dakyar ya kira number mahaifiyarsa, yana kokarin boye tashin hankalin da ke cin ran sa.
“Maa, an turo min da aiki wani gari. Sai na dan yi wata daya kafin in dawo.”
Hajiya Hawwa ta dakata na dan lokaci, kamar tana nazarin kalamansa.
“Wane gari ne? Kuma me yasa haka babu zato babu tsammani?”
“Akwai wasu ayyuka ne da suka taso kwatsam. Yana da kyau in tafi don yin su kafin lokaci ya kure.” Ya mayar da martani a takaice, yana kokarin boye hakikanin dalilin tafiyarsa.
A hakikanin gaskiya, ba wani aiki ake turowa da shi ba. Zuciyarsa ce ta tilasta masa gudu. Idan har zai cigaba da zama a cikin wannan gari, zai ci gaba da ganin Nabeeha da saurayinta suna magana, suna dariya, suna tafiya tare tamkar su ne kadai a duniya. Ba zai iya jure hakan ba.
"Shikenan fawaaz. Allah ya bada saa. Ya dawo da Kai lafiya."
"Aameen."
Daga nan ya kira mahaifinsa major general dawud yayi masa sallama. Ya kira gwaggo Hafsat kakarsu itama yayi mata sallama..
Duk yadda ya so ya musanta, gaskiya daya ce, ya kamu da kaunar Nabeeha fiye da tunanin da yake da shi a farkon al’amari. Soyayyarta ta yi masa yawa, ta cika shi ta ko’ina, ta hana shi sukuni. A duk lokacin da ya kalle ta, yana jin tamkar duniya ta tsaya cak. Amma ita, ko a jikinta. Ta riga ta zabi wani. Ta riga ta sadaukar da zuciyarta ga wani, kuma wannan ne abin da ke ci masa tuwo a kwarya.
Ko da yana daki, yana zaune shi kadai, yana jin tamkar yana cikin taron jama’a, jama’ar da suka cika zuciyarsa da tunanin Nabeeha. Idan yana tafiya a cikin gidan, yana jin kamar numfashinta yana nan, kamar tana kusa da shi, kamar yana jin dariyarta a kunnensa. Amma abin takaici, ba shi da matsayin da zai tsaya a gabanta ya ce mata,
"Nabeeha, ki saurare ni. Nima ina son ki!"Bai da wannan damar.
Shi mutum ne miskili, mutum ne mai nutsuwa, mutum ne da ba ya saurin bayyana abin da yake ji. Amma wannan karon zuciyarsa ta ruguje. Bai iya ci gaba da fuskantar wannan hali ba. Ya yanke shawarar tafiya. Idan har kasancewa cikin garin nan na nufin ci gaba da ganin Nabeeha da saurayinta, to gara ya bar garin gaba daya.
Ranar da zai bar gari, babu wanda ya san ainahin dalilinsa. A bakin gate ya ci karo da nabeeha ta karbi Sako daga hannun mai gadi...
“Yaa, Barka da safiya. ina za ka haka da safe?” Ta tambaya tana murmushi, kamar kullum.
Muryarsa ta dan shake, amma sai ya daure.
"Aiki"
Nabeeha ta dan kada kai. “Allah ya kiyaye hanya. Za mu yi kewarka.”
Ya kasa cewa komai. Ya dan yi murmushi kawai, sannan ya juya ya bar wajen. Bai ce zai yi kewarta ba. Bai ce zai rasa ganin ta ba. Amma a ransa, yana jin tamkar ya bar zuciyarsa a bayanta.
Lokacin da ya shiga mota, ya lumshe ido na dan lokaci, yana kokarin mayar da numfashinsa daidai. A zuciyarsa, yana jin tamkar yana gujewa kaddara ce, amma yana kuma jin cewa babu inda zai tsere daga son Nabeeha. Ko ya je wani gari, zuciyarsa tana tare da ita. Ya bar garin, amma son Nabeeha ya bar shi? A'a. Zuciyarsa ta tafi da ita.🥹🥹
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE: 80_*
*_BOOK ONE:_*
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Duhu ya lullube cikin dare. A cikin katafaren gidan Alhaji Uzairu, a sashen Hajia Ladi, wasu mata uku suna zaune kamar macizai masu jiran lokacin kai farmaki..Hajia Rumanah ce a tsakiya, mace mai yawan takama da girman kai, tana rike da kofin shayi amma ba ta sha ba. A gefenta, Hajia Karama da Hajia Ladi suna kallon juna, idonsu cike da tsananin tsana.
Fuskar Hajia Rumanah ta cika da baƙin ciki da takaici. Ta hura hanci sannan ta daka tsaki.
"Ba zan taɓa barin Zaytunah ta more rayuwa ba. Wallahi, bazan iya zama na huta a duniya idan har wannan munafukar ta ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali ba! Dole ne mu dauki mataki..mu dauki na ƙarshe!"
Hajia Karama ta dan sauke numfashi, fuska cike da ɓacin rai tache,
"Kina tunanin maganar kawai za ta yi mana maganin wannan matsala? Lokaci yayi da za mu ɗauki matakin da zai yi ajalinta. Muna nan muna zaman jiran ranar da za ta dawo gidan nan? Ko kuma mu ci gaba da bari 'ya'yanta su taso su kawo mana matsala? Wannan ba zai sabu ba!"
Hajia Ladi ta rankwafa kusa da su, tana wasa da yatsanta kamar wadda ke nazari.
"Ya kamata mu fitar da su gaba ɗaya daga duniya. Amma ba kawai sace su zamu yi ba. Muna bukatar mu tabbatar da cewa ba za su iya dawowa gida ba har abada!"
Hajia Rumanah ta harɗe hannaye, murmushi mai cike da mugunta yana bayyana a fuskarta.
"Na riga na samo mafita. Na samu lambar wani boka a can kauyen Bakin Dutsi. Ana kiransa Boka karfen-Kwarya. Mutum ne da ake ji da shi wajen muggan ayyuka. Zai iya yi mana aiki da ba za su sake dawowa duniya ba."
Hajia Karama ta gyada kai cikin gamsuwa,
"Amma kafin mu je wajensa, dole mu fara da matakin farko..mu sace su! Mu tabbata cewa su Zaytunah sun bace daga duniya kafin mu fara amfani da sihiri."
Hajia Ladi ta jefa takarda a tsakiyarsu, tana zana wasu tsare-tsare. Bayan sun gama tsara shirin, sai suka dauki matakin na gaba, wato zuwa wajen boka...
"Wannan matsaya da muka tsayar kwarai matuka tayi.. Tunda har ita matar dake gaya mana SIRRIN komai na can inda Zaytunahn suke ta lamince mana muyi komai. Ba wani haufi da zai kawo mana cikas.." cewar hajia rumanah ta fada tana girgiza kafa, Hadi da sakin dariyar mugunta..
Haka dai suka cigaba da shirye shiryen su har ya zuwa ranar da suka tsayar na zuwa gidan bokan su..Dare ne mai tsananin duhu. A cikin wata motar Prado mai duhun gilashi, Hajia Rumanah, Hajia Karama, da Hajia Ladi sun tafi can cikin jeji don ganin boka Karfen-Kwarya.
Bayan tafiya mai tsawon awa biyu a cikin dazuka da duhun dare, sun iso wani kauye mai suna Bakin Dutsi. Wurin kamar matattarar duhu ne, babu fitila, babu hayaniyar mutane. Duk da haka, suna iya jin kukan tsuntsaye da wata irin iska mai karfi da ke kadawa kamar ana ihu.
Lokacin da suka sauka daga mota, wani dattijo mai dogon riga da jan kwanyar mujiya a kansa ya fito daga wata bukka. Idonsa fari fat kamar bai da ganin duniya. Ya kare musu kallo daga sama zuwa kasa, sannan ya yi dariyar da ta sa duk jikinsu ya yi sanyi.
"Hahahaha... Mata uku masu zuciya mai duhu. Na san dalilin zuwanku, kuma na san abin da kuke so!"
Hajia Rumanah ta matsa kusa da shi, ta yi gyaran murya.
"Mun zo ne don ka yi mana aiki. Muna son a yi wa wata mata da 'ya'yanta asiri da zai sa su bace daga doron ƙasa!"
Boka ya rike gemunsa, yana murmushi.
"Kuna so na shafe su ne gaba ɗaya daga duniya? Ko kuna so su rayu cikin wahala har su roƙi mutuwa da kansu?"
Hajia Karama ta harare shi.
"Ba ma so kawai su mutu, muna so su sha wahala kafin su mutu! Muna so su rasa komai, su lalace, su zamo 'yan iska da ba su da wani amfani a duniya!"
Boka ya sunkuya ya dauko wani tsohon kwano mai cike da garwashi da turare. Ya hura wani hayaƙi mai ƙamshi, ya kalli sama, yana magana da wata murya mai nauyi.
"Za a yi musu sihiri mai tsanani. Za a dinga ganin su a matsayin cuta a idon mutane. Duk inda suka shiga, sai mutane su guje su. Zaytunah za ta rasa komai. Za ta zama mahaukaciya, ta manta da komai, har ta fice daga duniyar nan!"
Hajia Ladi ta bushe da dariya.
"Hahaha! Wannan shi ne abin da muke so!"
Boka ya dauki wata tukunya, ya hada wani matsi, ya shafa masa wani garin kashin kaho. Sannan ya daga kansa ya ce,
"Ku bar sauran a kaina. Bayan kwana uku, wannan aikin zai fara tasiri. Kuma idan har muna so lamarin ya tabbata har abada, dole ku kawo min wani abu daga jikin Zaytunah, zai iya zama tufafinta, ko gashinta, ko wani abu da take amfani da shi!"
Hajia Rumanah ta dauke numfashi.
"Wannan ba matsala ba ne. Za mu samo komai da kake bukata."
Boka ya yi dariya.
"Idan kun gama shiryawa, ku dawo min da abin da nake bukata. Sai mu kammala wannan aiki, kuma Zaytunah da iyalanta ba za su sake waiwayar duniya ba!"
Sai suka kalli juna, kowacce na murmushi. Sun san cewa shirin su zai yi aiki, kuma nan da kwanaki kalilan, za su tabbatar da cewa Zaytunah da yaranta ba su da makoma...
Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, wani yana bibiyarsu, kuma komai da suke shiryawa yana da shirin da zai rusa su baki daya.....
🎀🎀🎀
A cikin wani katafaren falo da ya kunshi kayan alatu, an jera manyan kujeru masu launin zinariya da shuɗi. Haske mai laushi daga fitilun bango yana bada wata irin annashuwa, amma hakan bai hana fuskokin mutanen da ke zaune a cikin falon bayyana gajiya da damuwa ba.
Gwaggo Zainabu, dattijuwar uwa mai cike da basira da hikima, tana zaune a tsakiyar ‘ya’yanta biyu, Alhaji Amiru da Alhaji Uzairu. Duk da shekarunta sun ja, hakan bai hana ta zama mai ƙarfin hali da kamun kai ba. Tana sanye da zumbuleliyar shadda mai launin toka da farin dutsi, kanta lullube da farin gyale. Idanunta na cike da damuwa yayin da ta kalli ɗanta, Alhaji uzairu, wanda ya dafe goshinsa da hannunsa yana tunani.
Alhaji Amiru kuwa yana jingine a kujerarsa, yana wasa da zobensa, alamar yana cikin nazari mai zurfi.
"Uzairu," cewar Gwaggo Zainabu cikin natsuwa, "ka dai kwana biyu ba ka da walwala. Tun da maganar Zaytunah ta taso, nake ganin damuwa a fuskarka. Me kake tunani ne?"
Alhaji uzairu ya sauke ajiyar zuciya, ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa da yaya Amiru,
"Gwaggo, zuciyata ba ta da kwanciyar hankali. Kullum idan na kwanta sai na yi mafarkin Zaytunah tana kira na. Har yanzu babu wanda ya tabbatar mana da halin da take ciki, ko da rai ko kuma a mace. Yana da matukar wahala a rayuwa ka rasa sanin inda ɗanka ko ‘yar uwarka take."
Alhaji Amiru ya gyada kai.
"Haka ne, uzairu. Mun yi shiru da yawa. Lokaci ya yi da za mu nemi wani mafita."
Gwaggo Zainabu ta gyara zamanta.
"To, idan haka ne, sai mu ziyarci Major General Dawud. Ni dai har zuciyata na ji akwai rufin asiri a cikin wannan lamarin. Yaron nan Muhammad da yake neman yar wajen ko? Sai muje mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya"
Alhaji Amiru ya gyaɗa kai da gamsuwa.
"Haka ne, Gwaggo. Major General shine mutum mafi karfi da zai iya taimaka mana. Ba wai don yana da matsayi kawai ba, har da cewa shi mutum ne mai tsari da mutunci."
Alhaji Uzairu ya yi shiru na ɗan wani lokaci sannan ya dubi mahaifiyarsu.
"To gwaggo, idan haka ne, wace rana za mu shirya tafiya?"
Gwaggo Zainabu ta ɗan yi nazari sannan ta ce,
"A ganina sai mu shirya tafiya ranar Laraba mai zuwa. Hakan zai ba mu damar samun lokaci na ganin Major General da samun bayanai na hakika."
Alhaji Amiru ya gyada kai.
"Hakan yayi daidai. Sai mu fara tsara yadda za mu yi tafiyar, kuma zan kira wani daga cikin mutanena don ya taimaka wajen jin ko yana gari a wannan rana."
Bayan da suka gama shawarar tafiya, sai hira ta juya daga zancen Zaytunah zuwa sauran batutuwan rayuwa.
Gwaggo Zainabu ta kalli Alhaji Amiru da fuskar da ke dauke da alamun sha'awar tambaya.
"Amiru," ta ce, "ka dai kwana biyu bana jin ka na magana akan Muhammad. Shi kuma fa ya shigo da wata sabuwar magana akan auren nan da yake so?"
Alhaji Amiru ya dan yi murmushi, sannan ya gyara zamansa.
"Gwaggo,Muhammad fa yana kan matsayinsa. Ya dage akan cewa sai Nabeeha, wato ‘yar Major General Dawud."
Gwaggo Zainabu ta ɗan zaro ido cike da sha’awa.
"Kai! Allah dai ya raya mana zuri'ah Amin"
Alhaji Uzairu ya kyalkyale da dariya.
"Wallahi kuwa, Gwaggo Muhammad ya ce tun daga ranar da ya fara ganinta, zuciyarsa ta kasa daina tunaninta. Yana ganin ita ce wadda ta dace da shi."
Gwaggo Zainabu ta yi murmushi mai cike da jin dadi.
"Haba Muhammad! Da kyau! Ai na san mai gidan nawa ba zai kawo min wata kishiyar da ba ta da mutunci ba. Amma dai zan so in ga wannan Nabeeha da idona. Idan har ta cancanta, to, ni dai zan ba da goyon baya." Ta fada cikeda wasan kaka da jika..
Alhaji Amiru ya gyada kai. Yana murmushin shima yace,
"Hakane Kam gwaggo, Ai Fahad dan gidan Alhaji Abdulfatah wato wanda ya wakilcemu shine fa yayiwa major magana a matsayin mahaifin Muhammad din..wallahi Muhammad yana gaya mun yace alhaji Abdulfatah din agaban su ya kira major general yace yana nemawa dan wajensa neman izinin zuwa tadi wajen yar sa Nabeeha. Yayi tozali da ita a makaranta yaji yana kaunar ta.. Maganar nan da nake miki bana tunanin har yanzu major general ma yasan gaskiar lamarin ni ne mahaifin muhammad. Na masa message dai kwanakin baya, bana tunanin ya karanta ma. Saboda nakeson dama zamu ware wani lokacin don turawa ko zuwa da kai don sanar masa qudurin mu. Ance yarinyar mutuniyar kirki ce. Ita mutum ce mai hankali da kamun kai. Kuma tun da yake son ta da gaske, ba zan hana shi ba. Sai dai zan so in san me iyayenta suke tunani game da batun."
Gwaggo Zainabu ta dafa kugu, tana mai tunani.
"To, idan haka ne, ai wannan tafiya da za mu yi ita ce damar da za mu yi magana da Major General. Mu gani ko yana da wata matsala da hakan. Ni dai ina so in ji irin halin Nabeeha kafin na amince gaba daya."
Alhaji Uzairu ya gyada kai.
"Gwaggo, ni dai bansan meyasa ba. Bantaba ganin taba. Amman yadda ake fasalta yarinyar nan Nabeeha na tabbatar tanada nutsuwa da tarbiyya, biyayya da kuma ilimin addini dana boko"
Gwaggo Zainabu ta saki murmushi.
"To, bari dai mu je, mu hadu da ita da idonmu. Idan Allah ya sa mun dace da ita, to, sai a kawo maganar aure gaba."
Bayan da suka gama tattaunawa, sai suka yanke shawarar cewa za su fara shirin tafiya. Za su je birnin Noka don samun damar ganin Major General Dawud da kansu, su kuma tattauna da shi a kan maganar hajiya zaytunah.
A gefe guda kuma, Gwaggo Zainabu ta riga ta kagu don ganin wacece wannan Nabeeha da jikanta Muhammad ke burin aura?
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE: 81_*
Zaune Major general dawud mafia yake a kan kujerar falo, yana kallo cikin talabijin da idanunsa ke duban allon ba tare da ainihin hankalinsa na can ba. Labarai ne ke tafiya a tashar da ya fi kallo, amma zuciyarsa na can cikin wata duniyar tunani mai cike da rudani...
A gefensa, matar sa, Hajiya Hauwa Maijidda, tana zaune cikin shigar shadda ruwan hoda mai ɗauke da ado na zinariya. Hannunta na dama na juyawa a wayarta, tana mai duba wasu sakonni.
Babu wanda ya yi magana a tsakaninsu na wasu mintuna. Shi kuwa, Major General Dawud, ya jingina da kujerarsa, yana mai lumshe ido lokaci-lokaci, sai dai can, wayarsa ta ɗauki kira.
Ya kai hannu yana duban screen din wayar..
"Chief Judge Abdulfatah" ne ke kira.
Bai yi kasa a gwiwa ba, ya ɗaga wayar cikin girmamawa.
"Salamu alaikum, Chief Judge!"
Daga can gefen aka amsa da murmushi...
"Wa alaikumus salam, Major General Dawud! Yaya aiki?"
"Alhamdulillah. Yaya gida? Matar gida da yarana fa?"
"Gida lafiya lau! Ai dama na san na wajen naka za ka tambaya, Ni kuwa ko wani hali nake ciki oho, kowa da komai kalau Alhamdulillahi. Musanman yaran naka suna cikin koshin lafiya"
Major general dawud ya yi dariya mai sauti kafin yace,
"A'a, Tuba nake, Kai na duqe wajen neman afuwa,Ni dai burina su tashi da ladabi da tarbiyya...Kuma Alhamdulilla"
Chief judge Abdulfatah ya sake dariya, yana cewa,
"Tabbas, babu gardama. Amma dai kana bukatar a baka lambar yabo ta dattijon shekarar nan.To ya madam? Ya nawa yaran? ya wajen su gwaggo tah."
"Kai dai bari, Chief Judge! Ka san ance dattako aiki ne, ba laifi ba... Alhamdulillah kowa kalau'
Suka yi dariya, Baki daya. kafin daga bisani Chief Judge ya ce,
"Haba dai! Ai kai fa kana da ikon shiga ko'ina a kasar nan. Hatta fadar shugaban kasa, da an ce ka shigo, kowa yana tashi tsaye."
Major General Dawud ya yi murmushi yana girgiza kai.
"Kai dai ka san kwarewarka a surutu. To menene labari ne?"
Chief