Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
Haka kurum Asabahu ya sake ni da wata farar safiya saki biyu a karo
na uku. Kuma zan tafi suka hanani ɗa ko ɗaya, yarana suna kuka ina kuka haka na baro
ƙauyannan. Tunda na sauka a tashar Bauchi gabana yake ta dokawa hankalina a tashe nasan
abun da zan tarar a gidan ba mai daɗi bane. Ai kuwa ilai abunda ya faru kenan.
Kwararam_kwararam na shiga gida da tulin tsummokina ina kukan fitar rai ko zasu ji ƙaina su
sassauta mun. Abun mamaki mahaifina nan ya rufe ni da duka, ya farfasamun jikina ko ganin
girmana bai yi ba. Sabida baƙin ciki da takaici na sai da hawan jini ya kama shi. Ni kuwa na
kasance tamkar mujiya, ko sallama akayi za'a shigo Mama sai ta turani ɗaki bata son mutane
su ganni sabida su basason su ji kunya a wajan mutane. Sun dai zaɓi ni su karya mun zuchiya.
Ga rashin iya zaman Aure, ga tsangwamar irin wacce kabilar Hausawa suke ma Bazawara, ga
rashin ƴaƴana, shi kanshi jawarcin raɗaɗine dashi. ( Zawarawane kaɗai zasu gane wannan
batun. Zawarci fa bashi da daɗi sam. Shi yasa wasu matan suke kashe kansu a gidan Aure,
sabida gudun zawarci, da gujema tsangwama) Haka nai ta rayuwata babu wani mashin shini,
na zama tamkar bora a gidanmu, aiki ake ledamun tamkar jaka, kuma fa haka na koma wannan
gidan abincin na ci gaba da wanke_wanke tana bani wannan abinci dafaffe sai ƙarin albashi da
tayi mun daga ɗari biyu zuwa ɗari biyar. Wannan shine labarin halin dana shiga a baya" kai na
jinjina nace.
Yaya batun komawarki makaranta ya akayi kika samu wannan damar, har kike kan matsayin
da kike a yanzu?" Dariya tayi mun, idanunta sun yi jawur.........
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 6
Batun komawata makaranta ya samo asaline ta dalilin Hajiya Hari mai gidan abincin da nake yi
ma wanke_wanke. Wata farar rana da bazan mance da'ita ba itace ranar da hajiya Hari take
shaidamun ta samomun aiki a gidan wata Hajiya ƴar boko ce, kuma ta kasance mai son tsabta.
Ganin tsabtata ne yasa ta zaɓeni a inje can gidan nata in yi aiki. Za'a dinga biyana albashin
nera dubu biyar. Wannan labari sai naji tamkar in zuba ruwa a ƙasa in shanye dan murna.
Hajiya Hari ta kaini gidan wannan Hajiya ƴar boko ta damƙani gareta.
"Habiba kin yi karatune, ko kuma matar Aure ce ke a zaune a gida?" Kafin in ce wani abun
Hajiya Hari ta tari numfashina da cewa.
"Bazawarace nan mai ƴaƴa uku. Aurenta uku zaman yaƙi yiwuwa, shine ta fito neman na kai,
ko dan bukatun yau da kullum" Numfasawa wannan Hajiyan tayi kawai, sai cewa tayi."
"Kinason komawa makaranta ne, ko me kika tsarama kan ki?"
Inaso Hajiya, dan auren ya gama fice mun a raina." Na bata amsa da haka. Ta umarceni gobe
in zan zo in tawo da takadduna zata gani, kuma tayi mun alƙawarin zata taimakamun. Ashe
wannan Hajiyar gidauniyace da ita domun tallafin mata da basu jari, masu son komawa
makaranta ta sasu a makaranta. Ko da na dawo gida bance ma kowa komai ba, washe gari na
kai ma Hajiya Boko takadduna ta gani, ta ajjiye a wajanta. Wata biyu da soma aiki a ƙarƙashinta
na samu gurbin karatun likitanci a jami'ar Jos. Lokacin da zan tafi mahaifina ya dage akan shi
ba da yawunshi ba, za'ace ya barni na tafi karuwanci Jos. Sai da amininshi maƙocinmu ya dinga
bashi baki. In baku a taƙaice Amininshi ne ya bani umarnin tafiya tare da shi mun albarka. Kunji
yadda akayi na zama haka kenan." Halima Bawa tace.
"To batun aure kuma fa Habiba Bala tunda dai yanzu duk namijin da zai aureki ma sai ya
shirya?" Dariya mu ka yi dukka, Habiba Bala tace"
"Ina da tarin tulin zawarawa a ƙasa wanda suke jin kamar zasu mutu a kaina tsabar so. To ina
lallaɓawa dai in sha Allah akwai wanda nake ganin kamar zamu iya dai_daitawa, sai dai yawan
shekarunshi ne dai yake tsorata ni. Duk da nasan nafi ƙarfin ƴan matasa haka waɗanda da
kadan suka haura arba'in." Hirarmu dai haka tai ta tafiya. Mu yi sallah mu dawo mu zauna mu
sake baje hira. Sai da mu ka kusan raba dare muna hira, daga ƙarshe duk a ƙasa mu kai bacci
saman kafet. Washe gari da rana Habiba Bala ta fita damu muka sake ziyartar sauran
ƙawayenmu, ta kaimu shopping mall tayo mana siyayya sosai, sai mahriba muka dawo gida.
Bayan munci abinci mun yi sallar Isha sai na ɗan shiga tattare kayana dan gobe da wuri nake
son shiga Jos, ta gida zan sauka in tawo da yaran.
"Shanono kar kice na rainaki ƴan kayayyakinane nayi miki kwalimarsu, atampopi da ƴan
ƙananan kaya na shan iska, da fatan kina so ko? Ke kuma Halima Bawa ga wannan babu
yawa" Ta miƙa mata kuɗi ni kuma ta miƙo mun babbar leda, baki a yashe nace.
Gaskiya na gode sosai. Kin ji ki da faɗe Habiba Bala ai wanda ya fika ya fika. Kinga na ɗan
samu na sawa, gashi kishiya za'ayo mana dama. Nagode sosai Allah ya bar zumunci" Kuɗi ta
kuma bani, na dangane da batun komawa karatu ta cika mu da goma sha tara ta arziki. Washe
gari ta fita damu, ni a titi ma na samu motar Jos na shiga, su kuma suka wuce zata kai Halima
Bawa tashar Gombe. Idanu na lumshe motarmu sai shatata uban gudu take yi a titi. Mamaki
nake yi duk da ba wannan bane na farko ba, Kaila ya saba nuna mun halin ko in kula, duk inda
zani baya hanani, bazai kuma kirani a waya ba ko da shekara zanyi ban dawo ba. Ya kamata in
san abunyi tun kafin Kaila ya gaji da bani ɗakin kwana da abinci ya koroni rayuwata ta sake
tagaiyara a karo na biyar. Amman ba lallai abinda nake tunani ya yiwu harya tabbata ba, domun
bani da wata madogara sai Allah, bani da mai taimakona ƙila iyayena su gwasaleni su ƙi ban
goyon baya ma. Kaila dai nasan ba sona yake yi ba balle kishina ya ratsa ƙirjinshi ya hanani
cikar burina. Wannan burin burine wanda ya daɗe da samun muhalli mai kyau a zuchiyata,
mahaifane suka ruguje mun burina da nake mafarki. Kuma ba wai na yasar da burin dan son
raina bane, face dan bani da yanda zanyi, bansan ta ina zan soma ba. Amman lokaci yayi da
zan soma koma ta inane da izinin Allah, kuma inna soma in sha Allah sai na idasa zan tsaya,
abu ɗaya ne zai yi mini cikas wannan cikin dake jikina, amman zan jinkirta har zuwa lokacin da
Allah zai saukeni lafiya."
"Hajiya mun iso fa, ke kaɗai kika rage a motarnan" Cewar direban motarmu. Sakkowa nayi ina
sauke ajjiyar zuchiya. Keke napep na tara zuwa layin idi mai barkono. Na kuwa taki sa'a a kofar
gida na samu Inno ita da su Sulaiman, Shafi'i na riƙe da buhun bararta. Balaraba tana ganina ta
rungumeni tana murnar ganina, Sani sai dariya yake yi na murna. Nima naji daɗin ganinsu
sosai. Inno tace
" Ƴar nema du wannan murnar ganin uwar taki ce lallai kuwa. Dama Amina ce tawa da su
Sulaimanu."
Inno bara zaku tafi, ni nama yi tunanin ba lallai in same ku a gidan ba"
"Wallahi kuwa yaranki ne suka makarar dani, amman ai da tuni ina can, Baffanku tun shidan
safe suka fice da su Habu da Indo. Yarannan dai ki tafi da su Balaraba, Amman Shafi'i da
Sulaimanu, da sani zasu rakani bara, inna taso komai dare zan dawo miki dasu.." Su Amina
suma suka kafe sai sun bi inno .Turus nayi domun akwai lokacin da Kaila ya taɓa wucewa ta
masallacin ƴan taya ya ga su Sulaiman tare da Inno suna bara yaran sun bita daga gida lokacin
ana hutun makaranta. Ranar nasha baƙaƙen maganganu da zagi iri_iri, kuma yayi mun mugun
gargaɗi akan kar hakan ta sake faruwa ba za'a mayar mishi da yara mabarata masu matacciyar
zuchiya ba. Ni kuma bazan iya hana mahaifiyata tafiya da yarana ba. Koma yaya take uwa
uwace.
To shikenan Inno sai kun dawo, ni zan tafi gida. Kwa gaishe da Baffa." Tare muka fito titi Inno
na cogala ƙafarta, Inno irin masu ƙafa ɗaya da rabinnan ce, a duƙe take tafiya hannunta ɗaya
dafe da ƙafar mai lalura. Shi kuma Baffana makawone, a wajan yawon bararsu tun a Shanono
suka haɗu Allah ya ƙaddari aurensu. Mun zauna a garuruwa da dama wanda yawon bara ke
kaimu. Amman tunda muka zo Jos Baffa yaji sanyi da daɗin garin yace yaga wajan zama, a
lokacin muna yara Yaya Use ce kawai babba a wannan lokaci. Keke napep na tara muka zo
muka wuce su, Su Sulaiman suna ɗaga mun hannu. Dan Inno basa hawa abun hawa duk inda
zata a ƙafa take zuwa tana yi tana bara, Indo na mata waƙa. Ina jiyo sautin muryoyin su Shafi'i
suna ma Inno amshin waƙar bara. Wacce muma muka taso da ƙwarewarta. Hawayene ya
gangaro a kumatuna, da sauri nasa gefen mayafina na sharce hawayen. A bakin layinmu na
sauka na ƙarasa. Tun daga baƙin ƙofar shiga cikin gidan nake jiyo muryar Ba Rammai
Mahaifiyar Kaila, da hausarta irin ta Hausawa mazauna Akwanga , maganarta dama a sama
take yi da tsawa da hargowa, kuma ba faɗa bane. In kuwa faɗan zata yi duk maƙota sai sun fito.
Gabana ya yanke ya faɗi dan bata da sauƙi musamman a kaina. Ajjiye kayana nayi a ɗaki na
shigo da sallama cikin gidan. A kan taburma na samu Baba Rammai da Kaila, Hajiyayye tana
daga bakin ƙofarta, Hindatu kuma tana aikin sharar tsakar gida, yaran na wasansu."
Sannu da zuwa Baba Rammai kece a tafe, maraba" Ban kai da zama a kan taburmar ba, cikin
hausarta ta Akwanga tace.
"Yau ga burun ubaaa ni kike cema a tafe sai kace sa'ar gurguwar uwarki Inno? Lallai Kaila ka yi
ƙoƙari da kaci gaba da ajjiye wannan tsohuwar bazawarar da taga maza kala_kala." Turus nayi
a durƙushe a gabanta, ji nayi kamar ta ɗauki wuƙa ta luma mun a cikina. Wai mai Hausawa
suka ɗauki kalmar zawarci ne da aure_aure? Ni naga ko karuwai basu cika fuskantar irin matsin
da Bazawara ko mace mai caccanja miji take fuskanta ba. Buɗar bakin Kaila sai yace mata.
"Wallahi Rammai sabida yaranta nake ɗaga mata ƙafa, bana son in ɗauketa a kansu dan babu
wanda zai kula mata dasu sai dai itan. Wannan dalilin ne yasa na bata ɗakin zaure ita da yaran,
ita kuma Bilkisa na bar mata nata kuma yafi ko wanne daki girma" Haƙiƙa maganar Kaila yayi
dai dai da zafin fitar rai daga gangar jiki. Wato ni amfanina ciki da rainone, da ba dan hakan ba
da tuni a karo na biyar ɗin ma koroni za'ayi. Ya Allah ka bani jumurin dauriyar ci gaba da
zaman gidannan ko dan in bama yarana tarbiyyar data dace, sune kaɗai sanyin idaniyata,
Dauda ma dana fita a gidan mahaifinshi na barshi ina mishi adda'a da fatan nasara a rayuwa.
Iska na fesar na ɗago muka haɗa idanu da Hajiyayye wani irin Murmushin nasara take yi mun,
Idanuna ya kaɗa yai kamar gauta. Da ƙyar na haɗiye wani kakkauran yawu kana nace.
Ina kwana Baba Rammai kin zo lafiya?" Sai da tayi tsaki sannan tace.
"Su yaran fa suna ina?" Kaila daya kafeni da mayaudaran idanunshi waɗanda ada suke da
matukar tasiri gareni yace.
"Ai na ɗauka ta gidan zaki biya ki tawo dasu ko? sai nagan ki ke kaɗai ya'isa haka ai ko. Ni kar
aje ma a dinga fita ma da yara yawon tumasanci suje zuchiyarsu ta mutu su ce sunga sana'a"
Duk dauriyar da na dinga yi gudun kar in yi kuka a gaban kishiya, da facala, sai da zuchiyata ta
gaza tayi wani irin raunin da bansan sanda na fashe da kuka ba. Hauwa'u na sauke na
dangwarar musu na tafi ɗakina. Ina jiyo shewar Hajiyayye, ita kuma Baba Rammai ta shiga
farfaɗan miyagun maganganu akan bara, ina ji tana cewa daga ranar kar a kuma kai mata jikoki
gidan guragu da makafi kar a koya musu maula. A kan katifata na kwanta a rigingine ina kallon
rufin ɗakin, hawaye kuwa sai makanta ganina yake yi. Wallahi bansan rashin darajata a rayuwar
Kaila ya kai hakan ba, yau da ba dan gudun tsinuwar iyaye, da gudun tofin Allah ya tsine daga
bakunan mutane ba, wallahi da babu abinda zai sa in ƙara ko awa ɗaya a cikin gidannan"
"Ke Shanono dan wulaƙanci Rammai tana magana bata sallameki ba shine kika dangwarar
mun da ƴa kika yi tafiyarki, wato ga mahaukaciya ko? To nagode Allah mahaifiyata ba
mabaraciya bace mai kwana a bakin masallaci ba. Yara kuma ki yi waya a dawo mun dasu.
Sannan muddin kinason kici gaba da amsa sunan matar Kaila, ki je ki tsugunna ki ba Rammai
haƙuri har sai ta hakura sannan. Abu na gaba wannan kayan da kika saka a jikin ki ranar da
zaki Bauchi ki fito mun dasu ki kawo mun, muna ɗakin Hajiyayye " Yana kai ƙarshen
maganarshi ya fice kamar kububuwa. Sai da nayi kukana ma'ishi na kusan minti ashirin, sannan
na share hawayena zuchiyarnan a cunkushe babu wani sassauci dana samu. Maganganun
Kaila na ɗazu dana yanzu su suke ta faman yi mun amsa kuwa. Jakata na buɗe na zaro
wannan kaya da Inno ta bani na fito. A tsakar gida na samu Hindatu tana ta waƙar kujerar
tsakar gida.
"Umman Sulaiman sannu da dawowa, ina aka baro mana su Sulaiman?"
Yauwa sannu." Iyakar abunda nace mata kenan, ai tasan inda suke kuma duk abinda aketa
taunawa ba tana ji ba."
"Tohh iko sai Allah wai na kwance ya faɗi. Me yayi zafi shi ba wuta ba, ai bani na kar zomon ba
rataya aka bani." Shigewata nayi ɗakin Hajiyayye da sallama. Hajiyayye na tsugunne tana haɗa
ma Rammai tea. Ga yarinyar Hajiyayyen a cinyarta, Hauwa kuma tana yashe a ƙasa, harta
soma ɗan kuka, Kaila yana harɗe a kujera yana aikin daddanna wayarshi. A gaban Baba
Rammai na durƙusa bakina na ɓari.
Baba Rammai dan Allah kiyi haƙuri. Nayi kuskure bazan sake ba in sha Allah, Allah ya huci
zuchiyarki." Ai nan tace ina wuta ta tsoma ni. Ta dinga faɗa tana ihun da babu makawa maƙota
duk suna jiyowa, ta dinga dawo da bara bana. Ai rannan da tazo ma banko yi mata fara'a ba
bani da kunya dake na saba da maza, kuma idona ya buɗe da rashin kunya irin na yara ƴan
jagora. Ni dai kaina na ƙasa ina haɗiɗiye zuchiyata, Hajiyayye ranta fes dashi har Murmushi
take yi, ni dai ban gushe ba har sai da tace ta haƙura na mata godiya, wajan Kaila na wuya.
Kaila ga kayan" Bai ɗago ya kalleni ba, sai yace.
"Hajiyayye karɓi kayannan, shikenan rigima ta ƙare dai ko?" Ni kuwa binsu nayi da idanu cikin
ɗaurewar kai ban gane rigima ta ƙare ba, rigima tayi akan kayan shine ya sa na kawo dan ya
bata ita tasa ko me suke nufi?"
"Rigima ta ƙare Baby, ai kayanne suna da tsada super ce fa kuma babbar" Kallon Hajiyayye
kawai nayi na sauke kaina ƙasa. Rammai ce tace.
"Ɗauki ƴarki kuje ya'isa haka kuma" Dama zaman ya gundureni gudun kar in kuma yin laifine
yasa na zauna ina kwasar baƙin ciki, Hajiyayye kamar zata koma cikin jikin Kaila, shi kuma sai
wani lallashinta yake yi. Hauwa na sunkuya na ɗauka tare da fice wuf a ɗakin, ina shiga ɗakina
na kuma ɓallewa da kuka. To mai Kaila yake nufi ne dani, meye dalilin da zai karɓarmun zani ya
ba matarshi alhalin ni bashi ya sai mun ba? Kuma wai har ake faɗin rigima ta ƙare, ita kuma
tana faɗin kayanne da tsada super ce. Dole na ture wannan damuwar domun akwai matsalolin
da suke da mahimmanci fiye da wannan su suka fi damuna. Haka na wuni cir a ɗakina a takure,
ragowar soyayyen naman sallana naci na sha ruwa, Hauwa kuma bacci take yi. Wajajen biyar
na yamma dai na daure na fito tsakar gidan dan ɗaura girkin dare, Hauwa sai kuka take yi na
rasa kukan na meye dan har jikinta ya soma zafi. Ni kaina jikina ya ɗau zafin zazzaɓi kau, ga
wani irin mugun ciwon kai dake damuna. Zulaihat na aika shago ta siyo mun omo. Ni kuma na
zauna ina jiran wuta ta ruru, Baba Rammai tana kwance tayi bacci a kan taburmar, Hajiyayye
Hindatu kuwa sai shewa suke yi.
"Gobe nima yace za'a haɗa da ɗakina ayi fentin. Kuma zai sake mun kujeru, kinga inna siyar
da wannan kujerun na ɗakina, nima sai in yo suturu duk da jiya ya kawo mun kala shidda.
Amman zan ƙaro wasu ni da tsinanniyar amaryar tashi sai dai mu zuba, bata isa ture mun
matsayina a zuchiyar Kaila ba" Cewar Hajiyayye kenan. Hindatu tayi shewa suka tafa tace. "Ai naga sai bala'i kuke yi, jiya ma fa haka kika fashe mai wayarshi sai wata ya siyo. Naga duk
ya rikirkice sai lallaɓaki yake yi" Ni dai ina jin hirarsu amman harkokin gabana nake yi. Zulaihat
ce ta shigo ta kawo mun omon dana aiketa. Ina tsaka da tsintar shinkafa na jiyo muryar Kaila
daga zaure yana rangaɗamun gigitaccen kira. Kafin in miƙe har ya shigo cikin gidan abunka da
tashi da ƙyar zama da ƙyar. Ihun kiran sunanane ya farkar da Baba Rammai. Bol yayi da tiran
dake hannuna Allah yaso na juye rabin shinkafar a roba. Tirannan ya faɗi ƙasa
gwangwarangwannnnnnnn...... Ƴar ragowar shinkafar