Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ƙoƙari ƙannenshi ma sun wuce shi, amman shi shekara guda yana wai
Abasa wata wallah. An sashi a garejin ma, ogan ya hana shi zuwa baya gane komai sai shegen
wasa da niman tsokana a cikin Dauda. Ga yawo" Tana cikin faɗar haka wani ɗan yaro ya shigo
da yagaggun kaya, yayi futu_futu, sai jan ƙafarashi yake yi. Ga sumar kanshi daka gani kasan
fulanine, amman kora ta cinye fatar kan."
"Tani kin ganshi nan ja'iri. Ga uwarka tazo dubaka" Ƙura mishi idanu nayi, ina jin motsin sonshi
a dukkan jikina, wani irin so nake yi ma Dauda so irin na yaran fari, so irin na uwar data soma
haihuwar ɗanta ta buɗe idanu ta ganshi a matsayin mallakinta fid duniya wal akira. Shima ni
yake kallo tamfar ya sanni. Fuskarshi ta yaiwatu da fara'ar data kusan karya kuzarin dana aro
na yafa. Sai nake ji kamar bazan iya tafiya in bar Dauda a cikin garin Shanono ba. Hannu na
miƙa mishi.
Tawo gun ummanka Dauda" Dariya yayi har wawalonshi ya bayyana, da halama famfara ya
soma. Cikin ɗingishi da yanayi na azabar ciwo ya iso gareni. Riƙe mishi hannu nayi dam.
Siraran hawayene suka gangaro a idanuna. Ji nake sake rabani da Dauda a karo na biyu
tamkar zare mun munfashine, ma'ana nabar doron duniya. A halin yanzu hankalina ya dawo
kan Dauda, kuma inason in da so samu ne yaci gaba da rayuwa a gabana, in sashi a boko,
wala Allah ko su sa samu damar cika mun burina, tunda ni aure, da yawan yara ya danne
burina."
Baka da lafiya ne Dauda, na ga ka kasa zama?" Runtse idanu yayi yana ta ƙoƙarin son zama,
amman ya kasa. Cikin nutsuwa na miƙar dashi tsaye na juya bayanshi, na ga jini a bayan
rigarshi. Gabana ne ya yanke ya faɗi ras. Hannuna na rawa na ɗaga mishi rigar, wandonshi ma
da jinin a jiki. Zuchiyata na tsalle na sa hannu zan zame wandon nashi, cike da tsoro Dauda ya
riƙe mun hannuna.
"Innata da zafi karki cire mun. Kema irin abinda Alh Zangina yake yi mun zaki mun? Ciwo nake
ji" Rugujewa zuchiyata take shirin yi. Cikin fitar hayyaci nace.
Ba irin abinda yake ma zan yi ma ba, gani zanyi, naga jini a wandonka" Iya mai Fura tace.
"Kaji mun ɗan baɗo, zaka cika mata hannu ko sai na buge hannun da sanda?" A firgice ya cikan
hannuna. Jikina a mace na zare mai wandon ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar.
Abunda na gani ya gigitamun lissafina. Tunanina ya gurɓace. Fata_fata takashin Dauda take,
ga wani irin mugun wari, ga ɗiwa, harda tsirarin tsutsotsi in ba dai haukacewa nayi ba. Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun kawai nake ta faman ambato. Yaya
Karime ta fashe da kuka. Ni a wannan lokacin wallahi kukan ma ƙin zuwar mun yayi.
"Tashi Tani maza mu tafi asibiti kar yaronnan ya mutu. Iya ku kuna ina wannan al'amari ya faru,
ɗan mutum ya ruɓe ba ruwanku. A ruɗe Iya tana kuka tace"
"Wallahi bansan komai ba Karime Tani. Bari matar Shehulle ta fito kuje" Ba wanda ya bi ta
kansu. Yaya Karime ta goya Dauda a bayanta. Ina biye dasu ina haki, ga ciki ga goyo, ga
numfashina na fita da nauyi. babban Asibitin gwamnati na Shanono muka shiga. Ganin yadda
Yaya Karime ta ruɗe da kuka. Ba shiri ma'aikatan jinya suka amshi Dauda suka shige dashi
wani ɗaku. Mu kuma akace mu jira a waje"
MRS BUKHARI✍
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 10
*INA MIƘA DUMBIN GODIYA GA DUK ƊAUKACIN MASOYA WANNAN LITTAFIN. HAKIƘA
SAƘONNINKU SUNA ZUWA GARENI. KUMA INA GANIN WAYOYINKU DAGA GARI_GARI
ƘASA_ƘASA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR ƊAUKAR WAYOYINSU BA, SUIMUN UZIRI
ABINNE DA YAWA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR BASU AMSOSHIN WASIƘUNSU BA,
SUIMUN AFUWA SUMA DAN ALLAH. ZAN AJJIYE LINK ƊIN GROUP ƊIN LITTAFIN NA
FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA, MAI SON KASANCEWA TARE DANI SAI YA SHIGA.
KU SANI INASONKU MASOYANA A DUK INDA KUKE.*
Kaila:
wani irin farin ciki Kaila yake ciki marar musaltuwa. Tun dawowarshi da asuba, ya dawo ya
samu Balkisa ta fesa ado da wata jar atampa ɗinkin riga da siket. Kayannan sun zauna mata
ɗas a jikinta, kirjinta ya bayyana sosai, sai wannan hasken Amarcin irin na amaren kwana ɗaya
tare da miji take yi. Kaila na ganin Bilkisa a cikin wannan ado, tuni ya mance da takaicin ganin
Tani da yayi a tsakar gida. Dan bayan ya gama magana da Tani, fata yayi a ranshi dama ace
Tani kar ta dawo in ta fita ta fita kenan, ko kuma ya ji labarin motarsu tayi dungure babu wanda
yayi rai. Da wannan mummunan tunanin ya shigo, ganin Balkisa ya yaye mishi dukkannin
cunkushewar zuchiyarshi. Tuni ya washe bakinshi tare da ware ma Bilkisa hannunshi. Da
shagwaɓa ta faɗa jikin Kaila, shima ƙamshin yake zubawa kafin ya fita Masallaci sai da yayi
wankan soso bayan wankan Sallah. Kan gadon suka faɗa suna dariya. Cikin so Kaila yace.
"Jina nake kamar nafi sauran maza sa'a. In ana cin ɓaure ba'a tona cikinshi Ɗanyan gwal,
amman abunda zance miki shine kin sabunta mun jinina, kin sake mayar dani fresh. Dan
ƙazantar su Shanono saura ƙiris ta shafe ni, ke kika ceceni. Matane gasu dai a gida, daga mai
warin dauɗa da kuɗin cizo, sai mai warin baki. In Hajiyayye ta yi magana bakinta kamar shadda
fa. Ke kuwa naji har yawunki ƙamshi yake yi" Dariya Bilkisa tayi na farin ciki. Ko wacce mace ta
fi son mijinta a kalleta a matsayin TA FI SU, shi yasa da yawan mata basa iya takama maza
burki in sun kwaso gulmar kishiya sun kawo musu. Sai dai tai ta zura miji shi kuma yana sakin
layi. To ki sani yin hakan tamkar cikin ki ki ka daɓa ma wuƙa, yau ga wani gobe gareka,
musamman sha'anin maza.
"Gwanda amman dai bakwa sumbatar juna in kun zo mu'amular Aure ko? Kyama har ta kama
ni, ji nake uwa in yi amai" Dariyar yaudara Kaila yayi, ya gyara mata kwanciyar tata, tare da
faɗin.
"Ai komai baya yiwuwa kamar yadda na faɗa miki tun kafin kizo. Ni fa duk wani soyayya da
tarairayar miji a gado ban sanshi ba. Ke baki ga hakan a haɗuwarmu ta jiya ba? So fa kika yi ki
buɗe mun kai" Dariya tayi mishi tace.
"Tarairaya Gwanda ai baka ga ma komai ba. Ni dai fatana shine kaci gaba da sona har izuwa
ƙarshen rayuwata. Ni kuma zan baka duk wata kulawa." Nan suka shiga musayar kalaman
ƙauna masu zafi, tamkar zasu koma ruwa, amman ina cikinsu na kiran ciroma, ba shiri Kaila ya
miƙe dan bashi da juriyar yunwar ciki da yunwar mace. "Bari in shiga gidan in samo mana abinda zamu ci ko?" Baki ta taɓe tace.
"To Allah yasa dai in iya ci Gwanda" Fita yayi daga ɗakin. Akan idon Hajiyayye Kaila ke ta
faman jan rigarshi a ƙoƙarinshi na san dai_daita kanshi daga fitinar dake cin ƙasan ranshi.
Wandon shi da yayi tudu tabi da idanunta. In da Hindatu take zaune tana wanki tabi da kallo,
itama Kaila take kallo harda riƙe haɓa. Wani ƙaton malolon baƙin kishi ne ya tokare mata
maƙoshi. Bata dawo daga duniyar takaici da zafin zuchiya ba, taji saukar sautin Kaila yana
faɗin.
"Ina abincin karin Amarya Hajiyayye na ɗauka sassafe za'a shigar mata dashi, kinsan dole da
yinwa ake wayar gari" Ji tayi muryarta ta dashe, ashar tayi niyyar lailayowa da ƙyar ta danne,
taci gaba da wankin da ta tashi dashi yau.
"Ba dake nake ba Hajiyayye dan rashin son albarka shine kina jina ki kai mun kunnen uwar
shegu, ko an faɗa miki ni sa'an wasanki ne?"
"Abinci dai banyi ba, kuma in sai Bilkisa taci abincina zata rayu sai dai ta mutu. Kayi haƙuri
Kaila bana son ka taɓo ni in fa ba haka ba zaka ga jajjagen rashin mutunci, alo tsiya alo......."
Tas ya wanketa ta wawan tafi. Da sauri ta dafe kuncinta tana mamaki, miƙewa tsaye tsaye tayi
dafe da kunci. Shi kuma ya haɗe rai ya kumbura jiran ƙiris yake ya fashe. "Ni ka mara Kaila sabida ƴar iskar Amaryarka?"
"In kika kuma kiranta ƴar iska sai na saki a cikin dana sani wallahi "
"An faɗa ƴar iska, an kuma ƴar iska" Cikin ɗaga murya da hargagi yace.
"Kije gidanku na sake ki. Tunda ke bakya ji, baki isa ki hanani sakewa da matata ba. Ki je gida
kawai" Kuka Hajiyayye ta ruguje dashi. Wannan kukan sakin ya zame ma mata dole. Ko da
mace ita ta nemi sakin, da zaran miji ya furta kalmar sai zuchiya tayi rawa gami da raunata.
Amman dake Hajiyayye itama A ce, kuma ita tayi dai_dai da Kaila. Bai yi aune ba ta juye mai
ruwan wankin da take yi a ka. Ta jiƙashi sharaf. Bilkisa da Amadudu tare suka fito a guje tsakar
gidan, a sakamakon hargagin Kaila da Hajiyayye. Da mugun gudu yabi Hajiyayye jikinshi har
yana ɓari. A guje ta fella bako mayafi daga ita sai doguwar riga. Kaila bai bar binta da gudu
suna ratsa mutanen anguwa ba. Sai da Hajiyayye ta faɗa cikin wani gida jikinta na rawa. Yanda
taga ɓacin rai a fuskar Kaila bata san me zai yi mata ba daya kamata. A ƙofar gidan ya tsaya
yana cizon yatsanshi. Amadudu ne ya iso da sauri wajan, dashi da Baban Mustapha mijin
Sabira, da wani dattijo maƙocinsu. Wannan dattijon ne yace.
"Haba Baban Sani, ya zaka take ka biyo mace da tsohon ciki waje, kana gudu tana gudu ko
mayafi babu. Ai koma meye tayi maka bai dace ku fito titi ku fallashi kan ku ba. Ka duba yadda
anguwa ta cika da mata, jibi can mata ne daga katanga suke leƙe fa" Kallon katangar da dattijon
ya nuna musu suka yi. Mata uku suka gani sai leƙe suke yi. Anguwar ts soma cika da mutane.
Dan da dama sun jiyo sautin muryar Kaila a lokacin da ya furta ma Hajiyayye saki. Haka dai
wannan Dattijo ya taushi Kaila ba dan haka ranshi yaso ba ya bar ƙofar gidan yana ƙuta. Yana
shiga gidan bai zarce ko ina ba sai banɗakinshi, dan takaicin bai gurje bakin Hajiyayye ba da
ruwan sanyi yayo wanka. Yana fitowa ya kintsa, Bilkisa dai tana zaune tana kallonshi, so take ta
bashi haƙuri amman tana jin tsoro. Ita yawan fara'ar Kaila da kashasshiyar muryarshi ta
yaudara kawai ta sani. Sai gashi yau taji muryar cikakkun maza tattare dashi" Kai tsaye Kaila
wajan mai indommie ya je. Kwai yasa aka toya mishi guda huɗu, ya sai kayan tea da ƙaton
biredi ya dawo gida. A inda ya fita ya bar Bilkisa anan ya sameta a harɗe, jira yake ta amshi
ledar hannunshi amman yaga ko gezau batai ba. Ba ta mishi ko sannu da zuwa ba. Amman
dake amarya ance bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida, haka ya barta.
"Ga kayan tea na siyo, ki dafa ruwa ko a kettle ne ki haɗa mana tea, akwai soyayyen ƙwai a
ciki sai mu haɗa da kazar jiya" A yangance ta ɗauki ledar ta fita zuwa kitchen ɗinta na langa
langa. Bata jima ba sai gata da trai a hannunta ta sako komai a kai, harda kaza mai turiri da
halama ta dumamata a oven ne ko microwave, dan an danƙara mata kayan wuta iri_iri. Suna
zaune suna karyawa babu mai cewa da kowa komai, sai da suka kusan kammalawa Bilkisa
tace.
"Gwanda kayi haƙuri da Hajiyayye ka dawo da'ita ɗakinta, ga ciki kuma naga ƴarta ƙaramace,
ɗazu ma daka fita ina jiyo kukanta a tsakar gida. In ka rabu da'ita waye zai riƙe mata yaranta"
Ƙur Kaila ya mata da mayaudaran idanunshi yace.
"Tunda fa na sanar musu da batun aurenki, bata taɓa barina nayi bacci mai kyau ba. Dama fa
fitinar Hajiyayye yawa ce da'ita. Ki barta kawai ta je gidan. Ala bashi in iyayenta su ka yi tunanin
dawo da'ita ɗakinta shikenan." Kai Bilkisa ta gyaɗa tace.
"To shikenan ba damuwa. Abu na gaba kuma ya batun mai aiki da kayi mun alƙawarin zaka
ɗauka mun washe garin ranar dana tare, kaga yau kenan. Dan gaskiya bazan iya haɗa
tarairayarka da shiga kitchen ba, ga aiki in na soma zuwa. Bani ma da wannan lokacin gaskiya"
Murmushi Kaila yayi yace. "Yanzu bari in kammala karyawa sai in fita, in sha Allah da ƴar aiki zan dawo cikin gidannan. Ai
ba wuya suke yi ba masu aikin. Gaskiya Ɗanyan gwal kina ji dani fa, sabida tsabar tarairayata
da kike son yine kika ji girkin ma ba zaki iya yi ba." Nan dai su kak ta faman tattaunawa, daga
ƙarshe Kaila ya fita, Bilkisa kuma ta koma ɗakinta. Babu abinda ta taɓa a ɗakin, kayan da su ka
yi kari suna wajan, kayan da Kaila ya cire suna zube a kan gadon. Kafin azahar sai ga Kaila da
ƴar aiki ya kawo ma Bilkisa. Tana harɗe a falonta tana kallo suka shigo.
"Ɗanyan gwal, wannan sabunta kwalliya haka, kai gaskiya ina morewa idona. To yanzu dai ga
ƴar aiki nan na samo miki ita, sai ki faɗa mata aiyukan da zata dinga miki, da kuɗin da za'a
biyata ko?" Bilkisa ta murmusa tace.
"Godiya nake ɗan maraƙin jimina gagara ɗaukar shawo. Ke me sunanki" Yarinyar tace.
"Sunana Shamwila Hajiya"
"Okey Shamwila, aikinki shine, girki duk ran girkina, wanke wanke, wankin kayana da kayan
mijina duk randa yake ɗakina. Sai gyaran ɗakina da turakar mijina, sai aika haka in ya kama
zan dinga yi miki. Ina ga shikenan iya aikin. Zamu dinga biyanki duk wata nera dubu bakwai.
Amman fa bana son fashi in ce dai gidanku babu nisa da nan ɗin ko?" Kaila ya shiga ruɗu da
mamakin yanda yaji Bilkisa ta lissafo harda gyaran turakarshi da wankin kayanshi ranar girkinta,
ya soma tantamar tana da hankali kuwa? Ta ya zata sakar ma ƴar aiki girkin mijinta, da gyaran
turakarshi, harma da wanki? Yarinya matashiya, mai jini a jika, kuma kyakkyawa irin haka.
Shiru yayi ya ƙudurce zai taka mata burkine. Muryar Shamwila ce ta dawo dashi daga taɗin
zuchin da yake ta faman yi da zuchiyarshi.
"Gaskiya ina da nisa Anty. Kuma dole sai dai in dinga tawowa da ƙafa, dan in nace kullum zan
cire kuɗin abun hawa kuɗin zai ƙare, kuma ni ke kula da mahaifana da ƙannena" Shiru Bilkisa
tayi tana nazari. Kaila yace.
"A wacce unguwa kike haka, sannan mahaifinki bashi da rai ne da yarinya ƙarama dake
nauyin iyayenki da ƙannenki yake wuyanki?" Shamwila sai ta saka fuskar tausayi tace.
"Mahaifina yana kwance ba lafiya shekaru biyar kenan. Kuma mu masu ƙaramin ƙarfine sosai.
mahaifiyata girma ya kamata. Shine nake buga _buga ina ciyar damu, danginmu dukka suna
Niger mu Sadaka yalla ne, waɗanda ake mana laƙabi da muna bara muna karuwa. A layin ƴan
ƙarya muke da zama can kusa da babtis." Kaila ya girgiza kan shi kawai. Balikisa tace. "To a gida za'a barki ki dawo nan da kwana, in yaso ranakun asabar da lahadi kya dinga
komawa gida? Sabida yanayin nisa, duba da cewar kuna cikin wani hali, zan baki nera dubu
goma duk wata, amman zaki samu ƙarin aiki" Shamwila ta zube tana ta faman godiya. Kaila shi
kuma aka barshi da mamaki. "A ina zata dinga kwana kenan to?"
Balkisa da take magana a gadarance tace.
"A ɗakina ga falo wadatacce, Gwanda sai ta dinga kwananta a kujera ai, tunda kai kana da
turaka" Kai ya jinjina yana tunanin taya kyakkyawar budurwa haka za'a turota aiki harda kwana
a gidan aiki? Tsabar haushi a wajan ya fice ya barsu. Shamwila kuma ta kama aikinta ka'in da
na'in. Dan a wannan rana ita ta gyare ɗakin Kaila tai ma ɗakin turaren wuta, ta wanke toilet, da
kayan da suka cire. Tayi sharar tsakar gidan da wanke_wanke fes. Hindatu sai kallon ikon Allah
kawai take yi. Bayan ta kammala ta tsugunna a gaban Bilkisa da take kwance tana charting da
Kaila tana tambayarshi wai ina ya tafi ne tun safe?.
"Anty inaso zanje in kwaso kayana kuma in faɗa ma Ummata."
"Yauwa Shamwila dama inason zan miki aike kasuwa. Kaza nake son ki siya mun, da kayan
miya, sai kayan lambu" Bilkisa ta lissafama ma Shamwila duk abinda take buƙata, ta bata kuɗin
mota ɗari biyar. Ba'afi awa biyu ba, sai ga Shamwila niƙi_niƙi da boron kayanta gari guda, da
ledar cefane. Bilkisa ta nuna mata bayan lungun show glass ɗinta tace sai dai ta ajjiye a nan. "Inason ki dafa mun jallof ɗin soyayyar taliya da pepper chicken. Akwai kayan zoɓo a kitchen ki
mun zoɓo mai daɗi" Nan Bilkisa ta tusa Shamwila a gaba suka shiga kitchen ta nunnuna mata
abinda ya dace ta nuna mata. Anan ta bar Shamwila tana mamakin yanda aka narkama kitchen
ɗin langa_langa dukiya haka, da tunane_tunane, da burika fal ranta ta shiga aikinta ka'in da
na'in. Cikin ƙanƙanin lokacin gida ya soma tashin ƙamshin albasa da tafarnuwa."
SHANONO:
TANI:
Allah kawai nake ambato, naƙuda ma nake ji kamar inayi. Matan ƙannen Narani ne suka Iso,
Shehulle na biye dasu faram_faram, ga Iya mai Fura itama tana tafe. Ni kuwa zuchiyata sai
tsalle kawai take yi.
"Ina Daudan yake, a wanne halin yake?" Cewar Shehulle kenan cikin ɗaga murya. Yaya Karime
ce ta mishi bayani, tare da nuna mishi inda aka shiga da Daudan. Ni ko hawaye kawai nake
fitarwa bana ko