Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 24

36K to 39K   out of 70.8K words

iya ganin gabana, kaina naji yayi wani gingiringin. Wata ma'aikaciyar jinyace ta
fito daga cikin ɗakin da aka shiga da Dauda. Ina gani duk suka rufu kanta, ni ko ina zaune ina
haki, dishi_dishi ma nake ganinta.
"Wannan yaron bashi da iyayene, ko dai tsintarshi kuka yi. Ya yaro kamar wannan za'a bari ta
kashinshi ta zazzage har ta lalace haka? Ina mahaifiyarshi take?" Take Shehulle ya nuno ni.
Wani kallon tsana wannan ma'aikaciyar jinya tai mun tace.
"Ke kuwa baiwar Allah kiji tsoron Allah. Shin a matsayinki na uwa, har kin mance da rainon ciki
da lauwaye_laulayanshi, shin bakiyi ƙwannafi da amai bane, ina kika mance da zafin fitar kan
yaro daga jikin uwa, ina kika bar buɗuwar da kwankwaso yakeyi yaro ya faɗo. Ga raino, ga
shayarwa? Kina ma yaronnan wanka ace har baki san halin da yake ciki ba, har sai da ya soma
tsutsa da ɗiwa tukunna? Anya kece kika haifeshi kuwa?" Duk illahirin jikina babu inda baya
rawa. Maganganun ma'aikaciyar jinyarnan sai huda mun tsoka yake yi, take tsigar jikina ta
soma tashi yar_yar_yar."
"A'a kar ki zargi mahaifiyarshi. Domin tun yana tsumman jinjirantaka ubanshi ya kwaceshi. A
hannun matar uba yake. Ita ta hofantar da rayuwarshi. Dan Allah yarinya yanzu meye abinyi,
wanne taimako ya dace abashi?" Yaya Karime ke magana cikin taushin murya. Dangin Narani
kuwa kamar ruwa ya cinyesu haka suka dawo. "Aiki za'ayi mishi. Amman aikin zai lashe kuɗi masu yawa. Shawarar da zan baku shine ayi
gaggawar kaishi cikin gari, domin sun fimu ƙwararrun likitoci, da kayan aiki. Muna bashi agajin
gaggawa dai a yanzu. Ke kuma baiwar Allah kiyi haƙuri, wallahi na zaci sakaci ne irin namu.
Ashe muguntace irin ta iyayen riƙo. Amman duk wanda yai ma yaronnan wannan aika_aikan ya
kamata lallai ku haɗashi da hukuma" Nan aka shiga ciku_cikun yanda zamu kai Dauda asibitin
Birni. Baffa da Inno tuni sunji labari. Inno da Kawu Junaidu har sun tawo. Shehulle kuma ya fita
samo mota. Ranga_ranga aka sa Dauda a mota, yana jikina sai ajjiyar zuchiya yake yi, ni kuma
na rungumeshi kamar jariri. Hauwa tana bayan Yaya Karime. Da Yaya Use zamu, sai Shehulle.
Su kuma su Inno banda su. Ta tagar mota Inno ta zuro kanta, ta danƙama Yaya Use dubu huɗu
tace.

"Gashi in ji Baffanku yace in baki Use. Sai munzo. Ke kuma Tani kar ki tashi hankalinki kinga
juna gareki. Naranin yana ma cikin garin Kanon yace zaku haɗu a asibiti." Ido na lumshe kawai,
idona yayi jawur dashi nama rasa abinda ke mun daɗi. Ga marata sai faman ɗaurewa take yi.
Haka muka kama hanyar Kano, baka jin ko tari a cikin motar, sai ajjiyar zuchiya da nake faman
saukewa a kufi_a kufi. A farfajiyar asibitin Murtala muka haɗu da Narani yana jiranmu. Dauda
ya zare a hannuna suka yi ciki shi da Shehulle. Mu kuma muna biye dasu a baya. Wallahi har
nafi Yaya Use dauriya, dan tunda muka tawo take rera kuka mai sauti. Cikin wani dogon falo
muka shiga, a lokacin Narani sun shige ɗakin jinya shi da wani ma'aikacin jinya, Shehulle da
halama dakatar dashi sukayi.
"Shehu cewa su kayi ka tsaya anan?" Cewar Yaya Use, Shehulle yace.
"E Narani kawai suka ba damar shiga. Dauda ya faɗi wanda yai mishi wannan aikin?" Banza
nayi dashi dan kowa haushinshi nake ji a gidansu Shehulle. Dan su su kai ruwa da tsaki wajan
banƙaremun hannuna a ƙwace Dauda a yayin da akeson raba uwa da ɗanta.
"Ya faɗa Shehu. Amman baza mu yadda ba, dole hukuma tayi aikinta. Duk da dai mu marasa
ƙarfine, amman ya kamata ace ko yayane mun ƙwato ma yaron hakkinshi." Kai Shehu ya jinjina
yace.
"Me sunan wanda yayi mishi hakan wai? Mu bamu san komai ba, kullum kuma zaki ga Dauda
yana baccinshi a tsakar gida, ko a ɗakin iya." Cikin jin haushi nace.
Alh Zangina ne wai yake yi mishi, haka yace" Ido Shehu ya zare yace.
"Alh Zangina fa? Wallahi zai aikata dan yana shiga da yara gidan gonarshi cike da mota. Kuma
ko ɓatan ɗan liman an yi zargin dasa hannunshi. An tasarma maganar, ana cewa hukuma zata
yi aiki. Wallahi Alh Zangina yabi dare yaje ya samu malam Liman ya cika shi da barazana.
Maganar bata sake tashi ba. a wata ruwayar ma cewa akayi yace in yayi magana sai ya ɓatar
dashi. Ku rufama kan ku asiri damu kanmu maganar nan ta mutu kawai. Karma ku sake kama
sunan Alh Zangina wallahi, in dai kuna son kan ku da arziki" Mun tsorata sosai da jin wannan
labarin. Haƙiƙa nasan mai ƙarfi ma sai ya shirya zai iya tunkarar Alh Zangina da irin wannan
maganar. Dan shahararren mai kuɗine sosai, yana da gonakai da wani irin wawakeken gidan
gona. Abun dubawan Alh Zangina babu wanda yasan mutumin inane daga kuma wanne nahiya
yake. Kuka na fashe dashi nace.
Na barshi da faɗuwar rana da tsaiwarta. Allah kana ganin abinda wannan bawa naka yaima
Dauda, mala'ikun Allah ku shaida, Allah ya saka ma Dauda, ubangiji Allah ka tagaiyara Alh
Zangina ka haɗashi da jafa'in duniya kafin ya tarar dana ƙiyama" Yaya Use ma kuka take yi
sosai. Muna cikin wannan tashin hankali Narani ya fito a gaggauce ya nufomu sai yarfe zufa
yake yi.
"Yaya ake ciki Narani?"
"Wallahi Use a taƙaice dai sun bamu gado. Jibi za'ayi mishi aiki, kuma sunce bama zasu
taɓashi ba har sai mun biya kuɗin aikin. Amman suna maganane akan wasu mahaukatan kuɗin
da ni banma taɓa riƙe irinsu a rayuwata ba. Ni harma nace su sallamemu mu koma gida sai ayi
na hausa mu jaraba ko Allah zai sa a dace." Nunfarfashi na shiga ja da saukewa. Yanzu
Daudan da yake buƙatar taimako shi za'a mayar gida? Ya Ubangiji Allah ka kawo mana agaji"
Yaya Use tace.
"Har nawa ne kuɗin haka Narani da zaka ce a komar da yaro gida? Shakirar tashi fa naga tayi
fata fata har ɗiwa take fitarwa, ya zaka ce haka" A rainace cikin ɗiban albarka Narani ya soma

magana da Yaya Use.
"Magana suke akan sai an sauke duɓu ɗari biyu da hamshin kwatan miliyan kafin ma a taɓashi,
banda kuɗin gado da magani. Lissafin rabin miliyan suke yi mini. Dani daku nayi imana har mu
mutu hanyar inda kuɗaɗennan suke bama zamu gansu ba wallahi. Yaro dai ɗanane gida zan
koma dashi ayi mishi na gargajiya. Ni dama tun farko da aka sanar dani gaku a hanyar asibitin
Birni, sai da nace ma a sanar muku ku koma. Kai Shehulle shiga ka fito da yaron mu koma
gida." Fuu Shehulle ya shige ɗakin da aka shigar da Dauda. Sai gashi saɓe dashi a wuyanshi.
"Ka saukeshi ɗan ƙwal uba ai yana iya tafiya. Ba sai da aka nemo shi a waje ba ma" Shehulle
da jin haka ya dire Dauda a ƙasa. Ni kuwa sai tsiyayar ruwan hawaye kawai nake yi. Na kasa
cewa komai, Yaya Use ma ta kasa magana. Fuu suka wuce suka barmu a tsaye. Dauda sai
waigena yake yi, shima kukan yake yi. Sai da na dena ganinsu sannan na sake fashewa da
wani irin kuka mai kama da fitar rai. Duk waɗanda suka zo wucewa sai sun tsaya sun tambaya
lafiya ko rasuwa akayi mana ne? Da "E" Yaya Use take amsa musu.
"Tani daure ki lallaɓa mu koma Shanono. Kinga mu kanmu bamu da kuɗin da zamu iya lura da
Dauda ko da da maganin gargajiyanne, ballantana wannan maɗuɗun kuɗin da lukitoci suka
yanko. Mu yi ta mishi adda'a, zo mu tafi" Da jan ƙafa na bar asibitin. Muna cikin motar komawa
Shanono Baffa yayo kiran wayar Yaya Use " "Use Yaya kun isa asibitin dai ko, yaya jikin yaron?" Cewar Baffa da yake magana ihu ihu.
Ajjiyar zuchiya Yaya Use tayi tace.
"E Baffa, amman gamu a hanyar komowa Shanonon ma." Baffa yace.
"Dashi Daudan ko an kwantarku ne?"
"Dashi zamu dawo, sai mun dawo zaka ji komai"
Gidan su Baffa muka wuce kai tsaye, a lokacin naƙuda ta kawo kai, ba shiri su Goggo mai riga
suka rufeni a ɗakin Goggo Marka. Nan na shiga sabuwar azabar naƙuda. Duk zafi irin na
naƙuda, da fita hayyaci da akeyi, sai wannan karon yazo mun da sauƙi. Dan raɗaɗin dake cinye
ƙasan zuchiyarta yafi naƙudarnan zafi. Cikin gumurzun awa uku na suntulo ɗana namiji ƙato
dashi lafiyayye. Cikin da babu awo bare shan ƙwayar bature ta masu ciki. Amman cikin
hukuncin Allah gashi na sauka lafiya, shima yaron yana cikin ƙoshin lafiya, dan ya karaɗe gidan
da inya_inya. Yara_yaran gidan sai murna suke an siyo musu jariri wai. Ni kuwa sai jinyar
zuchiyata nake yi.....✍


https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 11





https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm

Bayan nayo wanka na dawo. Na tarar da Goggo Marka tana gasama Jariri cibi, an sa mishi
kayan jirajirai yayi kyau abinshi, yana duƙunƙune a cikin zanina. Ina zama Inno ta shigo da
ɗumamen tuwo da kunun tsamiya.
"Shanono maza ki yayyanki tuwonnan da zafi_zafi. Ni kuma bari in kira Kaila in sanar dashi
haihuwar." Dubanta nayi bayan na tusa tuwon a gaba nace.
Inno inason inna gama cin tuwon in koma can gidansu wannan yaron dan in ji me ake ciki dan
Allah Inno kar ki hanani."
"Da ɗanyan jiki zaki fita Tani, ko Use da take can kina nufin kin fita iyawa, Karime ma tana can
gidan tama riga Use yin gaba." Goggo Mai riga ce tace.
"A'a Inno kada mu tauyeta in ta gama ta goya jaririnta taje ɗin tunda Allah ya sauketa lafiya.
Hankalinta ba kwanciya zaiyi ba muddin bata je taga yaron ba. Ke kuma Tani batun shigar da
ƙarar Alh Zangina wallahi karma ku kuskura a ta da zancan. A burne wannan maganar a cikin
gida, wanda yaji ya riga da yaji, waɗanda basu ji ba kuma shikenan , kuyi Allah ya isa kawai" Ni
dai sanyi naji da har suka fahimceni kuma basu hanani fita ba. Batun shigar da ƙara tuni mun
tsorata har mun haƙura .A gurguje na cinye tuwon na sha kunun rabi. Goggo Marka ta goya
mun baƙon duniya ta lulluɓemun shi da zani biyu lub_lub. Sallama nayi musu zan fita, ina jiyo
sanda Inno take waya da Kaila tana sanar dashi an samu ƙaruwa, jibi ma zan tarkato in komo.
Ni dai nayi ficewata, ina tafe Kaila ya kirawo wayata, sai da na samu gefe na rakuɓe sannan na
amsa wayar.
Assalamu alaikum Abban Sulaiman barka da yamma an wuni lafiya?" A daƙile yace.
"Lafiya lau. Yanzu Inno take faɗamin kin haihu, Allah ya raya, dan haka gobe sai ki kamo hanya
ki tawo gida ki nutsu." Da sauri na tari numfashinshi dan naji yana shirin kashe wayarshi.
Abban Sulaiman dan Allah ka barni zuwa jibi kaji? Wallahi jibi zan dawo, jikin nawa bashi da
ƙwari. Ne ina gudun yin tafiya mai nisa." Katseni yayi da cewa.
"Ko kuma baki gajiya da kallon tsohon mijinki wannan baƙauyen ɗan uwanki baƙauyiya ba ko,
ko so kike ki goma gidan tsohon mijinki? Ai in hakan kikeso yanzu sai in rubuto miki takaddarki
ta waya kinga ba ma sai kin dawo ba ko? Sai dai in zo in karɓi ɗana" Ƙit ya datse wayarshi.
Zuchiyata ta shiga harbawa da sauri, tarihi na shirin maimaita kanshi. Da ƙyar na saisaita kaina
naci gaba da lafiya. Ina shiga cikin gidansu Dauda na tarar ana rikici ko wacce daga cikin matan
gidan sunce babu wanda zai iya riƙe Dauda sabida wari yake yi, kowa yace ba za'a shigar mishi
da yaron ɗakinshi ba. Yaya Use da Yaya Karime sai basu baki suke yi, amman kowa yaƙi, babu
ma wanda yasan na shigo sai jiyo muryarta suka yi cikin sanyi ina cewa
In ba'a samu wacce zata riƙe Dauda ba, ina ganin mahaifiyarshi ita tafi cancanta ta kula da
abinta. Idan da Dauda zai narke ya zama tsitsotsi ni inason yarona. Narani na roƙeka a karo na
barkatai ka bani yarona, ko shari'a ta mallaka mun Dauda. Tunda yaronnan bashi da lafiya a

bani kayana" Kowa na tsakar gidan suka zuba mun idanu. Yaya Use da tasan ni kaina a dofane
nake a gidan Kaila tace.
"Baki da hankaline Tani, in kika ɗauki Dauda a cikin irin wannan halin kiyi yaya dashi, kina da
kuɗin da zaki yi mishi maganine ko yaya, sannan kin tambayi mijinki yace miki zai iya riƙe agola
ne?" Yawu na haɗiye nasan tabbas Kaila bazai yarda Dauda ya zauna a gidanshi dindindin ba.
Amman a matsayina na uwa ina ganin ban kyauta ma yaron ba in na barshi a cikin irin wannan
halin na ciwo. Gashi da dukkan halamu inda za'a barshi ya zauna ai mishi jinyar ma babu. Gani
nake kamar in na barshi mutuwa zaiyi, kuma alhakin mutuwarshi gani nake kamar a kaina zai
rayata, tunda nice uwarshi, kuma hausawa sunce Inna nafi uba ko da uban sarkine"
"Can dasu gada zomo ya jiyo kiɗan farauta. Gara ma ka bata ɗanta taje ta kula dashi. Dan ba
mahaukaciya bace ta yayeni da zan shigar da Dauda ɗakina yana tsaye yana ɓirɓishin tsutsotsi,
ɗiwa na gudana" Cewar Ta maulidi kenan. Tana magana tana fari da idanuwa. Iya mai Fura
tace. "Ni gashi ba ƙarfi ba balle ince ni a bani. Nima kula dani akeyi" Shi kuwa gogan duk wannan
maganar bai ce komai ba, yana tsaye sai hunhuna yake yi. Na tuno ranar da aka ƙwace Dauda
a hannuna yana tsumman goyo a wannan tsakar gidan. Yau gamu a tsakar gidan dai ina shirin
karɓar ɗana bayan tarbiyarshi ta samu tawaya ga halin jinya da yake ciki a sakamakon rashin
mahaifiyarshi a kusa. Ire_ iren waɗannan dalilinne ke sa iyaye su kasance ma yaransu a
matsayin madoraga, ko in ce kendir mai ƙone kanshi dan ya haske wasu. Cikin buyagi Narani
ya finciko Dauda ya dire shi a gaban Yaya Use yace.
"Gashi nan ku je dashi, tunda taji zata zame mai biyu a ɗaya ( 2 in 1) Amman ta sani muddin
tasa ƙafa ta fita da Dauda daga cikin ahalinshi, to yafita kenan har abada. In Dauda ya
gwamutsa sunanshi da sunana ko inkiyar ahalina Allah ya isa ban yafe ba. Aurenki in banda
bala'i babu abinda ya haifarmun mai farar ƙafa kawai, tunda na haifi Dauda asarori su kai ta
bibiyar rayuwata kuje ko na huta" Hannun Dauda na kama a raunace shi kuma kuka ya fashe
dashi, daga ni har Yaya Use kuka muke yi. Yaya Karime me ce idanunta a soye, sai mamakin
Narani da irin hukuncin daya zartar mai zafi take yi. Ni kuwa ɗana na riƙe nace.
Tawo mu tafi Dauda in sha Allah ni Tani Naroro Shanono zan tsaya ma a rayuwarka, zan zame
ma tsayayyar uwa." Juyawa muka yi zamu fita, idanuna ya rufe bana ji bana gani."
"Tani ki bar yaronnan a gidan mahaifinshi ina jiye miki kar Dauda ya zama sanadin mutuwar
aurenki. Kinsan furucin da Baffa yayi. Kaila bazai yarda ya riƙe Dauda ba" Cewar Yaya Use da
take ƙoƙarin farkar dani, dan a tunaninta na saki layi. Ni kaina zuchiyata cike take tab cikin
taraddadin me kaje kaxo. Sai dai ina roƙon Allah yai mun mafita ya kareni daga sharrin Kaila"
Dauda yace.
"Iyata dan Allah kar ki barni, ni zan biki." Murmushi nayi na share hawayena, wani irin ƙarfin
guiwane ya zo mun. Fuu na fice a cikin gidan riƙe da Dauda a hannun dama na. Ban nufi gida
ba. Wajen maganin gargajiya na nufa, ban ko bi ta kan su Yaya Use ba. Bayan na sa Dauda a
layi, sai da na keɓe kaina na ragema zuchiyata nauyi. Nayi kuka kamar bazan dena ba. Sai da
nayi ma'ishina sannan na fito daga ciyayin dana ɓuya na dawo kan layi. Sai wajajen magriba
muka samu shiga ɗakin maganin. Cikin ikon Allah jaririn dake bayana tunda na goyashi yake
bacci, sai dai yana ɗan motsi lokaci zuwa lokaci. Malam Mamuda Maƙeri ya zame ma Dauda
wandonshi ya duddubashi. Sai toshe hancinshi yake yi da tsumma. Bayan ya gama dubashi ya
mayar mishi da wandon nashi.

"Ciwonshi mai girmane kuma yana buƙatar kuɗi da jajircewa wajan bin ƙa'idar shan magani.
Zan baku na sha da shafawa kamar na kimanin wata ɗaya. In maganin ya ƙare sai ku dawo."
Har ƙasa na zube ina godiya, cikin rauni nace.
Malam meye abun sadaka to?" Murmushi yayi yace.
"Hala yau shine karonki na farko na zuwa karɓar magani ko?" Tsurewa nayi, cikin dibibicewa
nace.
E hakane, yau ne ranar farko Malam "
"To shi yasa. Ai ko ƙwandala bana karɓa har sai marar lafiya ya gama shan magani, in ya
warke sai in yanka abinda za'a bani. In kuma bai samu waraka ba bana cin sisin kobo. Amman
sau ɗaya na taɓa bada magani ba'a samu waraka ba. Shima ajaline ya cin mishi. Shekarata
hamsin ina aikin ceto" Wani sanyi naji a raina sosai. Godiya nayi mishi na fito. Muna tafe
raɓe_raɓe da Dauda, duk inda muka wuce sai wari buu, ga kudade sai bibiyarmu suke yi.
Baƙon duniya sai lokacin ya saki wani irin kuka mai zafi, inaji yai ta canyarawa. Abun hawa
muka hau muka nufi gida. A ƙofar gida naga su Inno harda Baffa sun yi cirko_cirko. Yaya Use
tana hangoni tace.
"Baffa ai ga Tani nan zuwa ita da Daudan" Ina isowa Baffa ya ɗaga sandarshi ya rabɗamun ita
a goshina, ji kake gab. Take wajan ya fashe jini ya soma wanke mun fuskata, jini har cikin
ƙwayar idandunana. Kuka na fashe dashi kawai, ina jiran me Baffa zaice. Cikin ɗaga murya
yace." "Wallahi muddin ki kai sake akan Dauda auranki ya mutu a karo na biyar. Kwarankwatsa

13 / 24