da dan uwan sa. Wato marigayi Malam Idris da marigayi Malam nataa’ala.
“Iyaye nagari, Allah ya jikan ku da rahama.Baku yada qur’ani ba har rasuwar ku. Baku dena yada kalmar Allah ba har ku ka koma gare shi. Allah ya dubi tarin alkhairin da kukai Allah ya jikanku da rahamar sa ya gafarta muku. Allah yasa kuna aljannarsa madaukakiya Amin. Yan uwan juna da basu yada zumunci ba. Allah ya dubu zumuncin da kukai ya haskaka muku makwancin ku Amin.”
Ta matar cikin locker ta janyo wani tana dubawa,
Girgiza Kai tayi Cikeda tu’ajjabi mai tattare da dimbin alhini. Cikin rawar baki mai dauke da magana mai ban tausayi Ahankali tache,
“Allah ya jikan ku da rahama…. Allah ya gafarta muku, duniya zancen banza. Allahu Akbar Yaa Allah ya gafarta muku. Yasa aljanna makoma ce agare ku. Mu kuma Allah ya kyautata namu zuwan. Ya sa muna da rabon ganawa Amin.”
Ta mayar da hoton cikin locker tana sauke nannauyar ajiyar zuciya mai dauke da labarin ban tausayi.
Katin hotuna suka rage saura guda biyu a hannunta.ta daga kanta sama ta sauke tana mai runtse idanunta
Hawaye ne masu matukar turiri suka shiga zubar mata daga idanuwanta.
ta sanya hannuwanta da sauri ta toshe bakinta Saboda yadda kuka yaci karfinta sosai,ta fashe da wani irin kuka mai kara.
Hannunta na rawa ta daga hotan ta kai fuskarta. Idanuwanta suka sauka akan fuskokinsu su. Tana tsakiyar su. Gwaggo abule mahaifiyar ta na daga gefe. Sai kannenta mata biyu suma kowacce tana daga gefenta.
ta saka yatsa tana Shafa fuskokin su d’aya bayan d’aya a hotan.
“Gwaggon mu…rai yayi halinsa Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Mai rai ba’a bakin komai yake ba. Shikenan ba zaku dawo ba’ shikenan mun rabu bazan sake ganin ku ba? Wayyo Allah, Na rasa Baba na rasa ku kuma,na shiga uku Mutuwa tai mun yankan kauna. Mutuwa ta rabani da rayuwata. Domin kudin kune rayuwata. Ina cikin wani Hali gwaggo Ina cikin wani Hali wanda da kinanan sanar miki kadai zai ragemun radadin da nake ciki
“Gwaggo sun mun zobe, Sun zagaye ni gwaggo,Banida wani matemaki Sai Allah gwaggo. Ina tattare da makiya da suka sha gabana suka sha bayana Gwaggo. A tsakiya nake banida wani madogari Sai Allah gwaggo. Gwaggo sa’anjo da zan gayawa itama gwaggo sunyi nesa dani bansan inda zan ganta ba. Gwaggo ba nida Kowa. Gwaggo ba wanda yake kaunata acikin gidan nan. Alhaji da nake kalla a baya nayi farin ciki gwaggo shima ya juyamin baya. Wayyo Allah na! Da yan uwana suna nan suma da na sanar dasu. Amma kaico mutuwa ta rabamu. Allah ya jikan ku da rahama ya gafarta muku. Allah ya shayar da ku ruwan alkausara. Allah yasa aljanna makoma ce agareku gwaggo da dukkan musulmi baki d’aya . Allah ya hadamu a aljanna. Allah kuma ya kyautata namu zuwan....
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _33.._
Ta Mayar da hotan locker tana goge Hawayen dake diga a wuyanta hannunta ya rage saura kati d’aya na hoto. Wannan hotan hadashi akayi aka jona. Mahaifin şu marigayi Malam idris ne da mahaifiyar şu gwaggo abule Wato zainab,Hotan sune a kati d’aya da aka hada.
Ta lumshe idanuwanta ta bude tana futar da numfashi mai zafi. Gabanta Sai tsananta bugawa yake Tamkar wadda tayi gasar gudu.
ta saka hannu a hankali tana goge hotan ta Kara shi a fuskarta sosai…
“Na yi rashin iyaye nagari? Na yi rashin bango na, Nayi rashin fefe na nayi rashin masu sharemun hawaye na, nayi rashin farin ciki na,da sanin komai na na rayuwa. Kudin jigone a rayuwata. Da bazar ku na ke rawa. Allah ya jikan ku da rahama, Allah ya gafarta muku. Allah ya gafarta muku. Allah ya gafarta muku….”
Tayi shiru na yan wasu mintina tana duban hotan kawai, Ta sanya hannu ta janyo locker ta dakko hotan dazu wanda take itada su gwaggo da kannenta.
ta hada hotunan guda biyu a hannuwanta, ta rungume su tsam a kirjinta. Ta saka hannuwa ta dage yadda ta rungume kai Kache dan mutum ta rungume
“Shikenan bani da kowa, Banida komai? na rasa farin ciki na alokacin da nafi bukatar su,Allah shikadai yasan dalilin haka, Ya Allah ka gafarta wa wannan dangi Nawa, Ka suturtasu da rahamar ka, ka gafarta musu da gafarar ka, Allah dan ludufin ka da bu wayarka da isarka kai din mubawayi ne gagara misali Allah Allah Allah kasa aljannatul firdausi makoma ce agare su. Allah kasa mu nada rabon ganawa, Allah ka kyautata namu zuwan kasa mu cika da kyau da imani Allah ka sassauta mun,ka shiga cikin lamarina ka kawo mun mafuta Ka yafemun? Ka bani ikon cin wannan jarabawowi da nake ciki Allahumma Amin. KIRJI na tattare yake da dimbin damuwa ya Allah. Hankali na a tashe yake yaa Allah. Ina cikin mawuyacin hali da kai kadai kasan hakurin da nake. Yaa Allah ka dubemu ka Shiga lamarın. Don tsarkakakkun sunayen ka cassain da tara. Domin kai din sarki ne da babu wani Kamar sa. Allah ka iya mun dan babu mai iyawa sai kai.
Ga Baiwar ka zainabu Allah ka dubeta da idanun rahama ka iya mata Amin”
ta mayar da hotunan locker cikin bedside drawer ta rufe,ta koma ta gyara kwanciyar ta akan gado. ta sake lulawa duniyar tunanin shekarun baya da suka shude ..
*KAUYEN BOKEZUWA*
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _34_
*GIDAN MALAM NATA’ALA*
Anata hada hadar yinin Amare. an zazzauna yan yini da abincin kala kala agaban su. Alala, waina,Shinkafa, kunu,zobo da tuwo lamarin sai wanda ya gani kawai.
Amaren kowacce da nata kawayen a gefe. Rumanah ta hana kawayenta kula Zaytunah Kasancewar Duk kawayen nasu d’aya ne. Don haka Zaytunah ita nata tsirari ne su uku kadai ne basu ke waye sun koma wajen Rumanah ba. Su sa’anjo ne kawai kawayen Zaytunah na amana.
Sunyi kwalliya cikin lesika kayan da aka kawo musu na futar biki. Kowacce kalar nata daban. Sun sha mayafi sun rike jaka Kamar dai amaren gata yan shekarun baya.
Fuskar nan yab’e yabe da hoda da Jambaki da kwalli. TubarkAllah sunyi kyawunsu. Dai dai misali don har daga kauyuka da suke makota anzo Kallon su Zaytunah amare. Don sunyi kyau sosai,kayan irin na yan birni bikin ma na yan burni Gashi zasu auri yan gata kuma a birni zasu zauna…
Su rumanah Sai feleke ake Za’a tafi birni. Duk inda tayi kawayenta na Binta riii. Sai yauk’i take ita ga Amaryar uzairu…
Iyayen nasu mashaa Allah sun sha kayan fitar biki shar da su. Gwaggo abule tasaka shadda kalar hoda ammata aiki mekyau. Inna goge tayi shiga cikin Riga da zani na atamfa. Sai gwaggo haire datayi cikin cikin Sai da aka bata lesi na kayan lefen Zaytunah ana Rumanah kuma aka bata shadda. Don haka lesin ta dinka Sai hura hanci take itafa yayan yan uwanta ana aure zasu tafi birni. Har kauyen mijinta tanko inda tayi aure se da taje ta gayyato mutane Kan suzo suga yayan yan uwanta Rumanah da Zaytunah. Da aka aura musu yayan masu kudi yan Birni suma masu kudi mazajen. Gashi birni Za’a Kai su.
Mutane sukayi cincirundo da wanda aka gayyata da wanda baa gayyata ba Duk sukayi dafifi. Wasu tun asubar fari suna kofar gidan sun zazzauna. Matan kauyen kuwa agidan suka tare. Kowacce an zuba abinci a samiru ankai gidanta. Sune suke girki. Daman matan bokezuwa Akwai karamci da sanin yakamata,daga su har Mazan su ba na yar wa.
Habule ne ya shigo da gudu wandon sa a hannu da hular sa tashi ka fiya naci yasha sabon kayansa na daurin aure yadi kalar madara..
“Haire… kutusun ubancan kai. Haire an daura aure ba dai dai ba…."
Gwaggo haire dake hada Hadar biki tanata handama abinci . Ta jiyo kalar barin zancen da bakin habule yake ratattakawa.
Ta durkusa ta rarami takalmi ta nufeshi itama tana kuzuzuwa. Dama ai barewa baza tayi gudu danta yayi rarrafe ba
Don haka ta cakumi hannunsa cikeda takaicin ta dubi zariyar wandon sa ta gasa masa uwar harara. Kafin ta daga hannu ta duma masa dundu a gadon bayansa jikake.
"Dumm dummm" har sau biyu.
"Dan haka kaza ta uba baiwar ka ko? Don ubanka. Da Yaya na Saka zariyar nan. Amman saboda baka da kunya baka da mutunci kaje ka zareta? " Ta karasa fada tana sakar masa wani rankwashi a tsakiyar kansa daya Sha aski jikake 'kwass'
Habule ya rasa da Wanne ma zaiji? Dundun da ta zuba masa a tsakiyar gadon bayansa har biyu? Bayan sa tamkar zai Burma saboda azabar radadi. Ko kuwa uban rankwashin data sakar masa a kwanyar kansa ji yake kan kamar an zaizaye masa naman wajen.
"Wayyo Allah na wayyo"
"Tukunna ma kafin na maka dan banzan duka. Zo ka cire kayan Dan uban uban ka"
"Kai haire"
"Haba haire meye haka? Yaro yayi wankansa yaci kawalliya ana biki agidan su cike ya cire kayan daya Saka?" Wata mata dake jefa alala abaki tana korawa sa zobo ta fada
Gwaggo haire ta juya ta mata uwar harara. Ta shige daki da hannun habule. Matan dake tsakiyar dakin sai binta suke da kallon Karin bayani.
Ganin zaa cinye ta da magana sai da sukaje can kuryar daki tukun sannan tache,
"Akan wane dalilin zaka zare zariyar wandon ka?"
Habule ya fara tuttujewa zai gudu haire ta matse shi gam. Da zafi ya ishe shi da sauri yace
"Ana raba murtala ne nan awajen daurin aure garin kokawa ne nan aka zareta. "
"Dan kan uba. An daura ai tini ko"
"E Amman anyi musanya Yasin"
"Agidan uwar ka? Ka taba. Ganin inda akayi haka?"
"Haire Yasin an daura auren zaytunah da uzairu Amiru Kuma da Rumanah...
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _35....._
Gwaggo haire taja dogon tsaki,
'Mtcwwww Habule ni me yasa makaryarci ne Kai? Banda karya ta yaya za’ayi haka ka rasa karyar dazaka hado ka fada ma sai wannan?"
"Yasin haire da gaske nake, Yasin ba karya nake ba."
Gwaggo haire ta rarumo abu akan yamfadin da aka nannade. Bama mayafi bane bakuma dankwali ba.Bujen wandon habule ne. Amman saboda tsabar tashin hankali batasan ma shi ta dauka ba.
Sai kache mota... Tiiii tafita waje. Maza yan daurin auren nata daddawowa. Kowa fuskar sa a washe yaci dafau ya koshi..
Gwaggo haire ta Sha gaban wani saurayi. Da ya riko leda fara gare garai kana hango kaza aciki. Da shinkafa . Dayan hannun lemo ne a hannunsa ragowar na walimar daurin aure ce ya kullo zai tafi gidah.
"Yushau ne dan larai me fanke ko?"
"Eh ni ne gwaggo... An wuni lafiya?"
"Ba kalau ba"
"To gwaggo wani abunne ya faru?" Ya fada yana duban kanta data daure da gajeren wandon habule. Ta sake cewa,
"Tabbas wani abunne ya faru. "
"Subhan'Allah menene gwaggo? Naga kila baki masan da abunda kika fito ba" ya karasa fada yana nuna wandon data yafa a kafada
Ta dubi wandon tana girgiza Kai tache
"Banma sani ba. Ina cikin tashin hankali ne. Duk da dai hankalina bai gama tashi ba a haka. Yaro ne nake tunanin yayi shirme ya buga karya Karna masa duka. Amman naga dai sai nanatawa yake cikin tabbatarwa. "
"Toh gwaggo Allah yasa na San menene. Wani abun kikeso? Wani abun zaa miki? Ah inata magana ma ban miki Allah yasanya alkhairi ba. Daga wajen daurin auren nake ai.an daura har munyi walima. Wallahi an ci an Sha. Kinga ragowa ma zan kai gidah"
"Allah sarki to sannu da kokari. "
"Yauwa gwaggo. Ina sauraron ki. Meya faru? Me za'ai miki?"
"Ba abunda zaa mun yushau. So nake na tabbatar ne. Cikin ikon Allah Kuma ka halarci daurin auren "
"Eh daga can nake ga sheda?" Ya daga ledar abincinsa da lemo
"Nagani ai. Dan Allah da Wa da Wa aka daura auren nan?"
"Rumanah da zaytunah da mazajen su yan birni"
"A'a ba abunda nakeson sani ba kenan. Ina nufin zaytunah Wa aka aura mata. Rumanah ma Wa? Sunayen kowanne"
Yushau yayi shiru can ya daga Kai yana jujjiya shi cikin son tunowa. Gwaggo abule ta ja dogon tsaki
''mtcwww"
Tana wulla masa harara. Cikeda bacin Rai tache,
"Matsa dallacan . sakarai sullutu da fanke ya cika masa Kai..yanzu yanzu kaje daurin auren Amma kamanta da wadanne aka daura..sunayen su kawai. Fanke duk ya cika masa tunani kawai"
Yushau ya bude baki zaiyi magana. Gwaggo haire ta bangaje shi ta wuce tana mita,
"Ba abunda Kuka sani sai hadama. Kaje ka kwaso.abinci harda lemo saboda mayatar yunwa. "
Shi dai yushau yayi gaba yana waiwayonta cike da mamakin maganganunta Ko meye abun gaggasa masa magana haka? Tabari ma ya tuna ya sanar mata Amma tabige da bakaken magana . Ya tabe baki kawai ya hau sauri ya wuce gidah
Gwaggo abule ta sake tare wani matashin dake tafe yana daddakar lemo
Ta dubeshi tana kakaro murmushi,
"Ah lalle anci an koshi ana korawa da lemo”
"Wallahi kuwa gwaggo... Ina wuni?"
"Lafiya kalau zailani. Daga wajen daurin auren kake da alama ko?"
"Eh gwaggo ga lemo na nan Ina korawa. Munyi kokawa da kaji Yasin. Gaskia akwai abinci Allah ya sanya alkhairi"
"Toh Amin zailani. Dan Allah tambaya nake yaro ne yazo yake mana shirme. Wai da Wa aka daura auren nanne. Sunayen su nake nufi. Rumanah da zaytunah da Wa sunan mazajen kowacce? Allah sa baka manta ha. Yanzu na tambayi yushau Dan larai me fanke ya manta sullutun wofi”
Zailani ya kada Kai yana murmushi yace,
"Dake da wuri naje har cikin masallacin na samu wuri mutum biyu na fara samu agabana na sai waliyyai biyar sai Liman, na zaytunah aka fara daurawa .sannan rumanah"
"Yauwa Toh sunayen mazajen kowacce,"
"Eh zaytunah da uzairu. Rumanah da Amiru.... Masha Allahu sada...
Ai bai karasa magana ba, gwaggo Haire ta juya ta koma gida fuuuuuuu ta kumbura kamar zata fashe. Ta shiga dakin gwaggo abule. Dake zaune da mutanenta .....
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _36..._
Ganin yadda mutanen dakin gaba daya suka tsaya suna duban ta. Hakan yasanya ta kutsa ta shiga dakin...
Kai tsaye ta nufi wajen gwaggo abule. Ba'ai aune ba sai gani akayi ta cakumi wuyan rigarta tun tana zaune sai data mikar da ita tsaye...
Mutane sukayi kanta suna kokarin raba su. Gwaggo haire ta sake rarumar gwaggo abule tamau. Dakyar gwaggo abule take numfashi,
"Me tayi miki haka?"
"Meye haka baiwar Allah?"
"Jama’a kuzo kuyi rabiyar fada. Haire ta cakumi abule gasu nan abule na kakarin mutuwa."
Mutane suka shiga dakin. Har wajen dakin da tsakar gidan saitin dakin ana kallon su. Yayinda wasunsu suka shiga raba su.
"Ku rabu da mu.ku kyaleni nayi kasa kasa da ita na chasa ta. Kunsan metayi da zaku shiga tsakani. Ina ruwanku?"
"Haba baiwar Allah. Koma metayi miki sai ki hakura. Ki bari idan aka kammala aka share biki kowa ya watse sai ku yi abunda zakuyi. Amman ga shi biki kuke fa Rana ce ta farin ciki saboda Allah danme zaki kokarin mayar da ranar haka?"
"Ina ruwan ki? Ji Dan Allah wannan waya gayyato ta? Adama me daddawa Ni banason shisshigi Amman tunda so kike kisan meya faru Tabbas ranar yau ta rikide ta zama ta bakin ciki. Saboda me? Saboda munafurci da algugumanci . Da hassada da bakin ciki. Da tsantsar tsibbu don ko tsibbu ne. Tasanya aka musanya mijin rumanah aka aurawa diyarta zaytunah. Daman Shidin suke harinshi suke so saboda yanada kudi. Bayan rumanah yace yanaso. "
Yan gidah sai suka fara salati. Wasu sunata leken tsegumi.
Zaytunah dake wajen tanata turmutsutsu dakyar tasamu ta shiga dakin.
Saboda tsananin bakin ciki cakumar wuyan rigar mahaifiyar ta da gwaggon nasu haire tayi. Gwaggo abule dakyar take numfashi Gashi kwana biyu Daman ciwonta ya sakota agaba tanata fama. Kuma gwaggo tasan da haka Amman take kokarin kasheta Don kuwa kokarin kisa take. Saboda gwaggon dakyar take numfashi idanuwanta sun firfito... Dama gashi gwaggo haire basamudiyar lukutace akwai karfi. Bata taba shiga tsakanin su ba saboda gudun magana. Amman yau zaytunah gwaggo su haire ta kaita karshe. Takasa hakuri. Da har sai data sanya hannuwanta tana kokarin janye na gwaggo haire
"Dan Allah gwaggo haire meye haka?Cikata meye haka kike kokarin yi wai?"
"Kai ke ni zakiwa rashin kunya? Ko da yake kinsaba ai. Idanuwan ki sun bude mahaifiyar ki ta koya miki annamimanci ta. Ta bude miki idanuwa , kamar yadda tayiwa Nata'ala. Ta hanyar tsibbu ya aureta. Shine tayi akan ki kema kika aure uzairu ko? To wallahi bazata sabu ba. Sai dai akai wata bake ba "
"Narantse da kadaitar ubangiji da babu wani sai shi. Gwaggo bata taba fitarda kwandala tace ayiwa wani wani abun ba. To Ina take zuwa ma? Bayan kowa yasan halinta? Gwaggo haire Ina baki girman ki dan Allah ki cika mana gwaggo mu,Sarai kinsan ba lafiya ce da itaba kiketa makureta haka .batin auren Uzairu Kuma yadda baki sani ba wabillahi bamuda masaniya. Ina ruwana da uzairu? Meye darangami na dashi da zaa hadamu aure bayan ga Wanda yace yana kaunata.?"
"Ke ni kike gayawa waɗannan maganganu. Bara kigani" gwaggo haire ta buga tsalle. Ta kwakwaso rantsuwa ta dire tacire dankwali ta daura a kugu. Mata nata kokarin hanata ta zille. Ta rarimi zaytunah tabuga sama ta tikata da kasa cikake tim...
"Kara mata gwaggo haire. Makira ce algunguma.Zaytunah Allah ya Isa tsakani na dake. Ki sani ni da ke har abada"rumanah ta fada tana Kuka sosai
Gwaggo Abule ma hawayen take tana jujjiya Kai tana duban gwaggo haire. Da takasa cewa komai saboda tsananin mamakin abubuwan da suke faruwa kamar mafarki yanzunnan fa kowa yaketa hada Hadar sa na farin ciki yanzu kuma ya rikide ya zama na akasin haka....
Tama kasa tabuka komai... Tana ganin sanda gwaggo haire ta daga zaytunah sama ta jijjigata. Dai dai sanda malam Nata'ala ya shiga gidan da sauri don tuni an Kai masa tsegumi.
Ya hango haire ta daga zaytunah sama ta yi juyi da ita. Yana kokarin turmutsawa don shiga dakin. Mata sun zaizaye dakin don haka ya daga murya,
"Haire meye haka? Haire karki soma"
"Wannan shine na biyu ma dan tayi dazu ta bugata da kasa" cewar sa’anjo kawar zaytunah tanata hawaye.
Gwaggo haire ta buga zaytunah da kasa