Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 24

57K to 60K   out of 70.8K words

da wata tara zasu sake zuwa wani taron. To na gaji, kya bari kuma in ji da bikin
sunan haihuwar Bilkisa in ta samu ciki, da Hajiyayye " Hannu nasa na karɓi ɗana. Shima ya
fice. Mamaki nake yadda za'a sa ma ɗana sunan uban kishiyata sabida mulkin mallaka, ko
turawan mulkin mallaka ai ba zasu yi wannan kama karyan ba. Da wannan surkullen tunanin
nayi bacci. Nayi bacci a wannan daren sosai, irin baccin da na daɗe banyi irinshi ba.
Magungunana akwai masu saka bacci.
Washe gari.

Tun sassafe nayi duk kaye_kayen daya dace. Ko da na fito tsakar gidan, sai banga buhunhunan
tsunmokaranmu ba. Sai Sani ne yake faɗa mun Sabira ce ta fita dashi, su suka rakata gidan
wankau ta kai mana kayan. Yarona nayi ma wanka. Ni kuma ko wankan banyi ba, bakina kawai
na goge da gawayi da gishir, sai ƙunzugu dana sake. Na ɗan yi kwaskwarima na shirɓina mai
mai gurguwa sai walƙiya nake yi. Ina cikin goya Salis Sabira ta shigo.
"Oya fito muje, dan ina da islamiyya yau" nera ɗari uku na ba Sani.
Ungo ka siyo muku masa kuci. Sai ku fitar da katifar fitsarinku ku sa ruwa. Mu sai mun dawo."
Adawo lafiya su kai mun, muna zuwa titi mu ka hau napep na unguwar rogo.
"Tani. Ga shawara akan lamarin fitsarin yarannan. Ni ina ganin kinga katifunku dukka ko? Ki
siyar dasu gaskiya sai a sai wasu na hannu a bayan masallaci, tunda Habiba Bala ta baki
isassun kuɗi. Sai mu sai ledar fitsarin kwance, yarannan kuma Tani ki dinga daurewa kina
tashinsu yin fitsari mana. Kayanku na kai gidan wanki, saida na yayyafa musu fiya_fiya kinga
kuɗin cizo yanda suke gudu a kayan kuwa? In an wanko sai ki tsince waɗanda suka yayyage
dan Allah ki zubar ko ki ba almajirai. Ni bana son kuje sabon gida da kuɗin cizo kuna ɓata
bango, maganar gaskiya ran kaila fa ba zai yi daɗi ba. Ga makaranta zaki shiga. Kina zuwa a
ƙazance daga malaman har ɗaliban rainaki zasu yi, ki gyara ke ma kiji daɗi mana"
To Sabira in sha Allah zan gyara." Haka mu kai ta tafiya har zuwa bakin lungun da zamu ɓulle
zuwa cikin makarantar. Muna tafe ina adda'ar Allah yasa su ɗauke ni. Makarantace ta gwamnati
babba, mai suna G S S UNGUWAR ROGO. amman sabida yanda sha'anin kasar tamu ta zama
ne yasa ake kiran makarantar da suna shaƙura, tsabar yanda malamai suka ƙi tsaiwa su yi
aikinsu, sai dai ɗalibai sui ta buga tamaula. Itama gwamnati taƙi tsaiwar daka wajan ware kuɗin
malamai. Sai makarantar ta zama gata_gata. Duk fa da haka ɗaliban shaƙura sunfi ɗari, in aka
tashi cika titin mota suke haka zaku gansu kamar fari. To ita wannan makaranta ta matan aure a
cikin shaƙurar take. Wasu malamai masu zaman kansu ne suke kula da makarantar, sai in
ɗaliban shaƙura sun tashi misalin ƙarfe biyun rana. Sai makarantar matan auren a soma biyu da
rabi, zuwa ƙarfe biyar a tashi. Kamar yadda wani malami yake yi mana bayani. Form muka
yanke nera ɗari biyar, yace in cike ran monday ma zan iya soma zuwa, sai in dawo da fom da
fasfo guda biyu. Na biya kuɗin karatu na zango na ɗaya wato S S 1nera goma. Sai jerin littafai
daya rubuto mana wanda zamu je bayan banki mu siya, dana rubutu dana katatu. Muka gama
komai tas. Kai tsaye sai gamu a bayan banki. A wajan inyamuran bayan banki muka sisiyi
littattafan da aka rubuta mana duka, na sai jakar gwanjo, da baƙin sandal shima na gwanjo, da
safunana biyu farare tas. A wajan mu ka yanki yadin inifom jan wando, farar riga da farin hijabi.
Sabira ta ban shawarin yankan yadin inifom ɗin islamiyya shi kuma mai ruwan toka ne duka, sai
baƙar safa da baƙin takalmi, sai ta kaini akai mun fasfo. Dan murna zuchiyata har tsalle take yi.
Duk muka sai abunda ya samu. Sha Allah sai muka dira a gidan mai ɗinki, ta mun duk gwajin
daya dace. Kuɗinta dubu da ɗari biyu ta cajemu. Muka yi da'ita gobe da yamma Mustapha yazo
ya karɓa mana. Bamu muka shigo gida ba sai tara da rabi. A bakin ƙofar gida mu kai sallama da
Sabira, dan tayi lattin makaranta tara dai dai suke soma kilas. Ina sa ƙafa ina shiga cikin zauren
Kaila ya hankaɗoni waje, na tafi taga_taga amman cikin ikon Allah ban faɗi ba. Sai ji nayi Bilkisa
tace.
"Baki ji ciwo ba ko umman Sulaiman?" Ashe tare suke taci ado na tada gari, kallon kaila nayi,
ashe farin takalminshi na na taka mishi. Gashi hatta kafata ƙurane bajaja balle takalmina. Ajjiyar
zuchiya nayi nace.

Banji ciwo ba Bilkisa. Kaila kayi haƙuri bansan ka tawo ba. Da sauri na zamo kallabin kaina ina
shirin goge mai takalmin dan gujema tozarcinshi ya dakatar dani cikin ɗaga murya.
"Kar ki sake ki ba ɗa mun ƙwarlwata. Jeki nagode, kece kina tafe bazar bazar, kamar akuyar
ballagaza, kinga kuwa ina akuyar ballagaza zata samu nutsuwa?" Tsaki ya ja ya dubi Bilkisa
yace.
"Ɗanyan gwal jirani in sako takalmi. Wannan ɗin sai a ba Shamwila ta wanke." Buu ya shige
ciki. Bilkisa tace.
"Kiyi haƙuri dan Allah ummun Sulaiman. Banji daɗin abinda yayi miki ba" Ɗan dariya nayi mata
nace.
La ai babu komai. Ai ibadar aure ta ƙunshi abubbuwa masu tarin yawa." Ɗan murmushi tayi
itama tace.
"Dama Gwanda ne yace yana son ya kaini gidan da yake ginawa in gani. Kinsan ai sati mai
zuwa zamu koma sabon gida ko, kuma kinsan ya siyar da wannan gidan ko?" Dariya nayi nace.
Na ji dai a bakin ki yanzu.
To Allah ya sanya alkairi yasa a koma a sa'a." Ina faɗin haka na shiga ciki tare da cewa da'ita.
Sai kun dawo."


*KAILA*
Yana shiga ya tarar da Shamwila ɗare_ɗare a kan gadonshi tayi goho tana lailaye mishi.
Mazaunanta yabi da idanu, sai wani muskutasu take yi suna tanjan_tanjan. A zuwan bata san
da shigowar Kaila ba. Kuma tana sane fes. Jikinshi taji ya haɗe da nata. Tayi wata iriyar zaburar
da babu inda bai kaɗa ba a jikinta ba. Tsam Kaila ya ƙanƙameta yana kokawa da numfashinshi
wanda yake shirin ɗaukewa. Da ƙyar ya lalubi kunnenta yace.
"Kaila ne. Kar ki yi ihu nine. Grayan gado kike yi?" Yanda yake jan maganar ba ƙaramin gigita
Shamwila yayi ba. Dama Kaila gwanine wajan iya sace zuchiya. Saurin fisge jikinta tayi a nashi,
tare da faɗawa kan gadonshi, tana wani irin ja da baya, ga wawan zama da tayi. Ba shiri Kaila
ya bita. Ƙaran wayarshi ne ya ankarar dashi aika aikar da yake shirin yi. Babu shiri ya fasa bin
Shamwila ba dan hakan yaso ba. Wayarshi ya miƙa mata.
"Samun number ki anan. Zan kiraki anjima ki je A 1 ki same ni ko S F C." Da sauri Shamwila ta
tiyfa mishi numbernta ta bashi wayar, bayan ta tabbatar hannunsu sun haɗe dana juna. Takalmi
ya sake a gurguje ya fice." Kama hanyar filin sukuwa su ka yi anguwar da Kaila yai gini kenan.
Unguwar masu kuɗi da amare, unguwa mai tsari marar hayaniya. Da a wajan ake yin polo (
KWALLON DOKI) A lokacin turawa ke yin wasan. Sai masu talle da ke ai kayan sana'arsu.
Daga baya gwamnati ta yanka filin, jama'a su kai ta tururuwar saye. Cikin ikon Allah unguwar
sai ta shahara, ta zama babu irin unguwar a cikin garin jos, sai dai ta bayan gari can. A wannan
unguwa Allah ya hore ma kaila katafaren gida mai ɓarayi uku. Sai ɗakuna falle falle guda uku.
Nan ya kai Bilkisa ta dinga yabon gidan. Ɓarayin da yafi ko wanne ɓarayi tsaruwa har da na shi
kanshi mai gidan nan Bilkisa ta zaɓa. Masu aiki suna ta gabatar da aikinsu, gobe fenti za'ayi
kuma. Suna gamawa da nan Kaila ya kai Bilkisa gida, shi kuma ya wuce wajan sana'arshi cike
da zabarin son kiran Shamwila dan jin shanyayyar muryarta. Ai kuwa yana samun sarari ya
danƙoro ma Shamwila kira, tare da karonto mata adireshin inda zata same shi. Shamwila a
lokacin tana kitchen ta gama abincin rana kenan. Dama a shirye take tsab. A gaban Bilkisa ta

tsugguna.
"Anty ummanmu ce ta kira ni jikin Babanmu ya tashi, suna bukatar in je zan kai musu kuɗi"
Bilkisa ta dubeta ta watsar, dan ita irin masu adankiya ne ( I don't care) Jaka ta ɗakko ta bata
dubu biyar.
"Gashi kwa ƙara. Amman kar ki daɗe, sabida girkin dare ko? Shi kuma Allah ya bashi lafiya." Da
"Ameen" Shamwila ta amsa mata. Tasa kafa ta fice. Sai A1. A harɗe a kan kujera ta samu Kaila
sai cika baki da guggurun A1 yake yi, bakinshi duk madara.( Jiki duk madara ) Yana
hango Shamwila ya shiga yashe bakinshi, harda wani kashe idanu. Waje ta samu ta zauna. "Barka da hutawa" Baki ya kuma washe mata mata.
"Shamwila, Shamwila, kin samu karasowa kinga yanda ki ka yi bala'in kyau kuwa. Zauna da
kyau yau ai rana ta ce. Me kike son a kawo miki, gugguru, ko abinci?" Fari tayi da idanunta
tace.
"Soma gabatar da abinda yasa ka kirani. Dan Ɗanyan gwal taka lokaci ta bani. Abincin darenka
na bisa wuyana" Murmushi yayi mai ƙayatarwa, ya kashe mata idanu yace.
"Ai sabida tsabar son abincinki da nake yi. Inason da zaran mun koma sabon gida zan sa ki
dinga mun girki ko da yaushe. Ko wacce mata tayi girkinta da yaranta, nawa girkin da ban." Ido
ta zare tace.
"Tayaya hakan zai faru to, alhalin Ɗanyan gwal ce ta ɗaukeni aiki?" Ƙur ya bi tsakiyar fararen
dara daran idanunta da mayataccen kallo, mai firgita ƴan mata, da narkar da zuchiyar mata.
"Ni zan ƙirƙiri hakan ya faru. Ke dai naki ido Ɗanyan jini." Dariya tayi mai burgewa tace.
"Nawa sunan kenan ɗanyan jini? Ina godiya da wannan suna. Amman har yanzu fa banji dalilin
zamana a gabanka ba"
"Ɗanyan jini. Sonki nake yi har cikin jijiyata. Tun kallon farko da nayi miki na jaraftu. Kuma ni
aurenki zanyi, amman sai zuwa nan da shekara ɗaya. Amman zaki zama matata ta bayan fage
kin gane yhah?" Yana magana irin na cikakkun ƴan duniya, waɗanda suka ga jiya su ka ga
yau." "Taya hakan zata faru, bayan matanka uku, sai dai mu yi sabgarmu a waje ina tsoro gaskiya"
Gugguru ya watsa tare da taunawa, kana yace.
"Ai kema matar gidance, yanda zan turmushesu a turaka ai kema ya kamata in turmusheki a
turaka" Kai ta gyaɗa tace.
"Ko in turmusheka ba, ai ni nafi karfin kab matanka" Daga haka suka shiga musayar kalaman
da suka shige ka'ida. Kafin su ankara har biyar na yamma ta gota." A zabure ta miƙe. Kaila ya
riƙo hannunta ya tafa mata dubu talatin, su kai sallama kowa ya kama gabanshi."




SHANONO:
Yau haka na wuni cikin farin ciki da nishaɗi, Allah _Allah nake yi monday tayi in soma zuwa
makaranta. Ina ta shirye_shiryen makaranta, na zube littattafaina duka a cikin jakata. Yaran
kansu suma cikin walwala suke sakamakon walwalar da suka gani tattare dani. Kuma daɗin
daɗawar farin cikina shine, waya da nayi da Habiba Bala take sanar dani, zuwa gobe za'a yima
Dauda tiyata yana asibiti yana karɓar kulawa ta musamman, ƴar aikinta na kula dashi a asibiti"

Sai naji zuchiyata ta yi wasai. Tamkar bana cikin wata matsala. Sani da Shafi'i sai guje_guje
suke yi. Allah sarki uwa, farin cikinta da walwalarta shine taga yaranta a cikin nishaɗi, haka
suma yaran ganin mahaifiyarsu a cikin walwala na sanya su kazar_kazar. Haka dai yau muka
wuni cikin annuri. A tire ɗaya mu ka ci tuwon dare. Bayan sun je sallar isha sun dawo muka
kulle ƙofarmu. Dan tun da Hajiyayye ta dawo wuni tayi tana ƙunduma zagi iri_iri, so take in
tanka ta jawo ni ta huce haushinta a kaina. Washe gari ma muka tashi zuchiyata fes. Sai dai
zuwa sha biyun rana sai ga sammaci an aiko mun daga kotu. Hakanne yai silar mutuwar jikina,
sukuku na wuni, sai jan ƙafa nake yi, bansan yanda shari'ar zata kaya ba. Sati biyu alƙali ya
yanka mana zamu soma shiga kotu. Shikenan gidan yari za'a aimu kenan ko? Tunda da kisa
ake tuhumarmu. Ban ɗaki na shiga naci kuka na na gode Allah. Da yamma Sabira ta shigo ina
tsakar gida ina kaɗa miyar kuka. Sai gata da ledar inifom ta kawo mun. Ganin idona yayi jawur
ne yasa tace.
"Wata matsalar ce ta afku ko me? Ba dai wani abun ya haɗaki da Hajiyayye bane, dan ina jiyo
buyaginta ina tsakar gida ina wanke ganye"
Hmm daga kotu aka aiko mun sammaci, nan da sati biyu za'a gurfanar damu. Shine jikina duk
yayi sanyi, kinsan sharia tamkar mace mai ciki ne, babu wanda yasan me zata haifa, sai abinda
Allah ya bata." Dafani Sabira tayi.
"Da yardar Allah Alkhairi zamu ji. Tunda dai ba Yaya Use bace ta kashe yaron Hajiyayye ba. Ke
dai ki dage da kai kukanki gun ubangiji Allah zai sa a dace. Kin kira Habiba Bala kin sanar
mata?
A'a zan kirata dai yanzu, so nake in sauke miya." Sabira ita tai ta tausar zuchiyata. Tare da'ita
muka kira Habiba Bala a waya. Hankali itama ta kwantar mun. Ta sanar dani cewar jibi zata
shigo ita da lauyan da ta ɗaukar mana. Ina kashe wayar sai ga Yaya Use tana kirana. Itama
jikinta duk ya mutu. Haka na kwanta cikin zulumi. Ban samu barci ba, gashi zani makaranta.
Haka na tashi tun kafin asuba, tsabar zumuɗi. Duk da batun kotu ya ture mun murnar da nake
yi. Yara na shirin makaranta, ni kuma ina bakin gawayi ina dumamen tuwo. Sani ne ya fito da
katifarsu ya jingina yana kwara mata ruwa. Ya ɗaga butar zai sheƙa ruwan kenan. Ashe kaila ya
doso. Ai kuwa yana watsa ruwannan ruwan fitsarin yai tsalle sai a jiki da fuskar Kaila. Ihu ya
sake harda cewa.
"Wayyo Allah Shanono zata halakani nima"......✍NA FAƊO DAGA BENE.......
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 16


Assalamu alaikum.
Allah ya nufeni na dawo. Nagode da jumurin jira. A ɗan hutun dana tafi naga zahirin irin
soyayyar da kuke ma wannan littafin. Ina godiya.


*(Domin soyayyarku gareni da rubutuna. Akwai promo da zanyi muku na turarukan wuta da
humra setine mai bala'in kyau. Kunsan dai Kanuri mune turaren wuta da humra, namu da
banne, ke kanki in kika yi amfani da waɗannan set zaki gode mun. Akan farashin 10k kacal na

bar muku farashin promo domin ku. Mutum ishirin kaɗai zan cire suke da damar mallakar
wannan setin mai sanyin daɗi. Kuma iyakar ƴan paid group ɗina ne kaɗai zasu samu wannan
garaɓasar. Ku yi hanzari duk mai buƙata ta kasance a cikin mutum ashirin da zan ɗiba.)*








Da sauri na miƙe tsaye kamar ba ni bace na wuni sukuku. Baki na riƙe kawai ina kallon Kaila. A
guje Bilkisa da Hajiyayye suka fito. Hajiyayye tana ganin abinda ya faru taja wani irin dogon
tsaki tayi komawarta ɗaki. Dama ɗakin nata cike yake da ƴan uwanta. Kamar yinwataccen zaki
haka Kaila ya dira a wuyan Sani ya far mishi da mahaukacin duka, tamkar yana dukan ƙato.
Dama haka yake musu irin wannan dukan. Bilkisa ta isa a guje ita da Hindatu, amman sun kasa
ƙwatar Sani a hannun kaila. Har ya fashe mishi ɗan bakin nashi. Tsam na miƙe na koma ɗaki.
Yaran suka biyoni ɗuu. Zaunar dasu nayi, ni ko na kasa zaune na kasa tsaye, ina jiyo Sani yana
kirana.
"Umma ki ceceni zai kasheni, wayyo Baba wallahi bansan kana zuwa bane, wayyyooo" Kuka na
fashe dashi, har muryar Sani ta dashe. Baban Mustapha ne ya burmo gidan namu. Ina jiyo
muryarshi tun daga zaure. Shine ya ƙwaci Sani a hannun Kaila. Da mugun gudu Sani ya shigo
bakinshi na zubar da jini da yawu, gefen idanshi ya kumbura. Ƙanƙameni yayi tsam sai cusa
kanshi yake a jikina. Hannuna na ɗaura a saman kanshi ina shafawa.
Ya'isa kayi shiru kaji Yaya. Babu komai, ai mahaifinka ne hukunci yayi maka. Muje in wanke
maka bakinka, ku ci dumame ku kama hanyar makaranta, kayi shiru ya'isa" Da ƙyar a ranar
nasa Sani ya yarda ya tafi makaranta, bakin shi ma ya aune sosai. Ko bayan tafiyar su Sani
makaranta na jima a ɗaki ni kaina bansan zaman me nake yi ba. Ni ba tunani ba, ni bansan
adda'ar da zan dinga yi domin kore damuwa da baƙin ciki ba. Habiba Bala ce ta sanyaya mun
raina data kira take sanar dani an yi ma Dauda tiyata cikin nasara, amman yana bacci a lokacin.
Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuchiyata. Kawai na sau ma Habiba Bala kukan farin ciki, sai
jero mata godiya nake yi, ita kuma tana ta rarrashina, da haka mu kai sallama. Ina dai zaune,
bani na fito ba sai wajajen goman safe. Kiki_kiki na ɗaura miyar dare, tana tafasa na kaɗa.
Miyar kuɓewa nayi bushasshiya, Sai na mayar da ruwan wanka kan wutar, na soma yanke
farata na, waɗanda suka cika da datti, sunyi baƙiƙƙirin dasu. Tas na yanke farcen ƙafata dana
hannuna, na faɗa bayan gida, ina cuɗawa na bi da ruwa na fito. Misalin dayan rana sai ga su
Sani sun shigo hajaran majaran sai warin rana suke dokawa."
"Umma yinwa" Cewar Shafi'i dama shi kam ba mai jurar yinwa bane sam. Sani da Sulaiman ne
dai masu dama dama. Balaraba ita bata zuwa boko, islamiyya kaɗai take zuwa. Abinci na zuba
musu su ka ci, dan zumudi ni ko abincin na kasa ci. Ƙarfe biyu bata cika ba na saka inifom ɗina
har nayi goyo. Yara suka kalleni suka kwashe da dariya, Sani har yana ƙwarewa. Nima dariyar
nayi bance uffan ba. Farin hijabina na saka na

20 / 24