Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
Gashi kin zo zamu shiga yawon sallama da maƙota" Ɗan dariya tayi tace.
"Ai sai mu je. Da fatan ba ki yi fishi ba. Kin haihu ko barka banzo ba, an muku amarya ma
banzo ba"
Babu komai. Isa barka da rana" Muka gaisa da Isa tare da mun murnar komawa sabon gida.
"Kaila ne yace in soma kai ku can gidan. Ku shiga maƙotan ku fito sai mu wuce in soma
ajjiyeku, sai in kwashi sauran matan nashi" Tare da Jamila mu kai ta bin maƙota muna musu
sallama. Sai Allah sanya alkairi suke yi mana. Muna fitowa Isa ya figemu a mota sai sabon
gida. Kaila ne ya buɗe mana get da sauri, ni naga sai dariya yake yi. Muna haɗa idanu ya gintse
dariyar tashi, ya sau get ɗin. Masha Allah gida yayi kyau ya sha fenti mai ruwan ƙasa, ga filin
tsakar gida masha Allah. Muna firfitowa Kaila ya soma masifa.
"Haba isa dana san haka zaka yi mun ai da ni zan ɗauki motar in je in ɗakkosu. Bilkisa baka
ganin baƙine suka zo mata daga Zaria? Da direba ma suke tafe, direban nasu yaje Bauchi
ɗakko wani saƙone. Da sai ka bar su Shanono su zama ƙarshe." Isa ya hararashi yace.
"Kai dai kaji kunya. Shanonon zan kawo a ƙarshe gidan da tare kuka zaɓi yanda fasalin gidan
kuke son ya kasance. Ko ka mance tare kuka dinga zuwa sauke block ne? Duk wani wahalar
ginin gidannan da itafa akayi. Dan kawai kayi amarya shikenan sai itace zata zama ƙarshen
shiga gidan?" Ni dai ina gefe kamar yajin ƙosai. Yara kuwa guje_gujensu ma suke faman yi a
tsakar gidan. Isa ya nuna mana hanyar babban falo, inda shine mahaɗar ko wanne pat na cikin
gidan.
"Bismillah ku shiga daga ciki, ai kinsan ɗakinki" Sai lokacin Kaila yayi magana yace.
"In kin shiga ki jirani a falo in na dawo zan nuna miki ɗakin ki. Kai kuma ka bani keyn mota in ka
gama soki burutsun zancan" Fisge keyn motar yayi a hannun me shi. Isa ya koma ɓarayin mai
zaman banza ya zauna, suka fita a gidan. Mu kuma muka shiga ciki. Masha Allah, ko ina yaji
tayil, ga ƴan kayayyakina a gefe a cikin babban falon, amman banga na bilkisa ba. Kuma duk
ƙofofin ɓangarorin uku a rufe suke da ƙwaɗo, dan Jamila sai da ta murɗa ko wacce ƙofa ta ji ta
gam. Doguwar kujerar da Sabira ta bani akai muka zauna, jikina kamar an watsa ma kaza
gishiri haka nake ji. Sai haɗiɗiyar yawu kawai nake yi. Minti ashirin bayan zuwanmu sai ga Kaila
da Isa motarsu ta shigo. Sabira ce ta leƙo take sanar mana.
"Gama su nan sun dawo, Amarya a motar da ƴan uwanta suka zo aka kawo su, Abban
Sulaiman kuma ya ɗebo Hajiyayye da ƴan uwanta. Ni dai ina zaune jigum, har su Bilkisa da
tawagarta suka shigo. Hajiyayye kuma suna wajan motar kaya data shigo yanzu. Ƴan uwanta
suka shigo cikin falon da muke, tare da Kaila. Key ya jefo mun cinyata, tare da nuna mun ƙofar
ɗakin dake gefe can. Ciki biyu da falo ne ɗakin sai bayan gidu a ko wanne ɗaki in ban manta
ba Dan da sunan Amadudu aka yanki ginin ɗakin. Ashe ni zan zauna a ciki. Hajiyayye kuma ya
miƙa mata keyn ɗakin da a da nasan turakarshi ne, Bilkisa kuma ya buɗe mata ɗakin da aka
gina shi da sunana, ɗaki mai babban falo da ɗakuna har uku, bayan gida biyu, ga kitchen
yalwatacce, har kantocin cikin kitchen ɗin ni da kaina na zaɓi samfurin wanda nake so, ashe
rabon wata ne. Wannan shine kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Ana cikin haka sai ga
Amadudu da Hindatu sun shigo babban falon da sallama. Key ya miƙa ma Amadudu.
"Ɗakunan dake tsakar gida, kai da Hindatu sai ku jera kayanku a ciki. Ɗayan yaranku sai su
dinga kwana a ciki. Ɗayan kuma Shamwila sai ta dinga kwana a ciki " Gaba mu ka yi abin mu,
Jamila ta buɗe ƙofar ɗakin muka shiga. Dukkanmu tsuru_tsuru mu ka yi a tsakar ɗakin muna
kallon abun mamaki, ni ko hawaye ne kawai yake gudana a Idanuna tsabar damuwa har wani
jiri ne yake ɗibata. Jan fentin mai kaila ya shirɓinamun a ɗakunan nawa babu ko sofane kalar
jinin kare ( maron). Ni ɗakin ma tsoro ya bani wallahi, dan tunda uwata ta haife ni ban taɓa
ganin fenti mai kalar jinin kare ido da idoba sai yau. Numfashi na ja mai zafi. Sabira ta kawar da
tunanina da faɗin.
"Kai Tabarakalla masha Allah. Waje yayi kyau. Tani Allah ya sanya alheri, Jamila mu soma
shigo da kaya ciki ko, mu kafa mata gado?" A tsaye suka fice suka barni ina kalle kalle. Ɗayan
ɗakin ma an toshe ƙofarshi da bulo ga halama nan ana gani. Shi yasa naga wata ƙofar a cikin
falon, kuma wannan ɗakin da aka toshe yafi girma, bayan gidan ɗakin kuma yafi kyau. A
wannan gidan ɗinma a falo yarana zasu dinga kwana kenan, gashi su Hindatu har nasu yaran
sun samu ɗakin kwana, Allah mai iko" Kama musu na yi mu kai ta shigo da kaya. Dake kayan
nawa babu yawa cikin ƙanƙanin lokaci muka kammala komai. Durowar dake jikin bangon uwar
ɗakina Sabira suka buɗe suna ta jera kayan yara. Ni kuma ina saman turmi ina buga labule da
ƙusa dan bani da ƙarfen labule amman mancewa nayi da zan siya na hannu a masallaci. Zama
nayi a kujera ina ba Salis Mama. Jamila tace.
"Umman Sulaiman me za'a dafa ne ya kamata ace an ɗaura abinci, naga gidan ya soma
ɗinkewa da mutane."
To Jamila bari in nemi Abban Sulaiman tukunna riƙe mun yaronnan ina zuwa" Kafin ta karɓi
yaron sai ga sallamar Bilkisa daga bakin ƙofa.
"Umman Sulaiman ki kawo kwano a zuba miki abinci ke da jama'arki"
To Bilkisa zan aiko yara su kawo" Komawa nayi na zauna. Sabira ce ta ɗakko wata
kwaraɓaɓɓiyar kulata babba ta kira yara ta basu su ka kai. Sai gasu da masa da miyar gyaɗa,
harda sinasir, da lemukan roba har katan biyu, da fiya wata leda biyu. Yaran Sabira ta soma cira
ma, su kuma sai da su kai sallar la'asar sannan suka zuba mana namu a tare muna ci suna
hirarsu har da dariya. Duniya lallai ta nai musu daɗi. Ga ƴan uwan Hajiyayye ma a babban falo
sai shewa da surutu suke yi. Dan Hajiyayye tayo gayya sosai, har maƙotanmu ƙawayenta duk
sun zo. Ni ce dai koma baya akan komai, komai nawa yana zuwar mun ba irin na gama gari ba.
Yau da Kaila bai hana Yaya Use zuwa inda nake ba da yanzu tana nan, yaranta. Nayi_nayi ta
turo mun su ma taƙi gudun fitina, ga shi Yaya Karime tana Shanono sai jibi zasu dawo.
"Tani kayayyakin kitchen ɗinki ina zamu jera miki ne, naga kitchen a falo ko nan ne zamu jera
naki kayan?" Cewar Jamila ba tun yau ba na fahimci Jamila tana da son dukan cikin mutum dan
taji zance. Murmushi kawai nayi mata nace.
Ku barshi ai kuma kun gaji, kayan kitchen ɗin ba wani kaya ba, ni kaɗai ma in na nutsa zan
gyara, dan akwai gyaran da ba'a ƙarasa a kitchen ɗin ba" Ni kuma harga Allah tsoro nake ji in
ba da umarni a jera mun kayan kitchen a kitchen ɗin falo in zo Kaila yai mun watsi da kaya a
gaban kishiyoyina, ya tsinkani kamar yadda ya saba. Gaga_gaga haka mu ka wuni cur muna
abu guda. Sai yamma lis Jamila, Isa ya zo ya mayar dasu gida, ashe Amaryar a gidan ta wuni a
ɓarayin Hajiyayye. Har gaban mota na kai Jamila sai godiya nake yi mata. Jamila ta kawo mun
gudumawar kofunan roba dozin guda. Ban jima da shigowa ba Sabira ma tai mun sallama, sai
kuma gobe in mun haɗu a makaranta. Abun sha'awa yara sai facaka suke da ruwan fanfo a
bayan gida, su shiga ciki da gudu, su fito da gudu, wannan rigimar harda Hauwa akeyi. Tana
biye dasu tana ihu da dariya. A babban falo kuma ina ta jiyo hayaniyar maza da muryar Kaila.
Har zuwa bayan Isha, nan fa yunwa ta soma sasuƙar yara, ni bansan tudun da zan dafa ba.
Ragowar masa guda goma sha biyu na basu, na juye musu miyar a kai. Nan da nan suka cinye,
ba sai sun ce mun basu ƙoshi ba, ni kaina nasan basu ƙoshi ba. Lallaɓasu kawai nayi.
Ku yi haƙuri babu abinci ne a gidan. Ai kuna gani yau muka dawo sabon gida ko? Sai gobe
zamu soma ɗaura sanwa." Buɗar bakin Sani yace.
"Umma Munga su Samira, da Jaxuli suna cin tuwo ɗazu" Sai nayi jigum nace.
To bari in leƙa in tambayo muku in bai ƙare ba." Salis na saɓa a kafadata yinwa kamar zata
kayar dani, na nufi ɓarayin Bilkisa. Ashe mugun gyara akaima falon namu. Wasu ɗima_ɗiman
kujeru aka baje, da ƙaton kafet, harda kayan kallo, ko ina sai hasken wuta. Gargaɗin dana tuno
Kaila yayi mun ne yasa na canja akalata zuwa ɓarayin Hajiyayye. Jama'a sun soma sassautawa
a ɓarayin nata. Da sallama na shiga falon. Abun mamaki ƴan uwanta suka watso mun wani
kallo. Daga masu jan tsaki, sai masu cewa wari suke ji, harma da masu toshe hanci. Wani
ƙududu na haɗiye ya faɗa cikina da zafi. Da ƙyar na buɗe bakina, dan jikina yayi mugun sanyi.
Da ba dan bana son yarana su kwanta da yinwa ba, da juyawa ma zanyi in haƙura. Amman
yaya zan yi, wanda bashi da gata ai yana ruwa.
Hajiyayye dan Allah abinci zaki sanmun in ba yaran yinwa suke ji." Wani banzan kallo tayi mun.
Ita da danginta suka saka shewa, kafin tace.
"Wannan abincin ba Kaila bane ya kawo aka dafa. Balle kice suma suna da hakki akai. Daga
gidan ubana ƴan uwana abun alfahari na suka yo aka tawo mun dashi kin gane ko? Sabida
haka bazan bayar ba." Yayarta Ta Bizaaro tace.
"Zamu haɗu a kotu nan da kwanaki zaki san kishi ba hauka bane. Gobe ba zaki sake yin kisan
kai ba. Tani baki ma da kunya, kinga ƙannenmu sai haƙuri aka basu dan dakaki ma su ka so yi,
nice na taushesu" Daurewa nayi dan bana fatan suga zubar hawayena. Juyawa kawai nayi da
sauri. Kiciɓis nayi da Kaila a ƙofar shigowa ɓarayin Hajiyayye. Idanu muka zuba ma juna. Sai
lokacin hawayen da na shanye suka shiga suntiri a kumatuna. Ƙur yayi da idanunshi a kaina,
bai tanka ba, nima ban tanka ba muna tsaye dukkanmu. Kaina na sauke ƙasa nace.
Yara yinwa suke ji Kaila. Bansan da wanne kitchen zanyi amfani ba. Sannan bansan kuma inda
kayan abincin suke ba waɗanda aka ɗebo daga can gidan..
"Dakata Shanono. Wannan gidan ba irin wancan tsohon gidan da muka baro bane. Duk wani
tsari ya canja. Zuwa gobe zan tara ku kuji sabon tsarin da zan fitar. Kayan abinci kuma ki
tambayi Hajiyayye yana store ɗin kitchen ɗinta. Kitchen ɗin falonnan zaki iya jera dattin
tarkacenki, amman ki sani ba kitchen bane na kunna gawaye ba. Yana da ƙofar waje, sai ki
dinga fita da gawayin ta waje. Wallahi muddin naga wani ƙazanta a cikin kitchen ɗin, to zaki
koma girki a cikin ɗakin ki zai fi mun sauƙi." Yana kaiwa nan ya wuce ni, bai faɗa mun yanda
zanyi da yaran ba. Nayi iya dubana ko gawayi babu ban gani ba. Haka dole na koma ɗakina.
Na samu ma yara mazan sunyi bacci a katifarsu wacce aka sa ma rigar leda. Ajjiyar zuchiya na
sauke, ina shiga ciki na tarar da matan ma sun yi bacci. Ni ko a darennan tunanika babu irin
waɗanda basu zo kaina ba. Na gaji da irin wannan rayuwar ƙasƙancin da nake yi a gidan kaila.
Na fahimci tozarcin da nake fuskanta shafi_shafi ne, kuma ko wanne shafi da salon shi.
Rayuwa kenan. Babu damuwa watarana sai labari, zaman gidannan inayine domin goben
yarana kawai, amman nayi imani baƙin ciki da ciwon zuchiya su za sui ajalina. Haka na kusan
raba dare ina kuka da tunano rayuwar da nayi a baya. Da irin mazajen dana aura, da irin
jarrabawar dana fuskanta, dama darasi, da ƙaddarar dake cikin ko wanne aurena biyar. Aure da
sha'anin maza ya gama fitar mun a kaina sam.
Washe gari.
Haka gari ya waye muka tashi cikin yinwa, ni kuwa cikina ƙullewa yayi sosai, da ƙyar na tashi,
na tashi yaran dan su ɗauraye jikinsu su yi sallah. Ni kuma na shiga aikin fitsari. Ruwa na
yayyafa a katifun duka biyu, nasa tsumma na goggoge,abun daɗin, rigar ledar da aka rufe
katifar bai ba fitsarin damar taɓa katifar ba. na fito dasu, ruwan fitsari na yarari. Kaila da
Hajiyayye suna babban falo, da dukkan halama Hajiyayye itace da Kaila. Ta ɗauki wanka tayi
kyau abinta. Da idanu suka bini harna fice da katifun duk biyu, na wanke zannuwan gadon da
zallan ruwa na yaɓa a katanga. Ina shigowa Hajiyayye tace.
"Ruwan fitsarinnan kisa tsumma ki gogeshi, wallahi Baby bazan iya ba. Yanzu ta babban
falonnan zata dinga fitar da katifa kullum?" Ina tsaye ina kallon Hajiyayye, da irin kallon tsanar
da kaila ke jifana dashi. Ko da ya tashi, da zagi ya rufeni, idona ya bushe babu ko sofanen
hawayen ma. Tsumma na ɗakko na goge, na basu haƙuri dukkansu na koma ɗaki. Salis na
tarar a hannun Sani sai kuka yake yi. Tun cikin dare yake jan nono, amman babu ruwan nonon,
kukan yinwane kawai. Sauran yaran ma sun yi jigum sai kallona suke yi, irin kallon ki yi mana
rai" Salis na saɓa a baya. Idanuna duk kwantsa, kumatukana duk busassun yawun bacci na fice
a gidan da karamar jakata. Jefa ƙafata kawai nake yi bansan inda ma na dosa ba. Wannan
masifa dame tai kama. Ni dai na kama tafiya sai nausawa nake yi, kafin in zo titi ma ba ƙaramar
tafiya bace, haka nai ta fama, ina tafe faram_faram Salis sai kuka yake yi........✍
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURENA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA.
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 18
Na ci tafiya sosai. Ƙafafuna su kai busu_busu dasu. Da ƙyar na ga wani shagon yarbawa yana
kallon asibitin Salman dake cikin anguwar. Na ko yi sa'a suna da gawayi, da komai. Kayan
miya, da taliya, maggi, manja na siya. Dubu ɗaya na kashe, na kuma juyawa faram_faram ina
haƙi. A tsakar gida na tarar da su Shafi'i suna wasan tsere ban bi ta kansu ba, na shige ciki na
fito da kurfot ɗina, ta bayan lungun inda ɗakina yake a wajan na hura gawayi. Kayan miyan
kuma na wanke na zuba a turmi, Sani na kira yana jajjage ni kuma ina ɗebo kayan kitchen ɗina.
Babban teburina dake kitchen ɗinmu na tsohon gidanmu na jawo. Akai na jejjera ƴan
tukwanena, da kwandon wanke_wankenmu. Kurfot ɗinma na kinkima na aza a saman teburin.
A daren jiya na yanke hukuncin bazan yi amfani da wannan kitchen ɗin na falo ba, dan akan
kitchen ɗin Kaila zai iya ƙila dukana ma, gara in kiyaye kaina in janye jikina in ƙara komawa
gofe, tunda ina da iyaka a cikin rayuwar Kaila. Taliya na ɓararraka mana na baje mana ita
gabaki ɗaya a tire. Ina gaba Sani na biye dani. A tsakar gida mu ka ci karo da Hindatu tana
wanke wanke a bakin famfon tsakar gidan. An kawata wajan da fararen tayil masu haske.
Gaisawa mu ka yi.
"Ya sabon gida Umman Sulaiman?"
Alhamdulillah sabon gida yayi kyau, yayi daɗi" Iyakar abinda nace kenan nabi bayan su Amina
da suka bi Sani ɗu sunga abinci. Muna shiga falon na tarar da su Bilkisa, da kaila, da Hajiyayye"
"Shanono ki zo ke muke jira, zan yi magana daku" Nufosu nayi na samu ƙasan kafet na zauna
kaina a ƙasa, su ko dake ƴan gaban goshin mijine, ɗaya na hannun daman Kaila, ɗaya na
ɓarayin hagu a saman kujera. Bilkisa na sanye da kayan aikin likitanci, da halama aiki zata
wuce. Itace ta gaisheni. Da fara'a na amsa mata gaisuwarta. "Dubi idanki duk ƙwantsa Shanono. Kai Allah ya sauwaƙe miki." Ƙasa na kuma yi da kaina.
"To dalilin da yasa na tara ku anan ba komai bane face canja tsare _tsare da zanyi a gidannan.
Daga yau ko wacce mace ta dinga girkin