KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   25 / 34

72K to 75K   out of 102K words

girmamawa yace,

"Tuba nake ranki ya dade, wane mutum? Barka da rana granny .. fatan Kuna cikin koshin lafiya? Barkan ku da rana Maa.  Aunty" ya Dan juya yana gayshe da mahaifiyar sa da hajia zaytunah bayan yayiwa gwaggon.

"Alhamdulillah Allah yayi maka albarka. A zubo abincin? Tukunna dai samu waje ka zauna ka huta. "Gwaggo zainabu tace dashi tana murmushi

"Alhamdulillah... Kace wai babanku jibii zai dawo ko?" Cewar hajia maijiddah mahaifiyar su

"Barkan mu dai fawaaz. Sannu da kokari. Allah ya temaka "hajia zaytunah ta amsa shi

"Aamin Aameen. Ehh Maa haka yace mun."

Fawaaz ya gyara zamansa sosai a kusada gwaggo daga kasa. Ya sanya hannuwansa biyu yana matsa mata kafafuwanta.

Baki daya parlorn ya gauraye da daddadan kamshin turaren sa daya gauraye baki dayan parlorn. Mai sanyaya rai da sanya nutsuwa Mai matukar musulmin kamshi Mai ratsa magudanar jini da tsoka... Nabeeha ta bude hanci tana shakar kanshimsa dake mata dadi . Don da kamshin sa kadai takan iya gane yaje waje. Ko yabar wajen. Ko yana waje. Ta bude idanu ta lunshe tana sauke nunfashi ahankali. Kanta a kasa ita dai. Hannuwanta tanata mutsikasu. Batason ma ta daga Kai su hada idanu ya harareta..

" A zubo abinci ko?" Gwaggo tace dashi tana daga kafadar sa.

"Aa granny... "

"Indo(humyrah) tace Ina Neman kanko?"
.yan parlorn suka Saka Daria. Don idan yar tsokanr sukazo kan gwaggo haka take tsokanar kowa da sunaye. Takan cewa humayrah Indo ko a'ishalle... Tacewa Raudah. Mai idanu zuru zuru. Ko ta raudaka. Tacewa Nabeeha. Nabeehalle tacewa Hashim dan shimi. Ta kira Hammad da gaye tacewa fawaaz sarkin sarakan miskilai na nahiyar afirka da ketare...

"Kai granny" cewar humayrah tana turo baki gaba

"Danma bance a'ishalle ba..." Cewar hajia zainabu

Suka fashe da dariya baki daya. Banda fawaaz da shi dai baiga abun dariya ba. Gaba daya ma lissafin kasafin dake zuciyarsa ma baya tare da su.

"Ko?" Cewar granny ta sake tanbayarsa.

Fawaaz ya daga Kai da sauri yana cewa,

"Eh... Gani granny"

"Yauwa mu bamu gane kan abunda take cewa kace ta fada ba. Da fari dai dawuda zai dawo jibi ko idan Allah ya kaimu da Rai da lafiya. ?"

"Inshaa Allah "

"Yauwa to mungane wannan. Allah ya dawo dashi lafiya amin"

"Aameen granny"

"Sai Kuma baki da kace kanwarku zatayi ko?"

Fawaaz yayi shiru tamkar Mai tunani sai daya nisa can yace,

"Haka baba yace afada mata"

"Wai ne ko ko?"

"Haka yace"

"Wanene bakon? Daga Ina yake? Meke tafe dashi? Yaushe zai zo? "

Fawaaz ya daga Kai da sauri ya dubi gwaggo sai Kuma ya mayar da kansa kasa yana girgiza Kai yace,

"Sai dai akira baban. Kawai yace agayamata zatayi bako yau"

"Yau? Yau Kuma?" Gwaggo tabude baki cikeda mamaki

"Haka yace"

"Kira mun shi awaya"

Har fawaz zai ce ai mahaifin nasu yace zai shiga conference sai Kuma yayi shiru. Sawun giwa ai ya 'badda na rakumi. Wai akace gaba da gabanta. Mahaifiyar mahaifin su ce. Don haka doke ya kirawo mata danta.

"Tohm" yace yana zaro wayar sa aljihunsa.

Ya lalubo number mahaifinsa ya kira. Bugu uku kuwa major general ya dauki wayar yana sallama. Fawaaz ya gayshe da shi sannan yace dashi,

"Ga granny zakuyi magana"

"Tohm tohm. Bata yi sauri. ",

Fawaaz ya dauki wayar ya mikawa gwaggo zainabu kakar su. Ta karba tana murmushi tamkar dan nata yana gabanta.

"Waalyim Salam dawuda .. Naam lafiya kalau Alhamdulillah. Kuna nan kalau? Alhamdulillah. Alhamdulillah kowa da komai kalau dawuda. Aa kalau nake dawuda. Aa babu damuwa dawuda. Nasan zaka kira ai, to ya aikin? Allah yabada Lada yayi riko da hannuwanka ya yi maka ludufi. Yacigaba da shiga lamuran ka , ya Kara tsare ka da tsarewar sa. Amin dawuda. Amin. Nagode Allah yayi maka albarka. Ehh yanzu nace ya rikawo ka saboda bamu gane ba. Dan wajen Wa? Okay eh eh. Toh Allah ya temaka eh Hakan yayi. Toh babu damuwa Allah ya kawo su lafiya. Toh Allah ya sa yazo a saa. Eh Allah ya temaka. Allah yabaku saa. To shikenan zata shirya yanzu. Saidai ba komai baayi wani abun ba? Toh shikenan eh baa rasa ba . Inshaa Allah. Sannu da kokari. To shikenan eh. Eh. Eh mana, ka Isa dawuda. Ai Kaine uban. To shikenan. Aameen inshaa Allah. Allah yasa mu dache. Yauwa to shikenan sai munyi magana. Allah yabada saa." Ta mikawaa fawaaz wayar bayan sunyi sallama da dan nata Alhaji dawud. Wato Major general.

Kowanne ya zuba nata idanu suna jiran me zatace tayi murmushi tana duban Nabeeha tace

"Wani dan abokin sane. Ya ganki a makaranta. Yaro ne Mai hankali da nutsuwa yace zaizo shi ya ganki ku gaysa. in anjima da yamma. Sai ki tashi ki shirya diyar albarka "

Nabeeha ta daga Kai da sauri suka hada idanu da fawaaz da alokacin ya juya yana satar kallon ta. Kowanne ya sunkuyar da kansa. Shi yana tunanin karta gano lagonsa a kwayar idanunsa irin dinbin damuwar daya shiga.. Ta rena shi... Ita Kuma na dinbin tsorone da fargaabar Karya mata kallon nasa dayake mata na reni da kaskanci tamkar yaga Kashi Mai cike da tsana da kyama aganinta

"Tohm gwaggo" tace cikin sanyayyar muryarta...

"Toh Allah yayi muku albarka gaba dayan ku. Ya kara bude mana kofofin albarka amin. "

"Iyye amaria"cewar humyrah tana zungurin nabeeha cikin tsokana.

Nabeeha ta daga idanu tana rafka mata harara. Raudah da humyrah suka cigaba da tsokanar nabeeha. Ta mike da sauri ta tashi suka bita suna wasa da dariya.

Hajia maijiddah ma ta mike tana kakaro murmushi tace,

"Nabar wayata a cikin gidah ko ya kira bara naje. Kafin zuwan bakin ko? " Tace tana yiwa gwaggo sallama

"To maijiddah sannu da kokari. Sai kin dawo"

"Sai anjima hajia"

"toh auntyn su"

Fawaaz ya Mike kawai bai masan Ina zashi ba. Gwaggo zainabu ta dube shi,

"Ah tafiya zakai Kai ma?"

Ya dan durkusaa yana zube hannusaa akan carpet cikin girmamawa yace,

"Zan dan duba wani aiki he a computer, granny"

"Toh sannu da kokari Allah yayi maka albarka "

"Aameen gwaggo. Sai na dawo"

Ficewa yayi da sauri yana zura takalmansa. Kai tsaye ya wuce sashen sa. Ya zube akan kujera yana dafe goshinsa da tafukan hannuwan sa.

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun " yarafka salati..

Zuciyarsa sai bugu take tamkar zata fadi kasa..

Tun daga lokacin da Fawaaz ya bar sashen gwaggo Zainabu, zuciyarsa ta kasa samun sukuni. Duk yadda ya so ya daure ya mayar da komai kamar ba komai, hakan ya gagara.

Ya nufi dakinsa da matukar sauri, yana jin kamar zuciyarsa tana kokarin fashewa. Ya zauna a gefen gadonsa, hannunsa yana dafe da goshinsa.

"Waye wannan bakon? A makaranta ya ganta? Who is he??" Ya tambayi kansa. Me yake tafe dashi? Wani ne yake son ya mallaki Nabeeha?

Wani irin tsananin kishi ne ya lulluɓe shi, wanda bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa. A karon farko, ya ji cewa yana tsoron rasa Nabeeha, yana tsoron wani ya shigo ya dauke mata hankali.

Ya lumshe idanunsa, yana tuno yadda idanunsu suka hadu da ita a sashen gwaggon. Da yadda ta dauke kai da sauri. Shin tana jin wani abu akaina? Ya tambayi kansa. Ko kuwa ni kadai ne nake shirme?

Ya furzar da iska a hankali. Bai taba jin kansa cikin wannan yanayi ba. Shi mutum ne da baya sakewa da kowa, amma yanzu ga shi yana jin zuciyarsa tana yi masa tawaye.

Ya kwanta a kan gadonsa yana tunanin abin da zai faru idan wannan bakon ya zo. Shin zai iya daurewa yaga wani yana kokarin kusantar Nabeeha?

A lokaci guda kuma, zuciyarsa ta fara yi masa fada. Me zai hana ka gaya mata gaskiyar abin da ke ranka?

Ya runtse idanu da karfi. Bai san me zai ce mata ba. Idan har zai fadi gaskiya, ya tabbata cewa hakan zai sauya komai. Kuma shi mutum ne da baya son sauyi, baya son rashin tabbaci.

Sai dai ko yana so ko baya so, AKWATIN SIRRIN SA yana gab da buɗewa.....

*HGL CHARITY FOUNDATION*

(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)


_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_

Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..

Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:

1. Kayan abinci:

Wake don yin kosai.

Shinkafa don yin waina ko tuwo.

Gero ko dawa don yin kunu.

Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.

2. Abincin buda baki:

Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .

Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.



3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...


Hanyoyin Bayar da Tallafi:

1. Ta hanyar kudi:

Asusun Banki: 9044191709

Sunan Banki: Opay

Sunan Asusu: HGL Charity Foundation

Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.


3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..

Tuntube Mu:

Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240

WhatsApp: 09044191709

Ziyarci Shafukanmu:

Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk

TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1

Facebook: @hglcharityfoundation

Ƙarin Taimako:

Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:

Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..

Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.

Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.

Manufar Gidauniyar:

Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.

Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)


Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.

HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"

We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.

How You Can Help:

1. Donate Food Items:

Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.

2. Provide Ready-to-Eat Meals:

Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.

3. Financial Donations:

Bank Name: Opay

Account Name: HGL Charity Foundation

Account Number: 9044191709


Contact Us:

Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240

WhatsApp: 09044191709

Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.

"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."

May Allah reward your efforts..

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_PAGE:72_*


A dayan bangaren kuwa, . Raudah ta tsaya akan Nabeeha tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta abaya. Ta nade kanta da wadataccen mayafin abayar. Batayi wata kwalliya ba. Ta dai shafa kwalli da man lebe. Tayi kyau kwarai matuka tamkar balarabiya. Da suka kammala shiryata sai suka nufi sashen su don hutawa kafin bakin su zo.. Sai ita kadai, zuciyarta cike da tunani iri-iri. Tun da ta ji maganar Fawaaz da baba wato Major general dawud. cewa za ta yi bako, zuciyarta ke bugawa da sauri.

"Waye shi? Ta tambayi kanta. Wane ne yake son gani na?"

Ta dafe kirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Wani sashi na zuciyarta yana raya mata cewa akwai wani gagarumin lamarin da ke kokarin kunno Kai..Tun lokacin da idanunsu suka hadu a sashen gwaggon, ta fahimci cewa yana cikin wani hali... Tsananin kiyayyar har ya Kai haka?

"Shi wannan bakon kuma meyasa yayi haka? Me yasa yabi takan manyanta mai yake nufii? Me yasa ba zai iya magana kai tsaye ba da ita?.. "

Nabeeha ta gyada kai, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama. Tana jin wani abu a cikin zuciyarta, amma ba ta da tabbacin menene.

Gidan ya dauki sabon salo. Maaikatan nata hada hada, Duk kuwa da ba a san ko waye ba. Su nawa ne? Shi kadai ne? Oho .Humayrah ta dage tana ta tsokanar nabeeha tana turo mata stickers din gwalo ta Whatsapp ..

Nabeeha kuwa bata ce komai ba, sai dai zuciyarta na ci gaba da bugawa. A ranta, tana jin kamar wani abu mai girma zai faru yau.

A daya bangaren kuma, Fawaaz na zaune a falo, yana jiran jin motsin bakon. Zuciyarsa ta kulle da tunani iri-iri.

Bai san dalilin da ya sa yake jin kamar yana kokarin rasa wani abu mai tsada ba. Amma abu daya ya sani, idan wannan bako ya kasance wani da ke son Nabeeha. So Mai tsanani, toh yana da matsala.

Sai dai, waye bakon? Ya dafe kansa yana furzar da iskar bakin sa Mai zafi...


🎀🎀🎀🎀


An gyara babban parlorn daya kasance na mazaunin baki na alfarma dake zuwa... Kamshin turarukan wuta ne na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE ne kawai ke tashi. Gefe daya gana mopping mist din kamfanin anyi amfani dashi an goge ko'ina. Ga deodorizer dinsu itama an feshe dukkanin lunguna da sako. Sai kamshi ne ke kamsasawa mai sanya nutsuwa da kwanciyar hankulan duk wanda ya shaka... Niimace ke gauraye mutum. Lamarin sai kambamawa kawai ga hamdala ga daddadan turarukan wannan kamfanin na YERWA INCENSE AND MORE..

Falon ya kasance a shirye, kamar yadda aka saba, amma a yau akwai wani abu da ya bambanta... Wato zuwan wannan bako na Nabeeha....

Tuni nabeeha dama humyrah ta kama hannunta sun nufi parlorn sun zauna bisaga umarcin gwaggo zainabu. Sai dai parlorn Kashi biyu ne. Yanada na ciki karami sai Kuma babba awaje. Ma'ana kamar fiiubda parlor. To karamin su humayrah suka zauna. Idan bakin sunzo an musu iso sai su fito babban...

Gate din gidan ne ya fara alerting cikin wani sauti dayake yi a duk sanda bakuwar mota ta dososhi zata shigo. Saboda da kansa yake budewa ya rufe idan ya san mota. an mata rajista da setting dinsa. Yana alert kuwa masu gadi suka danna madanni gate din ya wangale..

Hancin motar sa mai matukar tsada da nishi ta kunno kai cikin harabar faka motocin gidan... Ya samu waje ya faka motar suka fito daga ciki su biyu...

Sanye suke cikin manyan kaya sunyi matukar kyau kowannen su. Samari ne masu jini a jika dake tashen kyau da gayu. Da suka gauraya da ilimin addini daya cakuda dana boko sike Kuma aiki da su...

Malam harisuya tarbe su dashi da sauran maaikatan gidan suka gaysa sosai. Sannan yayi musu iso cikin parlorn kaman yadda aka unarce shi..

Humayrah ta futo da sauri daga karamun parlorn bayan sun amsa sallamar da sukayi. Hannunta ta Saka ta dafe bakinta tana murmushi,

"Ina wuni ku?" Tace dasu tana saukar da kanta kasa.

"Alhamdulillah dago kanki mana. Karku daukeni yau amatsayin malami kinji ni ko?" Cewar dayan dake gefe.

Humyrah ta hadiye wani kakkauran abu daya tsaya mata a wuya. Saboda tsoron malamin nasu. Don din department dinsu shakkar sa akeyi. Ga kyau ga gayu ga iya shiga gashi baya shiga harkar kowa. Kowa tsoronsa yake don haka a darare take.

Ganin haka yasa shi murmushi yana dafa kafadar na kusa dashi yace,

"Nayi rakiya ne yau. Na rako aboki na. Wajen yar uwarki. Tana Ina?"

Humyrah ta sauke gwayron nunfashi hankalinta ya kwanta. Don da shine yazo neman nabeeha tabbas ba zata wani yi farin ciki ba. Don bata so lamarin sosai ba. Saboda malamin baya burgeta Sam. Saboda Jin kansa.

"Tohm... Bara na kira ta tana ciki" da sauri ta mike

Muhammad Hammad ya mike ya futa baranda yana amsa wayar da aka kira shi. Alokacin Kuma nabeeha ta fito suka gaysa da malamin nasu malam Fahad.

Ya shigo cikin takunsa na izza da kwarjini, jikinsa sanye da farar shadda mai kyau, fuskarsa cike da annuri. Kallo daya zaka yi masa ka san ba dan garin bane..ma'ana ba dan school din bane, bai kalar students ba, salon tafiyarsa, yadda yake cike da kwarjini, da yadda idanunsa ke kallon komai da lura.

Yana shigowa, idanunsa suka fara yawo yana neman wanda zuciyarsa ta kasa daina tunani a kanta.

A daidai lokacin, Nabeeha tana zaune a daya daga cikin kujerun falon tare da humayrah, suna tattaunawa a hankali. Wata ‘yar dariya ta kwace mata a sakamakon hirar da suke yi, amma hakan bai hana jin alamun shigowar wani ba.

Ta dago a hankali, idanunta suka ci karo da na bakon. A take zuciyarta ta buga! Gabanta ya fadi, wata kasala ta shige ta. Wani abu mara fassara ya ratsa tsakanin su.

Shi kuwa Muhammad, tun kafin su hada ido ya riga ya ji bugun zuciyarsa ya karu. Amma a yanzu da suka hada ido, wani irin sanyi da kauna suka lullube shi.ya sauke numfashi, sannan ya karasa inda take.

"Assalamu alaikum."

Muryarsa mai laushi da nutsuwa ta katse mata tunani.

Cikin sauri ta gyara zamanta, ta amsa. "Wa’alaikumus salam."

Murmushi ya kwace wa Muhammad. "Kin san ko ni wa ne?"

Nabeeha ta girgiza kai, zuciyarta na kara bugawa da sauri.

Shi kuwa Muhammad ya gyara tsayuwarsa. Zaiyii magana kenan. Humyrah ta mike da sauri,

"Bara na baku waje .. " tana kokarin guduwa. Malam Fahad ya Mike da sauri yana dakatar da ita,

"Zo nan kimun presenting wani paper work"

Tamkar zatayi Kuka. Sai Kuma ta daure ta juya ta koma inda yake suka zauna akujerun farfajiyar wajen maaikatan suka kawo musu abubuwan motsa baki already dama cikin parlorn an ajiye komai wajen su nabeeha...

"Ni Muhammad Hammad ne, kuma..." Ya dan ja numfashi. "Tun ranar da na ganki a ajin......

*HGL CHARITY FOUNDATION*

(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)


_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_

Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar

25 / 34