Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
bansan sunanshi ba. Baffa ya sai mana abinci. Shinkafa garau_garau
ce ya siya mana akan wani ɗan tallah. An yi mata zubin ɗari_ɗari, kowa ya ɗauki ƙwano ɗaya.
Wata rumfa muka nufa anan muka yi zaman dirshan. Hauwa na sakko daga baya, sai da ta
ƙoshi sannan na ci abincin na bi da ruwan leda guda ɗaya. Inno tace.
"Baffa ni kam zan kama ruwa, kaga Shanono daga nan da tafiya sosai, gara in rage marata,
Indo muje ki rakani mu nemi wajan ciyayi haka sai in yi." Ai Inno na faɗin haka duk muka miƙe
ko wacce da guntun fitsarinta ga mararta. Wani gida muka samu daga bayan wasu rumfuna, a
gidan muka kama ruwan, sannan muka shiga mota, bamu tsaya a ko inaba sai a Shanono.
Idanu na lumshe na shiga tuno irin rayuwar auren dana gudanar a shanono, duk su ka dinga
dawomin. Tuno da Dauda ɗana ne yasa na ɗan saki ajjiyar zuchiya. Baffa ne ya katse mun
tunanina da cewa.
"Inno acan gida zamu sauka, jiya ina wajan bara Jafaru ya kirani, nace ya buɗe ɗaki ya ƙyara
mana. In yaso ko zuwa yamma ai sai ku kintsa kuje gidan Deluwan ko?" Inno tace.
"Tunda ka yanke hukunci ai shikenan Baffa. Amman ni kam ai so samuna daga nan sai gidan
Deluwa, ana can anata sha'anin biki ka sani. Tun shekaran jiya ya kamata ace na iso garinnan
fa haba Baffa" Da ihu_ihu Baffa yake magana kamar faɗa irin na makafi, sake ƙwalla muryar
tashi yayi yace. "Da wannan tulin tsarabar kike son ki je gidan biki, shingin duk abi a sace, bazai yiwu ba. Use
nuna mishi hanya kinji mu je unguwar Shakogi." Yaya Use tace.
"To Baffa. Lauwali kwana zaka yi, ka miƙe har gaba da ceɗiyar can. Kana yin kwana gidan
kenan"........
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 13
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE
Bansan sanda na fito zauren kamar zautacciya ba. Idanu muka haɗa da Kaila, ya jefe ni da
wani kallon tsana.
"Nayi ɗan daka ce ban je masallacin ƴan taya na ganku a wajan bara ba. Nayi nadamar wannan
haɗuwar tamu na farko. Na auro mata marar tarbiyya ƙazama, wacce babu abinda ta sani sai
ƙazanta da haihuwa, ga gayyar kuɗin cizo. Ki faɗama Yarki ta bar mun gidana wallahi in ta ƙara
shigo mun gida kotu ce zata raba ni da'ita. Ke kuma zaki ga irin mummunan hukuncin da zan
yanke miki akan wannan aika_aikar da kishi ya rufe miki ido kuka yi. Nan gaba ni zaku kashe ba
ɗana ba ai" Jikina tsuma yake ta ta yi. Kuka kawai nake yi, Yaya Use kuma ta yi kasaƙe tana
kallona, bata ce komai ba tasa hijabinta ta ratsa ta gaban Kaila ta fita, har jikinsu na gugar na
juna, dan Kaila ya ƙi matsawa, ita kuma na santa da zuchiya, dan Yaya Use asalin irin halin ƴan
jagora gareta, girmane yasa ta yi sanyi. Namiji kuma ya ƙara seseta mata nutsuwa. Da harara
Kaila ya bi yaya Use.
"Aikin banza aikin hofi. In banda tashanci taya wannan buhun fulawar zata yi faɗa da Hajiyayye
in ba dai dama shiryawa su ka yi ba. Ke kuma na dawo gareki Shanono." Nuna ni yake yi da
ɗan yatsa jikinshi har rawa yake yi, tunda nake ban taɓa ganin Kaila a cikin ɓacin rai
makamancin wannan ba. Ba shiri na durƙushe a gabanshi ina kuka. Hannayena na haɗe waje
guda cikin sigar ban haƙuri. Amman Wallahi in buɗe baki in yi magana na kasa. Babu irin zagin
da Kaila bai yi mun ba, ya buɗe baki yace uwarki Inno da ubanki Nanoma sunci ubansu ne
kawai baice ba. Amman ya zage su tas. Hakan bai mishi ba yasa ƙafa ya shureni sai da na
shige ɗaki. Sai gani a tsakiyar yarana. Kuka na kuma sakawa, ganin ashe kuka suke yi suma.
Hauwa da Balaraba ne kawai basa kuka, amman suma sun yi shiru kamar ruwa ya cinyesu.
Ban yi aune ba, Kaila ya shigo da bulala mai baki biyu. Yanda yake dukan Sani da Sulaiman in
sun mishi laifi haka ya shiga tabkata. Tsabar zafin duka da gigicewa sai da na kusa tsirara a
gaban Isa dake ta faman kokawar ƙwace dorinar a hannun Kaila, amman ya kasa. Amadudu ne
ya shigo da gudu da ƙyar suka ɓanɓare kaila a ɗakin.
"Zaki ci ubanki ne ƴar iska ƴar mabarata, ni zaku kashe ma ɗa dan baƙin hali." Allah kawai nake
ambato har zuwa lokacin ina jin zugin dukan na ratsa jikina. Yarana duk sun takure a lungon
katifa sun cure waje guda sai kuka suke yi. Jaririna dana tumirmushe na ɗauka da sauri. Ashe
shiɗewa yayi. Sai da na jijjigashi da ƙarfi sannan ya saki wani irin kuka mai karaɗe kunnuwa.
Nima na sake sakin kuka. Ina jiyo Bilkisa tana yima Kaila magana akan rashin dacewar dukana
da yayi. Sai faɗa yake yi kamar zai ari baki. Yana ta tsinkani a wajan Bilkisa, yana faɗa mata a
kwaroro ya tsinceni ya wankeni ya aureni ina bazawara mai aure huɗu, shi kuma yana saurayi
fil. Jaririna na duba, sai ajjiyar zuchiya yake yi, nono yake ja a hankali. Su Sani na duba, haƙiƙa
ƙaddarar zuwansu duniya ne ya haɗa aurena da Kaila. Dani dashi bamu da tsimi bamu da
dabara. Wannan shine karon farko da Kaila ya sa madoki ya dokeni. Ya kan mareni, ko ya sa
hannu ya hankaɗeni in faɗi, amman bai taɓa mun mugun duka irin wannan ba.
Da ƙyar na lallaɓa na rarrashi yaran su kai shiru. Ina zaune ina karanta wasiƙar jaki har wajajen
sha biyun dare, na rasa inda zan tsoma raina, fargabar abinda kaje kazo nake yi. Na san zaman
gidannan ya ƙaremun, to yarana fa wazai riƙe mun su? Jibi rayuwar Dauda yadda ta samu giɓi
sakamakon rashin uwa majingina a tare dashi. Taya zan tafi in bar gidannan, in tsallake yarana
ababen alfaharina? Ina cikin wannan taɗin zuchi wayata tayi kuka Yaya Use ke kira da sauri na
ɗaga"
"Tani ince dai babu wata matsala data biyo baya ko?"
Babu Yaya Use, kiyi haƙuri da abinda Kaila yayi miki"
"Hmmm Tani kenan, akwai ranar da zan mayar ma da Kaila wannan cin kashin da yayi mun.
Halin da kike ciki shi yafi damuna a yanzu, rintsawa wannan na kasa yi. Baban yara sai
tambayata yake yi, jikina yayi sanyi. Ki yarda dani Tani wallahi ban daki Hajiyayye a ciki ba,
makircine kawai irin namu na mata. In ce dai ƴan uwanta basu zo ɗaukar fansar dukan ƴar
uwarsu da akayi ba ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Basu zo ba, amman a cikin zulumi sosai nake Yaya Use, dan ƴan uwanta sunce ba zasu yarda
ba. Kuma Yaya Use makircin Hajiyayye yafi da haka wallahi, tayi mun abubbuwan da bansan
iyakarsu ba a rayuwa. Amman babu komai, kema nasan kin yi ne domin ki ƙwatar mun ƴanci ba
dan ki jefa ni cikin matsala ba. Amman tsorona tsinuwar da Baffa zai mun in ya ji mutuwar
aurena a karo na biyar. Dan ina da yaƙinin Kaila sakina zaiyi, Ɗa ba wasa bane yaya Use " Mun
jima muna tattaunawar da ba zata fisshemu ba, face mu ɓata bakunanmu da ƙone katin waya
kawai. A taƙaice kwana nayi kusan a zaune, kafin asuba jikina ya kumbura yai suntum, ko idona
bana iya buɗewa sosai. Kasancewar jikin nawa ɗanyene kuma gashi na daku iya duka, dama
goshina in da Baffa ya raɗa mun sanda a kumbure yake dama. Ko da na tashi yara su yi Sallah,
da suka ga fuskata sai tambayata suke yi banda lafiya ne? Ni kuwa shiru nayi musu kawai,
Dauda kuma yayi ƙuri abun tausayi. A ranar dai a ɗaki nayi ma Dauda wanka a bawo na shafe
mishi takashinshi da man da mai maganin ya bamu. Abun tausayi har wani ajjiyar zuchiya
Dauda yake ta saukewa, wari kuwa ya cika ɗakin fam. Ruwan wankan na fita dashi a bawo na
zubar. Nan da nan tsakar gidan ta kaure da ɗoyi ina jiyo Amadudu daga ɗaki yana faɗama
Hindatu.
"Ina ga bara gurbi ne ya fashe a maƙota kinji wani azabar wari?" Ina jin haka na koma ɗaki da
gudu, gudun karma su fito su ganni. Ina cikin yima jaririna wanka na jiyo tsaiwar mota a dai_dai
windo na, ni dai na jiyo muryar mace tana cewa.
"Ga gidannan, mun yi waya da mai gidan yana ciki" Sai muka jiyo sallama a zaure da wata
ƙatuwar murya. Ba'a jima ba na jiyo takun tafiyar Kaila. Ni ko gudawa harya taru mun. Yara su
kai tsuru_tsuru duk a cikin tsoro muke. Kaila ne ya bankaɗe labulen ɗakina. Ba shiri ya toshe
hancinshi harda runtse idanunshi. Tabbas na san warin da Dauda yake yi ya kai ayi fin hakan
ma. Nima dake uwace shi yasa ko a jikina.
"Ke kam ba dai ƙazanta ba. Ji warin da ɗakinnan yake yi. Ashe dama warin da Ɗanyan gwal
tace mun ta jiyo a tsakar gida daga nan yake fitowa? Ko da yake ba abinda ya kawo ni ba
kenan. Ƴan sanda na jiranki a waje sai ki goyo ɗanki ku je, nima zan biyo bayanku" Miƙewa
tsaye nayi a zabure ina kuka nace. Kaila kayi mun rai dan Allah. Wallahi Allah Yaya Use bata naushi Hajiyayye a ciki ba. Kaga jego
nake yi banda lafiya, ka tausaya mun dan Allah kar ka bari su tozarta ni"
"Kinga dakata Shanono. Dangin Hajiyayye suna da hakkin yin shari'a daku akan ƴar uwarsu.
Dan baki san girman laifin naku bane shi yasa ma har kike wannan magiyar ai. Wuce dallah"
Kaila ya hankaɗoni waje, sai gani a zaure kusa da wata ƴar doka mace. Goyona ya miƙo mun
na ɗamare shi, jikina fa bai daina kakkarwa ba. Yara suka fito suna kuka. Sai a lokacin kaila ya
kula da Dauda.
"Shi kuma wannan yaron fa Shanono daga wacce duniyar yake?" Ruɗun sai ya ƙaru mun, in yi
magana na kasa. Ƴar doka ce ta katse mana uzuri, wanda ni hakan yayi mun daɗi.
"Wannan kuma maganarku ce ta cikin gida. In ta dawo kwa tattauna, muje baiwar Allah " A
gaba ƴar dokar nan ta tusani, ina jiyo kukan Hauwa a kunnuwana, dukkansu yaran kuka suke
suna ambaton.
"Umma Umma" Babbar yar su Hajiyayye na gani a ƙofar gidan, da ƙaninsu Namiji. Haka aka
sani a motar ƴan sanda kamar ɓarauniya. Kai tsaye hanyar gidan su Yaya Use muka nufa.
Lamarin daya sake tunzura tashin hankalina. Damuwata ta ƙaru ainun. Ai kuwa sai gamu a
ƙofar gidan su Yaya Use. Basu jima da shiga gidan ba, sai gasu da ita an taso ƙeyarta. Ganin
Fatima yasa nace.
"Fatima ki je gida ki kula mun da su Sani, ki faɗama Sabira halin da muke ciki. Dauda ma
yananan, Saudat ta kula da su Inno ƙarama" Yaya Use sai kuka take yi. Ni ko idanuna a bushe,
haka mu kai ta tafiya tiryan tiryan har caji office. Bamu taɓa shiga caji office ba sai yau. Haka
aka zube mu bayan kanta. Suka ci gaba da aikinsu. Mu dai muna zaune jigum. "Tani me ya same ki, naga jikin ki yayi ja ja ja halamun shatin bulala kaddai Kaila ne ya dokeki
da ɗanyan jego a jikinki? Kinga yanda halittarki ta canja kuwa Tani. Ga wajan da Baffa ya kwaɗa
miki sanda ma ya sake aunewa" Kafin in bata amsa Babbar yar su Hajiyayye ta shigo ita da
ƙaninsu, Kaila na biye dasu. Ya ɗau wanka sai ƙamshi yake yi, ba ka ce kaila mijina bane. Shi
yasa ma bai son a dangantasho dani, na sani yafi karfina nesa ba kusa ba."
Zuwansu ne yasa har aka kulamu. Nan yar Hajiyayye ta shiga ba da labari ma ƴan doka. Yaya
Use tace.
"A'a Ta bizaro kar ki bada wannan shaidar. Wallahi ban naushi Hajiyayye a ciki ba. Tsautsayine
da ƙaddara su ka kashe abinda ke cikinta" Buɗar bakin Kaila yace.
"Zaki ga tsautsayi ganin idanki. Tsautsayi da ƙaddara su zasu kai ki gidan kaso kema" Yaya Use
tai ma Kaila kallon banza tace.
"In aka sani a gidan kaso a baka ɗan mabuɗin ka jefa a bahar maliya. Kaga in ba zamu tsaya a
gaban Ubangiji ba... Wata ƴar sanda ce ta daki teburi tace.
"Kuyi mana shiru anan. Ke kina bayan kanta amman bakin ki bai mutu ba ko? Zaki yi bayani ai.
Ku taso ko wacce ta rubuta statement, kuma ku sani duk abinda kuka rubuta zai iya zama
hujjarku a gaban kotu. " Cikina ne ya juya da naji ta ambaci kotu. Yaya Use tace.
"Mu bamu iya rubutu ba" Ƴar sandar nan tace.
"Zan dinga rubuta muku kuna faɗa mun. Sannan in kuna da lauya ku neme shi, dan ba ma
zamu ba da belin ku ba, dan maganar kisa akeyi. Ita kanta me jegon bama tasan in da kanta
yake ba har yanzu. Dan haka ku nemi lauya dan tattare bayananku zamu yi mu miƙa ku kotu."
Muryata na rawa na dinga karanto iya abinda na sani. Ƴar sandar nan nata rubutu. Haka na
gama Yaya Use tayi nata. Ana cikin haka sai ga Sabira da Baban Mustapha sun shigo. Sabira
ƙawa ta gari tana ganina ta fashe da kuka. Baban Mustapha kuma yayi iyakar ƙoƙarinshi a
bashi ko da belinane wallahi su ka ƙi. Sha'anin hukumomin ƙasarnan sai adda'a.
"Tani ki bani jaririn in tafi dashi, kema ki samu kiji da kanki. Zan dinga bashi madarar yara. Su
Sani ma suna gidana, harda yaronki Dauda"
"Dauda yaronta? Kut lallai Shanono kin ci ƙarya kin kwana da yunwa, nine ɗan iskan da kike
tunanin zan riƙe miki agolan ɗanki, bacin ubanshi yana da rai? Ai ko bashi da rai wallahi bazan
riƙe agola ba, kina fitowa daga gidan yari ki tattare ki mayar da yaro gidan ubanshi. In kuma
kina son ku koma gidan uban nashi tare ne ai shikenan Shanono" Cewar Kaila, Yana dasa aya
ya fice. Baban Mustapha ne ya bishi da sauri. Ni kuma na sunto goyona na ba Sabira.
Sabira wayata tana ɗaki, ki duba zaki ga number Habiba Bala a ciki. Ki kirata ki mata bayanin
halin da nake ciki dan Allah, nayi imani zata zo yau ɗinnan."
"Shikenan Tani, zan kirata. Kuma in Allah ya yarda ba zaku kwana a tsare ba" Keyarmu aka
tasa cikin cell. Zama nayi a ƙasa ina murmushi kawai. Yaya Use tace.
"Sai da na faɗa miki kar ki ɗakko Dauda Tani. Kinga yanzu abinda ya faru ko. Yanzu yaya
yaronnan za'ayi dashi? In kika ce gidansu Inno zaki mayar dashi bara zai dinga zuwa kema kin
sani. Mu ma kuma kinga halin da muke ciki. Amman wacece ita Habiba Balan da kika ce a
kirata?" A taƙaice na faɗa mata wacece Habiba Bala. "To Allah ya rufa asiri. Baban yara yana ciki fa. Amman Sabida ɓacin rai ko kallona yaƙi yi. Shi
yasa ma baki ganshi ya fito ba. Kuma nasan ko ɗaureni za'ayi igiya tayi saura bazai zo
ba...........✍
(MASU CEWA IN SASSAUTAMA SHANONO MASIFAR TAYI MATA YAWA. TO KU SANI KO
WANNE BAWA DA IRIN ƘADDARARSA. KUMA WASU MATAN SUNA FUSKANTAR MATSIN
RAYUWA NINKIN NA SHANONO. WANNAN LABARIN BA ƘIRƘIRARSHI NAYI BA. LABARINE
DAYA FARU A GASKE. BABU ABINDA NAKE DAƊAWA SAIMA RAGEWA DOMIN
MAKARANTA SU FAHIMTA. SHANONO TANA GAISHEKU, TACE KUYI MATA UZIRIN
ƘAZANTAR DA KUKE JIFANTA DASHI. KUMA KU BIBIYI LABARIN DA SANNU ZA'A
WARWARE MUKU KOMAI. NAGODE)
*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*
*INA Marubuta da masu business*
*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin
farashi me sauki*
Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu
Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776
*All netwk Data is available*
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 12
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*