Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 24

12K to 15K   out of 70.8K words

Naga hanyar da kike son bi ba mai
ɓullewa bace, in Kaila zai kwana yana waya da budurwa ke kuma sai ki kwana Sallah. Kin
mance lokacin da yake nemanki kusan kwana waya kuke yi ne, ai a lokacin kinsan yana da
mata a gida, yanzu dan yayi menene ai ke kika lalatashi kika kuma nuna mai hakan wayewa ce.
Ni kin ganni ina lallaɓa igiyar aurenane babu ruwana da duk abunda zaki yi akan hana Kaila
Aure"
"Au haka zaki ce ma dan kinga nazo inason mu haɗe kanmu?"
Haka na ce ma Hajiyayye." Ina faɗar haka na miƙe na tada kabbarar sallar isha. Fuu Hajiyayye
ta fice. Bayan na idar na zauna nayi azkhar sannan na jawo wayata na buɗe data na faɗa
group ɗinmu na FGGC. Anata magana da tsare_tsaren yanda za'a gabatar da taron. Magana

nayi musu akan goben zan shigo nima dani za'ayi taron" Sunji daɗi ainun nan su kai ta nuna
farin cikinsu. Mayafi na yafa na shiga cikin gidan a tsakar gida na samu Kaila a gaban lifan
ɗanshi yana duba tayunsu.
Sannu da dawowa" Shine kalmar dana ce dashi.
"Yauwa Shanono " Iyakar abunda shima yace kenan. Wajan Hindatu naje na aro dutsen guga.
A daren na goge kayan da Inno ta bani dukka ƙaramar jakar tafiyata na ɗakko nasa leshi kala
ɗaya da mayafi a ciki, nasa ma hauwa kaya kala biyu da famfams guda uku dana tsaya na siya
a bakin layinmu, ɗayan kuma na ajjiyeshi gobe in zamu tafi zan sa mata. Na daɗe a kwance ina
tunanin yanzu shikenan rayuwata ta mutu a haka zanta rayuwa kenan ni. Nice har karfe ɗayan
dare ban runtsaba. Dana ga dai baccin ya ƙauracema idanuna saina miƙe na fito dan ɗaura
alwala. Abun mamaki na jiyo tashin muryoyin Kaila da Hajiyayye, yana ambaton.
"Ki bani wayata, wallahi kika sake fasamun waya a bakacin aurenki. Wawuya mahaukaciya
kinga Shanono tana irin wannan haukar ne? Ko da aka auroki kin taɓa ganin ranar da ku kai
cacar baki ne. Amman kin kira yarinya a waya kunyi zage_zage sabida ki nuna mata kin rainani
ina cikin wayata kin fisge." Baki na taɓe na tuno wata rana da daddare da muna mu'amular Aure
ni da Kaila Hajiyayye tayo kiran wayarshi lokacin suna ganiyar soyayyarsu. Haka Kaila jiki na
rawa ya zare jikinshi a nawa ya shiga amsa wayar Hajiyayye kwanciyar da ba'a gamata ba
kenan. Har batsa yake yi da'ita a waya a gabana. Ina gani suna waya gabanshi zai miƙe ƙyam
sabida musayar maganganun batsa da suke yi da junansu. Hmm ashe wanzami bai son jarfa.
Alwala nayi na shige ɗaki abina, na dinga gurgura Sallah, dan ɗan karatun sallan ba wasu masu
yawa na iyaba, ko izifi biyu ban cika ba, ɗan abinda na haddace dasu nake gudanar da ibadar
tawa. Washe gari sassafe nayi wanka naima ƴata wanka. Masa na siyo a gidan maƙota ta ɗari
biyu muka ci ni da Hauwa. Nasa mata pampas da kaya. Wannan atampar ta jiya da inno ta bani
na saka ɗinkin riga da zani ne. Nayi ɗaurin ɗankwali na maryam babangida. Na ɗauki baƙin
mayafin jiya na yafa a kaina, na ciro baƙar ɗaya_ɗayar jakata na ɗan zuba kuɗaɗena a ciki da
ƴan tarkace, wayata, chaja, da dai sauransu. Banyi kwalliyar komai ba ko turare ni bani dashi,
bama ni da kuɗin saye. Kayan kwalliyar ma bani dasu kwalli kaɗai nake murzawa, in banda jar
hoda ta zazzzage Zainab da rannan Yaya Use tazo ta mance da'ita shine na samu na ɗan
barbaɗawa, haka nake yin wani janƙau in na shafata. Fitowa nayi na rufe ɗakina Hauwa tana
baya. Jakata a ajjiye a zauren na shiga cikin gidan Kaila yana tsakar gidan yana zaune akan
kujerar tsugunno yana waya sai wani ƙanƙance idanu yake yi, wandonshi na kalla ya cika fam.
Hmm maza mutanen mu. Banza nayi dashi na wuce Hindatu nayi ma sallama zani Bauchi. Na
dawo nayi sallama a ƙofar ɗakin Hajiyayye tana fitowa naga sai bin ƙasan zanina da kallo take
yi cike da mamaki tace.
"Yaushe kika ɗinka kayannan umman Sulaiman, sunyi miki kyau?"
Da sallarnan na ɗinka. Nagode" Na bata amsa kafin na ɗaura da cewa
Ni zanje Bauchi sallama nazo yi miki." Nan da nan naga ta murtuke fuska ta shiga jijjiga kai ni
dai wuce ta nayi a tsaye a wajan. Nazo zan wuce Kaila ya ɗaga mun hannu dan gudun kar in yi
magana budurwar tashi taji in kwabsa mishi. Haka ya dinga mun lokacin Hajiyayye gashi lokaci
yayi ana rama ma kura aniyarta. Fita nayi abuna zuwa Bauchi road a gefen hanya na samu
motoci masu zuwa Bauchi nera dubu. Shiga nayi baya mu uku ne a ciki dukka mata mutum
ɗaya ake jira na gaban mota sai mu kama hanya. Gaggaisawa nayi da matan motar. Wayata ta
shiga ruri ina ɗagawa naga Habiba Bala ce ke kirana. Karawa nayi a kunne.

Habiba Bala kin ganni na shiga motar Bauchi kenan amman motar mu bata tashi ba tukunna."
Daga cikin wayar Habiba Bala tace.
"To Shanono Allah ya kawo ku lafiya karfa ki mance a zaranda hotel zasu ajjiyeki in kika sauka
a bakin hotel ɗin sai ki kira ni zan zo in shigo dake ƙarfe tara muka sa lokacin taron gamu kusan
dukka mun hallara ku biyu ne baku ƙarasoba Halima Bawa daga Gombe take tawowa amman
tun asubar fari ta tawo duk yanda ake ciki nasan ta kusan shigowa Bauchi. To Allah ya tsare."
Sallama mu ka yi akan saina kirata. Ko da na sauke wayar saina shiga mamakin yadda Habiba
Bala take magana a mugun yangance. Ni dai da sanin dana mata ƴar karaɗice da son aba
hammata iska. Dan ko rigima muka kwaso ita ke shigewa gaba ta tare mana. Gata da kuri kuma
ƙatuwace a lokacin mai ƙiba sosai, ɗalibai na jin tsoronta. Ɗan guntun murmushi nayi dana tuno
rayuwa. Ban jima da zama ba motarmu ta cika muka biya kuɗi muka kama hanyar Bauchi.
Tafiyar awa ɗaya da rabi ne cib ya kaini Bauchi. A dai_dai zaranda hotel na sauka. Ina sauka na
ga Halima Bawa tsaye da goyo a bayanta. Duk da ta zama babbar mace amman kamanninta
yana nan yanda na santa.
Halima Bawa kaddai sai yanzu kema kika samu isowa?" Na yi magana ina nufota. Da sauri ta
juyo sai kawai ta ganni. Baki ta washe tana tafa hannuwa.
"La'ilaha illallah mahammadun rasulillah sallallahu alaihi Wasallama Shanono ashe da rabon
zamu gana? Kai Allah yaima Habiba Bala albarka ta da yi ƙoƙarin sake haɗemu waje guda a
karo na biyu." Ɗan rungumar juna muka yi ta kafaɗa muna cike da farin cikin ganin juna, ƙamshi
jikin Halima Bawa yake yi sosai, gata shar_shar da'ita cikin kwalliya da ado. "Ga ciki ga goyo kuma Shanono? Dama har yanzu ana haihuwar konika a wannan tsadar
rayuwar da muke ciki. Kai Shanono har yanzu kina nan da ƙauyancinki wai?" Kafin in bata amsa
muka hango wata mota ta tsaya a gabanmu. Baki dukkanmu muka sake muna kallon Habiba
Bala. Ni dai da idanuwanta kawai na ganeta dan wallahi na ɗauka wata balarabiyace ta sauka
daga masar. Ni sanin da nayi mata mai ƙiba ce sosai, kuma bata kai haka haske ba. Sai kuma
yanzu na ganta ƴar madaidaiciya da'ita, ga mota tana ja.
"Habiba Bala kece kika zama Hajiya haka?" Cewar halima Bawa. Dariya tayi mana haƙoran
matanta biyu sama da ƙasa suka bayyana tace.
"To ya sanki? Shegiya Halima Bawa kina nan yadda kike babu abinda ya sauya. Ke kuma
Shanono dan ubanki meya kawo wannan ƙanjamewar haka?" Dariya dukka mu ka yi. Motar
muka shiga Habiba Bala ta canja akalar motar zuwa get ɗin shiga hotel din. Halima Bawa tace.
"Ba dole shanono ta rame ba. Kinga fa ga ciki tulele a gaba, ga ɗanyen goyo kuma fa. Nima
ina ganinta na dirar mata" Ni farin ciki ya hanani magana ma sai dariya kawai nake yi. A wajan
ajjiye motoci muka tsaya dukkanmu muka fito. Habiba Bala ta karɓi jakunkunan mu tace.
"Bari in taimaka muku da jakar. Tana tafe muna biye da'ita zuwa sama. A sama ta huɗu muka
tsaya a bakin wani ɗaki. Tura ƙofar tayi tana gaba muna biye da'ita a baya. Tangamemen falone
babba sosai muka shiga. Ƴan set ɗinmu na soma cin karo dasu. Wasu sun canja irin Habiba
Bala, wasu kuma sun lalace ire_irena. Amman kowacce ta zama babbar mace sosai da sosai.
Waje na samu na zube a ƙasan kafet ɗin daya malale katon falon. Nan aka shiga gaggaisawa,
duk da na ga baƙin fuska har wajan rai biyar.
"Kinga waɗannan daga siniya suka shigo. Lokacin kin gudu gidan aure daga zuwa hutun gama
jiniya. Fatima wannan itace Shanono"
Allah sarki sannunku sannunmu. Barkanmu da zuwa dukkanmu ita Habiba Bala Allah ya saka

mata a alkhairi a bisa wannan zumunci data kuma haɗawa. Hakan yasa na tuno rayuwarmu a
baya lokacin duniyar tana kwance." Nan fa hirar makaranta ta ɓalle. Hauwa na zaro a bayana
na miƙa ma Habiba Bala ita. Fatima B Bello kuma ta fita samo mana abinci. Jallof din taliya da
kifi sadin muka ci da lemon kwalba. Bayan mun ɗan nutsa kuma sai Habiba ta miƙe tsaye har
zuwa lokacin Hauwa tana hannunta.
"Assalamu alaikum ƴan uwana abokan karatuna ina mana sallama irin ta addinin musulunci.
Ba komai bane yasa na dage na yi ƙoƙarin ganin na haɗa mu waje ɗaya sai san zumunci da
tallafin juna. Duba da yanzu yanda Aure ya taɓarɓare a ƙasashen Hausa. Sai dai muce
innalillahiwainnailaihilrajiun kawai. Naso ace na samu damar tattaro kanmu duka. Amman ƴan
ajinmu na A ma kaɗan na samu na iya tarkatowa. Kafin in ɗaura jawabina inaso wata ta taso ta
buɗe mana wannan taro mai albarka da adda'a" Wani jin daɗi ne mara musaltuwa naji yana
lulluɓeni sai nake ganin kamar zan samu sassauci matsalolina ko da da iya shawari ne, kuma
ƙila in samu waɗanda zasu fahimtar dani inda maganin matsalata take. Halima Bawa Amirar mu
a makaranta ita ta tashi ta buɗe mana taron da adda'a. Kafin kuma Habiba Bala ta ɗaura.
"To kamar dai yadda na faɗa dalilin assasa taronnan badan komai bane sai dan mu dinga
zumunci da ƙarfafar junanmu, da ba juna shawarwari masu kyau. Sannan inason mu ware wani
asusu na taimakon kai da kai. Ta hanyar ajjiye wasu ƴan kuɗaɗen da zamu taimaki junanmu
dashi. Gwargwadon abunda kake dashi shi zaka zuba tunda ba adashe bane, in ma baka da
halin zubawa mun ɗauke maka, hakan bazai sa mu kasa taimakonka a lokacin da buƙatar
hakan ta taso ba. Ba komai bane yasa nayi wannan tunanin ba face ɗan matsalolin dana ɗan
shiga a baya wanda wani sirrina ne, amman alhamdulillah komai yanzu ya dai_daita wannan
halin ne yasa na tuno daku. Nasam yanzu mata kaso casa'in na gidan aure haƙuri suke yi
kawai. A wannan zamanin ba ko wanne namiji ne yake iya sauke dukkan hakkokin da suka
rataya a wuyanshi ba. Kaso hamsin daga cikin mazan talauci ne yai musu katutu, ko yawan
yara da tarin mata daya zube a gida yasan bashi da halin kula dasu. Kaso hamsin ɗin kuma
mugunta ce da som ganin sun tauye matayen aurensu yake sawa su kasa sauke hakkokinsu.
Bance duka aka zama ɗaya ba kar maza su samu jakar tsaba. Mu kuma matan bama yi ma
kanmu adalci. Mun shigo zamanin da bayan zaman auren dole kina da buƙatat sana'ar da zaki
dinga juya taro ya koma sisi. Ko kuma kiyi karatu ki yi aiki. Ta hakane zamu tsira da mutuncinmu
a gidajen aure a dena ganinmu a tagaiyare a haɗu a rufa ma kai asiri. In ya kawo ayi, in ma bai
kawo ba ke zaki ɗauka da kanki kiyi. Amman fa in ma Allah ya haɗamu da mazaje masu tsoron
Allah, nagartattun mazan da suka san darajar mace kuma basa son suga mace tayi kuka ko ta
shiga damuwa ba. To zama haka fa bai ganmu ba. In kina da ƴan canjinki wani wulaƙancin ma
namiji bazai iya tunkaro inda kike dashi ba. Amman mazan yanzu in ba kya aiki ba kya
kasuwanci ganinki suke a matsayin nauyi a kansu. In talaucinshi ya bugoshi ya dawo gida ya
sauke miki buhun rashin mutunci. Ni kiran da zanyi mana shine ilimi yana da matuƙar
mahimmanci ilimin addini dana zamani, ko zamu haɗa da sana'a mata ya kamata mu yi ilimi ko
da mijinki bazai barki kiyi aiki ba, ke a_kan_ karan _kankin_ kanki zaki zauna lafiya jahilci ai
babban ciwo ne. Ni nayi karatu na karanta fannin ilimin limitanci ni likitan mata ce ina aiki a
babban asibitin Bauchi. Bari in ga waɗanda da suka ci gaba da karatu bayan gama sakandare"
Cikin zolaya tayi maganar tata. Naji daɗin maganganunta sosai wallahi, na yarda rashin ilimi bai
yi ba a rayuwa, ni dai na addinin ma iyakata makarantar allo da nayi a shanono ina dai dana
Sallah. Boko a ƙaramar sakandare na tsaya, kuma na taso da hazaƙa da son ganin nayi karatu

mai zurfi. Amman Baffa ya dakatar mun da karatuna yai mun aure. Ƙalilan ne daga cikinmu
suka gama jami'a suke aiki. Sune suka fita daban ko a cikinmu. Halima Bawa atampar dake
jikina tafi tata kyau a ido. Amman dake ƴar makaranta ce tana da wayewa sai ta fini haskawa, ni
ko kashe ma kayan kyau ma nayi. Mu sauran irin su Fatima B Bello iyayene mazauna gida.
Habiba Bala tace.
"To ku da ba ku ci gaba da karatun ba bakwa sha'awar karatunne ko sana'a dai kuke yi?" Nice
nayi Magana nace.
Ni dai bana siyar da komai Habiba Bala. Ina zaune a gida kusan duk shekara sai na haihu.
Yarana bakwai ga na takwas a cikina. Amman yanzu naji ina sha'awar karatun addini dama
kasuwancin ko da sai da daddawa da kanwa a cikin gida ne" Ai kamar na buɗe ƙofa ne, wannan
tace itama sana'ar take son tayi, sai masu son komawa islamiyya nan dai muhawara ta ɓalle." "To duk abinda kuke son yi zaku yi da izinin Allah, kusa a ranku zaku yi. Zamu dinga tara kuɗi
duk wata, sai a dinga raba ma mutum biyu. Duk abinda Allah ya hore muku ku kawo a soma
tarawa. Sannan zan ajjiye muku account number ɗina ta cikin group in wata yayi ko ɗari biyu ne
da ke turo. In baku dashi an yafe miki. Masu son makaranta kuma zamu yi magana in sha Allah.
In akwai me abun cewa tace sai mu rufe taron da adda'a" Da ƙyar na yunƙura na tashi tsaye
sunai mun tsiyar duk shekara da nace saina haihu, wasu daga ciki sai jinjina mun suke yi.
Hakika na ji daɗin wannan taron, kuma zuchiyata tayi mun fari tamkar audiga. Kuma taron ya
haskamun wata hanya wacce ta zamto hanyar cikar burina. Allah ya sani ina da son karatu ku
abokan karatuna kun sani. Wannan buri nawa bai cika ba a baya nazo mahaifina ya turani gidan
aure domin neman aljannata da ɗanyen shekaruna sharab. Amman in sha Allah zan shiga
makaranta in yi yaƙi da jahilci ƴar sakandare ɗinnan in kammaleta sai in ci gaba da zuwa ta
muhammadiyya kuma. Sana'ar ma in sha Allah zan soma kamar sai da daddawa ko kanwa da
kuka. Madallah da abokan karatu irinku. Kamar yadda muka haɗu a ɗakin hotel ɗinnan Allah ya
haɗamu a Aljanna haka" Ɗan tafa mun su ka yi. Nan aka tsai da matsaya mai kyau mu da
bama karatu muke son ci gaba Habiba Bala ta bimu da dubu biyar biyar bayan kowa ya bada
kuɗin shi na wannan watan kenan. Ɗari biyar na zaro na danƙa mata. Kafin ta bimu da wannan
kuɗin tace mu samu islamiyya mu soma zuwa tukunna, ni da nake son in karashe sakandare
kuma tace zamu yi magana. Ledoji viva ta bi kowa dashi ciccike kai Habiba Bala tayi ƙoƙari.
Mun kai bayan azahar kafin muka gama, mun rufe taron da adda'a sai da mu kai sallar azahar,
muka ɓalle da hirar yaushe gamu, kuma aka shiga haramar komawa. Musamman ƴan nesa da
mazauna ƙauyen Bauchi. Da dukkan alamu babu mai kwana dan ƴan cikin. Garin ma kowacce
ta yafa mayafinta a ka.
"Wai kuna nufin har kowa zai tafi kenan. Halima Bawa, Shanono kuma tafiya zaku yi yau. Mai
makon ku bari sai gobe sai ku tafi, sai mu je gidana mu kwana ai, akwai waje fa. Ni kam har ga
Allah dama banyi niyar komawa yau ba sam, ni da so samu ne in kwana biyu ma zuchiyata ta
huta tukunna kafin in koma. Ni da da niyyar kwana biyu ma nazo kinga jakata fa. Halima Bawa muje mu kwana a gidan
Habiba Bala mana" Itama Halima Bawa bata ja ba da dukkan Alamu da shirin kwanan tazo,
kuma itama tamkar cikin damuwa take. Dukkanmu muka ɗunguma zuwa waje. A wajan ajjiye
motocin muka tsaya jiran Habiba Bala. Aisha Aliyu itama mota take ja ashe, ita da Karinatu Jibril
sai Habiba Bala. Mutane duk suka ɗuɗɗura a mota muka fice a tare bayan mun yi sallama da
juna. Zukata sun yi sanyi, kowa yaji daɗin ganin kowa. Sai da muka shisshiga gidajen su Fatima

a tsattsaye dai haka bayan mun gama saukesu mu kai sallama Habiba Bala ta nufi hanyar
gidanta dake bayan tsohuwar Airport.
Ni dai muna tafe na lula cikin tunani mai zurfin gaske. Hoton tsaraicin Hajiyayye yana yawan
dawo mun, dana tuno sai gabana ya faɗi naji tsigar jikina ya tashi. Haka ina hango wandon
Kaila yanda ya cika dan kawai yana waya da budurwa. Magidanci mai yara takwas, shine da irin
wannan aiki, mazanmu na hausawa sun ɗaura zuchiyoyinsu a

5 / 24