Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
da bansan sunanshi ba. Baffa ya sai mana abinci. Shinkafa garau_garau
ce ya siya mana akan wani ɗan tallah. An yi mata zubin ɗari_ɗari, kowa ya ɗauki ƙwano ɗaya.
Wata rumfa muka nufa anan muka yi zaman dirshan. Hauwa na sakko daga baya, sai da ta
ƙoshi sannan na ci abincin na bi da ruwan leda guda ɗaya. Inno tace.
"Baffa ni kam zan kama ruwa, kaga Shanono daga nan da tafiya sosai, gara in rage marata,
Indo muje ki rakani mu nemi wajan ciyayi haka sai in yi." Ai Inno na faɗin haka duk muka miƙe
ko wacce da guntun fitsarinta ga mararta. Wani gida muka samu daga bayan wasu rumfuna, a
gidan muka kama ruwan, sannan muka shiga mota, bamu tsaya a ko inaba sai a Shanono.
Idanu na lumshe na shiga tuno irin rayuwar auren dana gudanar a shanono, duk su ka dinga
dawomin. Tuno da Dauda ɗana ne yasa na ɗan saki ajjiyar zuchiya. Baffa ne ya katse mun
tunanina da cewa.
"Inno acan gida zamu sauka, jiya ina wajan bara Jafaru ya kirani, nace ya buɗe ɗaki ya ƙyara
mana. In yaso ko zuwa yamma ai sai ku kintsa kuje gidan Deluwan ko?" Inno tace.
"Tunda ka yanke hukunci ai shikenan Baffa. Amman ni kam ai so samuna daga nan sai gidan
Deluwa, ana can anata sha'anin biki ka sani. Tun shekaran jiya ya kamata ace na iso garinnan
fa haba Baffa" Da ihu_ihu Baffa yake magana kamar faɗa irin na makafi, sake ƙwalla muryar
tashi yayi yace. "Da wannan tulin tsarabar kike son ki je gidan biki, shingin duk abi a sace, bazai yiwu ba. Use
nuna mishi hanya kinji mu je unguwar Shakogi." Yaya Use tace.
"To Baffa. Lauwali kwana zaka yi, ka miƙe har gaba da ceɗiyar can. Kana yin kwana gidan
kenan"........
Mrs Bukhari ce
Sai Allah ya sadamu ni da ku ranar Monday. Bana posting ranar asabar da lahadi
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 9
Asalin garin Shanono. Fulanine na usil waɗanda sukai fice ta ɓangaren noma da kiwo. Suna da
mata kyawawa ga gashi sosai, kuma ba ƙauye bane irin ƙayau ɗinnan ba, dan suna da kwalta,
akwai ruwan, suna da lantarki, asibitoci, kana suna da makarantu masu dama, kuma yara suna
zuwa makaranta ba kamar sauran ƙauyuka da muka ji su a baya ba. (Ƙaramar hukumar shanono) an kafa garin shanono zuwa ga sanannun ƴan uwa biyu. Jaukere
da shanu, waɗannan ƴan uwa biyun. Suna zuwa ƙasar domin yin kiwo, ana kuma kyautata
zaton sun fito ne daga garin Hadejiya dake jihar jigawan dutse a yanzu. Ganin cewa ƙasar tana
da tile kuma tana da kyau ga dabbobinsu suna kiwo manyansu sun zauna a wurin a ƙalla
shekara ɗaya kafin su ci gaba, amma da lura da yanayin yankin daya dace, sai suka yanke
shawarar ci gaba da zama a wurin tare da dabbobin nasu. Bayan samun wurin da ya fi dacewa
sai SHANU ya yanke shawarar komawa baya kaɗan don gabatar da garin Shanono ya bar
JAULERE ɗan uwansa a wurin. (JAULERE TA YANZU) ya zo ya kafa aikin sa (riga) a garin
shanono na yanzu har zuwa yanzu Rijiyar taushe a shanono. Garin a halin yanzu ana ganinsa a
zahiri. Ga jerin mutane da sarakunan da su ka milki Shanono. Kabiru isyaku ( ɗan shanono na
yanzu dakaci shanono) akwai Hakimi. Tun da Shanono ta zama ƙaramar hukuma suka fita daga
ƙaramar hukumar Gwarzo a 1989 sunansa Alhaji Bello Abubakar kambun bunun Kano daga
2004 zuwa yanzu. Shanono na da yanki na 697 km2 da yawan jama'a ² a ƙidayar 2006. Lambar
gidan waya na yankin ita ce 704(1) manyan mutanen garin sun haɗa da marigayi Alhaji Ibrahim
aka Ibrahim ( ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Barau (Ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Haruna
Muhammad Shanono. Mariga Alhaji Bawa Mashin (Man0mi) marigayi Ɗan Anni ( Ɗan siyasa)
marigayi Alhaji Haruna Naganga ( cocas chairman) marigayi Alhaji Shehu Shanono. Farfesa
Nura ( masan kwamfuta) dandalin matasa na shanono ( ƙungiyar ci gaba) da dai sauran fitattu a
Shanono da lokaci bazai bani damar jero su ba.
Shanono:
A daidai ƙofar gidan su Baffa Lauwali ya tsaida motarshi. Ai kuwa Baffa Jafaru, da Baffa Yusuf
suna gano mu suka miƙe daga kan kututturen da suke zaune, suna shan iska a kasan bishiyar
durumi. Rana ake kwanɗawa sosai da sosai, matasa gasu nan daba_daba sunata afkin fira,
kasancewar da rani ne, babu noma sai kiwo." " Naroro, Inno kune da tsakar rana haka, maraba da baƙin birrni. Use, Karime, Tani, Habu, Indo.
Sannunku da hanya. Babban direba sannu" Da murmushi a fuskata nace.
Barka da gida Baffa Jafaru da Baffa Yusuf." Baffa yace.
"Kuna gida baku je aikin hatsi ba Jafaru, ko su Tanimu kuka tura?" Inno tace.
"Lauwali mu je ciki kaci abinci, in kayi sallah Allah bashi sai ka kama hanya. Jafaru muna da
kaya a mota ku shigo mana dashi ku da su Use." Inno tayi shigewarta ciki, tana ta cogala
ƙafarta. Tausayi ta bani dan ƙasar da zafi sosai, gashi ko takalmi babu a ƙafar Inno. Allah ya
hore mini in sai ma Inno keke ta huta da zafin rana, ko sanda." Da tulin kaya muka shiga
babban gidan mai yalwar filin tsakar gida da yalwar matan gida da yaran gida. Dan Baffa su rai
ashirin cib mahaifinsu ya haifa malam Jauro Ja'e. Kuma a cikin ƴaƴa ashirin ɗinnan macen su
ɗaya ce itace Goggo Ige. ( Hausawa na kiran sunan Ige ne ga macen da ta biyo maza zuryan)
"Ah Inno maraba lale kune da rana haka, an tawo biki ko? Tani ashe ƙafafuwanki zasu sake
taka ƙasar garin Shanono idanunki kenan?" Inji Baba mai riga matar Baffa Jafaru, mace mai
faram_faram da son zumunci kenan. Dan duk da yawan yawonmu baisa ta dena ziyartarmu a
duk garin da muka ya da zango ba. Ɗakinta ma ta ja mu baki ɗayanmu. Baffa kuma su Baffa
Jafaru suka janyeshi shi da Lauwali. Bayan mun zauna mun sha ruwa. Nan fa ɗakin Baba mai
riga ya cika maƙil da matan ƙannen Baffa, da sabbin idandunan da ban sansu ba, da yara
rututu. Gaisuwa da taɗin yaushe gamo yaƙi ƙarewa. Da ƙyar muka yakice mu ka rama sallah.
Baba mai riga ta saukemu da kwaɗon ganyen dimkin yaji albasa da ƙuli. Baba Marka ta kawo
mana damammiyar fura da nono wacce ta ji zuma. Kowa ya bar gida gida ya barshi. Haƙiƙa
garin Shanono garine mai tsaiwa a rai sosai. Suna da son zumunci, da son taimako. Kuma
bugu da ƙari kusan kowa ɗan uwan kowane a Shanono. Inno tace.
"Oh Marka ni ko banga matar Katagi ba, shi kanshi Katagin ban ganshi ba" Ɗan dariya Baba
marka tayi tace.
"Wannan yaron ai yana legas da iyalin nashi, ya samu aiki a wani babban gidan abinci.
Shekararshi guda da tafiya, wallahi dawowarshi gida na uku, sai Baffansu ya bashi shawarar ya
tafi da ita iyalin nashi." Kasancewarshi Ɗan fari a wajanta yasa tai mishi alkunya da wannan
yaron, kamar yadda yazo a al'adar malam bahaushe. Hausawan zamanin da an sansu da
yakana da kunya, haɗe da kawaici da kara. Amman kwaikwayon al'adun wasu ne yasa tamu
al'adun suka samu tawaya, daga wannan lokacin mace macen aure yayi yawa a ƙasar Hausa.
Gabana ya yanke ya faɗi da jin an ambaci Katagi. Katagi ya nuna kwaɗayin aurena a fili, ni
kuma Allah yana gani tsanar da naima Narani ce ta shafi Katagi, da tuno da Kaila da nayi, da
irin kulawar da Kaila yake bani a dai_dai wannan lokacin muna matsayin saurayi da budurwa
kuma a lokacin soyayyarmu da Kaila tayi zurfin da bazan iya juya mishi baya ba, kuma ina jin
maganarshi fiye da maganar kowa a duniyata. Allah yayi Kaila mutum ne shi mai daɗin baki da
iya tsara zance. Daga baya ne na gane ashe tantirin gogaggen mayaudarine. Gashi da iya
ɗaukar wanka aljihu babu ko sisi. ( Wannan kuma ɗabi'ace ta samarin Jos. Allah yayi da dama a
cikinsu mayaudara masu iya layancewa. Bugu da ƙari akwai iya wanka ba ko tasi a aljihu. A jos
ne zaku ga gaye iya gaye, yayi wanka iya wanka, amman yana kan titin salisu Adamu yana tafe
ɗai_ɗai kamar bazai taka ƙasa ba. Jasawa ayi haƙuri nima ƴar Jos ce na rayu a Jos sama da
shekaru ashirin, nasan komai ). Muryar Baba mai riga ce ta katseni.
"Uhm Inno ai Katagi ya zama babban mutum, gonakin shi a shanono ai sunyi goma. Kuma duk
nomesu yake yi tsab, irin wannan yanayi na rani yake fitar da abincinshi cikin garin Kano.
Yananan yana ɗanɗasa gida a gaba dasu Tabawa kaɗan. Kuma yaron gashi da zuchiyar yi, in
ya tashi yo aikennan baki gani ba, baya mancewa da kab iyayen nashi. Yama kusan ƙarin aure,
mai Anguwar anguwar gabanmu ya bashi babbar ƴarshi." Ni dai nayi tsumu_tsumu dani. Su kai
ta rabtako zancen Katagi da irin samunshi. Baba Marka ce tace.
"Tani ai ko Dauda yana yawan zuwa gidannan. Su Tasi'u ne abokan wasan nashi. Kinsan
Narani ya sashi a gareji, to garejin nasu yana nan anguwar. Amman an kwana biyu baya zuwa
wallahi. In ce dai zaki daure ki mance da duk abinda ya faru kije ki ga ɗanki ko shima zaiji daɗi?
Tani rayuwar haƙuri akeyi, wallahi duk wacce kike ganinta a cikin ɗakin aure. Imma babba ko
yarinyar mace, zaman bazai yiwu mata ba madamar batai haƙuri ba. Yara_yaran cikin gidannan
da suka ɗaɗɗauko mata. Kusan rabinsu da kwata du sun yi saki, sakin fa a cikin ƙabilar
Hausawa ya zame ma mazan kamar wani ado. Face maza na gari da suka kasance sun san
abinda suke yi. Kuma ba rashin addini ba, ba rashin kyawawan al'aduba, face watsi da mu kai
da koyarwar Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama, mu kasa ƙafa muka shure al'adunmu, muke
hanyen turawa da mutanen kudu waɗanda addini da al'adarmu suka banbanta. Mu da ƙabilar
Hausawa bamu san wani yawan mutuwar aure ba. Sai kiga mace sama da shekaru saba'in tana
tare da mijinta na lalle. Ta ba gamu ba mun doshi shekaru sittin a ɗakin aure, ɗuwawu duk ya
dame da kashi, amman anata bugawa dai. Ke mu fa a al'adar malam bahaushen da, ko anguwa
bama fita da rana. Da asussuba muke fita, sai dare ya rufa muke dawowa. Ko kuma mu fita da
daddare. Sabida kunya, da killace mace irin na malam bahaushen da, ba irin na yanzu ba."
Take kawaye ya soma shatata a kumatuna. Sufa duk a ganinsu, nice nake ƙure duk mazajen da
nake aure har take kaimu ga macewar Auren. Da an magana suce mace tayi haƙuri. Sai hawan
jini ko ciwon zuchiya ya rabketa ta mutu suce Allah yayi, kwananta ne ya ƙare. Alhalin baƙin ciki
ne yai sanadin katse mata numfashinta. Wani sa'in macen ma nason ta zauna a gidan nata duk
rintsi duk wuya, amman mazajen basaso, duk hakkinta daya gama ɗauka, da gallaza mata daya
dinga yi, bazai isheshiba hakan, sai yayi mata tukuicin saki, wata ma harda tagonashin duka, ko
karɓe yaro, irin yadda Narani yayi mun akan Dauda. Inno tace."
"Kune iyayen nata ku dai sake faɗa mata. Dan ubanta ya lashi takobi a wannan karon in ta kaso
aurenta, to ba dai gidanshi ba, ba dai Shanono ba. Kuma ita tasan waye Baffa, shi a makafin
ma kafiyarshi irin ta kutarece, ga mitar tsiya. Dan a yanzu haka nasan Tani bata ƙi wannan
auren ya kuma turguɗewa ba. Kullum tazo gida da abinda zata ƙirƙiro ta faɗa. Sai da uban wata
rana data tawo raɓe_raɓe da ciki da goyo wai tayo yaji. Wallahi dukan da Baffa yayi mata ban
zaci yarinyarnan gata ba zata haihu a take a wajan ba dan tsabar duka. To da taji fa babu
daɗine shine ta dena ƙorafi shekara uku kenan. Sai dai kullum a rame kamar ita ake yanka ana
miya" Kuka nake rerawa mai fitar da amon muzanta da tozarta. Jina nake wata ta daban a cikin
ƴan uwana mata. Dangi duk sun bugamun hatimin rashin zaman aure. Wasu ma suna kirana da
mai auren sha'awa. Wasu suce mun mai ruwan ido. Sunaye maras daɗi dai. Akuyata ta riga da
tayi kuka a cikin dangi. Nina kafe tarihin aure biyar, bana fatan wata ta kafa irin tarihina." Baba
Marka daga baya su kai ta rarrashina. Inno kuwa wanka tayo ta shirya tsab, tana rabon tsaraba
tana sake jaddada musu labarun da in haddace sun riga da sun daɗe da haddacewa. Yadda
suke ji, da irin halin da suke shiga, da irin tsangwamar duk da suke shiga in ina gabansu ina
zawarci. Wai me yasa iyaye da jama'ar gari basa yi ma BAZAWARA uzirine? Har ta gama rabon
tsarabar batai shiru ba.
"To ni kam zan wuce gidan bikinnan. Ke Tani Karime ta raka ki ku je ku dubo Dauda. In yaso
kwa same ni a can gidan bikin zamu tafi da su Use. In shi Naranin ya amince muku sai ku
ɗauko Daudan ya ɗan zauna dake kafin mu tafi. In bai amince ba ku bar mishi abunshi" Ajjiyar
zuchiya na sauke, naji sanyi a raina sosai. Tare da adda'ar Allah yasa Narani ya amince ya ɗan
bar mun Daudan mu ɗan zanta" Da haka muka shirya. Na cire tsarabar da nayo ma Dauda na
kwancen kaya da takalmi na riƙe. Muka kama hanyar Unguwar Marabutawa. Muna kusantar
gidan ina hangoni a lokacin danai fitowar ƙarshe babu ko mayafi balle kallabi. Ina kuka, ina
ambaton Ɗana kar ka raba ni da gudan jinina Narani" Abubbuwa da yawa suka shiga yi mun
yawo. Bansan sanda na yar da ledar hannuna na wuya ba. Ji nayi na fasa shiga cikin wannan
gidan mai ɗumbin tarihi, gidan da anan matsalata ta soma. Gidan dana zama ɗanya ina wari
sabida wanka da ruwan sanyi da ɗanyan jego. Gidan da na kusan rasa hankalina tsabar
damuwar ɗa namiji."
Kuka nake yi mai ciwo, irin kukan wacce ta fama wani babban gyanbon daya daɗe yana ruruwa
a ƙasan zuchiyarta. Yaya Karime ce ta dafa ni.
"Haba Tani wai ke dan Allah ba kya mantuwane? Duk abunda ya faru ai ya riga da ya faru.
Yanzu yaro muka zo gani, Narani bai isa ya koro mu ba, bai kuma isa hana ki ganawa ko
keɓewa da ɗanki ba. Ki cije mu shiga gidannan ki ga ɗanki. Ki sani shima yana da hakki a
kanki, ba kya tsoron shi yaron ya girma ya dinga tunanin kamar kin watsar dashi ne?" Numfashi
naja, tabbas shima yana da hakki a kaina. Hawayena na share zuchiyata da hantar cikina nata
kaɗawa haka muka shiga gidan a bisa jagorancin Yaya Karime. Sai na tuno sanda aka kawoni
gidan a matsayin Amarya, su Baba marka na cewa in shiga da bismillah kuma da ƙafar dama.
Duk wani taku dai dai yake da bugawar zuchiyata. Sallamar Yaya Karime ce tasa hankulan
matan gidan ya karkato izuwa garemu. Na san da dama, da dama ban sansu ba, basu sanni
ba. Sai dai nayi imani ba zasu gaza samun labarina ba.
"Sannun ku, mun same ku lafiya?" Cewar Yaya Karime. Kallon ƙuda muke yi ni da Ta Maulidi.
Tana ganina ta datse annurin dake shimfiɗe a kan fuskarta, tsaki taja taci gaba da dakan
masarar yin tuwo, wanda ya zama ta'adar gidan. Fiddausi da Ɗausiyya matan ƙannan Narani
ne suka ce. "Tani ashe rai kan ga rai, umman Dauda ashe baki mance da mu ba?" Ɗan murmushi na ƙaƙaro
cike da ƙarfin hali da juriya nace."
Ba gashi yau rai ya ga rai ba. Ɗausiyya na same ku lafiya ya bayan rabuwa?"
"Sai Alkhairi Tani. Ku ƙaraso daga ciki Iya mai Fura tana ciki" Naga mun gaggaisa da kowa cikin
fara'a banda Ta Maulidi wacce take ta waƙa tana shilla taɓarya tana cafewa"
"Ina wuni Ta Maulidi, na same ku lafiya?" Harara Yaya Karime ta zuga mun tace.
"In ma ba lafiya kika same su ba, meye naki?" Ai Yaya Karime na faɗar haka Tamaulidi ta soma
tafi tana dukan cinya. Habaici da gori dai mun shashi, ƴaƴan mabarata. Da kyar na jaye Yaya
Karime muka shiga ciki. Iya mai Fura tana zaune tana cura fura muka shiga da sallama.
Idanunta ƙifi_ƙifi duk ya dame irin na tsofaffin fulani. Amman ras Iya mai Fura ta gane mu fes.
Bayan mun gaisa Iya mai Fura tace.
"Tani ni na ɗauka kin haƙura da Dauda ne ai. Kin tafi babu ko waiwaye, kuma ke iyayenki
fulanin tashi ne, ballantana mu mu neme ku mu kai muku shi yayi ziyara. Inno dai tana zuwa
ganinshi duk randa ta shigo Shanono. Kuma ana kawo mishi saƙo, kuma ana faɗa mishi daga
wajan gyatumarshi ne. Wacce Fatsumar ce a bayanki?" Yaya Karime tayi dariya tace. "Wannan Hauwa ce ba Fatsume ba?" Baki ta turo tayi zunɗe harda kashe ido tace.
"Duk shegiyar ɗarin ce, itama tsohuwarce ita ta haifi gyatumina" Dariya muka yi dukkan mu.
Tace.
"Tamaulidi ta nuna muku Daudan ne? Yanzu ma ya gama bacci a tsakar gidan fa"
A'a bamu ganshi ba" Tashi tayi tasa ƴan uwanshi nemoshi a waje. Fura ta dama ta bamu."
"Ai yana ko almajirci a can wani ƙauye mai nisa, yanzu haka ma sun kusan tafiya. Dan sauran
ƴan uwan nashi ma har sun yi gaba. Sun ɗan jima a Shanono wannan karon, tun fa damuna
suke, an ƙare noma abinci ya dawo gida, sai azamar komawa bakin karatu" ƙirjina naji ya doka
da ƙarfi data ambaci almajirci, yanzu Daudan ne yake ɗaukar nauyin cin shi da shan shi da
lafiyarshi? Bakina na rawa nace.
Ai na ɗauka yana zuwa makarantar boko, ta allon na ɗauka makarantar malam babba zai yi ai
Iya?"
"E hakane, hakanne ya dace kuma. Da har ya shiga makarantar yana aji uku a firamare, sai
uban yace bazai iya ba ya cireshi, sakamakon faɗuwa jarabawa da yake yi. Kinji yadda akayi,
ko a ta allon fa bai da