KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   4 / 34

9K to 12K   out of 102K words

ball a hannunsa da biskit.

Yana shiga duk suka juya suna duban sa. Shima ya tsaya yana kallon su sai kifi kifi yake da idanuwa,

"Daga Ina kake habule?"

"Daga waje nake "

"Nasan daga waje kake... Waɗannan kayan a..

"Aa dakata ba zaka kalawa da na sharri ba ku kun wanke naku.. Shi da yake namiji har a tanbaye shi inda ya samu kudi?"

"Ba zaa tanbaye shi ba? Shi babbanne ko akwai wani aikin da yake da yake samun kudi? Ji nake danace ya dinga zuwa gidan chiyaman yana ebo musu ruwa suna biyansa a wata ki kikay, nace miki yake ka bayar da kudin yana rage wasu abubuwan nasa da naku, kikace Allah ya kiyaye danki yayi aikatau. To Ina ya samu kudin?"

"Oho dai komai menene awaje ya samu kudinsa. Kudin cikin gidah Kuma yan cikin gidan ne Wanda suke cikin gidan ne suka dauka"

Zaytuna da tarasa yadda zatayI ta barke da Kuka. Malam Nata'ala yayi kanta yana rarrashinta..

"Me aka miki zaytuna menene? Kukaan menene?"

"Me kwa zaayi mata shaafaffuya da mai? Ni dai nasan yar gwal dindai itace ta dau ka mun kudi"

"Wallahi wallahi Abba ban dauki kudin gwaghoi haire ba. Kaji rantsuwar musulmi. Kudi dana shiga dakin mu na dauka ragowar kudin da gwaggo tabamu ne rannan kanta kwanta rashin lafiya tace mu Sayo kwakin jikawa. Shine fa sunajin yunwa su Rayyanatu nace su Sayo biskit suci kafin agama suci abinci. Sannan kudin da gwaggo haire take magana wallahi Abba habule ne ya dauka gashinan idan na masa Karya. Ina zaune awajen yazo ya daga kwarya. Nache masa meyasa zai dauki abunda banasa ba. Yace mun ce ai ba na mahafiyata bane abba, don haka babu ruwana. Jin haka yasa na tashi nabar wajen saboda ya fara zagina. Yana dauka yafice daga cikin gidan da zauri."

"Innalillshi Wa inna ilaihi rajiun... Wallahi sharri ne kaji wani sharri da yarinyar nan zatayiwa habule. Kai Amma wannan yarinya duk halin uwarki kika dauka na kitsa magana da shiya zance. Lalle "

"Allah gwaggo shi ya dauka miki gashinan"

Habule sai kokairin rantse rantse karya yake. Malam Nata'ala ya koma kusa da shi ya riko hannunsa,

"Tsakanin ka da Allah zamu mutu mu koma ga Allah. Wannan ball da kaya daka Sayo ni zan saya na bawa mahaifiyar ka kudin idan har ka tabbatar Kai ka dauka. Idan kuma ...

"Yo dama ka masa wannan zancen ba dole yace shi ya dauka ba Nata'ala? "

"To shikenan naji haire naji, habule ai kana zuwa makaranta kanaji ana fadan hukuncin Wanda yake daukar abunda banasa ba. Da hukuncin Mai Karya . Wannan abubuwan da kudin ka ka saya ko na cikin kwarya ka dauka?"

Habule yai rau rau da idanu yana matse ball dinsa a kafada yace,

"A kwarya na dauka..... Bansan bansan na haire"

"Kai Amma kuwa sai naci qundugurun buhun bura uban ka habule " haire ta karasa fada tana fafarashi da takalmi har waje.

Malam Nata'ala ya babbasu hakuri yace kowa yacitaba da abunn da yakeyi

Gaba daya komai yinsa suke a sanyaye musanman zaytuna da take Jin wani iri ,ba laka a jikin ta saboda kazafin da gwaggon tayi mata.

To haka sukaci gaba da garawa yau ba dadi gobe babu, Kuma gwaggo haire bata fasa halayen ta ba sai ma abunda ya karu...

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


_paid page 10_


🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️



A kishingide yake, Dawowar su kenan daga cikin birni, jikin gwagho abule da dan sauki zaa ce. Tana Shan Karin ruwa da allurori...

Yaja doguwar ajiya zuciya ya sauke... Alamun ya Kai kololuwar mizani a duniyar tunani.. ya saqaa ya ware shi kadai..

A haka dan uwan sa ya zo ya same shi. Hannun sa rike da leda baka dauke da awara manya manya Mai zafi..

"Tashi kaci.... Nasan cikin gidah tunda kaga haka basu karasa abinci ba"

Malam Idi ya gyara zaman sa sosai yana duban dann uwan nasa yace,

"Sannu da kokari.... Allah ya Saka da alkhairi "

"Kai saikace wani kayan gabas. Ja ledar kaci ni na ci tawa acan"

"Nagode kwarai" yaja ledar gaban sa yana basmala ya cinye awarar nan tas yana hamdala

"Ai kwa cikina ya dauka... Masha Allah allahu"

"Masha Allah ai haka akeso.... "

Malam Idi yayi murmushi bai ce komai ba yana duban kasan tabarma wajen zaren zaren...

"Dan uwa mene ne? "

"Bakomai fa. Meka gaimi?"

"Nagan kanne haka wani iri yau.... Inshaa Allahu zainabu zata wartsake. Cuta ai ba mutuwa bache"

"Ayyah ko kadan ba itama nake tunawa ba... Bakuma abunda nake ja wani tunani na daban. Haka dai na tsinci Kai na "

Malam Nata'ala ya sauke gauruwar ajiyar zuciya yana duban dan uwan nasa yache,

"Hakane kam.... Wani zubin mutum kan tsinci kansa a irin hakan Daman. Ubangiji Allah ya shiga cikin lamuran ka yayi riko da hannayen ka. Amin"

"Aameen Wa iyyakum...."

"Ya kake tunanin karatun su Amiru da Uzairu fa?"

"Gaskia Masha allahu... Yaran nada matukar kokari da kwazo. Amman dai uzairu ya fi Amiru. Duk da dama yatsun hannu ma wani yafi wani ai. Sai dai fatan Allah yasa suyi aiki dashi ya Kuma tsare kuruciyar su har girman su"

"Allahumma Amaaen, ai ba zama ka hada ba Kam duk da shima yana kokari Kam Amma uzairu na daban ne"

"Hakane. Allah yasa mu dache ysba daya. Allah ya iya mana"

"Allahumma aameen, mu shiga ciki ne?"

"Toh bari na taso"

Mikewa yayi, yabu bayan Dan uwan nasa suka shiga cikin gidah bayan sun yi sallama an musu iso...

Gwaggo haire ce taketa kururuwar fada an Mata shanya akan barkono sai tsine tsine take tana Allah ya Isa bayan gefen hijabi ne da aka shanya kadan ruwan yake diga ta daga can bayan barkonon.

"Dan Allah haire ki dinga hakuri haba. Zai kakatu kike tun daga kofar gidah ake jiyo ki"malam Nata'ala yavce da ita

"Su yaran naku bazaku iya musu fada ba kullum sai dai ni. Haba Dan Allah "

"Kiyi hakuri haire. Yanzu me sukayi?" Cewar malam Idi..

"Su sun sani ai. Ko ince Wanda sukayi sa gaya Muku"

Malam Nata'ala da takaicin kalaman ta suka Kona masa Rai sai ya Shura takalamnsa ya fuce daga gidan. Yayinda malam Idi ya shige nasa dakin yana kwalawa zaytuna kira,

Ba dadewa kuwa ta karasa dakin nasa tana amsa Kiran nasa cikin ladabi,

"Sannu da dawowa baba. Ya jikin gwaggon?"

"Da sauki Alhamdulillah. Kinci abinci kuwa?"

"Dumame ne mukaci, na rana Kuma rumanah bata karasa ba Amman bama Jin yunwa"

"Masha Allah to Allah ya Kara mama mufawaqa"

"Aamin baba amin"

"Allah Kuma ya muku albarka "

"Aamin baba..."

Chan dai sukayi shiru gaba daya batace komai ba shima bai sake magana ba. Zaytuna ta kalleshi kanta a aksa tace,

"Baba wani abunne?"

"Girgiza Kai yayi yana sauke numfashi yace,

"Babu komai....kawai Ina tunanin rayuwa ne"

"Allah sarki"

"Wato zaytunah. Abunda nakeson da ke shine. Duk abunda gwaggon ku zata ce kuyi Wanda tace kubari ku bari. Na tayi kiyi. Na aika kiyi. Idan tana zaune tsakar gidah ku dawo daki saboda gudun abunda zaije ya dawo ku bata girman ta kunji? duk da nasan babu mai matsala wallahi acikin ku"

"Hakane kam baba. Inshaa Allah allahu"

"Ki rike, Allah na farko kenan,kiyi biyayya, ki rike sallah, karki wasa da addini, ki zama Mai tausayi, Mai kirki, kada ki manta da hallaci domin zuciya Mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri. Sannan duk wuya duk rintsi Kada ki bari na waje yasan cikin ki ke ko na gidan ma idan har ya cancanta... Dubi nan menene?" Ya karasa fada yana nuni da KIRJIN sa,

"KIRJI NE baba..."

"To kisani KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA) ne .. ya zamto kina adana sirri a KIRJIN ki Wanda duniya ba zata san dashi ba. Ke ko zatasan dashi ya zamto sai da aka kada aka raya . Idan SIRRIN bai fito ba akwai matsala tukun sannan. Kinji ni ko?"

"Ina sauraron ka baba. Inshaa Allah ."

"Allah ya muku albarka ya raya ku yasa ku gama duniya da lafiya "

"Aameen.... Baba. Allah ya Saka muku da allhairin sa dawainiyar da kuke damu ya biya muku bukatun ku duniya lahira Amin"

"Aamin aameen.... Allah yabaku mazaje nagari. Wanda zasu so ku su kauna ceku har karshen rayuwar ku Amin. Allah Kuma ya baku zuriyah ta gari. Ya musu albarka. Ya sa su zama wani abu a rayuwa na alkhairi. Yasa mahaddata ne suma, Inshaa Allahu"

"Aameen baba. Aameen tafiya zakuyi ne?"

"Kinga inata nasihohi ko?"

Ta kada Kai. Malam Idi yayi murmushi yace,

"Aaah ba inda zamu. Kawai dai ji nai a jikina da yakamata na gaya miki kasancewar ki kece babba akan kannen ki..Allah ya shiga lamuran ki da su baki daya"

"Aameen baba aameen tare da ku. Allah kuma yabawa gwaggo lafiya da duk sauran marasa lafiya na gidah dana asibiti"

"Aameen Aameen.. Allah ya miki albarka."

"Aameen baba Ameen..."

Ya shiga mata nasiha Mai ratsa jiki dai, daga karshe yace ta tashi taje...Zaytuna ta mike ta futa tanata tunanin nasihohin sa musanman kalaman sa. Na KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA)....


°°°°°°°


*****Duk kan mai rai mamaci ne, Kuma mutuwa riga ce ajikin kowa babu mai zareta,

Kowanne Rai Wala yaro Wala babba, matashi da dattajo, budurwa da tsohuwa, jariri da Wanda ya fara tafiya Kai kowa sai ya dandana dacin mutuwa...

Allah ya karbu ran malam Idi a sahun sallah, A sujjadah ta tahiyar karshe. Shiru shiru bai dago ba. Can akaji tim.

Bayan wani ya shige gaba ya karasa sallar ne sunyi sallama duk sukayi kansa hankulan su a tashe...

Temako suka fara bashi Amma Ina. Anyi bugun an tattaba jikin sa dajijiyoyin sa tuni sun saki suma.. Rai yayi halin sa Allahu Akbar

Amman duk da hakan sai da aka dangana da shi da asibiti aka tabbatar ya rasu.

Gaba daya astagfirullah Allah mun tuba. Sai mutane suka rude musanman mata na cikin gidah dake karkarar bokezuwa. Malam Idi ya rasu ko dai gwaggo abule mai dakin sa? Dan itache babu lafiya sosai Rai a hannun Allah. Amman dake Allah buwayi ne gagara misali. Sai gashi mijinta da lafiyar sa kalau shi ya rasu itada batada lafiyar da ake kawowa mutuwar ma ba itan ta rasu ba...

A Kuma ranar ne kafin a masa wanka a kaishi gidan sa na gaskia. Aka sallamo su gwaggo abule daga asibiti

Nan Kuka ya dawo baya. Lamarin sai Wanda yake wajen kawai.... Anyi Kuka sosai na rashin malam Idi bokezuwa. Gaya muku yadda adadin alhinin da ya wanzu a bokezuwa baki daya ma alkalami karya zeyi...

Sai dai muyi masa adduar Allah yasa ya cika lafiya ya kuma kyautata namu zuwan...

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

_KMH (A/S)_


_The Vault Of His Secrets_

*NH✍️*


_11_


   Toh haka rayuwar ta cigaba da garawa, Ta malam Idi ta kare sai Kuma mu da mukai saura.

Sannu ahankali abubuwa nata tafiya yadda suka kamata... Yau da dadi, gobe akasin haka.

To dama duka gaba daya rayuwar duniyar ma ai hakuri akeyi. Zamane kakeyi kaman na ci rani. Idan taka mutuwar tazo ka tatttara ka tafi ka bar sauran masu jira..

Hakika marayar bokezuwa tayi babban rashin gwani, Kuma maabocin karatun alqurani Mai girma..

Kuma Alhamdulillahi tasa tayi kyau. Domin ya samu yabo daga cikin bokezuwa da wajenta dama sauran kauyuka na kusa dana nesa..

Bayan rasuwar malam Idi na dan wasu lokuya. Malam Nata'ala ya sanya akayiwa gidan da suke ciki kudi. Kan zai sayar da shi ya bawa iyalan malam Idi gadon su .

Ya sanya gidan a kasuwa, Gwaggo abule sam bataso hakan ba. Don idan ya sayar Ina zashi da nasan iyalin? Ita da nata yaran marayu Ina zasuje? Iyayenta sun dade da rasuwa a hannun kanwar uwa tatashi. Kanwat uwar ma tazo ta rasu ba inda zata ce yau akwai da zata bigi kirji tace suje su zauna acan..

×××

  Ranar wata asabar da sakaliya. Anata shirye shiryen yara almajirai zaa tafi hutun sallah. Wasu zasu tafi rani noma gidah

Malam Nata'ala ya fito daga cikin dakinsa yana gyara zaman hular kansa zai fita.

Gwaggo abule tayi saurin durkusawa tana gayshe da shi, cikin ladabi.

Ya amsa a sake yana tambayar Yaya yaran Dan uwan nasa. Ya kara da cewar,

"Akwai wani abu da kike bukata ne zainabu?"

Gwaggo abule kanta a sunjuye ta girgiza Kai tana matsa yatsun hannun ta tache,

"Dama idan ba damuwa magana nake so muyi"

Gwaggo haire ta juya tana duban su ta tabe baki.

"To ba damuwa zainabu. Muje can"

Ya fada yana komawa can wajen gefen juji. Yaja ya tsaya ita Kuma ta tsugunna kanta akasa tache

"Malam ni dai a yar tawa shawarar da baa sayar da gidan nan ba"

"Zainabu idan baa sayar da gidan na ba ya za'ai!? Gado ne na Dan uwana nan . Kuma yayan sa da ke kanki kunada hakki akai. Dole ne a sayar a futar muku..."

"Toh malam kayi hakuri dai. Amman ya zamuyi da matsugunin zaman?. Ni dai mun yaf.

"Ahh Dan Allah karki karasa, gadon zaki yafe? Ai karma ki soma fadin haka. Yanzu idan wasu acikin su Allah ya raya su auren su yazo . Dame zaa Kai su gidan mazajen su? Ai jari ne wannan din. Dama kadara amfaninta idan abu ya taso sai ka sayar kayi abunda zaka kayi dasu. Kuma wajen zama Allah ba zai hanemu ba. Zan samu Mai gari inshaa Allahu. Ko jinginar gona ne sai na bayar a aramana kafin Allah ya hore mu mallaki wajen zama"

"Toh shikenan malam.... Allah ya zaba abunda yafi alkhairi "

"Yauwa Aameen.. sai na dawo" ya fada yana hanyar fita ya juya ya dubu haire dake kurbar Koko,

"Na fita haire"

"Ta gama Kai tsegumin kenan ko? Banda munafurci a Fadi koma menene mana agaban kowa sai Kun koma daga baya"

"Kiyi hakuri gwaggon su... Wallahi ba da wani abun na fada ba. Maganar sayarda gidan nan ne nace masa da ya dakata dai. " Cewar gwaggo abule

"Banda salon munafurci kema ai so kike a sayar da gidan a baki rabon ki Dana yaran ki. Shine Dan kissisina zaki wani ce wai kar ya sayar. Uhm kwaji da shi" haire ta fada hade da mikewa tayi tafiyar ta cikin daki..

Malam Nata'ala ya girgiza kansa kawai ya fice daga gidan Kai tsaye ya wuce makarantar allon su data zama tasa a yanzu...

  Yara nata kara karaina sunata hada Hadar tafiya gidah. Daman malam Nata'ala sike jira don yi masa sallama..

Yana karasawa kuwa suka fara Kai gaisuwa. Fuskar sa a sake yaketa amsa musu yana shi musu albarka...

Daya bayan daya sukayita gaishe shi suna masa sallama. Wadanda ke cikin garin suka nufi gidah. Wadan da ke wasu kauyikan na kusa suka  fara tafiya suma.

Sai wadanda ke kauyika na nesa da Kuma wadanda suke wasu garuruwan motocin haya ne suka zo hayis biyu ta daukar su ..

Sai zuwa suke suna yi ma malam Nata'ala sallama. Shi dai sai bunsu yake da murmushi yana duban kwano rufunn da suke karatu a karkashin sa. Ba zai taba mantawa ba shi da Dan uwan sa marigayi idi sukayi shi alokacin da suka fara Almajiran ta. Har suka fara koyarwa..

"Allah ya jikan ka da Rahama idrisu, Allah ya gafarta maka, Allah ya kyauta ta namu zuwan Amin"

Yana zaune, hannunsa da charbi yana ja. Su Amiru da uzairu suka karasa wajen sa. Kowanne dauke da Akwatin sa. Kana kallonsu kasan tabbas su din tsatson yayan gata ne dubada yadda sukayi shiga ta alfarma da akwatinan su na yan gata..

"Malam barka da rana"

"Barkan mu dai yayan nan Allah ya muku albarka.tafiyar ta taso Ku ma?"

"Eh malam inshaa Allah. Zaa zo ma a dauke mu munyi waya da su"

"Masha Allahu. Allah ya kawo su lafiya. Allah yabaku ladan iliminda kuka dauka yasa kuyi amfani dashi Allah Kuma yasa mahaddata ne kudin na har abada Allah ya Kara muku dankon zumunci"

"Aamin malam" Amiru ya amsa shi

"Aamin aameen malam Kai ma kokarin da kukai mana da karantar damu dakukayi da sauran abubuwan hidima Allah ya biya da gidan aljanna Allah Kuma ya jikan gwani idrisu da rahama Amin" cewar uzairu

"Allahumma Amin, aameen Amiru. Nagode kwarai"

Cikin haka saiga wata zungureriyar mota Mai Nishin kudi ta faka a Dede inda su malam Nata'ala ke zaune dasu uzairu agabansa daga tsallake....

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

[12/2, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _KMH(A/S)_


_The Vault Of His Secrets_


*NH✍️*


_12_



   Daga cikin motar suka furfito, sanye cikin kaya na manyan mutane. Kallo daya zakai musu kasan wannan sun hau kan kudi sun zauna suna Kuma juya shi. Sai dai wani bangaren, zaka dube su zakaga su din basa cikin sahun masu da girman Kai ko dagawa. Tsantsar dattako ne da sanin darajar kimar dan adam

Karasawa sukayi. Malam Nata'ala ya Mike yana murmushi. Hannu ya basu suka gaggaysa. Da alama sune wadanda sukazo daukar su uzairu.

Dan su uzairun sun gayshe da su cikin ladabi da sanin yakamata. ..

Direban motar ya taso yana kokarin daukar akwatinan su uzairu zai Kai mota. Su uzairu suka Hana shi ta hanyar dauka da kansu su Kai cikin motar bayan booth su ajiye..

Mutanen suka juya suna duban su suna murmushi..Murmushi ne na Jin dadin halayyar tasu uzairu Mai kyau da suka samu

4 / 34