Daga fara magana har zancen aure ya shigo?
Hajia Zaytunah ta dubi Nabeeha a hankali. Ba ta so a matsa mata, amma kuma ba ta so ta hana ta damar yanke hukuncin da ya dace ba. Ta dan gyara zama, sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"Nabeeha..... " Ta kirata cikin muryar umarni da tunasarwa ga nabeehan da Kiran sunanta da major general yayi...
Nabeeha ta dago a hankali, idanunta suka sauka kan Major General Dawud. Tana jin kamar akwai wani nauyi a cikin zuciyarta. Idan har shi ne ya yanke hukuncin cewa Muhammad mutum ne mai kima, to babu shakka yana da kyau. Amma me take ji a zuciyarta? Ta yi shiru, sannan ta girgiza kai tache....
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
..
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE:76_*
“Ni… ni ban san me zan ce ba." Nabeeha ta fada cikin rawar murya.. Yayinda gabanta ya tsananta bugawa. Kunya da fargaaba sun tattara sun mamaye tah...
Gwaggo Hafsatu ta dubeta da kulawa. Tana murmushi tache,
"Kuna fahimtar juna da shi?”
"Eh..."
“Kin ji wani abu game da shi?” Gwaggo Hafsatu ta sake tambayar Nabeeha..
Nabeeha tayi shiru. Kanta a kasa. Wannan tambayar ta sa ji take tamkar wajen ya dare ta fada ciki...
“Diyar albarka... me zuciyarki ke gaya miki?” gwaggo Hafsatu ta sake tanbayar Nabeeha cikin muryar kulawa..
Gaba daya Nabeeha kunya ta gauraye ta. Musanman wannan tambayar ta karshe da gwaggo tayi...
Shiru ya sake biyo baya. Kowa yana jiran jin amsar ta, amma ba ta san mene ne zata ce ba. Idanunta suka yi kasa, zuciyarta tana bugawa.
A gefe, Fawaaz yana kallonta, zuciyarsa na tafarfasa. Shi ba zai iya cewa komai ba. Amma duk da haka, yana son jin abin da zata ce. Idan ta ce tana son Muhammad.. to ya san cewa ba shi da mafita. Amma idan ta ce bata so… Shin zai samu damar cewa wani abu?
"Ba zan iya yanke hukunci yanzu ba,” in ji Nabeeha a hankali.... Tana sauke katuwar ajiyar zuciya..
Gwaggo Hafsatu ta jinjina kai. Don sam batason a tursasa yaran. Gara ko wacce idan ta amince da kankin kanta shikenan...
"Hakan da kyau,” Gwaggo hafsat tace da Nabeeha, Ta Kara da,
"Babu matsala. Sai ki yi tunani, ki yi addu’a, sannan ki san me kike so.”
Hajiya Maaijidda Hauwa ta dan gyara zama.
"Alhaji,”
Major general ya daga kai yana mayar da tunanin sa gare ta,
"kai da kake cewa Muhammad yana da kima, shin akwai wani abu da ya gaya maka game da Nabeeha?”
Major General Dawud ya saki murmushi.
"Wallahi akwai. Yadda shi dan uwansa abokinsa yake fada. Saboda sunada kunya. Kowanne dan uwansa ne ke fadin raayin dayan sa.. yace ranar da ya ganta, bai daina tunani a kanta ba. Ya ce yana jin kamar ita ce macen da zuciyarsa take bukata.”
Fawaaz ya runtse ido, yana jin kamar zuciyarsa zata faso kirji. Bai taba jin irin wannan zafi ba.
Gwaggo Hafsatu ta danyi murmushi.
“Masha Allah! Abu ne mai kyau. Amma mu ba za mu tilasta wa kowa ba. Sai dai kawai mu tsaya a matsayin iyaye, mu ba da shawara.”
Major General Dawud ya jinjina kai.
“Haka ne,” ya fada.
“Zaytunah, ke ma ki yi tunani.gwaggo a yanke shawara idan komai ya zama tsayayye. Dukan mu, sai mu hadu da mahaifin su Fahad mu tattauna.”
Hajia Zaytunah ta jinjina kai.
"Tohm Yaya dawud, Nagode, Allah ya zaba abin da yafi alkhairi.”
A hankali, zaman ya dan yi shiru. Kowa ya shiga tunani. Amma daga cikin su duka, babu wanda zuciyarsa ke kuna kamar Fawaaz. Yana jin kamar yana kallon wani yana kwace masa abinda yake da daraja a gare shi, amma bai da ikon cewa komai.
Sai dai koda yaushe idan suka hada ido da Nabeeha, sai ya gaggauta kau da nasa. Yana jin kamar idan ya cigaba da kallonta, zai iya furta abu da ba zai iya janye shi ba.
Nabeeha kuwa tana lura da shi, amma ba ta fahimci me ke damunsa ba. Shin yana da matsala ne? Ko kuwa kawai halayensa ne na miskilan ya motsa?
Amma abu daya ne kawai tabbatacce – zuciyar Fawaaz ba ta da sukuni...
Shiru ne ya sake ratsa falon. Daga gefen Hajia Maijidda Hauwa, Raudah da Humayrah suna duban juna, suna jiran jin abin da zai biyo baya. Hammad yana wasa da yatsunsa, bai fahimci girman lamarin sosai ba, amma yana kallon yadda mahaifiyarsa ke shiru, yana jin kamar akwai wani abu mai muhimmanci da yake faruwa tunda shi daga baya yazo hutu. Kuma matashin saurayi ne da baida tsoma kansa akan abunda bashi da masaniya akai, musanman wanda manyan sa ne akai. Yakan tsame hannuwansa ya bar musu..
Nabeeha kuwa, tana jin wani nauyi a zuciyarta. Ta rasa yadda zata bayyana abin da ke ranta. Ba wai tana da wata soyayya da wani bane, amma tun daga yarinta, ragamar rike rayuwarsu a mahangar dan Adam a duniya ,tana hannun Major General Dawud da mahaifiyarsa Gwaggo Hafsatu. Su suka tsare su, suka kare su, suka ba su ilimi da kulawa. Su suka maye gurbin mahaifinsu da sauran dangin su da babu...
Shin, za ta fara da ce musu bata amince da hukuncin da suka yanke ba? A’a, hakan ba zai yiwu ba. Ba wai don ba ta da damar furta ra’ayinta ba, amma saboda ta yarda da su. Ta yarda da cewa su ne iyayenta, kuma ba za su zaba mata abu ba tare da la’akari da alkhairinta ba.
A hankali, ta dago kai, tana kallon Major General Dawud, sannan idanunta suka sauka kan Gwaggo Hafsatu. Ta numfasa a hankali, kafin ta furta da murya mai ladabi,
"Babu abin da zan iya cewa sai dai na godewa Allah da kuma ku da kuka rikemu tun muna yara. Ba ni da wani tunani da ya fi na biyayya gare ku. Tunda kuka amince da Muhammad mutumin kirki ne, to babu shakka ba zan ce a’a ba. Na amince.”
Kamar daga sama, shiru ya sake ratsa falon. Kowa ya juyo yana kallonta. Major General Dawud ya dan sauke ajiyar zuciya, yana jin wani sanyi a zuciyarsa. Shi mutum ne mai son gaskiya, kuma bai taba son tilastawa kowa abu ba. Ya yi matukar farin ciki da yadda Nabeeha ta fahimci matsayinsu a rayuwarta.
Hajia Zaytunah ta jinjina kai, idanunta sun dan cika da kwalla. Ba don komai ba, sai don yadda Allah ya azurta ta da iyayen gata da suka kula da ita da yaranta tamkar su suka haife tah..
Gwaggo Hafsatu ta kalli Nabeeha da kulawa, kafin ta saki murmushi.
“Masha Allah, Allah ya yi miki albarka Nabeeha. Kin kasance yarinya mai hankali, mai biyayya, kuma muna alfahari da ke.”
A gefe guda, Hajia Maijidda Hauwa ta saki murmushi. Koba komai zata huta da ala qaqai..Komai dai ya kusa yazo karshe ta huta itama. Su tarkata su tafi...
“Allah ya sanya alkhairi, Nabeeha,” in ji ta.
Humayrah da Raudah suka dubi juna, suna dariya a hankali.
"Wow, Nabeeha zata zama amaryar Air captain Muhammd” Humayrah ta rada wa Raudah.
Raudah ta dan harare ta da wasa, sannan ta kalli Hashim, wanda ya saki ajiyar zuciya yana kallon ikon Allah.
Fawaaz, Yayi shiru... Bai taba jin wani nauyi a kirjinsa irin wannan ba. Kamar ana takawa zuciyarsa da nauyin dutse. Kamar zuciyarsa na tafasa a cikin kirji, tana neman fashewa. Bai yi tunanin cewa da gaske ne har sai da ya ji Nabeeha ta furta kalmar “Na amince.”
Numfashinsa ya dan tsinke. Ya rike hannunsa a kan cinyarsa, yana jin yadda gumin zufa ke fara taruwa a goshinsa. Babu wanda ya lura da shi a farkon lokaci, sai Raudah da Humayrah, wadanda suka ga yadda ya dan jingina da kujera kamar wanda ba ya jin dadi.
"Yaa Fawaaz,” Humayrah ta rada Raudah,
"Kamar bashi da lafiya ko?"
"Ehh,” Raudah ta amsa, tana dan binshi da kallo.
“Ko yana jin ciwo ne?”
Ba ita kadai ba, har hajiya Maijidda Hauwa ta lura da yadda fuskar dan nata ta dan chanza.
“Fawaaz, lafiya?”
Fawaaz ya ji muryarta a kunne, amma kamar ba ya jin ta sosai. Idanunsa sun kada, numfashinsa ya dan canza. Sai dai da yake miskili ne, bai ce uffan ba. Ya san cewa idan har ya bude baki, zai iya furta wani abu da zai tona sirrinsa.
A lokacin da idonsa suka sake kaiwa ga Nabeeha, sai ya sake juyawa da sauri. Kamar idan ya cigaba da kallonta, zuciyarsa za ta fashe. Bai taba jin irin wannan damuwa ba a rayuwarsa.
Gwaggo Hafsatu ta kalli hajiya Maijidda Hauwa da alamar tambaya.
“Shi kuma me ke damunsa?”
Hajia maijidda Hauwa ta dan tabe baki.
"Bari mu gani,” ta fada tana gyara zama. “Fawaaz,” ta kira sunansa.
Ya juyo da sauri, yana kallonta, amma daga yadda idanunsa suka yi jajir, sai ta san cewa ba lafiyarsa ke damunsa ba. Da alama zuciyarsa ce ba ta da kwanciyar hankali.
“Mene ne?” ta tambaya
“Babu.. Nothing.” ya fada da sauri, yana kokarin gyara zaman sa.
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
..
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE:77_*
Amma duk wanda ya san shi, ya san cewa akwai matsala. Fawaaz mutum ne mai kamun kai, mai kwarjini, mai jan aji, amma ba a taba ganinsa a wannan yanayi ba.
Hashim ya dan rankwafa yana kallonsa.
“Yaya Fawaaz, me ke damunka?”
“Na ce babu komai,” ya fada da dan daga murya.
Amma daga yadda ya kasa maida ido ga kowa, sai kowa ya gane cewa akwai abu a zuciyarsa. Kawai dai bai da ikon fada.
A hankali duk aka kammala maganganun da akeyi. Aka shiga wata hirar, amma Fawaaz bai san lokacin da suka karkare komai ba. Har lokacin zuciyarsa na tafasa. A lokacin da Nabeeha ta mike don taya Humayrah dauke manyan pillows zuwa mayar dasu karamin parlor, sai suka hada ido da Fawaaz. Idanunsa sun kada, yana kallonta kamar yana son cewa wani abu, amma sai ya kauda kai da sauri.
Nabeeha ta lura da yadda fuskar sa ta canza, sai ta dakata a hankali.
"Yaya Fawaaz, lafiya kuwa?”Ta furta a hankali, murya cike da kulawa.
Zuciyarsa ta buga. Amma bai san ya zai ce ba. Bai san ko yana bukatar fada mata gaskiya ba. Bai san ko yana bukatar kau da kai ba. Sai kawai ya girgiza kai.
“lafiya" Amma zuciyarsa na fadin “A’a, ba lafiya ba.”
Nabeeha ta tsaya cak, tana kallon Fawaaz. Daga yadda fuskarsa ta chanja, da yadda muryarsa ta yi sanyi, sai ta fahimci cewa babu lafiya. Amma da yake mutum ne mai matukar kamun kai da miskilanci, ba abu ne mai sauki ba ya amsa cewa yana cikin damuwa.
Sai ta matsa a hankali, ta dan tsugunna kusa da shi, cikin kulawa da girmamawa.
"Yaya Fawaaz, idan wani abu ke damunka, dan Allah ka fada. Ka san cewa kowa a nan yana tare da kai.”
Idanunsa suka sake kadawa. Zuciyarsa ta daka tsalle. Kamar yana jin ana zungura masa wani sanyi da daci lokaci guda. Me zai ce mata? Me zai iya cewa?
Akan ido zai fada mata cewa zuciyarsa ce ke tafarfasa saboda ita? Zai iya cewa tun da aka fara maganar aurenta da Muhammad. Zuciyarsa ba ta samun natsuwa? Ko kuwa tunda sukazo gidan su tun tana karama daya fara dora idanunsa akanta zuciyar sa ta kamu da kaunar ta?
A’a, hakan ba zai yiwu ba. Fawaaz mutum ne mai tsananin girman kai, ba zai iya furta irin wannan magana ba.ya dan juya kai gefe, yana kokarin hadiye wani nauyin zuciya.
"Nabeeha,” ya kira sunanta da wata murya mai sanyi da ba a saba jin ta ba.
Da sauri ta juya. For the first time in her entire life.. yau ne ta taba ji fawaaz ya ambaci sunanta dai dai. A Kuma irin wata murya mai wutar fassarawa . Zata iya rantsewa ba Wanda ya iya Kiran sunanta yaja shi da luggar tajwid irin fawaaz. Kafin tace wani abu tuni ya sake cewa,
“bakomi"
Ya mike da sauri, yana