Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 24

39K to 42K   out of 70.8K words

Tani
tsine miki zanyi kibi duniya, ba za ki yi albarka ba tunda kin kasa faranta mun raina. Ke ba ma
zaki tafi da Dauda ko ina ba. Kai Muttaƙa ka kama hannun yaronnan kai da junaidu, Ige ta
raka ku." Ni dai ina dafe da kaina sai kuka nake yi, hannuna rike da Dauda. Ige ce tace. "Naroro ni gaskiya ina ganin kabar ma yarinyar nan ɗanta tai mishi jinya. Ala bashi in ya warke
sarai sai ta dawo dashi gidan ubanshi. Ke Tani karma ki sanar ma Kaila cewar riƙon Dauda zaki
yi sam. Ki faɗa mishi jinya kika tawo dashi ki yi mishi, yay haƙuri da zaran ya warke shikenan,
sai ki dawo dashi. Ni da kaina zan mayar dashi. Junaidu Yusufu, Muttaƙa, me kuka ce ko ba
gaskiya ba?" Akan hakan duk su kai na'am Inno ta jawo hannuna muka shiga ciki yarare_yarare
jini na bina. Sai lokacin na samu ɗan kuzari har nayo wanka da ruwa mai zafin gaske, kafin in
fito daga wankan goshina ya kumbura yai suntun, kaina dan ciwo kamar zai dare gida biyu. A
tsakar gida na tadda Inno ta tuɓe Dauda zata yi mishi wanka. Sai toshe hancinta take faman yi,
tsutsotsi sai yawo suke ɗaiɗaiku a gefe_da_gefen cinyarshi. Kasa tafiya nayi har sai da Baba
Marka taje.
"Ki shigo daga ciki sanyi na kaɗaki da ɗanyan jiki" Sannan na shiga ciki na sake kaya, aka
bani tuwo naci, sai bacci ya shiga yanko mun. Amman tunanin yadda zamu yi da Kaila in yayi
tozali da Dauda tuni ya yakice mun baccin. Nan kuma na harba duniyar tunani. Su Inno suka yi
tafiyarsu zuwa gidan biki. Ni kuwa maƙota sai abkin shigowa yi mun barka su ke yi. Dauda yana
ɗakin yaran gidan a kwance, Baba Marka ce ta kaishi tace ya kwanta acan, dan duk matan da
suka shigo barka sai sun tambaya abune ya mace a ɗakin ne yaketa busa wari. Ni a karan kan
kin kaina warin isata yake yi, nima kenan uwa, ballantana kuma su Baba marka. Allah sarki
rayuwa Allah ka kawo mun sauyi na alkhairi a cikin rayuwata, kasa goben yarana tayi kyau, a
wajensu kawai nake fatan samun salama. Sune kaɗai zasu ji ƙaina su sani Murmushi.

JOS KWATA TA YAMMA DA BAUCHI:

GIDAN KAILA:
Anty Maryam ce ƙanwar mahaifiyar Hajiyayye ta tusota a gaba dab magriba suka shigo gidan.
Idanun Hajiyayye yayi luɓu_luɓu da halama anci kuka an ƙoshi, rannan nata a mugun murtuke.
Shigowarsu tayi dai_dai da fitowar Bilkisa daga cikin turakar Kaila. Taci wani irin uban kwalliyar
da ba mijinta Kaila kaɗai bane zai gwaɗa. Duk wani mai idanu muddin ya gani tabbas yasan
anba kyau hakkinshi ta hanyar ƙara ƙawatashi da kayan ƙawa. Sanye take cikin gajeren baƙin
wando iyakarshi guiwarta. Sai wata riga ɓaka ɗamammiya mai hannu ɗaya. Gashinnan yasha
gyaran Amarci sai sheƙi yake yi, babu ko ɗankwali a kanta, da baƙin ribbon ta tubke sumar tata.
Ba wani gashi gareta can ba, tana dai da nayin kwalliya, da yake ta gyarashi tsab sai yayi mata
mugun kyau. Fuskarta tasha janbaki da hoda, sai ƙamshi kawai take. Hatta tsakar gidan ya cika
tab da ƙamshin turaren wutan da aka sa Shamwila ta bunka a ɗakin Kaila. ( Turaren wuta ne na
matan aure, wanda ake kunnawa da yamma domin jawo hankalin da nutsuwar mai gida. Matan
Kanuri suna saka wannan haɗin turaren in suka kintati dai_dai lokacin dawowar mai gida sai su
kunna. Da zaran mai gida ya shigo gida da gajiya ko ɓacin rai. Yana shaƙar wannan ƙamshin
sai yaji wata iriyar nutsuwa na gangaromai. Hakanne yake sa miji ko a ina aka ɓata mishi rai
Allah _Allah yake yi ya dawo gida dan ya samu nutsuwa. Ga masu buƙatar wannan turare sui
mun magana) Cikin yanga Bilkisa ta dubesu tace.
"Sannunku da zuwa, Maman Samira kin dawo?" Wata uwar harara Hajiyayye ta sakar mata
kamar idanunta zasu faɗo ta ja tsaki. Murmushin cusa haushi Bilkisa ta sakar mata. Anty
Maryam ce ta amsa ma Bilkisa gaisuwarta tana ƙarema shigarta kallo."
"Shamwila" Ta kira Shamwila da ɗan ƙarfi. Da sauri ta fito daga kitchen ɗin.
"Anty gani"
"Ki kai plate da cokali ɗakin Gwanda, in kin kai sai ki rufo ƙofar ki same ni a ɗakina" Tana idasa
faɗa ta shige ciki, ta bar Hajiyayye da sakakken baki. Motsi wannan Hajiyayye ta kasa yi.
Yanayin Bilkisa ya firgitata ainun. Bilkisa tafi ƙarfinta tako ta ina, in ma gasa tace zata yi da'ita
ta'ina zata soma? Duk inda take jin tana da buɗewar ido. Bilkisa ita nata idon tsabar yagewa
ɗayan ya haɗe da ɗayan. Da jan ƙafa Hajiyayye ta nufi ɗakinta da ko rufewa bata yi ba. Anty
Maryam tace.
"Hiye irin matar da Kaila ya auro kenan ƴar boko maras kunya? Danƙari Hajiyayye akwai
gagarumin aiki babba a gabanki. Domin kishi da macen data fi ƙarfinka aikine ja. Amman
abinda zan faɗa miki shine kar ma ki sake ku sake hayaniya da Kaila har ta kai ki da dawowa
gida. Mijin da yake da irin wannan Amaryar taku ko ya rabu daku duka kune da asara. Ni dai
fatana Allah yasa kafin Babanku ya iso muji labari mai kyau" Hajiyayye tana zaune sai jijjiga
kawai take ta dunƙule hannunta ɗaya tana nausan tafin hannunta dashi. Chaji kawai kanta yake
ɗauka. Tunani take ta wacce hanya zata fitar da Bilkisa a gidan, dan in ita Hajiyayyen bata fitar
da'ita ba. To zahiri ita zata fitar da'ita. Ita Shanono ba'a sata a lissafi dan bata ma san ciwon
kanta ba, a cewar Hajiyayye wacce tayi zurfi cikin zancan zuchi.
"Ita Shamwilar da aka aika turaka da'ita tazo ne a saman gara koko yaya?"
"Ni ban sanma tsinannu ba. Nima yanda kika ganta haka nima na ganta. Anty Maryam amman

kinga irin shigar da Amaryar kwana ɗaya tayi kuwa?" Anty Maryam tayi dariya tace.
"Na gani sarai kuwa. Ke dai ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki zaƙulo salo_salon kissa da
hilatar miji ki ƙara akan yaƙin ki da Uwargidanku, dan wannan yaƙin shine asalin yaƙi, kinsan
wannan kam sai dai ku fafata dan sai inda ƙarfinta ya ƙare. Amman ki kiyaye abinda zai taɓa
igiyar aurenki, kinji dai furucin mahaifinki kunsanshi da zafi dai akan irin waɗannan
maganganun. Rabi kina gani da mijin ya sakota ta dawo gida, da duka mahaifinku ya rakata har
ɗakinta, wallahi ki kiyaye kema dan sunan gyatumarmu ne dake da kin yaba ma aya zaƙinta."
Suna cikin wannan tattaunawa suka jiyo Sallamar malam Tsaiha mahaifi ga Hajiyayye. Ita da
kanta ta fita tayo mishi iso har ciki. Rannan nashi a murtuke, bayan ya zauna ne yayi shiru
kamar mai tunani har na tsawon minti biyu. Daga bisani kuma yace.
"To da ƙyar da siɗin goshi mijinki ya aminta ya dawo dake ɗakin ki. A hakannma sabida
darajarmu ne. Yace tunda ya bijiro da batun aurennan baki sake barinshi yayi bacci ba. Kiji fa
Maryam har sau biyu tana fasama bawan Allah wayarshi salula. Sabida kawai ƙazamin kishi, ko
haka taga iyayenta suna yi ohon mata. Ni gidana ko kara na ajjiye ai cikin iyayenta ba wacce ta
isa ta tsallake wannan karar gabanta gaɗi. Wallahi in baki yi wasa ba sai in miki baki tunda baki
da mutunci, so kike ki mayar dani dattijon banza ake ganina a matsayin wanda ya gaza wajan
baku tarbiyya? Jibi abinda Rabi ta aikata itama fa. Kinci sa'a ke uwatace wallahi da sai na
dakaki a cikin ɗakinnan tunda baki da hankali. Ke baki rasa ci ba, baki rasa sha ba, baki rasa
suturaba da an taɓo ku ku dawo mana gida, alhalin iyayenki duk sun rasa abinda ke baki rasa
ba a naki gidan mijin. Matar Bahaushe kenan, ire_irenku ke sa adadin yawan zawarawa yake
sake hauhawa a ƙasar Hausa, da gangan ake ɗaura mana laifin kacokam, ai in ɓera da sata
daddawa da warinta. in zaki bi mijinki ki bi mijinki, kin ganni nan aure zan ƙaro ni kaina nan da
sati biyu masu zuwa, kuma yarinyace bata shige sa'arki ba. Yaushe za'aita zama da tsofaffin
guzuma bayan Allah ya bamu damar da zamu more rayuwarmu." Ta inda mahaifin Hajiyayye ya
shiga ba ta nan yake shiga ba. Shi ba kuɗi ba, sana'ar tashi ba wata ta kawo makudan kuɗi ba
amman yana maganar cikace mata ta huɗu. Matanshi uku, yara kuwa sunfi ashirin, shagon
siyar da gwanjo na yara yake dashi a kasuwar gwanjo dake katako. Yanayin sana'ar tasu hawa
da sauka ne. Haka su Hajiyayye suka taso babu yabo babu fallasa, abincin da zasu ci wani
sa'in sau biyu kacal yake iya ciyar da iyalanshi, na ukun sai dai iyayen su yi buga bugarsu a
ƙuƙuta aci. Ko makaranta yaran da dama iyayensu mata su suka ɗau ɗawainiyar makarantar
yaran nasu. Matsalolin yau daban na gobe daban. Amman a hakan yake neman yayo ƙarin
Aure da ƙaramar yarinya sa'ar Hajiyayye. Mahaifin Hajiyayye yana ɗaya daga cikin mazan
ƙabilar Hausa masu cisgunawa matansu da yaransu. Dalilina kuwa shine, ƙarfin samunshi bai
wuce na mata ɗaya da ɗan yara ƙalilan ba. Kuma shima yasan da haka, amman dake babu
sunnar da Hausawa suka fi ɗabbakawa sama data ƙarin aure a hayayyafa dan manzon Allah
yai alfahari dasu ranar ƙiyama. Fahimtarsu ce ba dai_dai ba. Domin babu a inda akace a haifi
yaran iska, a kasa basu tarbiyyar islama kuma ayi tunanin wai wannan yaron zai zama abun
alfahiri ranar ƙiyama. Ai ko ku da kuke iyayenshi ba za kuy aifahari dashi ba. Sannan babu a
inda akace sai an auri mata biyu, uku, huɗu dole, akwai mazan da auren ma ya sauka a kansu
baki ɗayanshi. In kana da halin ɗaukar nauyin lalurorin mata huɗu da yaransu, kuma kana da
lafiyar jiki da zaka dinga iya biyan buƙatunsu, kana da dukiyar da zaka ɗauki nauyin karatu da
tarbiyyar yaranka, zaka kwatanta adalci a tsakaninsu. Alh ai baka da matsala sai kayi mata
huɗu abinka. Gargadi muddin kasan baka da wannan halin to maganin kar ayi kar a soma, ko

dan gudun haifar ƴaƴan iska masu addabar anguwa da sace_sace da harkar daba, fyaɗe, da
sauran gurɓatattun abubbuwa. In kunne ya ji jikinmu ya tsira.
Haka mahaifin Hajiyayye yay mata tas, sai kukan baƙin ciki take yi. Tafiya su kay suka barta a
cikin damuwa da tashin hankali. Rana zafi inuwa ƙuna. Gida ba daɗi, iyayenta haƙuri su ke yi da
Babansu. Gidan Auren ma babu daɗi Kaila ya ƙaro samfurin rashin mutunci. Tana zaune
dirshan a tsakiyar ɗakinta ta jiyo dirin shigowar lifan ɗin Kaila. Da harara tabishi ta labule ba dan
tana ganinshi ba. A cikin kunnuwanta take jiyo oyoyon da Kaila ke ma Bilkisa, itama tana mishi
oyoyon cikin muryar kirsa irin tamu ta mata. Yatsa Hajiyayye ta ciza. Tana ta jiran shigowar
Kaila yau zai shigo, gobe ne, ko jibi. Har bayan isha bata jiyoshi ba. Ba shiri ta miƙe da cikinta a
gaba ta nufi turakar Kaila.

Kaila:
Shi kuma Kaila a dai_dai wannan lokacin yana zaune Bilkisa na bashi abinci a baki. Sai washe
mata baki yake yi. Yana shigowa gidan ta jashi bayan gidan ɗakinshi, dama tasa Shamwila ta
haɗa mai ruwan wanka. Yana fitowa ya wuce masallaci, bai shigo ba sai da akayi isha.
"Amman Ɗanyan gwal yarinyar ta iya abinci babu laifi. Ni tunda nake ban ma taɓa cin soyayyar
taliya ba, ga kazar ta ɗau maggi da tafarnuwa." Murmushi kawai tayi mishi tace.
"Nima da na ci abincin na yaba mata. Kaga bani da wata fargaba ko ran girgikina in na samu
aikin kwana, Shamwila zata yi maka duk abinda ya dace, ba tare da na shiga hakkin abokan
zamana na ɗaura musu hakkin da ba nasu ba." Dariya yayi yace.
" Ƙwarai ma da gaske, Shamwila za tai mun komai da komai daya dace. Da kike maganar
ɗaura hakki, ai Shanono ce kaɗai zata iya yarda tayi wannan aiki ko ba ranar kwananta ba.
Hajiyayye ai baza ta taɓa yarda ma tayi ba. Wannan da kike ganinta ƙwayar boris ce zafi gareta
fa sosai." "E babu shakka an zauna ana kwance mun zani a gaban kishiya. Tur da kai Kaila wallahi . "
Suka jiyo saukar muryar Hajiyayye a kansu, sai jijjiga take faman yi, basu ji shigowar tata ba
ma. Kaila yace
"Zaki fita a ɗakinnan ko sai na turaki gidan tsoho kin je kin ɗan ja koriyar miya ne? Nifa shi yasa
naso a barki a gida, ko nima na huta amman mahaifinki ya dinga mun magiya darajarshi na
duba har kika ganki a tsaye a kanmu" Hajiyayye tsabar kunya sai taji kamar ƙasa ta tsage ta
faɗa. Masu iya magana na cewa, in baki yasan me zai furta, bai san me za'a mayar mishi ba.
Jibi yanda Kaila ya tsinkata a gaban kishiya yana jifanta da kalaman da zasu zubar mata da
mutuncinta. Cikin borin kunya ta ɗaura hannunta a bakinta ta shiga yi mishi ele.
"Woooo woooo wooo kaji kunya Kaila kaji kunya. Yarinyar da na yi imani sai da ka gama zakuɗa
hannunka cikin ramar kayi kwaɗo kafin ka kawota cikin gidan kamar yadda nima kayi mi...." A
mugun fusace Kaila ya dakatar da'ita da cewa.
"Ƙarashe kalmar da kike son fesarwa dai_dai yake da saki Hajiyayye. Baki da hankali ne, ni zaki
ci ma mutunci a gaban iyalina?"........✍



NA FADO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA

HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 8



_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*

https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE







Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa.
Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera
hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi
ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace. To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki
sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace.
"Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai
da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake."

Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora
girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa
da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin
dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi
komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci
suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira
da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau
sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin
Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya.
"Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada."
Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye
da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka
zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace. "Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a
matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni,
dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu."
"To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku
amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe
fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu
faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita
shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani,
uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta.
"Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace.
Lafiya lau Amarya Bilkisa ya baƙunta?" Murmushi

14 / 24