Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ta tarwatse. Ya cika gidan da ƙara yana
huci yace mun.
"Sabida kin ɗaukeni ɗan iska shine zaki tura mun yara gidanku su dunga fita yawon bara kamar
ni Shanono? Yanzu na dawo daga ƴan taya, wucewa nazo yi Shafi'i ya riƙe mun riga yana ce
mun babiye Allah ba tare da yasan ko wa ya riƙe ba, ina juyowa ya ganni, Sulaiman shima yana
can wani kirista na bashi sadakar nera ɗari. Dan iskanci da raini sau nawa na faɗa miki kar a
sake zuwanmun da yara wajan bara?" Ni dai tunda ya soma wannan tonon sililin jikina ke rawa,
ada in ma masifar ce a ɗaki yake yi mun kisan mummuƙe, amman a yanzu a gaban kowa
tozartani yake yi, yau na ji na mugun muzanta a idanun kishiya da, facala. Salati suka shiga
rabkawa dukka Baba Rammai harda tattafa hannaye. Hakan ya kuma tunzurashi yace.
"Kar a kuma ɗaukar mun yaro a kai mun shi gidan makafi ni dai na faɗa miki. Ke daya zame
miki dole sai ki je. Kuma yanzu_yanzu ki je ƴan taya ki ɗakko mun yarana wallahi in ba haka ba
a gidanku zaki kwana, bara harda su Balaraba an baza su a titi ana son kashe musu
zuchiyarsu. Wannan wanne irin masifa ce nayi ni dai nadamar auro ki da nayi, wannan ai kece
kara da kiyashi." Baba Rammai tace.
"Ɗaukar marar sani ba. Ai ni tunda kace mun aurenta huɗu nasan ba za'ayi abun arziki ba.
Amman dake a lokacin sun yi ma asiri kana saurayinka da kai zarkaɗeɗe a rasa wacce zaka
auro sai bazawara mai Aure huɗu mai yaro. Ke kuma ai sai ki bi umarnin mijinki ki je ki ɗebo
mishi yaranshi tun kafin ya sallameki a koma kwana a ƙarƙashin gada. Ai dama ance mana a
ƙasan gadar legas aka haifeki da rana" Ji nayi zuchiyata na harbawa da ƙarfi, jinin da take
watsawa ya wuce kima. Ƙafafuna sun gaza motawa kaina kamar zai tarwatse nama rasa wanne
irin tunani ma zanyi. Ana cikin haka na jiyo muryar Inno tayi sallama da yaran. Shigowa tayi da
sallamarta, tana duƙe riƙe da ƙafarta kamar yadda take. Ganin Baba Rammai ya faɗaɗa
fara'arta tace .
"Rammai kece a garin? Maraba lale ga jikokin naku na kawo miki su, nima duk sun isheni suna
san ganin uwasu." Sama da ƙasa Baba Rammai tayi ma Inno wani kallon wulaƙanci, cikin ba'a
tace.
"Ai fa ga jikokina, daga yawon barar kuke ne naga duk kun haɗa zufa Inno ƙafafunku duk ƙura"
Da dariyar wulaƙanci ta ƙarashe maganar tana jayo hannun Balaraba. Inno da bata san ba'a
tayi mata ba tace.
"Wallahi daga bara muke can muka wuni dasu, shine dai nace bari in kawo su" Hindatu ce ta
ƙaraso inda muke dan gulma ta gaisa da Inno. Kaila kuwa bai ma kalli inda inuwar Inno take ba
yayi shigewarshi ɗaki. Baba Rammai taja hannun su Sulaiman suka zauna a tabarma, Hauwa
da rarrafe ta bisu tana murna taga ƴan uwan nata.
Inno muje daga ciki kici abinci ko?" Baki Inno ta washe tace
"Kamar kuwa kinsan yinwa nake ji wallahi, dan tun fitarmu rogo na sai mana na nera ɗari
kawai" Ɗakina na da tayi ƙoƙarin shiga cikin dakiya nace
Inno na canja ɗaki kin mance ne?" Bata ce dani komai ba, na shige ta biyo bayana. Sai ga
Hajiyayye da wata koɗaɗɗiyar nera ishirin ɗinta a hannu, muna haɗa idanu ta wani yamutse
fuska.
"Inno ga sadaka ko?" Juyowa Inno tayi ta kalli Hajiyayye kana ta dawo da kallonta gareni. Sai
lokacin ta fahimci halin da nake ciki. Ajjiyar zuchiya inno ta sauke ta kalli Hajiyayye a karo na
biyu tace.
"Allah shi karɓa Allah yasa a mizani ƴannan, amman ki bar kuɗinki ai kema ƴata ce. Rammai
Allah ya bamu alkhairi ni zan koma" Baki Hajiyayye ta taɓe tayi komawarta tana ƴan surutan da
bazan ce ga abinda take cewa ba. Sallama Inno tayi da Baba Rammai. Muna shiga zaure tace.
"Me kika yi musu haka Tani, in ce dai ba Auren kike son kuma kashewa ba a karo na biyar? Ki
buɗe kunnenki da kyau a wannan karon in kika sake aurenki ya mutu sai dai ki nemi wasu
iyayen ba mu ba, Baffa ma zai iya tsine miki kibi duniya. Ina fatan ba akan auran da Kaila zai
ƙara bane ko? Hawayene suke fita a idanuna wasu kan wasu sai kai kawai na girgiza ma Inno
amman na kasa magana.
"Abincin ki samun ko a leda ne in naje gida maci da ƙannenki, ni bazan shiga ba kar uwar
mijinki ta zargi wani abun, ni da nasan tazo ma babu abinda zai kawo ni gidan" Bance mata
komai ba na shiga ɗaki na zuba mata abinci a kula dukka na juye musu, nasa musu miya da
nama ban ma ko ɗumama miyar ba tunda na dawo, dake soyayyar miya ce babu abinda ya
sameta.na fito da ledar abincin a hannuna."
Inno ina zuwa bari in tambayi izinin Kaila sai in kai ki gida dan ba zaki iya riƙe kayan ba" Kafin
tace wani abun sai ga shi ma ya shigo zauren shi da su Sulaiman da dukkan alama masallaci
zasu je, dan anata kiraye_kirayen sallah.
Kaila dan Allah zan raka Inno gida kaga dare yayi hankalina bazai kwanta ba in ta tafi ita kaɗai"
Sake shan kunu yayi ba tare da girmamawa ba yace.
"Wanne irin zaki rakata kuma, naga har dare kuke kaiwa a wajan bara, kuma da ƙafa kuke
zuwa gida kuna tafe kuna bara. Yau kuma sai kin rakata? To adawo lafiya" Yana dasa aya ya
raɓa ta bayan Inno ya wuce, yaran suka bishi a baya, dake Sani yaro ne mai hankali naga
ranshi bai yi mishi daɗi ba. Kuka mai sauti na saki da naga fitarmu. "Banda kuka Tani, kiyi haƙuri ba komai bane ai wannan mu dai in zai riƙe mana ke ai shikenan,
wuce muje ki rakani titi in kika sani a abun hawa ma ya'isa inna sauka a kan layinmu zan samu
matasa su kai mun ledar gida" kiran Balaraba nayi, da gudu tazo nace.
Ku zauna a wajan Baba Rammai zan kai Inno gida. In Yaya suka dawo daga sallah ku jirani a
cikin nan ɗakin kinji ko? Wannan shine ɗakinmu yanzu" Fita mu ka yi ni da Inno, muna zuwa titi
na tara mana abun hawa mu ka shiga. Babu mai iya cewa komai tsakanin ni da ita. Ita kanta
cikin tunani take. Ban bar Inno ba sai da na kaita har gida nayi sallar magriba kafin nayi mata
sallama a gurguje su Baffa basa gidan basu dawo ba tukunna. Tun daga ɗan nesa da gidanmu
nake jiyo kukan Hauwa hakanne yasa na ƙara sauri dan in shiga gidan. Ina shiga na ji kukan a
cikin ɗaki da sauri na shiga. Hauwa na bayan Sani yana jijjigata sai kuka take ta haɗa hawaye
da majina. Sauran yaran suna zaune jigum daga gefen katifarsu. Zare Hauwa nayi a bayan
Sani na nemi kujerar tsakar gida na zauna, sai da na zura mata nono tayi shiru sai ajjiyar
zuchiya take faman yi, nima ajjiyar zuchiyar nake ta faman saukewa. Ga haki daya dame
ni..........
MRS BUKHARI[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 7
*Ina miƙa ɗinbun miliyoyin godiya ga duk ɗaukacin masoyana, masoyan Shanono. Haƙiƙa
littafinnan yayi karɓuwar da ni kaina banyi tunanin zai yi ba. Ta dalilin wannan labarin manyan
mutane sun kirani a waya sun jinjina mun. Zawarawa suma sun kira sunce na taɓo musu inda
yake musu ƙaiƙayi. Ina godiya ga duk makaranta wannan littafin, Mrs Bukhari gidan ƙamshi taku
ce*
*Yana da kyau ko wacce mace ta karanta littafinnan tun daga farkonshi izuwa ƙarshenshi.
Domin makaranta ne mai zaman kanshi wannan labarin*
Me yasa baka kaita ko da wajan Baba Rammai bane ka barta tana ta kuka?" Sulaiman ya dube
ni yace.
"Koro mu tayi har Abba yana ce mana jikokin makafi da guragu. Umma Hajiyayye kuma ta daki
Balaraba dan tace yinwa take ji" Da sauri na miƙe na fita tsakar gidan, ruwan wanka dana ɗaura
a wuta yana ta tafasa har ya ƙune kusan rabi. Saɓa Hauwa nayi a baya na sauke tukunyar na
girgije kurbo ɗin na ƙara gawayi, kana na mayar da tukunyar kan wuta. Taliya na ɗakko a
kitchen guda ɗaya na zuba a ruwannan. Sai da nayi sallar isha na juye musu taliyarnana a
babban faranti da miya. Sai da suka ci sannan su kai Sallah. Ni ko ruwa na kasa kurɓa sam. Ina
zaune a bakin katifa yara duk sun yi bacci, mazan katifarsu daban, matan kuma muna katifa
ɗaya. Kaina ya ɗaure da tunani nama rasa wanne irin tunani zanyi ma. Ga yinwa data addabeni
yaron dake cikina sai juyi yake yi, ni kuwa ko ruwa bazan ma iya kurɓa ba, hawaye kawai nake
zubarwa. Ina tuno irin so da kulawar dana samu a wajan Kaila a lokacin farkon aurenmu.
Wallahi in wani ne yace mun Kaila zai ƙyamace ni har haka bazan yarda ba. A yau na gane
nadamar aurena yake yi, ko ko in ce nadamar haɗa tsatso yake yi da ɗiyar mabarata wanda
ubanta yake makawo, uwarta kuma take gurguwa, ni Shanono wacce aka haifa a ƙarƙashin
gadar legas a tsakiyar kutare da guragu, da makafi. Ni na yarda wannan itace ƙaddarata, na
aminta cewar maza basu karɓeni ba, Aure biyar amman babu wanda naji daɗinshi, gashi
wannan ma lilo yake yi.
Ban taɓa yarda da masu cewa yanda suka ga rana haka suka ga dare ba, sai lokacin da
matsalolin gidajen aurena suka farma rayuwata. Kamar kullum yau ɗinma banko iya runtsawa
ba. Washe gari na tashi da zazzaɓi da ciwon mara mai tsanani ko tashi bana iya yi."
Sani zaka iya hura mun wuta?" Na tambayeshi cikin muryar tsananin ciwo, yaran duk sun
kewayeni sai sannu suke yi mini.
"Umma zan iya, nasan yadda akeyi"
To ka hura mun wutar, sai ka ce da Ammanku dan Allah tazo banda lafiya" Da sauri Sani ya
fita, ni kuma naci gaba da juyi a tsakar ɗaki. Kamar minti goma sha biyar da fitarshi sai ga Kaila
ya buɗe labulen ɗakin yana tsaye a kaina sai wani ajjiyar zuchiya yake faman yi.
"Lafiya kike neman Hajiyayye? Mun kwana gida ɗaya baki iya fitowa kun gaisa da Rammai ba
balle ki dafo abinci ki kawo mata ko? Jiya haka kika kwashi abinci tab leda mai zane kika ba
Inno, amman ita Rammai baki iya bata ba ai." Baki na cije nace.
Kai haƙuri bani da lafiya ne, shi yasa ma nace a kira mun Hajiyayye ta taimaka ko asibiti ne ta
raka ni"
"Allah ya ƙara sauƙi ko haihuwar ce?" Sai kuma ya sassauta murya ganin halin da nake ciki.
Wallahi ban sani ba, Amman zai iya yiwuwa haihuwarce wata takwas da ɗan ɗoriya ne. Naga
sai cikina ya kusan wata goma nake haihuwa ne" Baki ya taɓe.
"To bari in kira unguwar zoma zaifi, in ma asibitinne sai ku tafi tare. Kike wani raki haihuwa ke
da kika ɗauketa kamar ki saki ƙaton kashi. Ba za'a fi wata biyu ba zaki sake shiga wani laulayin
ai in dai kece Shanono ciki da goyo shi kadai kika iya ai, duk wani abun arziki baki sanshi ba.
Ga shegiyar ƙazanta ɗaki sai warin annakiya da tsummokin bara " Ana cikin wannan halin
Hajiyayye ta iso, ganinshi a bakin ƙofar ne yasa tace.
"Baby lafiya kuwa inata jiranka karyawa fa kake yi?" Murmushi yayi mata.
"Kinga naƙuda inaga take yi, ki kira mata Rammai. Yaran kuma ki ja su basu karyaba zan shigo
musu da masa sa ci nasan kin gaji. Bari ina zuwa, sannu Shanono Allah ya raba lafiya " Nan ya
fice ya barni a tsakar ɗaki. Ji nake dama zan iya haɗiye zuchiyata in mutu ko na huta"
Sulaiman ka kira mun Sabira maza" Da gudu Sulaiman ya fita, Hajiyayye ta wuce cikin gida da
sauran yaran ko uffan ta kasa ce mun. Har sai da Sabira ta ƙaraso kafin Baba Rammai ta leƙo,
a dokin ƙofa ta doge."
"To tunda kin iso ma ai shikenan, kinga ni surukace, Hajiyayye kuma kishiyace, Hindatu kishin
sauri, kinga ba sa ga tsaraicinta ba sai dole." Tana idasa faɗa ta saki labulen, ba sannu, ba
Allah ya raba lafiya. Haka naita gumurzu Sabira na yi mun sannu. Anguwar zoma ce ta shigo
ɗakin jikinta saye da fararen kaya na ma'aikatan asibiti. "Tun yaushe kika soma jin halamun naƙudar?" Ta tambayeni tana duba ni"
Da safennan ne kamar wasa naji ciwon sai tsananta yake kuma yi. Cikin bai kai haihuwa ba
amma" Dubani tayi da kyau tace.
"Ai kuwa ba haihuwa bace juyi ne. Amman ki je Asibiti likitoci su duba ki." Kaila ne ya leƙo
ɗakin. Ba shiri Sabira ta rufe wuyanta zuwa ƙirjinta da gyalenta, shi kuwa yaƙi ɗauke ido a
kanta. Ni kuma ina zaune zaman ɗabaro a ƙasa, marar na lafawa kaɗan_kaɗan.
"Yaya akayi haihuwarce dai ko?" Ya tambayi unguwar zoma.
"A'a bazai wuce juyi ba, ba haihuwar bace. Amman ya kamata taje asibiti" Hanya Kaila ya bata
ta fita dan sauri take yi da gani wajen aiki zata. Tsaki Kaila yayi yace.
"Sabida shegen raki irin naki juyin cikin kike ma murƙususu haka sai kace mai haihuwar fari,
haihuwa ta barkatai? Allah ya kyauta, sai ki fito da tsunmokin ki ai, da gaiyar kuɗin cizo masu
fenti in sun gama na ɗakin Bilkisa sai su yi miki kamar yadda nayi alƙawari." Ni dai na ma rasa
ta cewa, Sabira kanta a sauke har Kaila ya gama magana ya tafi. Ita ta fitar mun da komai na
ɗakin nawa zuwa tsakar gida, ni kuma ina zaune akan taburma a tsakar gidan. Baba Rammai
ce ta fito daga ɗakin Kaila da waya riƙe a hannunta tana waya da amaryar Kaila. Masu fentin
ɗakin Amarya suna ta tayi, wasu suna fentin tsakar gidan namu. Har haf door akayi a ƙofar
ɗakin Amarya, daga gefen ɗakin kuma kafinta na buga kitchen irin na langa_langa, da dukkan
Alamu Kaila na ji da wannan Amarya dan shima kwalima yake yi a ɗakinshi. Ana gama fentin
ɗakin Amarya aka shiga fente ɗakin ango. Hajiyayye sai kumbure_kumbure take yi, motsi ɗaya
ta jibgi ɗiyarta. Ni dai ina zaune jigum, Sabira ce ta kama yaran tayi musu wanka suka yi
ficewarsu waje. Ita ta ɗaura abincin masu aikin fenti da Kaila yazo yace in ɗaura. Amadudu da
Baba Rammai kuma fita su ka yi zuwa kasuwa. Ni dai ina kwance a kan taburma ciwon jiki dana
zuchiya na neman rayuwata. Bayan masu aiki sun gama aikinsu Sabira ta zuba musu
abincinsu, ni kuma sai da nayi Sallah na ɗan taɓa abincin, ta haɗe yaran du ta zuba musu
abincinsu. Kaila yana ta kai kawo tsakan kanin ɗakinshi da ɗakin Hajiyayye dan fishi take yi
dashi sosai, shi kuma babban tashin hankali ne fishinta gareshi, har sabunta mata fenti itama
akayi. A haka dai ya shirya ya fice a gidan. Ko awa bai yi ba sai muka jiyo sallamsrshi da wasu
maza suna kiciniyar shigowa da setin gado. Gado da wadrope Kaila ya sake filla_filla daga
kamfanin ɗan sogai. Tsofaffin kuma aka fice dasu. Sabira kuwa sai hidima take yi dani, ita ta
share mun ɗaki ta goge ƙasan ɗakin Sani da Sulaiman su ka kama mata suka shigar da katifun
da buhunhunan tsunmokaranmu.
Sabira nagode sosai Allah ya bar zumunci. Ya kamata ki tafi gida kinga magriba ta kawo kai,
kije ki ɗaura ma mai gidan Abinci, ragowar abincin dake cikin tukunya zai ishi yaran, naga ma
kin dumama musu." Murmushi tayi tace.
"Babu komai ai Tani, in ruwan wankan naki yayi zafi sai ki sa Sulaiman ko Sani su juye miki.
Su Balaraba kuma zan aiko Mustapha zuwa bayan isha ya zo ya tawo mun dasu gidana, zuwa
gobe sa dawo kya samu kiyi bacci sosai " Sabira ƙawace wacce samun irinsu da wuya a
wannan zamanin. Godiya marar iyaka nayi mata, sallama tayi mun ta tafi, ni kuma na lallaɓa na
tashi. Fitowata daga banɗaki kenan Baba Rammai suka shigo ita da Amadudu kici_kici da
kaya, harda su katan_katan na ruwa da lemo. Sannu da zuwa nayi musu zan wuce, Baba
Rammai tace.
"Ungo wadannan ledojin kayan miya da kayan lambu ne a ciki, wannan kuma kaji ne an fige an
yanka ma. Gobe sassafe sai ku tashi da aikin ƴan jere zasu tawo daga Zaria kuma fitowar safe
zasu yi." Ledojin na karɓa a hannunta, sauran suna ƙasa. Kayan ruwa da lemun kuma
Amadudu ya shiga dashi ɗakinshi. Ɗaki na kai kayan sai da nayi har sallar isha sannan na aika
Shafi'i kitchen ya ɗauko mun bahun ƙarami. Kajin na juye sai da suka cika madaidaicin bahun
dam. Haka na kinkima da ƙyar zuwa tsakar gida na shiga aikin gyaran kaji nan. Mustapha yayi
sallama ya tafi da su Sulaiman Hauwa kawai suka bar mun. Ina wanke kajinnan marata na karta
mun. Gawayi na haɗa na ɗaura tafashen kajinnan a ƙatuwar tukunya dan kajin sun yi guda
takwas masu abun ne to da abunsu kura da kallabin kitse. A kan kujerar tsugunno Kaila ya
shigo ya same ni, ni ni kaɗai a tsakar gidan gashi ba wuta, sai hasken waya na kunna. Sannu
da zuwan da nayi mishi ma da ƙyar ya amsa ni, yayi shigewarshi ɗakin ƴar gwal. Sai goman
dare na sauke tafashe na tafi dashi ɗaki, ko lomar tuwo ban kai bakina ba. Haka na kwana ina
ciwon mara, washe gari kuma na shiga hidimar aikin ƴan jere, Hindatu da Hajiyayye babu
wanda