KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   33 / 34

96K to 99K   out of 102K words

ta a wani masallacin matafiya dake kan hanya. Yayin da mazan kuma sun dan fita daga motocin, wasu na hutawa, wasu na duba tayoyin motocin..

Alhaji Amiru ya tsaya a gefen motarsa, yana dan tsaye, hannayensa a cikin aljihunsa. Idanunsa na kallon kasuwar da mutane ke yawo cikin sauri da hanzari...

Muhammad shi da driver din dayar motar suka shiga cikin kasuwar bisaga umarnin gwaggo zainabu suka sassayo kayayyakin da zasu kai wa gidan da zasu je. Wato gidan major general dawud mafia. Sunyi siyayya ta girma irin ta gidan arziki da Kamala. Komai Alhamdulillah anyi barnar farare bugun Abuja... Suka kammala komai suka dora daga inda suka tsaya daga tafiyar da suke...

A hankali motar da ke dauke da su Alhaji Uzairu, Alhaji Amiru, Gwaggo Zainabu, da Muhammad ta cigaba da sharara hanyan Birnin Noka. Kowa na cikin natsuwa, amma zuciyoyinsu cike da tunani daban-daban.

Tafiyar ba kawai don ziyara ba ce, akwai manyan dalilai da suka tilasta wannan haduwar. Sun yanke shawarar ganawa da Major General Dawud don rokon sa ya kara kaimi wajen binciken halin da Zaytunah take ciki. Sun dade suna neman labarinta, amma har yanzu babu wata sahihiyar matsaya da suka cimma.

Dake tafiya ce mai dogon zango, kowannen su da tunanin da zuciyar sa take yi.

Alhaji Uzairu ya dafe gemunsa, yana kallon hanyan da ke gabansu. Kamar yadda motar ke tsallaka lunguna da sako, zuciyarsa ma cike take da rudani.

"Meye dalilin da ya sa Zaytunah ba ta dawo gida ba?"

Tun daga lokacin da ta bar gidansa, ba ta taba neman komawa ba. A matsayinsa na mutum mai iko da martaba, yana jin cewa hakan wani irin raini ne. Duk irin binciken da suka yi, sun kasa gano inda take.

"Idan har tana raye, to dole ne mu san dalilin da ya sa take boyewa."

Yana jin zafi. A ganinsa, ko menene dalilinta, bai kamata ta tafi tsawon zango haka ba da ya’yansu..

"Wane irin abu ne zai hana mace dawowa gidanta, in banda asiri ko wasu abubuwa na makirci?"

Wannan tunani yana matukar cin zuciyarsa. Ya nisa cikin zuciyar sa dik yake waɗannan maganganun ya cigaba da cewa,

"Yaa Rabbi. Na fawwala lamurana gaba daya a gare ka. Rabbi ka dubeni ka kawo mun dauki. Idan har zaytunah tana raye da yaranmu zainab da Muhammad Rabbi ka bayyana mana su kasa suna cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali. Idan kuma basa raye Rabbi ka karbi rayukan su cikin aminci kasa aljanna ce makoma agare su. Yaa Allah ka kawo mana gaskiyar wannan al'amari. " Ya cigaba da adduoin sa da zancen da yake da zuciyar sa cike da damuwa...

Alhaji Amiru kuwa a nasa bangaren, Ya jingina kansa da kujerar motar, yana sauraron numfashin da ke fita daga cikinsa a hankali.

Shi ba shi da wata matsala da Zaytunah. Ya dauke ta a matsayin matar dan uwansa, kuma uwa ga ‘ya’yan kanin sa. Duk da haka, yana jin wani nauyin da ba zai iya kawar da shi ba.

"Shin da gaske an san inda suke? Kuma suna a raye? Sannan Nabeeha da Muhammad ke neman aure yar zaytunah ce ma'ana yar Amiru ce kanin sa? Shin wannan lamari da gaske yake major general yanada masaniya akan sa? Zaytunah da iyalanta suna wajen sa? Gaskiya ne ko makirci ne? Ko kuwa akwai wani sirri da ake boyewa?"

Zuciyarsa na yawan yawo da tunani. Idan har Major General Dawud ya san wani abu game da Zaytunah, zai so a san gaskiya. Ba zai boye ba... ya numfasa kawai yana furzar da iskar bakin sa...

A gefe guda kuwa, Gwaggo Zainabu tana cikin farin ciki mai tarin yawa. Da farko, batun Zaytunah ne ya fi dauke mata hankali, amma tun daga lokacin da Muhammad ya gaya mata yana son auren Nabeeha, zuciyarta ta fara kallon tafiyar da wani hangen daban...

"Yakamata in ga wannan yarinyar da zuciyata ke matukar son ganawa da ita...!"

Tunda Muhammad ya gaya mata, ta kasa daina tunani akanta. Ta yanke shawarar idan sun isa Birnin Noka, ba za ta koma gida ba sai ta ga yarinyar da jikanta ke burin aura.

Muhammad yana zaune a bayan mota, zuciyarsa tana ta kissima masa hotan fuskar Nabeeha sahibar sa.. Ya lumshe idanu ya bude yana sakin tattausan murmushi. Hadi da zillon son ganin sahibar tasa. Zuciyar sa na rarratako masa zantukan kaunar da bakin sa zai Isar mata idan suka hadu...

"Nabeeha.... My only love! Ina kaunar ki fiye da yadda baki na zai furta mi ki. ..."

🎀🎀🎀

A cikin motar da ke tuki cikin hanzari, Hajiya Zaytunah da Nabeeha da Hammad suna cikin shiru, dukansu suna dauke da wani nauyi na damuwa a zuciya. Zaytunah tana cikin tunanin lafiyar Gwaggo Hafsatu, wanda ta ke jin wani nauyi game da rashin lafiyarta. Duk da haka, zuciyarta tana cike da wani abu mai ƙarfi, kamar wani abu mai faruwa, wanda ba za ta iya fahimta ba. Nabeeha da Hammad suma sunyi shiru acikin motar, suna kallon hanyar gaba cikin natsuwa, ba tare da sanin abin da zai faru ba.

Hajia Zaytunah ta yi ƙoƙarin sake duba wayarta, tana mai sake karanta sakon da Hajia Hauwa Maijiddah ta turo, Na rashin lafiyar Gwaggo Hafsatu a asibiti...

Suna kan hanya mai nisa daga gida zuwa asibitin. Don akwai tazara sosai, yayin da motar ta cigaba da tafiya cikin sauri. Hammad yana tuka motar cikin hankali, yana kallon hanya cikin natsuwa. Sai dai, Hajiya Zaytunah ta lura da motsin wata mota daga baya. A cikin gaggawa, wata mota baka wuluk mai dallare da fitiloli.. ta bayyana a cikin duhun hanya, tana tafe cikin sauri. Mota mai ɗauke da wasu mutane fuskar su a rufe..hajiya Zaytunah ta karkata idonta cikin hankali, zuciyarta ta fara bugawa cikin tsoro, amma bata san ko me zai faru ba. Wannan ya zama alamar wani abu mai haɗari yana zuwa.

Motar ta tsaya a gaban motar su cikin sauri. Hajiya Zaytunah da Nabeeha da Hammad sun yi ƙoƙarin daukar matakin tsare kansu, amma sai dai lokacin ya ƙure. Daga cikin motar , wasu daga cikin 'yan fashin sun fito cikin gaggawa, suna dauke da makamai masu haɗari. Hajiya Zaytunah ta lura da yadda suka rufe fuskarsu da manyan hular fata da ke hana su bayyana ko wanne daga cikin su. Wannan ya ƙara tsoratar da su, saboda suna tabbatar da cewa ba za su iya ganin fuskokin su waye ba...

Suna cikin gaggawa, Hajiya Zaytunah ta dakko purse ɗinta cikin sauri, tana mika musu cikin wani hali na roƙo. Tana neman su yi hakuri, ta bayyana musu cewa su kyale su, su bar su su tafi da lafiya. Ta roƙe su da su bar su, domin ba su da wani abu, kuma tana fatan su sauƙaƙe musu cikin wannan mummunan yanayi. Tana jaddada musu cewar mahaifiyar ta ce ba lafiya sike kan hanya don zuwa asibiti duba ta...

Amma, 'yan fashin sun daka musu tsawa cikin ƙarfin ƙarfi, suna tura su cikin motar zinariya cikin gaggawa. Suna ƙara riƙe su da ƙarfi, suna buɗe ƙofofin motar da sauri. Hajiya Zaytunah ta yi ƙoƙarin jurewa, tana ƙoƙarin tabbatar da cewa Nabeeha da Hammad suna cikin lafiya, Nabeeha ta rike wayar ta gam. Tana fatan kar barayin su karbe wayar...

Hajiya zaytunah tana jin zuciyarta tana bugawa da sauri, Tsoro da fargaaba sun dabaibaye ta. Fatanta Allah yasa kar su musu komai. Ga budurwar yarta Nabeeha da suke tare. Allah yasa kar su taba wani abu na daga martabarta..tana cikin wani irin kunci. Koda yake tana ƙoƙarin jurewa da fatan Allah zai ba su sauƙi, ba ta san ko me zai biyo baya. Tana jin tsoron cewa wannan abu ba zai ƙare da kyau ba. Nabeeha da Hammad sunyi shiru, suna jin ƙuncin zuciya, Bayan babbar motar aka zuba su. Suka ja suka tafi dasu..

Dai dai lokacin da wayar Nabeeha data boye a hannunta ta rike gam. Tayi haske. Messages ne suka fara shigowa tayi azamar matse wayar gam. Gabanta na tsananta bugawa. So take ta bude ta karanta. ..

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_PAGE: 83_*

*_BOOK ONE:_*

_EPISODE FINALE/SHAFI NA KARSHE_


_BOOK ONE: COMPLETED/LITTAFI NA DAYA YA KARE✔️_



🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️



Duk da motar na tafiya cikin nutsuwa, zuciyar Fawaaz tana gudu fiye da kowanne lokaci. Numfashinsa ya dan rikice, tamkar wanda ke shirin daukar babban mataki a rayuwarsa. Ya jingina kansa da kujerar motar, idanuwansa na kallo amma hankalinsa na wani duniyar daban. duniyar da ita kadai ce a ciki... Wato bargon jikin sa. Jinin da ke gauraye ilahirin jijiyoyin sa wato, Nabeeha.

Gaba daya tunaninta ya cika zuciyarsa, yana yawo cikin kwakwalwarsa tamkar fim da ke tafiya a hankali. Kallon idanunta masu zurfi, murmushinta mai sanyi, muryarta da ke ratsa zuciyarsa tamkar ana busa sarewa ta soyayya. Yau ya gaji da boyewa, ya gaji da jan kansa baya.

Direba na tukin cikin nutsuwa, amma a cikin Fawaaz, zuciyarsa na tafarfasa. Hannunsa ya zura a aljihunsa, yana lalubar wayarsa kamar wanda aka tilasta wa. Ya jima yana tunanin hakan, amma yau ba zai iya danne zuciyarsa ba.

A hankali ya dakko wata wayar da babu wanda ya san da ita sai shi kadai. Yar karama da ke da wata number ta daban, Bai taba jin bukatar amfani da ita ba sai yau. A hankali ya bude sakon wajen rubutu, ya fara daddana,

"Nabeeha..."

Ya tsaya. Ya runtse ido, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi fiye da yadda ya saba. Yana jin yatsunsa na dan rawa, amma hakan bai hana shi cigaba da rubutawa ba.

"Kwanan nan... Ba zan iya danne zuciyata ba. Na gaji da kau da kai. Dole ne ki sani."

Ya numfasa. Zuciyarsa na bugawa da karfi, yana jin yadda hannunsa ke dan karkarwa. Wani yunkuri ya sake yi, ya sake duba sakon da ya rubuta. Da alama har yanzu ba zai iya fadar komai a fili ba.

Sai kawai ya rage sakon zuwa kalma daya,

"Ina bukatar ganin ki."

Ya danna send ba tare da ya sake tunani ba. Zuciyarsa na bugawa, yana jiran abin da zai faru... Ya kamo salati ya sauke yana rokon Allah ya shiga cikin lamuran sa ..

Tunanin sa ya gama yanke masa daya tura masa sakon zuciyar sa gaba daya. Ya sake sauke gwarun numfashi kafin ya shiga rubuta mata dogon sako ya tura mata,

"Assalamu Alaikum Nabeeha, A cikin zuciyata na dauke da wani abu wanda na kasa boyewa ko kuma riƙewa. Wannan ba abu ne mai sauki ba, amma yau na yanke shawarar bayyana miki gaskiyar zuciyata. A lokacin da na fara jin wannan abu, ban san yadda zan yi da shi ba, amma yanzu, babu yadda zan iya ci gaba da boyewa. Wannan sirrin yana dauke da kaunar ki. KIRJI na cike yake da kaunar ki, wani nauyi ne mai girma, wanda ba zan iya ci gaba da riƙewa a cikin zuciyata ba. Koda yake na yi ƙoƙari na boye wannan, duk lokacin da zuciyata ta kira sunanki ko na ga murmushinki, tana motsawa, tana jin wani farin ciki da ba zan iya bayyanawa ba. Ke ce hasken da ke cikin zuciyata, wanda ke cike da annuri da farin ciki. saboda ban san yadda za ki ji ba ko yadda za ki dauki wannan sako, amma daga cikin zuciyata, na san cewa wannan SIRRI ba zan iya boye shi ba. Zuciyata tana jin wani abu mai zurfi, mai ƙarfi, wanda har yanzu yana ƙara girma cikin zuciyata. Wani sirri ne wanda ya dade yana burgewa a cikin kirjin nawa kamar wata garkuwa, yana cike da soyayya da ƙaunar da ba zan iya bayyana ba. Acikin zuciyata, akwai wani sirri wanda bai taɓa bayyana ba, amma yana cikin zuciyata, Ke ce a koyaushe cikin tunanin zuciyata, kamar yadda akwai SIRRI mai tsawo a cikin AKWATIn zuciya na, wanda yake cike da dumi da kauna.

"Duk lokacin da zuciyata take kiran sunanki, tana jin wani motsi, wani ƙarfin da ba ta taɓa jin irinsa ba. Soyayyar ki ta zama wani ɓangare na zuciyata, tana motsawa a cikin ranta, tana dauke da kowane tunani da ra'ayi na yau da kullum. Ke ce, Nabeeha, wacce zuciyata ta dauka a matsayin wani abun ƙauna wanda ba zai taɓa ƙarewa ba. Soyayya ta gare ki ta zama abin da ba zan iya shafa ko sauya wa. Nabeeha, If you would love me...I will leave the way you want.. Zan sauya kaina zuwa yadda kike so..Banason ki da wannan saurayin na ki, He wants what's my mine.. you're mine and mine only...Nabeeha..

"It’s so difficult to put into words, Nabeeha, but my heart has been carrying this secret for so long, and I can’t keep it inside anymore. The truth is, I’ve always loved you, and this love has only grown with time. I never imagined how deep this feeling would go, but here I am, heart full of you, full of love, and full of everything I never knew I could feel🥹

"Acikin zuciyata is where this love resides. This secret has stayed within me for so long, like a treasure that I now know must be shared. It’s not just about love, it’s about who I am when I think of you, it’s about what my soul feels when I’m near you, or even just thinking about you. It’s a bond I never want to break.

"Ba na roƙonki da wani abu, Nabeeha, kawai ina so ki sani cewa wannan SIRRIN yana cikin zuciyata, kuma na dade ina jin shi. Ko da ba za ki amince ba, ko da ba za ki yarda da ni ba, wannan kaunar ba ta da iyaka. Ni ba na tsammanin soyayya tana buƙatar wani lamari na musamman, bari zuciya ta faɗa maki abin da ta ji. Zuciyata tana kaunar ki, kuma wannan soyayya ba za ta taɓa ƙarewa ba. wannan sako, sakon zuciyata ne, love confession ne from my heart.. Nabeeha. Wannan ba kawai sanarwa ba ce, amma wataƙila mafi kyawun abu da na taɓa aikatawa ne sanar da ke cewa zuciyata tana dauke da soyayya da nake jin daga gare ki.kauna ce ba surke.. I love you, Nabeeha, deeply, truly, forever..."

Bayan mintuna kadan da tura sakon farko, Fawaaz ya sake duba wayarsa. Babu amsa daga gareta, amma hakan bai sa ya ji damuwa ba. Sai ma wani yanayi mai dadi da ya rufe shi, yana jin zuciyarsa na bukatar ya sake tura mata wani sako wanda zai bayyana yadda zuciyarsa ke tafarfasa a kanta.

Ya dan lumshe ido, yana jin numfashinsa na fita a hankali. Sai ya fara daddana,

"Nabeeha...Ban san yadda zan fara bayyana hakan ba, amma abinda nake ji game da ke ya fi kowanne abu da na taba ji a rayuwata. You are the unspoken poetry in my heart, the melody that soothes my soul, the warmth I never knew I needed😍Kullum ina kokarin kau da kai, amma zuciyata ta kasa. You live in my thoughts, in my dreams, in the quiet moments when the world fades away. I see you in every beautiful thing, in every sunrise and every gentle breeze. I don't know if you feel the same, but one thing I know for sure...you are special to me in a way words can never truly capture. Sleep well, Nabeeha...... Fawaaz."

Ya danna send ba tare da ya sake tunani ba. Wannan karon, wani irin nutsuwa ta daban ya lullube shi. Ya jingina bayansa da kujerar motar, yana jin zuciyarsa na bugawa a hankali. Wannan shine karon farko da ya taba budewa wani haka. Kuma ba kowa ba... ita ce kadai wadda ta cancanci hakan.

Fawaaz ya jingina kansa da kujerar motar, numfashinsa ya sauka a hankali. Wani irin farin ciki ya lulluɓe shi, zuciyarsa ta samu nutsuwa fiye da yadda ya zata. Yanzu ya fitar da abinda ke ransa, babu wani tunani da ke cin zuciyarsa.

Ya lumshe idanu, wani murmushi mara kaifi ya kwanta a saman fuskarsa. Bai san dalili ba, amma yana jin tamkar an sauke masa wani babban kaya daga zuciyarsa. Yana jin tamkar iska mai sanyin dadi na shigarsa, tana ratsawa cikin zuciyarsa.

Babu tabbas ko zata amsa sakon, ko zata fahimta, ko ma zata yi shiru. Amma hakan bai dame shi ba. Abu mafi muhimmanci shine ya fitar da abin da zuciyarsa ke raya masa. Ko da kuwa bata ce komai ba, ya riga da ya yi abinda bai taɓa yi ba a rayuwarsa.

Ya bude idonsa, yana kallon hanyan da ta rage kafin su isa gida. Bai damu da lokacin da zai ga sakonta ba. Yanzu dai, yasan daya daga cikin manyan SIRRIN SA ya shiga hannunta... kuma zuciyarsa ta samu kwanciyar HANKALI fiye da kowane lokaci.

🎀🎀🎀

A cikin wannan mummunan yanayi na fushin wadanda suka sace su, Hajiya Zaytunah tana kokarin zama a natsuwa duk da tsoro da tashin hankali da suke cikin motar. Ta fahimci cewa ba za ta iya guje wa wannan halin ba, don haka ta yanke shawarar rokon su da ƙoƙari. A hankali, ta juya ga 'yan fashin da suke kusa da ita, zuciyarta na bugawa cikin hanzari.

Hajiya Zaytunah ta ɗago kai, tana kallon ɗaya daga cikin ‘yan fashin, wanda ke rufe fuskarsa da hula mai

33 / 34