nan kanwar ka kace mata zatayi bako anjima ta shirya."
"Raudah ko Humayrah?" Ya tanbaya gabansa nata faduwa.
"Banason sakarci. Su kadai ne kannen ka?"
"Tuba nake Babaa."
"Nabeeha nake nufi... Later" kit ya katse Kiran
Fawaaz ya zare wayar daga kunnensa yana duban screen din. Bakinsa abude. Hannunsa a sage da wayar a hannun sa ta sulale ta Fadi kasa.
Ya Mike tsaye har yana tuntube ya take screen din wayar tasa ya wuche ta kanta. Bai ko Kalli wayar ba. Ya sanya hannu a bakinsa yana furzar da iska Mai zafi...
"Bako? Wane irin bako? Dan uwa ko saurayi? Wait. Inaga dai Dan uwan su ne can?"
Ya girgiza kansa yana mai dunkule hannunsa ya nausawa bango Hadi da cije kasan leben sa cikin zafin rai...
"No no no these can't be happening. Nabeeha tah? No no no. Allah dan Allah..." Ya durkusa akasa tamkar Wanda zai sujjada.
"Ko Baba zan kira naji waye?" Ya daga kansa yana tanbayar kansa kamar zaucacce.
"No ai kuma yace zai shiga taro. Kuma ma Ina nake da guts din tambayar shi wane bakon ne? Tunda har yabi ta kaina saurayi ne. Tunda na hanaso zance.. God.... I'm done! La'ilaha Illa Anta Subhanaka Inniy Kuntu Minazzalimin... I'm in pains I'm in pains I'm in pains.... Yaa Rabbi" ya karasa fada yana rike saitin zuciyar sa .
Mikewa yayi ya dauki mukullin motarsa. Har yaje kofa ya tuna da wayar sa dake culle a kasa ya dauka ya zura a aljihunsa.
"Morning sir" junior cardets dinsa suka shiga Sara masa
Ya daga musu hannu kawai ya nufi motar sa ya shiga. Allah ne kadai ya tsare shi ya mayar da shi gidah. Don zuba gudu kawai yake a titi baya tsayawa.
Yana karasa shiga gidah ko gama parking baiyi ba ya shige sashen sa. Wanka ya shiga yayi. Ya dauro alwala yayi sallar nafila. Ya dauki Qurani ya karanta. Saboda haka yakeyi a duk lokacin da tunanin nabeeha ya hanashi sukuni musanman yanzun da yake cikin tsantsar tashin hankalin da bai taba shiga ba ..
Sai daya samu nutsuwa sosai ya Kai aya sannan ya ajiye Quranin hannunsa. Wayarsa ya dauka sai alokacin ya lura screen din Yama fashe. Yaja tsaki ya janyo daya wayar dake kan gadon sa.
Ya lalubo number Humayrah kanwarsa da yayi saving da Humayrah Dawud Mafia. Har zai mata message sai Kuma ya fasa ya danna mata kira .
Duk suna azaune a parlor gaba daya wayar humayrah ta fara ringing. Tana zaune sai ta mike tana rufe baki cikin dimbin mamaki. Don baya kiranta a waya. Ko ta Whatsapp tamasa magana baya kulata. Sai tayita naci kafin ya tura mata emoji. Kudine dai kafin su tanbaya zai basu dukansu har Hammad kanin Nabeeha...
"Menene ke kuma haka?" Hajia Hauwa Maijidda mahaifiyar su ta tanbaye ta.
Duk Yan parlorn sai suka juya suna dubanta. Kowa yana sauraron ta
"Yaya ne..." Ta fada tana amsa Kiran ta zauna tana zare idanu,
"Hello Yaya... Ina wuni?"
"Lafiya..." Ya danyi shiru kuma.
"Hello Yaya. Abinci zaa kawo? Ka dawo ne?"
"No no need.... Tell Maa and granny and Aunty and others dai duka. baba ya kira waya yana tanbayan kowa yana gayshe da kowa. Jibi zai dawo inshaa Allah"
"Tohm Yaya zan gaya musu inshaa Allah. Allah ya dawo da shi lafiya amin."
"Amin... And then...."
"Inaji Yaya. Sai me? And then what?"
"Tell that girl... Baba yace zatayi bako "
"Which girl Kuma?"
Duk suka zuba mata idanu dake suna jiyo muryar fawaaz dinma. Ya yamutse a Kuma yangance tamkar Wanda aka tursasa yayi maganar yace..
"The girl named Nabeelaa ne ko me...."
"Ohkay Nabeeha. Tam inshaa Allah"
Kit ya katse Kiran. Yana jiyo sanda suke cewa menene. Ya Kuma San sunajin maganar da yayi. Fisabilillahi menene haka? Yadda ya fadi maganar nabeeha ko sunan nata ma yaki ya fada Dede bayan ya sani...
"Yaa Allahu ka bani Nabeeha..." Ya fada yana rufe idanunsa....
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
May Allah reward your efforts abundantly.
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_LITTAFI NA DAYA*_
_PAGE: 70_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
***Humayrah ta ajiye wayar hannunta akan kujera tana duban Nabeeha cike da farin ciki tache,
"Zaki bako wai.... Tashi ki shirya dear sis" Ta karasa fada cikin rawar jiki.
Duk yan parlorn suka tsaya suna duban humayrah cike da madaukakin mamaki marar misaltuwa. Kowanne da abunda yake kissimawa cike da mamaki.. Bayan suna dan jiyo sautin muryar fawaaz din. Amman gaba daya basu tsammaci abunda yace daga karshe ba kenan.
"Fito ki fadi abunda ya gaya miki. Wanene wannan dinne ku ke wayar? Wanne bako kuma?" Cewar hajia maijiddah.
"Tamkar kin shiga zuciyata maijiddah. Sai dai ni na tuna da yayan su fawaaz take magana ai. Amman bakon da za'ai ne. Da kuma manufarsa ta wajen zuwa wajen nabeehan bugu da kari daga Ina yake wanene shi. ? Waya Aiko shi ke kira fawaaz dinnan mana. Kice nace yazo" gwaggo zainabu ta fada tana murmushi .Kirjinta fal da farin ciki. Na nabeeha kilan wani saurayin ne na kwarai yazo da aurenta Kuma fawaz din ya aminta dashi tunda har gashi yace acewa nabeehan zatayi bako. Don a baya duk samarin su cayake kar wadda wani kato ya sake zuwa kofar gidan su zance da sunan saurayinsu ne wai.
Hajia zaytunah dai batace komai ba. Haka zalika nabeeha da gabanta ya tsananta bugu. Suka hada idanu da mahaifiyar ta hajia zaytunah. Hajia zaytunah ta sakar mata tattausan murmushin daya sanyata nutsuwa hankalinta Kuma ya kwanta... Ta sauke gwauron numfashi tana mutstsika yatsukan hannunta tayi shiru batace komai ba itadai ..
"Kema Humayrah anata miki magana. Me Yaya fawaaz din yace ne? Wane bako? Kiyi elaborating mana. Kinyi magana a gajarce . Sai kache wata yar kauye?" Cewar Raudah yayar su
"Kai Yaya" humayrah ta fada tana dariya. Sannan tache,
"Kinsan Yaya da yanayin maganganun sa in brief. Cafa yayi baba zai dawo jibi idan Allah ya Kai mu. Sannan agayawa nabeeha zatayi bako inji baba"
"Okay toh Alhamdulillah Allah ya dawo dashi lafiya amin. " Hajia maijiddah ta fada tana Maida kanta tv
"Ameen Yaa rabbi. Toh Wanne bako ne zaizo wajen nabeeha? Meke tafe dashi? Wanene shi? Kuma yaushe zai zo? "Cewar gwaggo zainabu.
"Sai a kirashi gwaggo. Kamar yadda kikace din. Wallahi bansan wanene ba. Kawai yace na gaya mata haka inji baba"
"Mashaa Allah. Allah ya dawo dashi lafiya" hajia zaytunah ta fada
"Allah ya dawo da baba lafiya cikin aminci Amin" nabeeha ma tayi addua kanta a kasa
Duk suka amsa da Ameen ... Humayrah ta dauki wayarta ta lalubo number fawaz ta kira shi. Bai dauka ba. Tasan hali dama. Don haka ta masa message da,
"Yaya kazo inji granny yanzu" ta tura masa message tana duban gwaggo,
"Na masa message granny, da bai dauki wayar ba."
"Toh bari mu saurare shi Allah ya sa Muji alkhairi Amin"
Halin da Fawaaz ya Shiga na Tashin Hankali ne matika... Fawaaz yana zaune a cikin dakin sa, ya jingina da kujera, amma zuciyarsa ba ta da natsuwa. Tunanin da ke yawo cikin ransa ya mayar da shi wani hali na tashin hankali da ya kasa fita daga ciki. Idanunsa sun lumshe, amma a cikin zuciyarsa, hoton fuskar Nabeeha yana fitowa a hankali kamar ana zana shi da farin kwali a kan duhun dare.
Ya sake bude idanunsa, yana jin zuciyarsa tana bugawa fiye da yadda ta saba. Ya dade yana kokarin boye son da yake yi wa Nabeeha, yana daurewa da miskilancin sa, amma yau ga shi yana ji kamar zuciyarsa za ta fado daga kirjinsa. Dalili kuwa shine, An ce wani saurayi zai zo wajen Nabeeha.
"Saurayi… Bako?"ya ambata kasan zuciyarsa tamkar zaiyi kuka..
Wane ne ke tunanin ya mallaki zuciyar da har ni Fawaaz ban samu zarafin furta soyayyata a gare ta ba?
Ya girgiza kansa da sauri, yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Bai san yaushe ya fara jin tsoro ba, amma ya tabbata cewa yanzu yana jin wannan tsoron matuka. Shi da bai taɓa tsoron komai ba, sai dai abunda yafi karfinsa bayan na mahaliccinsa, iyayensa, manyansa, Dan halal wato a musulunci, shi da ko a makaranta kowa ke kallonsa da mutunci saboda miskilancinsa da rashin sakewa, yau ga shi yana jin wani irin shakkar abu wanda bai taba jin irinsa ba a rayuwarsa.
Sai dai me zai yi? Idan ya fita waje ya ci karo da ita, zai iya cewa mata wani abu kuwa? Ko da ma ba za ta fahimci zurfin son da yake mata ba, zai iya fahimtar cewa yana da ikon ajiye girman kan sa don ya gaya mata gaskiyar zuciyarsa?
A hankali ya mike tsaye, yana jin tamkar kafafunsa sun yi nauyi. Wani abu yana daga masa zuciya, wani tunani da ya kasa kawarwa daga ransa. Idan bai gaya mata ba, idan ya ci gaba da boye soyayyarsa, wata rana za ta wuce ta bar shi da bakin ciki.
Sai dai kuma, me zai ce? Shin yana da kalmomin da za su iya bayyana tarin soyayyar da ke ransa?
Ya dafe goshinsa da hannunsa, yana jin tamkar wani yana murza zuciyarsa da hannaye. Zuciyarsa tana tafasa, tana masa gagarumar dariya.
"Kai Fawaaz, ka farka daga wannan mafarki! Ai tun farko baka da shi a kan ta. Kayi tsammanin zata iya fahimtar shiru da miskilanci? Kana tsammani zata fahimci SIRRIN dake tattare acikin KIRJIN ka? Ko kuwa har yanzu kana tunanin HANKALIN zai isa ga AKWATIN dake dauke da kaunar ta da ka ke?"
Wani yanki a cikin zuciyarsa yana yi masa dariya, yana yi masa kashedi. Idan har yana son ta, me zai hana ya gaya mata? Idan kuwa bai gaya ba, me zai hana ya hakura da ita gaba daya?
Ya zauna a bakin gado, yana runtse idanu kamar wanda ke kokarin tuno mafarki mai dadi. Ya tuna da yadda take dariya, atattare da yan gidan idan suna hirar su yana sauraron su, yadda take sakewa da kawayenta idan yaje yana labe med school dinsu., amma idan yana kusa, sai ta sunkuyar da kai kamar mai jin kunya. Ko Mai tsananin Jin haushin sa. Gaba daya dai zuciyarta da KIRJIN ta da HANKALIn ta basa nutsuwa idan har ta ganshi. Saboda tsananin tsanar sa da takeyi...
Ya yi tunani sosai. Idan har wani saurayi ya zo wajen ta, zai iya jurewa kuwa? Idan ta fara kulawa da wani, shin shi kansa zai iya ci gaba da rayuwa da zuciya mai cike da nadama?
Bai sani ba. Sai dai abu daya ya tabbata, yana cikin tashin HANKALI fiye da wanda ya taba shiga a rayuwarsa...
Karar shigowar Sako message ne ya sanya ya sauke zuciya Mai tattare da damuwa ya dubi screen din wayar yana karantawa. Sako ne Humayrah ta turo masa na yaje Inji kakar su gwaggo zainabu yanzu.
Dakyar ya iya mikewa yana tangadi da layi tamkar Wanda yasha yayi tatul yana dafe bango dakyar ya iya wuce wa. Ya nufi sashen gwaggon bakinsa dauke da istigfari. Dakyar ya samu nutsuwa ya iya sallama ya tura kofar sashen ya shiga. Yadda ya wani gyara kansa ya seseta yana wani Shan Kai kaikace ba wani abunda ke damun sa. Lalle fawaaz namijin gaske ne Mai wuyar sha'ani. Kuma miskilancinsa ya Kai ya zarce fiye da koma…….
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
May Allah reward your efforts..
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE:71_*
Cikin muryar sa mai karsashi da yanayin sa dake nuna shi din jajirtaccen namiji ne mai cikeda kamala da zatin haiba.
"Wa'alaikumus salamu wa rahamatullahi Wa barakatuh." Suka amsa baki daya..
"Ga irin ta ku" gwaggo zainabu tayi masa jinjina tana murmushi..
Fawaaz ya karasa wajenta ya zube gwiwoyinsa har kasa ya tsugunna yana sakin tattausan murmushin sa shima. Wanda kakaro shi kawai yakeyi. Zuciyar sa na bugawa cikin tsananin tashin hankalin da yake ciki. Amman dake mazantakar sa ta hau har ta ketare ba zaka taba ganewa ba...
Ya sanya hannunsa yana sosa keyarsa. Cikin