salis, wannan dattijuwar ta dubeni tace.
"Wannan goyon ai ɗanyene, kuma zai barki kina fahimtar karatun kuwa?" Ɗan murmushi nayi
nace.
To zan jaraba dai, amman ban fahimci duk abinda akayi ba ma yau. Ƙila sabida na daɗe rabona
da shiga aji "
"To ki dinga tawowa da wacce zata dinga miki renon yaron. Ke kuma sai ki nutsa kiyi karatun
dan yana da matuƙar mahimmanci sosai. Kuma nan ai makaranta ce duk wanda kika gani koyo
yazo yi. Duk abinda ya shige miki ki yi tambaya ko malami ko ɗaliban ilimi. Sai gobe ko?"
Godiya nayi mata, muka fita a tare kowa ya kama gabanshi. Inata ta tafe, kwasham_kwasham
bani na samu abun hawa ba har sai da na nazo kan babban titin zangon baƙi tukunna, Minti
goma ne ya kawo ni bakin layinmu.
Da shigata gidan nayi maza na buɗe ƙofata na ƙule bana son kowa ma ya ganni. Kayan
makarantar na tuɓe na mayar da kayan gida. Salis yana kwance yana baccinshi rai ɗaya. Da
Bilkisa naci karo tana riƙe da ƙatuwar leda.
"Umman Sulaiman kin dawo ashe? Nazo har sau biyu baki nan" Yangar maganar Bilkisa
burgeni yake yi, harma nake jin kamar tafi kowa iya sarrafa harshe. Duk da naji Habiba Bala ma
haka take karya murya.
Na dawo yanzu" Na bata amsa. Kaila ne ya nufo mu sai ƙamshi yake yi, cikin ado da kwalliya
yake. Yana ganinmu tare ya dubeta yace.
"Wai me yake kawo ki wajan Shanono ne Ɗanyan gwal? Ni sai in ga kina shige mata da yawa
ai" Da zafin harshe ya fesar da kalamin. Wani mugun kallo ta watso mishi tare da ƙare mai
kallon sama da ƙasa.
"Kar ka sake ka sake ɗaga mun murya. Ko mun yi da kai duk abinda zan yi sai ka sani ne? Ni fa
ko a gida banga uban da ya isa ya takura mun ba." Baki ya sake yana kallon Bilkisa data mugun
haɗe ranta, kallona tayi tace.
"Kaya ne dama na fitar suna nayi miki ke da Dady na. Mummy ma tace in miki Barka ranar suna
ƙanwata zata zo suna. Allah ya raya Dady." Da dariya na karɓi ledar.
Kai amman na gode sosai Bilkisa amman babu ma suna kar ki wahalar da me zuwa."
"Amman me yasa ba suna?" Ta jefo mun tambayar amman idanunta na kan Kaila wanda ya
ƙula ainun. Murmushi nayi nace.
Babu kawai dai, haihuwa bata fari ba, taron bikin suna ai sai ku" Baki ta taɓe ta yi wucewarta.
Tana shiga cikin gida nima na faɗa ɗakina. Kaila ya bita fuuu zuwa turakarshi.
KAILA:
Tsabar jaraba har baya iya gani. A hargitse ya shiga ɗakin ya tarar da Bilkisa a tsaye ta riƙe
ƙugu.
"Ke Bilkisa yanzu dai_ dai kenan a gaban shanono ki dinga nuna ban isa dake ba? Ni fa duk na
soma gajiya da lamarin zaman aurennan wallahi. Mu kenan bama kwana biyu cikin jin daɗi.
Jiya ina ji ina gani kika hanani kanki a shinfiɗa............... Dakatar dashi tayi da cewa.
"Dakata mun, ni ba'a mun faɗa, kuma na gaji da aurenka tafiyata zanyi gidanmu, na gama
aurenka kenan. Bansan dama kai ba adali bane a gidanka ba da bazan shigo ba ma" Hanyar
fita ta shiga nema. Carab Kaila ya riƙeta ƙam. Shine harda tsugunnawa yana roƙonta tayi
haƙuri, da ƙyar ta haƙura, da taga kaila na shirin zubar da hawaye. Amman sai ta shiga fishi
dashi. Kiran sallar magriba ne yasa ya fice daga ɗakin jiki a mace.
SHANONO.
Ina tsakar gida ina jiran ruwan tuwo ya tafasa in zuba talge. Littafin lissafi ne a hannuna ina
duba shafin da akayi mana, ina bin misalan ciki a hankali a hankali. Haya_hayar yara ce tasa na
rufe littafin na kallesu.
Yaya akayi yinwa ko Sulaiman?"
"Lefi yayi ma malam shine ya zane shi" Cewar Amina uwar kanzagi kenan. Shi Sulaiman ashe a
wuya yake, sai yasa hannu ya shararama Amina mari. Tas naji sauran hannun kaila a fuskar
Sulaiman. Yaron ya fashe da kuka ya durƙusa. Tsaki Kaila yayi tare da bin mu da kallo yana
muzurai. "Kizo shanono mu yi magana" Jin yace haka sai Hajiyayye ta ɓata rai daga dariyar data gama yi
ina ganinta. Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ilai kuwa ina zuwa na same shi a tsaye
kamar soja.
"Bani kayan da Bilkisa ta baki maza" Suna kan katifa dama. Ɗakkowa nayi na bashi abinsu.
"To daga yau sai yau in kika sake tsaiwar minti uku da Bilkisa ranki zai ɓaci. Wallahi Shanono ki
fita sabgarta in kina son aurenki ya tsira" Yana kaiwa nan ya fita. Kaila na lura barazanarshi
gareni bata wuce ta saki. Domin yasan babu abinda na ƙi jini irin saki. Kuma yasan wahalhalun
da na shiga sanadiyyar mutuwar aure. Wannan dalilin ya riƙa yake tsorata duniyata da kalmar
saki. Sabida ya lura zaman auren nake so, burina in zauna da daɗi babu daɗi. Kai na girgiza
kawai, na fita nayi talge abuna, na ci gaba da duba littafina.
"Ni da su Gwamma, oh ni Hajiyayye in da ranka ka sha kallo, an koma makarantar balagaggu,
dan miji ya auro kishiya likita." Ni dai hankalina yana kan littafina domin na soma fahimtar yadda
abun yake, saura ƙiris in gano bakin zaren. Amman in na kwashe tuwo zan leƙa Sabira ta ɗan
ƙara ɗaurani bisa layi. Kafin isha na game tuwo na baje ma yara a faranti, nima na zuba nawa.
Sai da naci na yi ƙat, na goge miyar a kaina tas na mayar da ɗankwalina. Sai na miƙe na goya
Salis.
Yaya ka kula dasu zan je in dubo Sabira. Haka dai kiki_kiki Sabira ta koya mun abinda ya samu,
sai taran dare na baro gidan. Duk aikin gida da aka bamu a makaranta sai da mu ka yi tukunna.
Ko da na shigo gida yara sun jima da Bacci. Amina harta tsula fitsari tana cikinshi. Salis na
sauke a baya a daddafe nima na haye katifar nan nayi kwanciyata. Gaga_gaga dai anata rayuwa a haka, kullum da sabon tashin hankalin da kaila zai sani a ciki,
bayan kwana biyu da kawo sammaci. Habiba Bala tazo mana da lauya. A gidan yaya Use mu
ka haɗu, acan muka tattauna, yai mana tambaoyi cikin ƙwarewar aiki. Iyakar abinda muka sani
muka sanar mishi. Shi kuma ya ɗaura mu a kan matsaya ɗaya. Habiba Bala bata daɗe ba ta
koma, sabida Dauda. Ranar dana kwana bakwai da haihuwa da safe ina ɗaki yara duk sun tafi
makaranta. Nima aikin gida da malamar Physics ta bamu nake yi, da kuma aikin gida da aka
bamu a islamiyya, Baƙaƙen larabci zamu rubuta daga farko zuwa ƙarshe, inata fama na barbaje
sai cin rubutu nake yi. Makaranta da daɗi sosai, naji daɗin makarantar islamiyya dana je sosai,
gashi muna da yawa ainun, akwai ƴan mata da matan aure, harma da zawarawa. Ga manyan
mata ƴan gayu sosai a ajinmu, ko wacce tas da'ita. A bencinmu mu uku ne, dukkanmu muna da
goyon yara ƙanana, kuma naci sa'a suma sababbin zuwanne, sai kowa ya sake da kowa dai.
Kaila ya ɗago labule ba ko sallama yace.
"Ki shirya kaya nan da awa biyu motar ɗiban kaya zata iso. Za'a kwashi kayanku zuwa sabon
gida" Kafin in yi magana ya saki labule ya ficewarshi. Ina jiyo dirin lifan ɗinshi." Ba shiri na haɗe
littattafan sai gidan Sabira. A falo na sameta tana turarashi da kayan ƙamshi daga Mrs Bukhari.
Ko ina tsab sai ƙamshin daɗi. Ka ga mata ƴan lelen miji. Wallahi kya yi Sabira Abban Mustapha yana yabawa kuma yana ba
da gudunmawa" Zama nayi a kujerarta, ita kuma ta ajjiye kaskon tace.
"Yaya karatun, yanzu na kira Habiba Bala na ji jikin Dauda, mun gama wayar kenan na soma
turara gidan sai ga ki"
Hmmm yau zamu tashi Sabira. Yanzu ya leƙo ɗakina yake sanar mini. Wai nan da awa ɗaya
motar ɗiban kaya zata iso." Waya kawai naga Sabira ta zara, ta yi danne dannenta ta kara a
kunne. Jim kaɗan ta soma magana.
"Hello Ahmad kana ina yanzu haka? Kaya nake son ka ɗaukar mun daga gida zuwa masallacin
ƴan dankali. Wajan masu sai da kaya na hanu.? " Daga wayar ina jiyo Ahmad na cewa.
"To Anty motar ma tana ƙofar gidanki, in shigo in ɗebi kayanne?" Da jin haka Sabira ta miƙe
tsaye.
"Mu je Tani maza bamu da lokaci sosai." Fita mu ka yi, Ahmad ya taimaka mana muka saka
katifunnan a mota. Yayi gaba dasu, mu kuma mu ka bi bayanshi a Napep. Da waɗannan katifun
guda biyu Sabira ta amsar mun gado 6 by 6. Sai mu ka sai katifu guda biyu a cikin kuɗin da
Habiba Bala ta bani. Sabira ta siyamun kafet na hannu mai kyau ja da kuɗinta. Cikin awa guda
muka gama siyan komai Ahmad ya dawo damu. Motar mu na tsaiwa motar ɗiban Kaya itama ta
tsaya. Kaila ne a gaba a lifan ɗinshi. Kamar bai ganmu ba haka yayi.
"Ahmad ga motar nan, ka zuba kayan a ciki. In ka zuba ka shiga ɗakin su Mustapha zaka ga
doguwar kujera ka fito da'ita ka haɗa mata." Godiya naso yi, amman Sabira ta doka mun harara
ta ja hannuna zuwa ciki. A lokacin me motar kaya da Kaila, da Amadudu sun soma fitar da kaya
waje. Sabira ta zazzage tsunmokaranmu tas a ƙasa ta sake zaɓewa, ta cire mana marasa
yawa, sauran kam ni kaina nasan babu amfanin da za'ayi dasu. Tsabar sabo da tulin
tsunmokine kawai. A buhu ɗaya ta haɗe ma yara kayansu. Ni kuma nawa ta je gidanta sai gata
da katuwar jaka. A ciki ta shirya mun kayana. Ta kirawo Ahmad ya fita dasu. Kayana dana
Bilkisa su kai gaba. Kayan Hajiyayye da Hindatu kuma sai an dawo. Hajiyayye ta kai wuya kuwa
da ita da ƴan uwanta da tayo gayyarsu. Itama Bilkisa ƴan uwanta biyu sun zo jiya daga Zaria,
ga me aikinta kuma. Allah sarki, ni ko daga ni sai Sabira, Yaya Use sai dai waya kawai mu ka yi
da'ita nake sanar mata. Habiba Bala kuma, dana kirata ɗazu a wajan siyo katifa tace in yi haƙuri
sai gobe zata iya shigowa.........✍
*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*
*INA Marubuta da masu business*
*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin
farashi me sauki*
Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu
Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776
*All netwk Data is available*
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURENA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 17
Ana cikin wannan Gaga_gaga sai ga ƴan makaranta sun dawo. Ganin mu a tsakar gidane yasa
suma suka shigo ɗu. Amina ta kusan murjema ƙanwar Hajiyayye ƙafa. Ai kuwa ta lailayo
ashariya ta mako mata ta ɗaura da cewa.
"Shegiya mai kama da uwarta, dangin ƴan maula, masu kwana a bakin masallaci" Wani zafi
naji a zuchiyata, nasan haushi suke ji da abinda ya faru da Yaya Use da Hajiyayye, da kuma
haushin an soma tafiya da kayana ita nata gasu nan jibge a tsakar gidan. Ina ganin haka na
miƙe dan take takensu so suke a tanka su yi buyagi a tsakar gidannan. Su ja mun sale salin
tsiya.
Sabira mu soma yi ma maƙota sallama, kafin lokacin tafiyar tamu tayi, yau dai ba zuwa
islamiyya sai kuma gobe." Fita mu ka yi a gidan har da yaran. Bilkisa tana ɗakin Kaila ita da ƴan
uwanta. Muna fita mu ka samu isa a waje isowarshi kenan da matarshi uwar gidanshi Jamila.
Itace muke mutunci, amaryarta kuma ƙawar Hajiyayye ce unguwarsu ma ɗaya. Jamila kece a tafe?