Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
wandunan ciki, da singileti, da shaddajinshi, da dai kaya da
dama. Tana gamawa ta koma cikin turakar ta rufo ƙofa. Sai na jiyo wani irin daddaɗan turaren
wuta na shigar mun hancina mai daɗin gaske" Habiba Bala ce ta fito tana sharce zufa. A kusa
dani ta zauna da ledar magunguna da ruwa. Tana zama yara suka shigo a guje harda Mustapha
yaron Sabira. Habiba Bala ta bisu da idanu tana Murmushi.
Kuje ku gaisa da ummanku Sani" Dauda na ƙurama idanu, babu kuzari sam a jikinshi da gani
yana cikin raɗaɗin ciwo, gashi bai saba da ƙannen nashi ba sam. Hawaye na soma zubarwa.
Habiba Bala ta dubeni tana riƙe da hannun Amina da Balaraba, cikin ƙasa da murya tace.
"Menene kuma Shanono?" Hannun Dauda na riƙo na juyar dashi, na zame mishi wandonshi
ƙasa. Salati Habiba Bala ta saka tana kallona.
"Me ya same shi, waye shi Shanono? Shine aka barshi a gida sai ya mutu. Jibi tsutsotsi fa
yanda suke fito mishi." Wani irin kukane ya turniƙeni mai tuƙuƙin gaske. Sabira da Hindatu sai
kallonmu suke yi, amman basa jin abinda muke cewa, kukana ne ya jawo hankalinsu garemu
ma. Habiba Bala ta ce ma yaran su je su yi wasa, sai da ta ga sun fice sannan ta dawo da
hankalinta gareni.
Ɗanane Habiba Bala. Dauda shine yarona na farko. Yana hannun matar ubanshi ne a shanono
fyaɗe akayi mishi. Rashin kuɗine yasa kika gammu zaune a gida. A gidan uban nashi ma an
rasa wacce zata kula mun dashi. Shine na ɗakko abuna, duk da nima a ɗofane nake a nan ɗin."
"Shine ba zaki kira ni ba? Na taimaki waɗanda ban san su ba balle ke Shanono. A gaskiya baki
kyauta ba. Zan tafi da Dauda asibitinmu za'ayi mai duk abinda ya dace. Ba dole sai kin yi ta
sunturin zuwa Bauchi ba. In Allah ya bashi lafiya sai in dawo miki dashi. Ki share hawayenki. Ni
kaina fa Shanono babu irin rayuwar da ban gani ba a baya." Ajjiyar zuchiya na shiga saukewa.
Duk wannan maganar da muke yi cikin ƙasa_ƙasa da murya mu ke yi, babu mai jin mu.
Magunguna ta dinga ɓallemun tana bani ina korawa da ruwa. Sabira ta dure mun tea mai zafi.
"Gashi ki sha Tani ki warware hanjinki"
Nagode sosai Sabira." Muna cikin haka sai ga Bilkisa ta fito daga ɗaki cikin kwalliyar shuɗiyar
atamfa, tayi kyan da ba'a buƙatar kwatanta ma masu bibiyar labarin. Tana ganina ta ɗan yi
dariya.
"Umman Sulaiman kin dawo ashe, ai banji dawowarki ba da na fito mun gaisa" Murmushi nayi
mata.
Ayya Bilkisa bamu daɗe da shigowa ba. Nagode" Gaggaisawa akayi baki ɗaya. Tayi shigewarta
turaka tana lanƙwasa.
"Ita wannan ɗawisuwar daga ina Shanono?"
Amaryar Kaila ce daya auro" Kai kawai ta girgaza bata ce komai ba ta leƙo ɗakina ta dawo.
"Mu je ɗaki ya bushe mu yi magana ni inason in kama hanya" Binta nayi zuwa cikin ɗakin
"Shanono ashe haka kike tabka ƙazanta. Ƙazanta taci uban na da ashe. Yaya ba zaki sha
wuyar zaman aure ba? Ɗaki sai ɗoyi yake bugawa, ke kan ki wari kike yi, haka yaran. Ni ina
ganin ai Kaila fa kamar yayi ƙoƙari da yake zaune dake a haka, kuma a haka yake ɗirka miki
ciki duk shekara sai kin jiye. Dubi katifunku duk yanda suka mace. In fa anason ɗakinnan ya
dena wari sai fa an siyar da katifunnan an sai wasu tukunna, suma sai an sa musu irin rigar
katifar nan irin wacce bata barin fitsari ya ratsa katifa Jibi jinin kuɗin cizo a ɗakin ki shanono ko
kunya ke ba kya ji dan Allah? Ba dole sai Kaila na kulaki ba zaki tsabtace yaranki, da ke kanki,
da muhallin ki ba. Wannan ƙazantar fa zata iya taɓa ƙwaƙwalwarki. Kuma ƙazanta zubar da
mutunci take yi, kuma raini dole ya shiga tsakaninki da kishiyoyi, maƙota, da ma miji. Kuka na
saka mata ni kaina bansan me yasa nake hakan ba. A ganina ba wani abu bane dan na dena
jin daɗin komai da kowa. Wa zai fahimci macen da ta auri mazaje biyar, kun tambayeni yaya
rayuwata ta kasance ne a sauran gidajen?. Duk da na san ban taso na ga iyayena a cikin gida
ba, balle har su koya mun gyaran jiki dana muhalli. A titi na taso na ga kaina, wasu garuruwan
muna da ɗakuna mai cike da tulin tsumma, wadu garuruwan a ƙasan gada muke rayuwa. Jina
nake bani da maraba da mahaukaciya, bana ɗaukar kaina a matsayin mace. Duk wannan
maganganun a cikin zuchiyata nake aiyanasu.
"Shanono ki dena kuka, in na fahimta a cikin deepretion kike wanda ke kan ki baki sani ba, baki
san kina ciki ba, baki san tsawon lokacin da kika kwashe a ciki ba. Abunda zan faɗa miki shine.
Ki tabbatar kin koma makaranta, arabi da boko. Akwai boko ta matan aure ai a garinnan ko?
Shine hanyar da zaki samar ma kan ki nutsuwa shanono" E akwai zan bincika ni ko zuwa gobe ne, tunda dai zaki tafi da Dauda. Shima islamiyyar zan
bincika ko ta su Sabira ne sai in shiga, duk da ma dai tasun da ɗan tsada.
"To shikenan, sana'a itama ya kamata ki soma Shanono, ki ji tausayin kan ki da ƙwaƙwalwarki,
da ma yaranki. wani abun rashin ilimine duk yake ja kiyi shi." Kuɗi ta zaro a jakarta masu yawa
ta saka mun akan cinyata.
"Ki nemi makaranta duk inda take ki soma zuwa. Kuma kar ki yi sake ki bari yara ko miji su
hana ki karatu. Sannan shawarar da zan baki shine, ki fita sha'anin maganar haihuwa haka. Ki
yi ƙirgen kwanaki kamar yadda na faɗa miki a baya, duk abinda ya shige miki duhu ki kira
wayata. Shanono so nake ki kama kan ki ki nutsa, ki fita harkar kowa a cikin gidannan, ki zauna
a gefe, shi kanshi kailan ki ba banza ajiyarshi, tunda yana da wasu matan ki matsa gefe ki zama
ƴar kallo. Ga wannan ku yi shawara da Sabira wacce sana'a zaki soma. Ta sake ajjiye mun
wasu kuɗin.
"Ni kam zan tafi, ina da aiki da yawa a asibiti, tiyata zan shiga lokacin da Sabira ta kira ni.
Tiyatar da ban shiga ba kenan. Sai abokin aikina ne ya shiga ɗakin tiyatar." Godiya marar adadi
na dinga rakarkatoma Habiba Bala, har bakin mota muka raka su ni da Sabira. Dauda yana
gaban mota. Suna tafiya sai ga Kaila da dillalai masu duba gida sun shigo. Mamakine ya kama
shi da ya ganni a gida. Rai ya ɗaure da mu ka haɗa idanu, har wata harara da ƙuta duk yayi
mun. Ɗakin shi ya leƙa ina jiyowa yana ce ma Bilkisa karta fito akwai maza masu ganin gida a
tsakar gidan. Ni ko haka su kaita wuce ni nono a waje ina ba jaririna. Wato dake ba sona Kaila
yake yi ba, babu batun kishina sam. Sai da suka gama kewaye gidan kana suka fita. Tabarma
Sabira ta shimfiɗamun a tsakar ɗakina, ina kwanciya wani wahaltaccen baccin gajiya ya sureni,
maganin da Habiba Bala ta bani harda mai sa bacci. Bani na farka ba sai la'asar. Wayata na jiyo
tana kuka a tsakar gida. Da sauri na fita dan in ɗauko. Ina fita su Hajiyayye suna shigowa an
sallamesu daga asibiti. Cirko_cirko mu ka yi a tsakar gidan dukkanmu daga ni har su. Cike da
kallon tuhuma Hajiyayye tace.
"Ki kashe mun Ɗan Amman har ƴan sanda su sako ki. Ubanki waye tukunna a garin Jos?"
Kusun uwa in na yarda me nake.............✍
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURENA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 15
*(Assalamu alaikum masoyana. Haƙiƙatan naji daɗin yanda kuke yaba rubutuna, da yanda nake
tafiyar da salon labaraina. Babu abunda zance daku sai kodiya. Yau na tashi sai wasu uziri suka
same ni, wanda bazai bani zarafin yin typing akan kari ba. Sai na yanke hukuncin sanar da
masu bibiyar rubutuna cewar su yi haƙuri ina da uziri, ba zasu samu jina ba har sai na samu
al'amura sun warware mun. Allah cikin ikonshi jim kaɗan da yin wannan maganar, saina soma
samun kiraye_kirayen waya daga masoyana. Na kuma dinga cin karo da saƙonninsu wanda in
na karanta wani ban isa na karanta wani ba. Duk dai ƙorafinsu shine, in taimaka zasu yi kewar
Shanono. Wata tace tana cikin ɗakin jarabawa amman hankalinta na kan wayarta. Duk wanda
zai yi ma rubutunka haka ai ba ƙaramin masoyinka bane. Ummu nabeeha, da su Khadija
Amarya, Maman Amal, Khadija mai doki, Salma musa, Mamagee, da duk members na cikin
zauren NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. duk sun tashi hankulansu. To ga page 15
na baku. Amman zai iya kaini mako guda kafin in gama uzirin dake gaba. In sha Allah zan dawo
da zafi. Nagode)*
SHANONO
Bance da Hajiyayye komai ba, sai buyagi take yi. Nazo nayi wucewata ko sake kallonta ban yi
ba. Ina jiyo Yayarsu tana ƙunduma manyan zagi a tsakar gidan. Sabira ce ta shigo ɗakina da
sallama, hannunta riƙe da kwanon abinci. Wayata ce ta shiga ruri a karo na biyu. Yaya Karime
ce take kirana, dagawa nayi tare da kara wayar a kunnena. Yaya Karime ina wuni?" Daga cikin wayar akace.
"Inno ce Tani. Yaya kun isa gida lafiya dai ko?"
Lafiya lau Inno yaya biki?" Dariya tayi tace.
"Ƴan uwanki sun so ganin ki. Barinma ƙawarki Shafa, yaranta goma fa yanzu, jin labarin kin
shigo Shanono sai gata a gidan biki. Yaya Kaila ya yarda da zaman Dauda ba wata matsala
ko?" Tsintar kaina nayi da cewa.
E ya yarda Inno." Baki ta washe tace.
"To barka ni dama dalilin da yasa na kira inji kenan. in na dawo zan zo in ɗaukeshi. Sai mu
yawata dashi muna bara ina nuna ma mutane ciwon nashi. Ba karamin kuɗi zamu samu ba,
kinga muma ma samu a jikinshi. In muka tattare kan kuɗin ko asibitin miya barkatai ai sai a
kaishi su yi mishi aikin ko Tani?" Idanu na lumshe na tuno lokacin da muka sauka a Bamaina
dake jihar jigawa, Inno ta ɗaure mun ƙafata, ta samo jini a kwata ta kwara mun a kafata, haka
mu ka fita mu kaita neman kuɗi a haka. Na sha wuya sosai, Amman mun samu kuɗi sosai.
Watanmu biyar kullum sai Inno tayi mun haka
A'a Inno ai Dauda wata ƙawata da mu kai karatu a Bauchi ta ɗauki nauyin biyan kuɗin aikin
nashi. Yanzu haka ma suna Bauchi tare." Inno ta yi sanyi da murya, a maimakon taji daɗi, sai
ma ta nuna irin ita tafison ta yawata da Dauda, sabida ba karamin kuɗi zata samu ba. Yaya
Karime ce ta karɓi wayarta muka gaisa. Daga ƙarshe su kai mun sallama tare da kashe
wayarsu.
"Tani ga abinci maza kici. Wai Hauwa tana Shanono ne a wajan su Inno?"
Hmm tana can, sai sun dawo zasu kawo mun ita. Nagode da hidima Sabira " farfesun kan
saniya ta zuba mun da farar shinkafa. Ai kuwa naci sosai, ta bani magungunana na sha suma.
Sannan nace mata.
Habiba Bala ta bani kuɗi in koma makarantar islamiyya, da boko. Kuma nima dama na riga na
ƙuduri niyyar hakan. Dama jira nake in haihu, zaman rashin karatu bazai fissheni ba Sabira.
Kinga kuɗin" Ƙasan fulon da nake kwance na bankaɗa na ciro kuɗin, na ba Sabira a hannunta.
Kinga kuɗin ko. Tace abinda ya ragu sai in soma ƴar sana'a domin dogaro da kai. Ke meye
shawararki akan hakan? Wacce makaranta kike ganin ya dace in shiga?" Sabira dake riƙe da
kuɗin a hannunta tana jujjuyasu tace.
"To tunda naga kuɗin da yawa. Inaga a shawarce ki shiga islamiyyar matan aure *UMMAHAT*
Ta cikin al'iman. Kinga Mrs Bukhari ma makarantar tayi, nima gashi ita nake zuwa. Jumma'a,
asabar, lahadi ne ranakun zuwan, kinga bazai taɓa makarantar bokonki ba. Kuma zaki ji larabci
sosai dan ba'a Hausa, ( Allah sarki malama musriyya, malama Hajara, malama Zarah, mun sha
larabci) zaki haɗu da mata wayayyu ƴan ƙarya. Nima gaskiya makarantar ta sake gogar dani na
sake fahimtar yanda zan mallake Baban Mustapha. Bokon kuma zamu bincika wata makarantar
matan aure dake cikin shaƙura, can unguwar rogo ƴan kwaba. Akwai wata makarantar matan
aure masu jajayen wando sai mu bincika. Maganar islamiyya kuma zan sa Baban Mustapha yai
ma abokinshi magana suna ɗarasawa da munir director ɗin makarantar asamu a saki a aji
ɗaya. Kinga in kika gama makarantar nan har zuwa aji shida? To zaki samu takaddar zaria,
zaria suke kiran takaddar, da wannan takaddar zaki iya samu admission a jami'a kai tsaye in
islamic studys kike son karanta. Mu kinga saura shekara ɗaya mu gama." Ajjiyar zuchiya na
sauke nace.
To sabira Nagode sosai. Yanzu ni gobennan nake son mu je shaƙuran mu ji yaya za'ayi in samu
makarantar nan. Tunda dai kuɗin sun samu, ba'a bori da sanyin jiki."
"Ke zaki iya fita ne da wannan kumburarriyar fuskar Tani?" Da sauri nace.
Ai ko yanzu kika ce mu je, miƙewa zanyi kawai" Dariya tayi tace.
"Goben sai mu je sassafe in Allah ya kaimu. Batun sana'a kuma mu cire sati guda mu yi tunani
tukunna. Dubawa zamu yi muga menene a cikin anguwarnan yake da wuyar samu,wanda har
sai mun dangana da titi, koma kasuwar ƴan tifa ( new market)?
Kayan miya, musamman attarihu da albasa" Na ce mata.
"To kinga shikenan sai ki soma zuwa farar gada kina sarosu, shikenan ma muma mun huta.
Kuma zaki sha ciniki sosai."
"Ɗazu da ki ka yi bacci ai gida na shiga Baban Mustapha ya dawo. Shine yake faɗa mun jiya ya
ba Baban Sulaiman aron million biyu, yana son zai ƙareshi abubbuwan da bai yi ba a sabon
gidanku. Wai yana son nan da sati ɗaya ku koma sabon gida. Sabida wai Baban Bilkisa ya
kirashi wai ita Bilkisan ta yi ma mahaifinta ƙorafin ita wannan gidan ba zata iya rayuwa a cikin
shi ba. Shine na ba Baban Mustapha shawarar tunda Baban Sulaiman ɗin siyar da nan gidan
da kuke zaiyi, to ya siya kawai tunda dama zai siyar ne dan ya biya shi kuɗinshi. Na taya ki
murnar zaki rabu da wannan akurkin, tunda kince a sabon gidan yara ma suna da ɗakinsu.
Amman Tani zan yi rashinki da yaran baki ɗaya. Sauƙinta ma zaki soma zuwa makarantar mu"
Ni dai kai kawai na gyaɗa ma Sabira, tamkar ya jin ƙosai na kasance wato a rayuwar Kaila. Ada
har sai na kori Kaila yake iya zuwa gareji. Ni tunda nake aure, ban taɓa haɗuwa da masoyi irin
Kaila ba. Amman jibi yanda komai ya juya, duk a sanadiyyar shigowar Hajiyayye rayuwarmu.
Yawu na haɗiye kawai. Mun jima muna tattaunawa ni da Sabira. Na ce mata ta riƙe wannan
kuɗin a hannunta tukunna. Sai da aka fito sallar magriba ta tafi. Bayan ta shigo mun da katifuna.
Bata jima da fita ba yaran suka shigo. Nan suka dame ni da haya_haya. Bayan isha sai ga Kaila
bayan har yaran sun soma bacci. Idanu ya ƙura mun kawai, yana tsaye ƙerere a tsakiyar
kwanyata.
"Shanono kenan. Yaya akayi kika dawo gida, kuma wa yayi belinki?"
Ikon Allah" Iyakar abinda nace dashi kenan.
"Shi yaron da kika ɗakko a Shanono kin fitar mun dashi ne ko kuwa yana nan? In kuwa yana
nan wallahi daga ke har shi baku isa kun kwana mun a gidaba. Dan bazan iya riƙe agola ba.
Kema da kike zaune a gidannan dan yarane fa, amman wallahi da baki isa amsa sunan matar
Kaila ba." Kayi haƙuri, Dauda baya nan. Amma zai dawo. Kayi ma Allah kaila ka barni in rayu da Dauda.
Yaron yana cikin damuwane. Fyaɗe akayi mishi kuma acan gidan Baban nashi an rasa wanda
zai iya kulawa dashi ne. Yaron yana buƙatata. Dan Allah Kaila. Ƙur yayi mun da idanu yace.
"Hiye ba shakka Shanono. Acan gidan uban nashi an kasa riƙeshi sai ni ne zan riƙe shi ko? To
sai ki zaɓa ai ko riƙe yaronki da kika haifa a Shanono. Ko riƙe su Sani, zaɓi ya rage gareki.
Shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Bani yaro in mishi huɗuba ni, wani irin tunani irin na jahilan
ƙauye" Jiki a sanyaya na miƙo mishi yaronshi, ina tsugunne a wajan ko tausayina zai taɓa
zuchiyarshi. Huɗuba yai ma yaron ya miƙo mun yace.
"Na sama yaro suna Salis, sunan mahaifin Bilkisa. Kuma bana buƙatar wani taron suna, in sun
zo ma nan