Na Fado Daga Bene Na Zarce Rijiya Book Compelet

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 24

66K to 69K   out of 70.8K words

abinda take so, ko wacce zan bata kuɗin cefanenta na
wata, ta sai duk abinda yai mata. Amman na dena cin abincin ko wacce mata, Shamwila ce zata
dinga mun girki a kwanan ko wacce Mata. Sannan na bata ɗakin tsakar gida, zata gyara ta
zauna a can. Kuma ita zata dinga gyara mun ɗakina, da wankina kamar yadda Ɗanyan gwal
take sata. Ko wacce mata ta gyara ɗakinta, tayi wankinta dana yaranta. In akwai me magana
tayi" Yayi shiru yana sauraren mai magana. Ni dai ai yasan banda ta cewa, ni banga ma ta inda
wannan maganar ta shafeni ba da har aka tara har da ni.
"Gwanda lokaci zai ƙure, kaga ina da nisa da asibiti sai na dawo." Cewar Bilkisa wacce ta miƙe
tsaye tana kallon agogon hannunta.
"Naga ƙannenki kince sun tafi sassafe, amman kuma motar da suka tawo da'ita tana tsakar
gida." Idanu ya ƙura mata. Sai da ta kai bakin ƙofar fita waje kana tace.
"Dad ne ya aiko mun da'ita in ci gaba da jigilar zuwa aiki" Tana kaiwa nan ta fice. Kaila ya daɗe
sosai a zaune yana bin ƙofar da kallo, har motar Bilkisa ta fice a gidan baice komai ba. Abinda
na lura shine ranshi ya ɓaci. Hajiyayye ce ta katse shirun ta hanyar cewa.
"Baby me kake nufi. Yarinyar da matarka ƴar boko ta kawo cikin gida a matsayin ƴar aikinta
itace zata ci gaba da yi ma girki ko ba ranar girkin uwargijiyarta ba? To ina da ja gaskiya, irin
ƴan iskan yarannan ne zaka sakar ma girki, da gyaran turaka, harda wankin miji."
"Hukunci dai na riga na yanke. Yayi daɗi ko karma yayi dai dole abi. Wacce taji ba zata iyaba
sai ta tafi gidansu ai." Zuruf Hajiyayye ta miƙe tace.
"Zan ko tafin. Ai gara in san aurenta kake yi zai fi mun. In san gumurzun kishi nake yi da'ita"

Fuu ta wuce abunta ta bugo ƙofar ɓarayinta. Ni dai bance uffan ba na miƙe na bar Kaila a
zaune yana ƙananun maganganunshi. Ni ko dan yinwa ko gani bana yi sosai haka na shiga
ɗakina. Nako ci sa'a sun rage mun taliyar, na dira akai nan da nan na lashe. Ko wanke baki
cikinmu babu wanda yayi. Miƙewa nayi na shiga banɗaki nayo kwaskwarima, na wanke
tsumman jini, na shanya a windo. Ban wanke bakin ba, sauri nake yi in na dawo na wanke.
Yaran dai na miƙo musu roba mai murfi da muke zuba gawayi dakakke da gishiri na wanke baki.
Ku goge bakin ku Sani. Ke kuma Amina ki fita waje ki yi mun wanke_wanke. Da kin gama ku
dawo ɗaki ku kulle, dan Allah kar ku fita babban falo kar ku ja mun abun faɗe, ni sai na dawo."
Fita nayi, na hau abun hawa sai makaranta.



KAILA:
Bayan watsewar su Tani a falon. Sai ya shiga ɗakinshi, wanda yake manne da falon
shanono.wanka ya shiga yayo. Ya fito ya cakuɗe jikinshi da kamshi. Ya ciro wasu ƙananun kaya
masu kyau. Duk da kasancewar kayan na gwanjone, a wajan Baban Hajiyayye ya siya, amman
a gwanjon ma su masu tsada ne, dan giredi ne sosai. Wani silifas yasa mai taushi, shima na
gwanjonne. Ya ɓare ledar cingam ya jefa a bakinshi, ya shiga tsuna kamar tsohuwar kilaki.
Wayarshi ya ɗaga ya danna number Shamwila. Ringin ɗaya wayar tayi zuruf aka ɗaga. Ita kanta
dama zaman jiran wayar tashi take yi, tunda ta ji fitar Bilkisa.
"Ɗanyan jini mu haɗu dake yanzu a moonshine hotel, kinsan wajan ko, ta wajan cobe?"
Murmushi tayi mishi tace.
"Ai na karaɗe hotels da dama a garinnan. Gani nan fitowa, ƙila in rigaka ƙila ka rigani" Sallama
su kaima juna. Ita ta rigashi fita, amman kuma shi ya rigata isa tunda shi a abun hawa na gida
yake. A wannan ranar Kaila yai rub da ciki akan Shamwila. Wa'iyazubullah a wannan ranar kaila
da Shamwila sun aikata abubbuwa masu yawan gaske. Amman dake Shamwila mai wayo ce,
sai da ya bata kuɗi masu tarin yawan gaske, kafin ta bashi kai bori ya hau. Abunka da aikin
shaiɗan nan take yaji dukkan matanshi ashe salab suke shi bai sani ba, sai daya haɗu da
gogaggiyar ƴar bariki sannan ya sani. Nan Kaila ya shiga rawar jiki akan Shamwila.
Tsugunnawa yayi akan guiwarshi .
"Ɗanyan jini yaushe zaki kaini wajan Abba ne? Wallahi a yau ne nake jin dai_dai da kwana
ɗaya bazan iya jure rashinki ba. Ni gara muyi aure hankali a kwance." Dariya tayi mishi.
"To ya maganar ginin ɓarayina, ba kace zaka yi mun ginin daya zarce wanda kwashi kwarab ɗin
matanka suke ciki? Aure kam ai zamu yi ka soma gamawa da ginin tukunna" Shiru Kaila yayi
yasan a yanzu baida kuɗin soma yin wani gini, nan da shekara guda ma ba lallai ya samu kuɗin
soma yin sabon gini ba. Wannan ɗin ma daya aka ƙare. Rarrashin shi Shamwila ta shiga yi, tare
da yi mishi alƙawin kasancewa tare dashi a duk daren duniya. Haka ne kuwa yaci gaba da
kasance.


SHANONO:
Ina dawowa daga islamiyya na samu Kaila ya ba Sani dubu uku wai kuɗin abincinmu ni da yara
na wata ɗaya. Ban dai yarda da abinda Sani yace ba, na adana kuɗin ina jiran in ya dawo in

tambayeshi. Na riga nayo mana cefanen ɗan kayan masarufi daya sauwaƙa. Garin rogo da ƙuli
kuwa na siyo su da yawa sosai. Gari na jiƙa mana, muna cikin sha Habiba Bala ta kira ni. Gata
ta shigo jos. Kwatance na dinga yo mata harta iso. Itama ta zo mana da tsarabar sabulan
wanki, dana wanka, harda man shafawa. Nako ji daɗi sosai, dan harna siyo sabulu da omo na
wanki a cefanen da muka yi. Video call ta kira mai aikinta, suka haɗa ni da Dauda. Yana
kwance ya sake ramewa, da gani yana jin jiki, dan sai da na zubar mishi da hawaye. Yaran na
kira duk su kai mishi ya jiki. Sai tambayata yayi.
"Innata yaushe zaki zo?" Daurewa nayi na haɗiye kukana nace.
Zan zo Dauda kaji. Allah ya baka lafiya mai ɗorewa, ubangiji Allah ka raya wannan bawa naka"
Habiba Bala ta kashe wayarta. A wajanmu ta wuni cur.
"Sabon gida ba zarni sai kaɗan Shanono. Akwai turaren wutan tsinke na sako miki ki yi kokari ki
dinga kunnawa. Kuma ki yi kokarin gyarawa, ki dage da karatu. Sannan ki binciki sana'ar data
dace dake" Godiya nayi mata sosai. Tayi mana sallama akan sai mun haɗu a kotu gobe." Wunin
ranar sukuku nayi shi dan tsoron zuwa kotu gobe. Ko da Yaya Use ta kirani itama jikinta duk a sanyaye haka dai mu ka yi wayar. Da yamma lis
nasa yara mazan su yi wanka. Ni kuma na tafi baya dan yin girki. Wuta na hura na dawo ciki.
Hauwa da Salis nai ma wanka, su Amina da Balaraba da kansu suke yi. Ni da kaina na ciro
musu kayan da zasu saka, ba kamar yadda na saba barinsu su zazzage buhun kayan a ƙasa
ba. Dana tsayar da sanwar miya, nima sai na shiga bayan gidan nayo wanka, nayi wankin
tsumma. Wajajen magriba na haɗu da kaila a tsakar gida, ni kuma na fito daga baya da
tukunyar miya a riƙe.
"Shanono Sani ya baki dubu uku ko?"
E ya bani.
"To sai ki jalauta kuɗin abincinku na wata guda kenan. Sai kisan yanda zaki tanana ya kai muku.
Kina sane da batun zaman farko a kotu gobe ko?" Numfashi na ja.
E ina sane Allah ya nuna mana. An gode Allah ya saka da Alkhairi " Na wuce ciki abuna.
Ni fa a wannan daren Wallahi masu karatu banko runtsaba, nayi kukan harna gaji. Na yi tashin
hankalin, har zazzaɓi sai da ya ci nasarar kama ni dan farbaga......✍





_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani
supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*

*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*

https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN
KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK
MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA
ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA
ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI
WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar
*ABIN BUKI*

*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURENA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 19



Washe gari sassafe ni da yaran muka fice a gidan. Basu ci gaba da zuwa makaranta da
islamiyya ba sai gobe in Allah ya nuna mana. Ni kaina ba lalle bane in iya zuwa school yau ba.
Dan zazzaɓine magashiyan a jikina, ga wani irin sanyin mashasshara da nake ji. Gidan Yaya
Use muka wuce. A tsakar gida na same su harda Baban yara. Yaya Use tana raba ma yara
kokko. Ganin mu yasa aka ƙara yawan kofuna. Aliyu ne ya shigo da ledar ƙosai. Kowa ta danƙa
mai kosai bibbiyu a hannu. Nima ta miƙo mun nawa kokko da ƙosan.
Baban yara ina kwana" Nace a sanyaye.
"Lafiya Tani. Za'a soma shiga kotun ko?" Kai na iya gyaɗa mishi kawai, dan harshena yayi
nauyi. Ya nuna Yaya Use wacce idanunta su kai zuru_zuru yace.
"Kin ganta tun daren jiya take faman yin gudawa, har wayewar garin yau. Sabida tsabar tsoron
zaman kotu. Idandunanta har sun faɗa. Ai irin abinda dama nake guje mata kenan. Itafa bata da
aiki sai rigima da zafi, duk da a hakanma tayi sanyi" Kai ya girgiza yace.
"Allah ya kyauta. Sai kun dawo ni na fita kasuwa" Na dubi yaya Use nace.
Nima tun daren jiya zazzaɓi me zafi ya rufe ni. Gashi yau su Inno zasu dawo, ai in Baffa yaji
wannan labarin daga ni har ke mun shiga uku. Barenma ni da abun lefi baya mun wuya."
"Tani na tsorata, gani nake yi bazan kuɓuta ba wallahi. Sabida tabbas na daki Hajiyayye,
amman tabbas ban daki cikinta ba. Amman wa zai fitar dani a wannan ƙullin sai Allah " Kafin in
yi magana Habiba Bala ta kirayi wayata.
"Shanono in shigo cikin gidan Yaya Usen ne?"
E Habiba Bala shigo muna ciki" iyakar abinda nace mata kenan. Na datse wayar. A hankali
nake ɗan kurɓan kokkon. Ƙosan ma danƙama Hauwa ɗaya nayi, Balaraba ɗaya. Ruwan kokkon
ma ya isheni. Da sallama Habiba Bala ta shigo. Tana sanye cikin riga doguwa fara mai shegen
kyau. Ƙamshi take yi mai kwantar da zuchiyar mai shaƙa. "Maraba Habiba Bala. Zauna ga waje dan Allah"

A ɗofane Habiba Bala ta zauna. Ta faɗaɗa murmushinta suka gaisa sosai da Yaya Use. Ni
kuma ta dube ni.
"Shanono lafiya dai, naga jikin naki babu ƙwari sam. Menene damuwar?"
Hmmm babu Habiba Bala. Ya hanya?"
"To ya kamata ace ki yi wanka sai mu je ko, Yaya Use ku shirya, lokacin yayi mana a gaban
kotun." Yaya Use tace.
"Kayya Habiba Bala. Tani dai ta shiga tayo wankan in zata iya. Ni kam har sai na ji yadda
shari'ar zata kaya. Babban damuwata in da gaske alƙali ya tura mu gidan kaso, ni Use ya zanyi
da raina Habiba Bala yarannan ina zamu kaisu?" Habiba Bala ta dube mu tace.
"Ko ɗaya Yaya Use, ai in Hajiyayye ta san farkon shari'a bata san ƙarshenta ba. Ku dai ku
shirya kawai mu tafi" Da ƙyar na tashi nayo wankan na fito. Kayan jikina na mayar, ina fitowa
Yaya Use ta shige ɗaki danta kintsa.
"Shanono na lura duk nasihar da nake yi miki akan ƙazanta baki dena ba. Kinsan Allah in na
zuchiya ko wallahi bazan sake tako inda ma kike ba. Ke fa macece, ya kamata ki nutsu ko dan
ummu nabeeha ki gyara. Na tabbatar sabida ƙazantarki ne yasa mijinku yayi miki jan fenti.
Gashi ni nayi cinikin kujeru inaso in sai muku ko dan farin cikin yaranki, amman ƙila kujerun
barinsu zaki yi yara su lalata a banza. Jibi kayan jikin ki, ba koɗewarba, ji dattinsu kin yi wanka
tsabar iskanci kin kuma damɓarawa, meye amfanin wankan naki to? Jibi kanki dana yara duk
datti. Ji Hauwa yarinya ƙarama ji tarin tulin ƙasa a kanta. Shanono sai fa kin miƙe zaki iya
kwatar ƴancinki a idan duniya ma. Ki ajjiye damuwa da komai a gefe ki gyara kanki da yaranki,
ki nutsu ki basu tarbiyya. Yaranki mata in kikai sake suka taso a haka wallahi kin kashe su.
Suma fa korosu za'a dinga yi a gidan miji.?" Tabbas maganganun Habiba Bala sun ratsa duk
jijiyoyin jikina. Kuma tabbas ita da Sabira burinsu shine su ganni cikin rayuwa da yanayi mai
kyau. Nima ya kamata in faranta musu kamar yadda suke faranta mun.
Kiyi haƙuri Habiba Bala in sha Allah Shanono daga yau ta canja, bazan sake ba, zaku sha
mamakin haɗuwarmu ta gaba" Ina faɗin haka na miƙe zuwa ɗakin Yaya Use."
Yaya Use ki ban wasu kaya da zasu yi dai dai da jikina" Ba tai mun musu ba ta zaro wata
doguwar riga
"Kinga wata Inno ce ta hado mun a kayan data aiko mun. Dama ke naso ba ko Karime " Godiya
nayi mata tare da saka wannan kayan. Na ari hijabin ƴan matan Yaya Use na saka. Na fito,
Habiba Bala tayi murmushi tace.
"Koke fa. Kema kya ji daɗin jikin ki ai ƙazanta fa babu kyau Shanono, haka ki kai ta bamu
wahala a makaranta, kai kin cutar damu da warin hammata irin na sabon balagarnan. Dariya
mu ka yi duka. Sai ta tuno mun da wannan Dattijuwar da muke zaman benci ɗaya a makaranta.
Ranar laraba daya kasance zuwana makatanta na uku, bayan an tashi na fito daga aji, hijabina
duk jirwayen ruwan nono, muna ƙarni. Wannan dattijuwa sai ta tare ni tace.
"Ƴata in babu damuwa bari in baki shawara. Muddin ki kai amfani da ita zaki ji daɗi." Tsaiwa na
gyara.
"Kin ganni nan yara ɗaiɗai sai da na haifi yara goma sha bakwai a cikinnan nawa. Ƴan bibbiyu
sai da na yisu sau uku. Amman bamu yi ƙarni ni da yaran irin yanda kike wannan ƙarnin ba. Ke
ƴata ce, yadda zan ma ƴar cikina haka zan yi miki. Kinga ajinmu duk gulmarki suke yi. Sabida
cika ajin kike da ƙarni da warin rana da kin shigo. Ƴata ki dinga tsabtace jikinki, ko dan lafiyar ki
da lafiyar jaririnki. Jiya da tsarabar kuɗin cizo na koma gida, kuma nayi alƙawarin yau zan yi

miki magana. Ƙazantarki tayi yawa, jibi hijabinki duk datti, littafin turanci jiya da muka haɗa aka
kaima malamin da ya bamu aikin gida a ciki. Naki fa da kika ciro duk manja. Tani Shanono ki
dena kin ji ko ƴata?" Ta mun jan kunne, da nuni masu dama, amman nasa ƙafa na shure. Ni
ganina nake tamkar ba mace ba, gani nake yi ni kowa ma ya tsaneni, wallahi bansan abinda ke
damuna ba, amman ko iyakar cunkushewar zuchiya da haki dake yawan taso mun aka barni
dashi shima jarabawane. Yaya Use ce data fito ta katse mun tunanina.
"Mu janku. Ku kuma ku kula da gidan banda yawo kune manya" Adda'a yaran su ka yi mana.
Manyan kuwa sai da suka ga ɓacewar motarmu tukunna. Damuwa duk ta damesu, kamar
yadda muma ta damemu. Shiru kuke ji a cikin motar babu motsin komai sai ƙaran Ac da Habiba
Bala ta babbaka mana. Tafiyar minti goma sha biyu ce ta kawo mu kotun wajen amingo. Muna
fitowa muka ga su Hajiyayye da tawagar ƴan gidansu birjik a zaune a gefen kotun. Kaila kuma
yana gefe yana waya, da ganin yanda yake suntiri na gano yayi wata sabuwar budurwar kenan.
Gefe guda muka ja muka zauna. Dangin Hajiyayye suna ganinmu suka soma tsaki da
harare_harare. Babu wanda ma yabi ta kansu damuwar dake damun mu ma ta ishemu...




NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA.
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 20.




Gefe guda muka samu mu ka zauna. Kaila sai yawo yake a filin kotun yana ta wayarshi. Can
lauyanmu ya ƙaraso a gurguje. Isowarshi ke da wuya aka buɗe kotu tare da bamu umarnin
shiga. Wallahi ƙafafuna da ƙyar suka ɗauke ni izuwa cikin kotun. Wannan shine karon farko
dana shiga kotu, ina fatan na ƙarshe in sha Allah. Kujeru ne a jejjere kamar makaranta. Sai
wani gidan katako daga sama, da ɗan akwaku a gefe. Kowa ya nemi waje ya zauna. Lauyoyi
suna gefen wajan zamansu.
"A yau ashirin da biyar ga wata. Wannan kotu mai alfarma zata yi shari'ar Hajiyayye wacce take
unguwar layin ɗanmaraya, gida mai lamba Z2110. Inda ta shigar da ƙaran kishiyarta Tani, da
Yar kishiyarta Use, akan kashe mata yaro da su ka yi a ciki sanadiyyar lakaɗa mata na jaki da
su ka yi" Yaya Use ta zare idanu tare da riƙe ciki. "Gudawa nake ji Tani. Nashiga uku" Cikin raɗa take magana. Kafin in san abinda zance sai mu
ka jiyo Alƙali na

23 / 24