Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 24

9K to 12K   out of 70.8K words

Hindatu yace.
"Yaya Tani Allah dai yasa lafiya ba auren naki bane ya sake mutuwa a karo na barkatai?" Naji
zafi da ciwon maganar Amadudu amman na riga na san mazauna Akwanga, Lafiya, da makurɗi
basu iya tauna zance ba, kamar fitan zawo suke Magana. Ban kai da bashi amsa ba Hindatu ta
labarta mai Abunda yake faruwa. Kayana naci gaba da shigarwa cikin ɗakin. Katifata na
shinfiɗa a ƙasa, katifar yara kuma na jingineta daga bango ɗaya. Buhunhunan kayanmu kuma
na lodasu lungun dake ɗan gefen katifata babu laifi filin tsakar ɗakin ya ishemi. Amman kenan
a haka zamu dinga gwamutsuwa dani da yara a ɗaki ɗaya, taya hankalina zai kwanta gani ga
yarana a cakuɗe a ɗaki ɗaya. Irin wannan sakaiyar Kaila zaimun babu komai. Sai magriba na
gama suyan naman laiyannan. A take na raba na fitarma da kowa nashi. Na ba Hajiyayye nata
dana Yariman nata nace ta ajjiye mishi, na ƙullama ƴarta a leda kamar yadda na ƙullawa su
Sulaiman, na miƙama Hindatu nasu nayi shigewata ɗaki. Ina zaune ina shan shayi da nama na
jiyo muryar kawata tana tambayar bana gidanne. Ina jin Hajiyayye tana faɗa mata cewar.
"Ta koma ɗakin zaure Aure mai gidan zaiyi zai sa amaryarshi a nan ɗakin" muryarta fes cikin
nishaɗi dama nasan wannan rashin darajar da Kaila yai mun dole zai faranta mata. Da sallama
maman Zuhura ta shigo ɗakin da nake, taci ado irin na asalin mata gaske waɗanda maza suka
amshesu har suka samu yardarsu. "Tani kece haka a cikin wannan ɗakin mai kama da akurki?" Murmushi nayi mata kawai. Waje
ta samu ta zauna, shayi na zuba mata, na miƙo mata nama leda ɗaya.
Bismillah jiya kika ce zaki shigo baki shigo ba, bismillah zauna a bakin katifa mana" Zama tayi
a sanyaye.
"Tani kuma kin yarda kin amince Kaila ya fitar dake a ɗakin ki kina uwar gidanshi yasa amarya
a ɗakin ki? Ya kasa bari kici albarkacin yara ma, bacin in ya mutu a halin yanzu sai dai a
tsakurama matanshi da sauran yaran wani ɗan abu. Ai kinci gidan taya zaki rayu a irin wannan
ɗakin ke da yara? Me yasa ba zakiy tsaiwar daka wajan ganin kin kwaci ƴancin kan ki ba, bari
kiji iyayenmu bafa zasu goyi bayanki su barki ki ƙwaci ƴancinki ba ma, balle kiyi tunanin su da
kansu su ƙwatar miki ƴancinki. Ya da jininki a jiki zaki zauna baƙin ciki Kaila dana kishiya ya
halakaki? Yanzu fa Hajiyayye fa cikin farin ciki take faɗamun abunda ya faru. Shigowa nayi na
samu suna gulma da facalarki fa. Kema Tani ƙazantarki tayi yawa, dubi jikin ki fa, ji nono yanda
ya ɓata miki riga, ko rigar mama bakya sawa, kullum ke kenan cikin riga daban zani daban. Ko
kitson sallah ma baki samu yi ba, kin kama ƙafarki data yara kin muku baƙin lalle wanda ake
sama gishirin lalle. Wallahi in baki gyara ba, ke ma fa ba zaki ga da kyau ba. Sannan tunda kun
dawo ɗakinnan kuɗin cizo ku dena kasheshi a bango dan Allah, ki ke gyara jikin ki ko kema zaki
samu iska mai kyau" Ajjiyar zuchiya na sauke cikin nauyin ƙirji nace.
"Sabira bari in faɗa miki na jima da tsanar gidannan da mai gidan baki ɗaya, bani da kuzarin
iya gyaran jikina, kina gani kullum zaki ganni da goyo da ciki, ni fa sai in yi wata ban kama nera
biyar ma tawa ba, miji baya yi da kai, kowa ma haka ni yaya akeso in yi ne. amman yaya zanyi

ne da rayuwata Aure na huɗu ne suka mutu wannan shine na biyar. Iyayena basu da wani burin
daya wuce suga ina zaune a ƙarƙashin inuwar aure. Sabira dukka wannan aurarrakin da nayi
suka mutu. Mahaifina ya ɗaura alhakin mutuwarsu a kaina. Gani suke rashin haƙuri ne, da kai
mazajen bango yasa duk aka koroni. Dauda dana bari a Shanono tunda na bar Shanono ban
sake sashi a idanuna ba Sabira. Inno dai tana zuwa dubashi in suka je ganin gida, kuma ina
mai aiken duk abunda Allah ya hore mun. Yaronnan yana tsakiyar shan nono mahaifinshi ya
tsigeshi a kan cinyata bazan mance ba, ya danƙashi ga kishiyata Tamaulidi ni kuma yai mun
korar kare. Naga abubbuwa da dama da bana so ma in shiga labarin. Wadannan yaran
zamansu nake yi bana so su yi maraici kamar yanda Dauda ya taso cikin maraicin uwa, kuma
an faɗamun ba ƙaramin azaba matar uban take gana mishi ba. Inno tace in zata je wannan
karon in mun je zata kaini in ganshi.
"Amman Tani ni ina ganin akan yara bai kamata mu dinga nuna ma maza dole sai mun rayu
dasu ba. Kinga wannan maganar zaman yaran da aka ƙirƙireshi a cikin kabilar Hausawa ita ta ja
kusan rabi da kwatan matsalolin matar Bahaushe. Da ace yanda kika haƙura kika tafi kika bar
Dauda kuma baki sake waiwayarshi ba, da hakan ki kai ma Kaila ki zube mishi yaranshi ki samu
ki shaƙi iskar ƴanci" Murmushi nayi mata wasu hawaye suka surnano mun. Sabira bata san
raɗaɗin dake zukatan iyayen da suke rayuwa a wata duniya, ƴaranta suma suna rayuwa a wata
duniyar ba ne. Da tasan irin tashin hankali da uƙubar dazan tarar a gida, da irin tsangwamar da
ƙabilar Hausawa ke ma bazawara da bazata ce in kashe auren ba. Nashiga kunci rayuwa kashi
daban_daban wannan yasa banason shiga cikin ainihin rayuwar dana tsinci kaina a gidajen
sauran mazajen nawa huɗu. Mahaifina har cemun yayi na zama karuwa in ɗanɗana wannan
namijin, in fito in ɗanɗana wani, auren sha'awa kawai nake yi da mazajen. Babu sanda aka taɓa
jana a jika domun in samu sauƙin zugin zuchiyata. Haka Sabira tai ta bani baki tana bani haƙuri
akan cewar wataran sai labari. Ni kaina ina roƙon Allah yaimun tsawon ran da zanga ranar
labarin. Sai da ta ɗan kwantar mun da hankali sannan tace mun zata tafi. Samosa ta kawo mun
cikin leda, har bakin ƙofar gida na rakata ta tafi. Ina jiyo Kaila da Hajiyayye suna cin uwar
sabada, a wannan daren Kaila yayi jaraba da masifa tamkar zai doki Hajiyayye ina ji yana cewa
gobe ta tafi gidansu taje ta koyo tarbiya. Ina kwance ina fama da marurun zuchiyata. Sassafe
Kaila ya ƙanƙasamun ƙofa ya miƙo mun Samira har zai wuce nace.
Zanje wunin gida yau. Sannan dan Allah inason zuwa gobe zani Bauchi akwai wani taron ƴan
makarantarmu da za'ayi." Ranshi a haɗe ya juyo yace.
"Ni dai bani da kuɗin dazan baki zuwa wani Bauchi hidimar aure ce a gabana, in kina da kuɗin
mota ki je in baki dashi ki haƙura."
Ina dashi dama izini nake nema" Nace a sanyaye.
"To kije kwana nawa zaki yi to?" Nace mishi.
Bazan wuce kwana ɗaya ba ƙarƙari ƙwana biyu zan dawo" umarnin zuwa ya bani, nayi mishi
godiya. Da wurwuri na kammala aikina nayi wanka naima Hauwa. Goyata nayi a bayana na
saka hijabina na fito hannuna riƙe da leda da Samira. Kulle kofata nayi, na miƙa ma Hindatu
Samira. Nan taso ta neme ni da gulma, tana son sanar dani abinda ya faru, tafiyata nayi na
barta nan da Samira a hannu. Ina isa titi na tari keke napep zuwa layin idi mai barkono (Allah ya
jaddada rahamarshi gareshi). Tun daga titi na soma gaisawa da maza_mazan anguwar da suka
sanni nazo na wuce gidan mariyagi idi mai barkono a raina nace Allah sarki iya ta lungu mai
maganin gargajiya na kashin jarirai alkhairin Allah ya kai miki. Da sallama na shiga gidan namu.

Da Baffa naci karo shi da Habu yana mishi jagora da dukkan halama bara zasu fita. Yana jin
muryata ya caɓe abunka da makawo akwaisu da gane murya ballanta na kuma muryata.
"Tani kema kin iso kenan? Yanzu shigowar Use kamar tare kuke." Tsugunnawa nayi har ƙasa
na gaisheshi duk da nasan ba gani yake yi ba. Da fara'a ya amsa mun gaisuwar tawa.
"Ya mai gidan naki Kaila ince dai kina zaune lafiya kuma kina mishi biyayya ko? Gara ma ki
haƙura ki dena wannan auren ɗanɗanen dan wallahi duk ranar da kika zo mun gidannan da
sunan yaji ma, wallahi zaki sha mamakin abunda zanyi miki Tani. In auren kika kaso karma ki
nufo gidannan dan wallahi zaki sani in aikata miki abunda ƙila sai dai in ƙarashe rayuwata a
firzin." Ni dai da to Baffa naita binshi harya gama mun nasihar.
Bara zaku je ne Habu, har hutun sallar ya ƙare?" Baffa yace.
"To in bamu fita ba Tani wa zai bamu abinci? Kwana biyunnan dana zauna a gidan duk babu
daɗi sam, dan ma matan gida da maƙota sun kawo mana abinci da sadakar nama shi yasa na
ɗan huta. In muka zauna a gida babu mai bamu muci. Rannan ma Kaila ya biyo ta wajan barata
ya bani ɗari ko Habu ɗari biyar ce ko?" Habu yace. "E Baffa ɗari biyar ya ajjiye mana a kwanon barar"
"To kinji kya yi mishi godiya" Wasu hawayene suka gangaro akan kumatuna shar_shar_shar,
cijewa nayi nace da Baffa.
Zan yi mishi godiya sai kun dawo Baffa. Ga wannan ɗari biyar ɗin kwa yi cefane" Karɓa yayi
yana ta yi mun addu'o'in masu daɗi. Shiga cikin gidan nayi na samu su Yaya Use a barandar
ƙofar ɗaki a zaune akan tabarma suna dabdalar cin farfesun kan rago. Mu namu kan ragon
Hajiyayye aka ba takai ma iyayenta da fatar ragon waccen laiyar ma ita aka ba. "Kaga matar Kaila mai tukubar gashin kajin gidan gona da zabuwa" Cewar Yaya Use kenan
uwar barkwanci da tsokana. Dariya nayi mata na zauna a hankali na sakko da Hauwa ja'ira
idanta biyu akan cinyar Inno na ajjiyeta.
"Inno ina wuni anyi Sallah lafiya?"
"Lafiya ƙalau ya mai gidan da abokiyar zamanki, da facalarku kowa lafiya dai ko?" Dariya nayi
nace
Lafiya lau Inno, ina yaran suke?" Inno tace.
"Na aikesu ƴan dankali gidan wata Hajiya kira tayi a waya tace in tura Indo tayi kwalima ta
karɓo mun kaya. Shine fa yarannan su kaita magiyar su sai sun bita shine fa na basu kuɗin
abun hawa suka tafi." Kai kawai na girgiza na juya muka gaisa da Yaya Use da Yaya Karime.
Yaya Use tace. "Tani rannan Baban Abas ya siyo mana kaza a tukubar Kaila gaskiya dole ma Kaila ya dinga
uban ciniki gaskiya ya iya gashi sosai." Dariya nayi mata nace.
Babu laifi kam ya iya ciniki kam yana yi gaskiya tunda yanzu da kanshi ma yake kiwata kajin
nashi, zabi da kajin gidan kuma daga ƙauye mahaifiyarshi ke turo mishi da yajin gashin ma duk
ita take aiko mishi dashi. Yaya Karime matar babban direba Baban jafaru ya dawo kuwa?"
Murmushi tayi ita ba mai son magana bace tace. "Ya dawo a gida yayi Sallah, amman yanzu haka motarshi tana kan layi a farar gada ana mai
lodin kayan gwari zuwa Port Harcourt, ai matan direbobin manyan mota, da matan masu kaki
sai dai mu yi ta haƙuri kawai." Nan na shige cikin ƴan uwa mu kai ta hira, da dariya Inno tayi ta
binmu, wanda ya kama tasa baki takan sa. Farfesun kan ragonnan nima na zuba kaɗan na sha
yayi daɗi gashi yaji kayan ƙamshi. Ana haka sai ga Indo dasu Sulaiman da kaya niƙi_niƙi a

buhunhuna sun shigo. Nan na shiga washe baki dan nasan zamu samu kwance ko da
ɗaɗɗayane, dan yawancin kayan nawa Inno ce take bani kwancensu. Dan tunda na haifi
Balaraba Kaila bai sake mun zani ba, ko na sallah baya yi mun, sai wanda ya bamu jiya na
faɗar kishiya. Yara suna ganina suka shiga murna. Anan tsakar gidan Inno ta zazzage kayan
tana wawwarewa, gaskiya wannan karon kayan suna da kyau sosai, harda su mayafai na ƴan
gayu da takalma. Carab na riƙe wani mayafi baƙi mai kyau, ashe Yaya Use itama ta hangoshi
ganin na rigata ɗauka yasa ta bar mun. Atampa da leshi Inno ta miƙo mun da ƙarin mayafi ɗaya.
Na karɓa ina murna dan kayan kamar sababbi, gashi ɗinkunan jikin kayan bana banza bane
ɗinkunane masu tsada. Ta wari wani ta miƙa ma Yaya Use, ta sake warema Yaya Karime nata
itama. Ta ware ma Indo ma. Daga baya ta sake ƙara mana kala bibbiyu, ni nawa riga da skirt na
wani jan yadi ta bani, da shadda mai surfani a jiki, na samu mayafai har uku takalmi kala ɗaya
ne yayi daidai da ƙafata wani ɓaki. Yaya Use ce ta more takalma dake ita ƙafarta da girma naji
daɗin kayannan sosai dama harna tawo da ƴar atamfar da Kaila ya bamu ta faɗar kishiya zan
ba wata maƙociyarmu ta ɗinka mun in samu na zuwa Bauchi dan bani da wasu kayan fitar
kunya in ba wannan abayar dana sa ran sallah ba. Sai gashi na samu kaya masu kyau sosai.
Haka dai muka wuni na ba su Yaya Use ɗan ƙullin nama tsoka uku uku, na ba Inno nata itama
ba wani yawa nawa kason ne ma na bata ni na haƙura, su Yaya Use kuma a cikin na yaran na
cira musu.
"Tani saura sati biyu bikin Momiyo ƴar wajan Shafa ƙanwata ya kamata wannan karon aje
Shanono dake, daga nan dai mu je kiga Dauda. Daɗi sosai naji a raina dan ina kwaɗayin son
ganin Dauda sosai dannewa nake dan gudun kar in jawo ma kaina jangwam."
Allah ya kaimu. Nima gobe nake son zan je Bauchi. Ɗaliban makarantar kwana ta Bauchi da
nayi ne suka haɗa taron ƙarfafa juna shine zani. Kuma sati biyu masu zuwa Kaila zai ƙara
Aure." Su Yaya Use ne su ka ji wani iri, Inno kuwa saima washe baki da tayi tace.
"Ayya namijin duniya to Allah ya baku zaman lafiya. Kar dai kice zaki yi wani zafin kishi ki je ya
sako ki a banza. Wallahi in ma ya sakoki kisan tayi dan Baffanku yana jirace ne dake, nima a
wannan karon ba barinki zanyi ba. Aure biyar fa sai kace wata karya. Babu abinda yara suka
sani na biyayyar aure in banda sakarci da hauragiya. In ce dai da yardar shi zaki je wani Bauchi
ko? Dan na sanki sarai da ƙulafacin son makarantar yahudawa." Jiki a mace nace.
E da yardar shi zanje. Kuma in sha Allah babu abinda zai sa in bar wannan gidan sai in
gawata za'a fitar, in dai yi nayi bari na bari shine aure to da izinin Allah sai dai a fitar da gawata,
ko na mutu Lokacin mutuwar baiyi ba, ko kuma wa'adinane ya cika" Ai da faɗar haka Inno tace
ina wuta ta tsolma ni. Nan ta shiga mun faɗa tana cewa dama duk take_takena ya nuna so
nake Aure na biyar ɗin ma ya mutu in sake auran wani, wai na gaji da ɗanɗana Kaila inason
ɗanɗana wani. Nayi kuka ainun wannan kalmar fa iyayena ke jifana dashi bansan kuma mai
mutanen waje zasu ce dani ba. Ban karashe wunin da daɗi ba, kafin magriba duk mu ka ɗauki
haramar komawa gidajen mazajenmu, har zuwa lokacin Baffa da Habu basu shigo gida ba, har
barar dare suke yi wani sa'inma a bakin kasuwar suke kwana ko bakin masallacin ƴan taya a
cikin ƴan cirani dake dako a ƴan kwalli.....✍
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FADO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA 4.












Anan na bar yaran akan in na dawo zan yo kiran waya Habu ko Indo su rakosu." A titi muka
rabu da su Yaya Use kowa ya nufi gidan mijinshi. Ina shiga na hango Hajiyayye a zaune a
tsakar gida tana alwalar magriba idanun nata taci kuka na fitar hayyaci da gani.
"Kin dawo umman Sulaiman?" Ni mamaki ma nayi sosai dan Hajiyayye ko ni na kulata sai ta
ga dama take kulani.
Nadawo Hajiyayye sannunku da gida. Key na ɗakko na buɗe ɗakina na shiga na ko ci sa'a
akwai wutar nefa. Shinfiɗe Hauwa nayi na fito tsakar gidan dan yin alwala. Ina zaune akan
sallaya na idar da sallah sai ga Hajiyayye ta shigo da sallamarta, waje ta samu a bakin katifa ta
zauna. Da ido kawai na bita, to yau Hajiyayye ce a zaune a ƙazamar katifata mai wari?". "Umman Sulaiman ni dake so nake mu haɗe kanmu ta hanyar gasa Kaila a cikin gidannan duk
inda ya yi yaji babu daɗi, nifa ina gani bazan bar wata macen ta shigo gidannan ba ko da tsirara
zanyi yawo. Kuma ita matsiyaciyar da yake nema zan ɗakko mana number ta mu yi mata
kashedi da barazana mai ƙarfi na tabbatar zata fasa auren. Wannan bazai faru ba sai na samu
haɗin kanki. Jiya da daddare sabida na fasa mishi wayarshi suna waya shine fa Kaila yasa
hannu ya wankeni da mari, har nayi yaji ma na je gida, dawo dani akayi a bisa tilas ba son raina
ba. Yanzu in banda maza da shegen kwaɗayi bamu isheshi ba mu biyu? Gamu farare babu
wacce za'ace tana da muni jibi yawan gashin kanki dana yaranki fa me Kaila yake nema ne?"
Ai ya faɗa miki abunda yake nema da irin macen da yake burin son mallaka. Kinga kuwa dani
dake in aka haɗemu bamu kaita ba ko kusa. Ni da zan baki shawara ki ɗauka ko, da kin fita
sha'anin batun aurennan in dai kina son tsira da igiyoyin aurenki. A lokacin da Kaila zai auroki
da ban kwantar da hankali ba da tuni bana cikin gidannan.

4 / 24