KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   21 / 34

60K to 63K   out of 102K words

_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_PAGE:64_*




*** A tare suka daga kai tamkar gate din yana gaban su. Major general ya ceda mahaifiyar tasa cikin ladabi.

Bayan sun kammala tattaunawa da mahaifiyarsa a cikin parlorn nata,

"Inaga gashi nan ya iso ma.... Bari naje naji yadda zamu kaya da shi Gwaggo. In shaa Allah ba zaa samu matsala ba"

"Toh shikenan. Allah ya maka albarka Amin"

"Aameen gwaggo, Allah ya Kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka Amin"

Major General Dawud ya tashi daga kasan kujerar da yake, yana mai mayar da hankali kan abinda ke gabada shi. Gidan yana cike da yanayi mai kyau, amma zuciyarsa tana ciwo saboda SIRRIN da yake dauke da shi. Yana sanin cewa komai ya fara zama mai wuya fiye da yadda ya zata...

Waya ya kira tuni maaikatan sashen suka kai kayan motsa baki babban parlorn nasa. Inda bakon nasa yake...

A cikin babban parlor na gidan, Alhaji Amiru ya zauna cikin dakiya, daurewa kawai yakeyi. Bayan sun gaysa shi da major general. Alhaji Amiru harda dansa yazo...

Bayan sun gaysa. Major general ya matsa musu kan lalle su dan ci wani abun na daga abubuwan da aka ajiye agabansu. Suka dan tsattsakuna suka ci..

Daga nan alhaji Amiru yayi gyaran murya ya shiga sanarwa major general abubuwan da ke tafe da shi..Ya karasa fada yayi shiru yana

jiran jin ra'ayin Major General kan bukatarsa. Shahararren soja mai babban mukami Wanda ke da kwarjini a boye da fili. Jin Shirun da major yayi. Hakan ya sake tabbatarwar lalle lamarin zaytunah yayi tsamari tunda ga manyan kasar ma lamarin ya sashi dimuwa. Lalle al'amura sun fara rikitarwa. Alhaji Amiru ya kalli major general Dawud cikin girmamawa.

"Ranka ya dade,"

"Naam!!! Na tausaya ne matuka. Kuma inshaa Allah komai zai daidaita alhaji Amiru"

Alhaji Amiru ya kara da cewa,

"Ina jin dadin tattaunawar mu, kuma na gode da cewa ka yarda ka taimake mu. Amma fa, wannan lamarin yana da wuya. Muna neman Zaytunah, kuma ba mu san ko tana raye ko ta rasu ba. Munyi yi duk abin da ya kamata, amma ba mu sami nasara ba... Itada yaranta biyu kanana. Daya ma shayar dashi take"

Major General ya danyi shiru, yana kallon Alhaji Amiru da idanuwansa cike da tunani.

"Na fahimci damuwarka," ya ce da sanyi. "Amma ba zai yiwu mu dauki matakin da kake bukata ba cikin hanzari. Wannan binciken yana bukatar lokaci da kuma tsare-tsare na musamman."

Major general dawud ya fada yana tuno mahaifiyarsa da ta dinga rokon sa da gaske. SIRRIN Zaytunah yana rike a matsayin al'amari mai matukar muhimmanci ga iyalinsu.

"Zai dauki lokaci," ya cigaba da cewa. "Na fahimci abin da ka ke nufi, amma dole mu bi hanya mai kyau da hankali."

Alhaji Amiru ya amince da wannan, yana fitar da ajiyar zuciya, yana kallon Major General da girmamawa.

"Na gode, Major General. Allah ya saka da alheri."

"Aameen Yaa Rabb. Allah yabamu saa. Sai ka sake rubatamun address dinku, da numbers da za'ai reaching dinku. With valid emails haka... "

"Toh ranka ya dade. Allah ya Saka da alkhairi yabamu saa"

"Aameen Yaa Rabbi... Inshaa Allah akwai nasara agaba. Amma addua itace gaban komai"

"Anayi wallahi. Sai dai a sake zage damtse. "

"Toh Allah ya datar da mu. "

"Aameen... Aameen. Bari na baka card dina . Ina yaron nan yaje dasu shi na bawa su na ce ya ajiye. Kasan tafiya zanyi. Maganar da zanyi da Kai ne tadawo Dani"

"Allah sarki ranka ya dade. Allah ya kara girma da daukaka."

"Aameen jam'an inshaa Allah"

Wayarsa ya janyo ya kira . Saidaya kira sau uku baa dauka ba. Tukun sannan ya kira daga baya.

"Ahap. Zo toh"

Fawaaz ya katse Kiran ya zura wayar a aljihunsa. Ya nufi cikin gidah sashen mahaifin su bakinsa dauke da sallama.

Ji yayi tamkar ya juya ganin mutane aciki. Yadda ya sauya zubinsa lokaci daya Kai kasan miskilancinsa ne ya motsa ganin bakin fuskokin daya gani. Ya karasa a dadare yana musu sallama. Sallamar ma a gayance a Kuma cikin mulki. Suka amsa gaba daya

Ya gayshe da mahaifin nasu ya gayshe da alhaji Amiru ya Kuma mikawa dan gidan Alhaji Amiru hannu suka gaysa..

"Ka sheda shi kuwa? Ko da yake shekarun da yawa..."

Alhaji Amiru ya daga Kai yana duban fawaaz. Hannunsa rike akan bakinsa yace,

"Ba dai yaron wajen ka bane. Ya girma haka?"

Fawaz ya dubi alhaji Amiru dake kiransa yaro. Ya danyi murmushi kansa a kasa.

"Shine fawaaz... Captain fawaaz kenan. Soja ne ai"

"Mashaa Allah kyan da ya gaji ubansa. Wai akace gado girman da"

"Ga Muhammad ma.. shima ya zama pilot"

"Mashaa Allahu. Kaga Yara da kokari Ubangiji Allah ya yi riko da hannayen su Amin"

"Aameen Yaa Rabbi"

"Fawaaz Ina cards dinnan? bani guda biyu pls."

Fawaaz ya zaro cards din a aljihunsa ya mikawa mahaifin nasa yana sosa keyarsa..

"Tashi kaje... Sarkin miskilai na duniya"

"Ah ai naga alama yana shigowa"

"Haka yake tun yarintar sa. Nayi nayi nayi har na hakura da halinsa"

"Ai ba wani abu bane mara kyau. Miskilanci Allah na tuba yanzu ai miskilai sunfi kamewa...Allah dai ya raya su Amin"

"Aameen Aameen... Ga cards din"

Alhaji Amiru ya sanya hannu biyu ya karba yana duba katin yana karantawa... Shima ya zaro nashi ya bawa major general dawud.

Daga nan sukayi masa sallama suka fito daga ciki suka shiga mota suka dau hanya suka tafi ..

---

Hajiya zaytunah ko da ta koma cikin dakin ta, zama tayi, tana jin cewa lokaci ya yi da za ta yi magana game da asalin su ga Nabeeha da Hammad. Saboda haka, ta nemi dasuu zauna tare. Wannan dama ta kasance mai muhimmanci domin bayyanawa Nabeeha yadda rayuwa take a matsayin su, da kuma bayyana wasu abubuwan da take boye musu.

"Nabeeha,"

Hajiya Zaytunah ta fara cikin laushi, "Na san cewa akwai abubuwa da dama da basu bayyana miki ba, amma lokaci ya yi da za mu yi magana. Zai iya zama mai wahala, amma na san za ku fahimta."

Hajiya Zaytunah ta dauki lokaci kafin ta cigaba, tana ba da labari mai taƙaitacce game da rayuwarta da takaitaccen usulinta.

"Duk da cewa ni da ku Muna cikin wannan gidah, Kuma gwaggo Hafsatu itace tamkar mahaifiya agare ni, muna cikin wannan gidan, ba za ku iya fahimtar duk abin da muka fuskanta ba. Kodayake na kasance cikin kariya, wannan sirrin yana rufe wani bangare na rayuwarmu wanda bai kamata ku sani ba. Amma akwai bukatar ku fahimci cewa ba wanda zai iya fahimtar wannan ba sai mu."

Nabeeha ta kalli Haj zaytunah da idanuwanta, tana jin cewa akwai abubuwa masu yawa da ta rasa. Ta fahimci cewa mahaifiyar su haj Zaytunah tana cikin damuwa, kuma wannan abu ya sa ta zama mai sirri

"Na fahimta Ammi. Ko da yake ba zan iya fahimtar cikakken labarinki ba damu kanmu gaba daya, zan yi duk mai yiwuwa don taimaka mana gaba daya."

Zaytunah ta yi murmushi, tana jin nauyin zuciyarta yana saukewa.

A ranar anan ta iya dakatawa. Saboda Kiran intercom da gwaggo hafsat tayi kan hajiya zaytunah taje tana nemanta..

---

A bangaren Hajiya Hauwa mahaifiyar su fawaaz kuwa ta fara kallon yanayin zaman su Zaytunah a gidan. Wannan ya sanya ta fara shakku, tana jin cewa akwai wasu abubuwa da ba a bayyana mata ba. Wataƙila akwai abubuwa na asiri da za su iya canza yanayin zaman ta a gidan. Zuciyarta na jin cewa akwai wani abu mai zurfi wanda ba a bayyana ba, kuma hakan yana kawo rarrabuwar kai a tsakaninta da sirikarta aganin ta dama yayan ta...

___
Fawaaz yana cikin dakin sa, yana kallon Nabeeha ta balcony din sama daga nesa ta windown dakinsa dake facing bangaren su nabeeha. Wanda windown dakinta irin manya manyan nanne fawaaz na hango komai. Munsaman idan ta fito yar barandar dakin nata...

Wannan yana kara jaddada halin da zai yi amfani da shi wajen kula da ita, yana tunanin yadda zai tabbatar da cewa tana cikin kwanciyar hankali, ko da yake bai bayyana mata ba..Baya ga gaisuwa, yana jin cewa akwai abubuwa da suka faru a cikin rayuwarta da ya kamata ya kulla tunani mai kyau wajen kula da ita. Wannan zai kasance sabon lokaci ga Fawaaz, wanda zai yi kokari wajen samar da mafita ga Nabeeha, ko da yake bai taɓa jin wata damuwa ba....

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
[1/23, 9:17 PM] MY AIRTEL: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_PAGE:65_*



Bayan tafiyar Alhaji Amiru da dansa, Major General Dawud ya zauna a kujerarsa yana nazarin duk abinda ya faru. Sirrin Zaytunah yana ci gaba da nauyaya a kansa. Wannan batu na neman rushe tunaninsa, amma ya san cewa dole ya cika alƙawarin da ya dauka wa Gwaggo Hafsatu.

Ya mike tsaye da sauri, ya nufi dakin mahaifiyarsa. Lokacin da ya shiga, Gwaggo Hafsat na zaune tana lazimi. Ta daga kai tana kallonsa, cikin kulawa ta ce,

"Dawuda, na ga damuwa a fuskarka. Kayi hakuri, amma kada ka bari wannan al’amarin ya bata maka tunani."

Major General ya zauna kusa da ita, yana murmushi mai rauni.

"Gwaggo, lamarin ya fi yadda nake zato. Amma zan yi duk mai yiwuwa don ganin wannan sirrin bai taba zaman lafiyarmu ba."

Gwaggo Hafsatu ta dora hannunta kan nasa.

"Allah yana tare da mai hakuri, Dawuda. Ka ci gaba da addu’a. Na tabbata zai zo da mafita."

"Inshaa Allah gwaggo .. bari na koma na fan karasa abubuwan da nakeyi. Tunda na daga tafiyar sai zuwa jibi ko gata"

"Toh Ubangiji Allah yasa hakane yafi alkhairi. Allah Kuma yayi riko da hannayen ka ya dora akan makiyan ka. Allah ya cigaba da temakon ka ya sanya albarka a dukkanin lamuran ka Amin"

"Aameen gwaggo .. aameen.a huta lafiya" ya fada yana sake durkusawa yayi mata sallama cike da ladabi..

...

A cikin babban parlorn gidan, Major General Dawud ya zauna yana nazarin wasu takardu. A duk lokacin da ya fuskanci wata matsala mai girma, koyaushe yakan nemi mafita a cikin shiru da tunani. Sai dai, yau ma tunaninsa ya tafi kan wata matsala daban wato ta hajiya Zaytunah.

Cikin nutsuwa, Hajiya Hauwa ta shigo parlorn. Ko da yake kullum tana shiga cikin sauri da alfarma, wannan karon ta shigo da sannu, alamar akwai abu mai muhimmanci a zuciyarta.

"Ranka ya dade .," ta ce cikin ladabi, tana zaunawa a kujerar da ke kallonsa kai tsaye.

"Na’am, Hauwa. Lafiya lau?" ya tambaya cikin kulawa, duk da cewa yana ganin damuwa a fuskarta.

Hajiya Hauwa ta yi ajiyar zuciya, sannan ta fara magana,

"Dawud, na dade ina tunanin maganar nan, amma har yanzu ban samu damar yi maka ba. Abin da ke damuna shi ne Zaytunah."

Major General ya dago kai, yana kallonta da idanuwansa masu karfin hali, amma bai ce komai ba.

"Na lura da zaman ta a nan, amma gaskiya, ban fahimci komai ba game da ita. Su waye Zaytunah? Me ya sa take nan har yanzu, ba tare da wani bayani ba? Ga yaranta har sun girma kowanne ya mallaki hankalin kansa? Ina jin tamkar akwai wani abu da ake boyewa."

Major General ya yi shiru na wasu yan dakiku, yana nazarin yadda zai mayar mata da amsa. Sai ya tuna da hudubar da mahaifiyarsa, Gwaggo Hafsatu, ta yi masa kwanakin baya,

"Dawuda, ka rike sirrin nan amana. Ba kowa ne ya kamata ya san labarin ba. Yin hakan zai iya kawo matsala mai girma. Sai lokacin da ya dace ka bayyana gaskiya."

Wannan tunanin ya sa zuciyarsa ta dan yi nauyi. Sai ya dan yi murmushi mai rauni, ya sauke takardun hannunsa, sannan ya kalli Hajiya Hauwa.

"Hauwa, na fahimci damuwarki," ya kara da nutsuwa. "Amma ina so ki yi hakuri da ni. Wannan batu yana da alaka da wasu al'amuran iyali ne da kuma amana da aka dora min. Ba komai, Haj Zaytunah yar uwace agare mu. Kuma mafi soyuwa a zuciyar gwaggo, musanman da batada kowa sai gwaggon, Zaytunah tana cikin kulawa, kuma komai zai daidaita a lokaci mafi dacewa."

Hajiya Hauwa ta hade girarta, tana kallon sa da tambayar rashin gamsuwa.

"Amma Dawud, ka san ba na jin dadin rashin fahimtar abin da ke faruwa. Wannan sirri yana sa ni jin tamkar ba mu cikin gida daya. Me ya sa ba za ka iya fada min gaskiya ba?"

Major General ya dan yi shiru, yana kallonta da idanuwansa masu nuna girmamawa...

"Hauwa, ba wai ba na yarda da ke ba ne," ya ce cikin rarrashi. "Sai dai wannan batu yana da wuyar bayyanawa yanzu. Ki yi hakuri da ni, zan fada miki idan lokaci ya yi. Amma abunda duk kike tunani bashi bane..."

Hajiya Hauwa ta mike tsaye da dan fusata.

"Dawud, ka san ni matar ka ce. Ina da hakkin sanin duk abin da ya shafi wannan gida. Amma tunda haka kake gani, zan jira. Amma ka sani, ba zan daina neman gaskiya ba."

Ta juya ta fita daga parlorn, tana jin zuciyarta cike da damuwa. Sai dai Major General ya zauna a wurin, yana kallon bayanta tare da jin nauyin sirrin da ke hannunsa. Duk da haka, ya san cewa ya dauki matakin da ya dace domin kare amanar mahaifiyarsa da kuma Zaytunah.

"Allah ka kawo mana mafita," ya furta a hankali, yana rufe idanunsa cikin addu’a....

*HGL CHARITY FOUNDATION*

(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)


_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_

Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..

Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:

1. Kayan abinci:

Wake don yin kosai.

Shinkafa don yin waina ko tuwo.

Gero ko dawa don yin kunu.

Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.

2. Abincin buda baki:

Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .

Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.



3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...


Hanyoyin Bayar da Tallafi:

1. Ta hanyar kudi:

Asusun Banki: 9044191709

Sunan Banki: Opay

Sunan Asusu: HGL Charity Foundation

Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.


3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..

Tuntube Mu:

Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240

WhatsApp: 09044191709

Ziyarci Shafukanmu:

Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk

TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1

Facebook: @hglcharityfoundation

Ƙarin Taimako:

Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:

Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..

Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.

Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.

Manufar Gidauniyar:

Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.

Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)


Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.

HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"

We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.

How You Can Help:

1. Donate Food Items:

Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.

2. Provide Ready-to-Eat Meals:

Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.

3. Financial Donations:

Bank Name: Opay

Account Name: HGL Charity Foundation

Account Number: 9044191709


Contact Us:

Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240

WhatsApp: 09044191709

Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.

"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."

May Allah reward your efforts abundantly.

[1/23, 9:43 PM] MY AIRTEL: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_PAGE:66_*


*Daman* yana dauke da timetable dinsu. Wato jadawalin tsarin karatun da sukeyi na makarantar koyan harkar lafiya. Wato humayrah da nabeeha.

Don haka wani lokacin da yake less busy. Kafin driver yaje ya dakkosu. Yakanje da kansa da wuri ya dakko su. Domin Hakan na karaa sashi yanajin kusantakar sa na kara matsuwa da nabeeha. Don dakko su kawai da yake wasu lokutan yana sanya shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali..

Yayin da Fawaaz ya iso makarantar don daukar Humayrah da Nabeeha, sai ya lura cewa su biyu suna tsaye a kusa da gate din makarantar, suna jiran zuwan mai daukarr su. Duk da haka, hankalinsa ya fi karkata ga wani

21 / 34