KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   20 / 34

57K to 60K   out of 102K words

ya sanar nun Sanda yake gari zanje na sameshi acan capital territory. Ko idan yazo gidan sa na nan garin"

"Toh Allah yasa mu dache. Kafin ma ayi masa maganar"

"Aameen Yaa Rabbi"

Haka dai suka cigaba da zama. Sai da zaa kakkawo abinci nema. Matan suka futa harda hajia rumanah dataketa hawayen karya ita alallai ta rasa yar uwar ta da yayan yar uwarta .

Suna futa suka koma sashen su hajia karama. Hajia rumanah ta saki Dariya tana kecewa harda rike ciki. Su hajia ladi suka biye mata sunata babbaka daria..

"Ai dama na gaya muku. Ance aikinsa kamar yankan wuka yake."Hajia rumanah ta fada tana yabaawa malamin su da yayi asirin da zaytunah tabar gidan...

"Gaskia na yarda. Ai kamar yarda yayi rubutu a kasar nan ya Saka hannu ya shafe ta, yace haka ya shafe son waiwayen gidah a zuciyar zaytunah. "

"Bama wannan ba. Kinga Muna sakin kurciyar nan tana tashi fa zaytunah naga ta fita da sauri..."

"Shegiyar ba. Ai yarda kurciyar nan ta tashi ta lula sama batasan inda zata ba. Hana zalika zaytunah ma ba zata waiwayi gidah ba. Haka zatayita tafiya. Sai idan wani ya mata magana ko wani abun. Danma mun mata mutuntaka.. bamu rabata da yaran ba. Tatafi da su"

"Ai kuwa dai. To wa zai zauna da gayyar dangin muguwa. Gwara data tafi dasu can su karata. A hayye. Duniya sabuwa"

"Sama lintin yayi yayi ladi" rumanah ta fada tana mikawa hajia ladi hannu suka tafa suna shewa...

Haka suka karasa jera abincin suka daddauka suka nufi sashen hajia zainab mahaifiyar su alhaji uzairu.

Saboda tsabar kissa da tuggun su na makirci. Kai kache suna cikin jimami, yarda suka wani lanjre sukayi rau rau da idanu tamkar suna cikin madaukakiyar damuwa Mai wuyar fassawara..

To haka dai rayuwaa ta kasance agidan alhaji uzairu dama dangin baki daya. Kullum ne ba ranar da zata fito ta koma ga mahalliccinta baai zancen zaytunah da yaranta ba. Gashi babu wani labarin ganin su. Ba wata dacewa da akai. Lamarin dai yana nan jiya I yau. Har ta kai ga alhaji uzairu ya kwanta ciwo sosai ya rufe shi. Abun sai ya sake tunzura ilahirun dangin gaba daya... Anata adduoi ana rokon Allah daya kawo karshen wannan annoba data kunno musu. Ya Kuma bawa alhaji uzairu lafiya ingacacciya...


_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

[1/23, 12:49 AM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_



_PAGE: 62_


🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️


*MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE:*


Daga sama NABEEHA ta sakko da sauri tana dauke da wasu litattafai masu matukar girma da yawa..

Ta sakko kasan ta shiga dakin mahaifiyar su hajia zaytunah. Tana kwance hannunta rike da charbi. NABEEHA tayi sallama ta shiga tana murmushi

"Ammi .."

"Naam NABEEHA"

"Zanje wajen su ya raudah zata koya mana homework ni da Humayrah"

"To sai kin dawo"

Ta futa daga dakin ta sauka kasa ta karshe inda gwaggo Hafsatu take.. gwaggon na zaune a parlor ta kurawa tv kallo tana kallon Shirin news da akeyi...

"Granny..."

"Naam... Diyar albarka"

NABEEHA ta tafi ta rungume gwaggo hafsatu tana murmushi. Gwaggon ma ta riketa tsam ajikinta tana duban ta,

"Ina zuwa yarinyar kirki?"

"Ya Raudah zata koya mana homework ni da Humayrah"

"Toh sai kin dawo .Allah yabada saa...."

"Tohm granny"

Ficewa tayi da sauri ta nufi sashen su humayrah. Tana zuwa ta tarar da Raudah da humayrah suna fitowa harda Hashim. Ya sakarwa humayrah da NABEEHA rankwashi,

"Ouch Yaya...."
Suka hada baki suna sosa wajen rankwashin daya musu

"Gerrout... Olodos. Sai dai ayita koya muku homework ba ku iya ba. Zan saka Mr Daniel nace masa tunda dakikai neku ayi muku repeating class"

"A'a fa munada kokari"

"Kai Yaya"

"Toh inde ba zaku dinga homework da kanku ba Allah zan gaya masa"

"Inshaa Allah. Yaya zamuyi "

Ficewa yayi ya nufi wajen masu gadi inda suke zama dasu suyi hirah, yayinda Raudah taja hannun su suka nufi garden anan suka zauna take koya musu homework din da aka basu..

××××


A haka rayuwar tacigaba da garawa. safiya ta zama rana, rana ta zama yammaci yammaci ya zama dare, lalle Allah qadirun ne ala manyashau..

🎗️🎗️🎗️

FAWAAZ ya dawo kasar mu ta gado. Inda ya nufi can makarantar sojoji yayi specialization a courses da yawa. Ya zamaa cikakken captain Mai star uku. Masha Allah da karancin shekarunsa basu ja ba ..

Ya yinda Alhamdulillahi NABEEHA da humayrah sun kare sakandire suna karatun fannin lafiya na likita wato medicine/ mbbs a jami'a...Sai Hashim daya tafi turkey ya zama babban pilot na Turkish airline. Raudah kuma babbar lawyer ce dakeda chamber ma..

Fawaaz na zuba kambun mulki da ikonsa akan su Raudah. Ba shiga harkar su yake ba ma. Amman kowannen su shakkar sa yake. Gashi baya magana. Miskili ne na karshen zance. Haka kawai ya Saka hukuncin kar wadda ta kara kawo masa gardi kofar gidan su da sunan yazo zance... Sannan ba magana yake musu ba. Amman kullum shi zaije ya dakko humayrah da NABEEHA a med school. Gaisuwa ce kadai ke hadashi da nabeeha. Shima sai yaga damar amsawa idan ta gayshe shi. Zai amsa a kasan makoshi. Har dai ta gama tsayarwa ranta da zuciyar ta wannan yaya fawaaz din ya tsaneta kawai. Kuma inshaa Allah ko dan shi sai wataran Ammin su tabata labarin usulin su...

CAPTAIN FAWAAZ DAWUD MAFIA, Fuskarsa tana da zubin kyau na musamman, mai daukar hankali. Idanunsa suna da zurfin gani, kamar suna boye SIRRIKA masu yawa, suna da launi mai duhu, ko kuma kore mai haske. Fuskar Fawaz tana da kyau, mai siffar gaske, da kyallen haƙoran da ke sanya murmushinsa zama abin burgewa. Gashinsa mai kauri, baƙin zinariya, yana kintse cikin tsarin soja na tsafta da kula, Saboda kasancewarsa soja, yana da jiki mai ƙarfi da tsari, yana nuna ƙoshin lafiya da kuzari. Yanada tsayi, yana kara masa karsashi. Fawaaz dawud, Ko da yake yana da kyau, yana da ɗan kyuwar hali na SIRRI da nesa. Muryarsa tana da taushi mai kwantar da HANKALI, amma yakan yi magana ne kawai idan ya dace. Yana da nutsuwa amma idan ya kalli mutum, zaka ji kamar yana karanta zuciyarka. CAPTAIN FAWAAZ DAWUD yanada wani boyayyen SIRRI. Wannan SIRRIN kuma ba komai bane fache, boyayyar Kaunarsa ga NABEEHA, Fawaz yana soyayya mai tsanani da Nabeeha amma ya kasa gaya mata saboda wani babban dalili da ya shafi rayuwarsa ko aikinsa. Duk da haka, yana nuna tsantsar ƙiyayya gareta kamar yana son ya koreta daga rayuwarsa, musamman a bainar jama’a. Amma idan akwai matsala, shi ne na farko da zai tsaya mata da ZUCIYA daya. Yakan kalli NABEEHA ta hanya mai cike da raɗaɗin kauna, amma idan ta lura, sai ya kawar da kai cikin gaggawa. Yana ɗaukar matakai don ya kare ta daga nesa, ba tare da ta gane cewa shi ne yake taimakonta ba.A takaice, FAWAAZ mutum ne mai kyau na waje da ciki, mai tsananin so amma kuma mai sanya kansa cikin wahala saboda tsananin SIRRI da ya sanya a zuciyarsa... Amma yana kaunar NABEEHA yana mata wani irin so fiye da yadda alkalami zai bayyana..

Dr. NABEEHA UZAIR MUHAMMAD..Nabeeha ita ce mace mai kyau na zahiri da na zuciya, wadda ke da halaye masu daukar hankali.Fuskarta tana da haske kamar alfijir, mai kyau da sanyin kallo. Idanuwanta suna da zurfi da annuri, suna nuna hikima da tausayi. Idanuwan suna da wani haske na dabi’a, kamar suna bayyana zuciyarta mai kyau.Gashinta mai laushi da tsawo yana da launin baki. yana da tsari mai kyau, yakan zube kan kafadunta cikin kwanciyar hankali.Hmm. NABEEHA Jikinta yana da matsakaicin tsayi, mai kyau da kuma daidaito, wanda yake bayyana ta a matsayin mace mai tsafta da kula da kanta.Muryarta tana da taushi da sanyin zuciya, tana jan hankali da kwantar da hankali idan ta yi magana. Nabeeha tana da nutsuwa da hikima, halaye da suka dace da ta kasance dalibar karatun likita. Tana da tausayi sosai, musamman ga marasa galihu ko kuma waɗanda ke cikin wahala. Ita mai gaskiya ce, kuma tana da kyakkyawar zuciya wadda ba ta son ganin wani cikin bacin rai.Ko da yake tana da kyau sosai, tana da kawaici da kunya. Tana kiyaye mutuncinta, ba ta yarda da duk wata dabi’a mara kyau ba.Kyawunta da kyan halayyarta sun janyo mata hankalin samari da yawa, amma tana kula da koyon karatunta fiye da komai. Daga cikin samarin da suka damu da ita, wasu suna zuwa gidansu suna neman ganawa da ita, wasu kuwa suna nuna soyayyarsu kai tsaye. Wannan yana ciwo sosai a zuciyar FAWAAZ, duk da cewa yana boye son da yake mata.Saboda tsananin kishinsa, FAWAAZ ya saka doka mai tsauri a gidan.. yana gargadi cewa kar wanda ya kara zuwa kofarsu don neman ganawa da ita NABEEHA ko humayrah.Duk lokacin da ya ga wani saurayi ya nufo ta, zai nuna masa fushi ko ya kira shi a gefe, ya yi masa barazana kai tsaye. Amma duk wannan Nabeeha tana daukarsa a matsayin tsantsar ƙiyayya gareta, ba ta san cewa yana ƙoƙarin kare soyayyarsa bane, Nabeeha ita ce cikakkiyar misalin mace mai kyau da kyan hali, wadda ke da daraja a wajen mutane da yawa, har ma da FAWAAZ da yake ƙaunarta cikin SIRRIn da ya barwa zuciyar sa ajiya....


_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/23, 12:50 AM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


_PAGE: 63_



🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️🎗️🎗️


A haka suka cigaba da rayuwa. Ranar nan dai ranar wata asabar da sakaliya.. gwaggo hafsat ta kira hajia zaytunah suka zauna su kadai a parlor suka taba hira, Anan ne gwaggon ta tanbayeta game da labarinta

Hajia zaytunah tayi murmushi, Alhamdulillah duk tsawon wannan shekarun hajia Hafsatu bata taba tanbayarta ba sai yanzu dama tace mata sai lokacin dataga dacewar hakan. Ai kuwa tache,

"Gwaggo a iya abunda zan iya furta wa, Sunana zaytunah. sunan mahaifiyata gwaggo abule sunanta na gaskiya zainabu. Mahaifina sunan sa malam idrisu. An haifeni na Kuma tashi a kauyen bokezuwa tare da yanuwana. Da kanne na Rayyanatuu da Sharifa. Amma dukan su Allah yayi musu rasuwa.

"Kafin rasuwar mahaaifiyata da kannena. Aka daura mun aure. Daman tuni mahaifin mu ya ruga rasuwa. Aka aura mun wani dalibin mahaifin mu amman yan birni ne. Aka aura mun shi aka kawo ni birni. Iyaye na da kannena da yayan mahaifina. Da kishiyar mahaifiyata da Babar kawata. Allah ya musu rasuwa sukayi hatsari. Na cigaba da zama da Mai gidana da matan sa biyu. Allah bai azurta ni da samun haihuwa ba sai daga baya.. rana daya Kuma naji bana kaunar zama acikin gidan ko cikin garin. Bansan inda zani ba. Naje tasha nahau mota muka hadu dake anan gwaggo. Wannan shine takaitaccen labari ne. Sai dai kila akwai wasu SIRRI kan da zuciya ta gaza bayyana su. Amman dai Ina rokon da ki sake mun hakuri. Har yanzu banajin shaawar son waywayawa gidan mijina. Zamana anan nafu samun nutsuwa. Banason na sake zaman aure dashi. "

Gwaggo hafsat tayi shiru... Tana tattauna maganganun hajia zaytunahh a zuciyar ta .can ta nisa tache

"Allah ya jikan su da rahama..Allah ya gafarta musu ya Kuma kyautata namu zuwan zaytunah idan zan iya cewaa dan Allah ki zauna dani har abadah wallahi shi yafi komai dadi awajena. Ina kaunar ki tamkar yar Dana haifa acikina wallahi haka nake jinki. Don haka ki daina bani wani hakuri ni nake kaunar na zauna dake zaytunah domin duk tarin shekarun nan naki ban nemi sanin labarin ki ba sai yanzu.saboda banason na rabu da ku ne, Ina Kuma son ki sake samun nutsuwa sosai, Na Kuma saurara na fahimta. Kishiyoyin nan naki atare dasu kike?

"Eh gwaggo"

"Kece ta fari?"

"A'a akwai wata sai ni sai ta karshe"

"Allah sarki. To babu damuwa zaytunah. Nan gidah ne kin zama yar gidaa ai kinji? Kin dade da zama yar gidah har gaban abada. Kuma ki sani yadda kika duakeni tamkar mahafiyar data kawo ki duniya. Inason kisan bazan kaiki inda zaa cutar dake ba. Bakuma zance ki koma matsugunin auren ku ba har sai na kammala bincike na na kuma tabbatar ya dace ki koma din... Allah yasa mu dache Amin"

"Aameen gwaggo Ameen..."

"Yanzu yayan ki (major general dawud) ai ya kirawo ni. Da zaiyi tafiya gobe ya fasa. Saboda yanada appointment da wani abokin kasuwancinnsu.. yasan shi a bayaa. Anyi zaman mutinci. Mahaifiyar suma kusan mun zauna a asibiti daya lokacin da zaa mun aikin kafa. Daga garin da muka dakko ki kenan"

"Eh" zaytunah ta amsa

"Suma yan garin ne. Yace wai suma suna cigiya ne suna so ya tsaya musu. Zuriyar muhammadu. Gidan su uzairu"

"Uzairu....?" Hajia zaytunah ta tanbayeta idanuwanta awaje

"Eh ko shine Mai gidan naki?" Gwaggo ta tanbaya cikin rudewa

"Sunansa uzairu Muhammad shima"

"Toh shine. Wanda zai zo nan din dan uwa ne ga uzairu. Alhaji Amiru"

"Sune gwaggo. Zasu tafi dani... shikenan bakiji KIRJI na ba gwaggo, HANKALI na ya tashi. Shikenan SIRRI na ya bayyana.."zaytunah ta fada tana fashewa da kuka sosai

"Bar zubar da hawaye zaytunah. Ba Wanda zai karbeki awajena. Bazama susan munsan da batanki ba bare sanayyarki . Don tuntuni rabanmu dasu an dau shekaru wallahi .. yanzu zance ne ya kawo zancen. Yasan yamun sallama yatafi. Sai Kuma ya kira yana shedamun..ki sani zaytunah na San muhimmancin SIRRIn ki. KIRJIN MAI HANKALI AKWATIN SIRRIN SA..Duk wani mutum mai hankali da wayo ba ya bayyana sirrinsa ga kowa, sai dai ya boye su a zuciyarsa. Wannan karin magana na nuni da muhimmancin kiyaye sirri da kuma yin taka-tsantsan wajen yin magana. Zaytunah duk mutum mai hankali yana da iya sarrafa bakinsa don kada ya tona abin da bai kamata ba... Bazan bayyana SIRRIN ki ba, zuciyar ko kwakwalwar mutum mai hikima, wanda ya san yadda zai rike sirrinsa da muhimman bayanai. Zaytunah mutum mai hankali yakan kasance kamar AKWATIN SIRRIN, yana rike abubuwa da ba kowa zai sani ba, kuma ba ya watsa maganganu barkatai. Wannan ya Kara nuna kima da darajar HANKALIn ki wajen kiyaye SIRRI da nuna nutsuwa.Amman karki damu zan kira shi yanzu yazo muyi magana tashi ki hau sama"

Hajia zaytunah ta mike da sauri ta haye sama. Kuka take sosai. Haka kawai taki jinin komawarta gidan alhaji uzairu. Shi kanshi batason akawo zancensa. Sunann sama batasan taji... Wutar tsabar tsagawaran asirin da aka mata na dada ruruwa a zuciya da gangar jikin ta...


Hakan kuwa akayi. Tafiyar zaytunah sama ba dadewa, major general dawud ya shiga wajen mahaifiyar tasa yana gaysheta .. sai da suka dakko zancen su Amiru yanata tanbayarta yana gaya nata abubuwan yadda sukayi . Bayan sun gama ta masa magana ta hankali ta Kuma ce dashi,

"Wannan dai yar uwata ce. Don haka aure ne ya hadasu. Kuma bata kaunar ta sake kasancewa awajensu ayanzu dai."

"Gwaggo to ya za'ai kenan sun damu da son ganin ta wallahi. Ni kinga banma saniba. Amma yadda yaketa kokorin haduwa Dani an dau tsawon shekaru gwaggo. Bai hakura ba Kuma suna ganin akwai hope . "

"Toh sai kasan dai abubuwan da zaka sanar masa.ai dama maganar batan ta zai maka ba sai sunada masaniyar inda take ba. Bayan kaima bakada sanayyar Hakan sai yanzu da nake gaya maka wacece itan.. sai ka tattaushe shi ka gaya mishi wani abun daban. Mu sake bata lokaci mugani Kuma dubada maganganun da tamun yadda na lura harda sa hannu gaskia. Rabata akayi da gidan aka Kuma sanya mata kiyayyar mijinta awajen ta..don haka da sannu komai zai warware Nima zan bada temako sosai ta wajena. Zan kira kauye ayiyyi sauka atayata da addua. Muma Kuma zamu cigaba dayi. Wannan maganar da nayi da Kai ta zama SIRRI dan Allah. Banason zancen nan ya futa. Don itama SIRRIN ta tagayamun.. don ya zama ance abin nufi cewa kana da SIRRI wanda ba kowa zaka fadawa ba.. to wannan SIRRIN zaytunah ne ..

"Domin Sayyiduna Umar bn khattab yake cewa duk KIRJIN daya gaza riqe SIRRIN SA idan yaji maganar a wajen wani to kada ya kuka da kowa ya kuka da kansa. Don haka AKWATIN SIRRIN duk wani MAI HANKALI ne ...."

"Hakane kam gwaggo kinyi gaskia ... KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA...)."

Yana rufe baki gate din gidan ya wangale bayan yayi horn alamar bakin sun iso, wato Alhaji Amiru dan uwa ga Alhaji uzairu ya iso gidan don ganawa da major general dawud mafia akan binciken da za'ai musu don gano masaniyar inda Hajia zaytunah da iyalan ta suke a raye ko a mache? ..........


_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*

[1/23, 9:07 PM] MY AIRTEL: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_

20 / 34