barin falon ba tare da ya kalli kowa ba.
Hashim ya bishi da kallo, yana jin mamaki. Don yana daga gefe yana lura da komai...
“Lallai akwai matsala,” ya fada a hankali.
Raudah ta tabe baki.
"Ba sai an fada ba. Yaya Fawaaz yana cikin damuwa.”
Humayrah ta sunkuyar da kanta kasa,
"Ai kowa ya gane... Bawan Allah ko daga wajen aiki ne?"
Major General Dawud, wanda ya dade yana lura da shi, ya dan sauke ajiyar zuciya. Bai ce uffan ba, amma ya san cewa da alama yana da abu a ransa.
Gwaggo Hafsatu kuwa ta yi dariya a hankali, tana kallon inda ya fice.
"Wannan yaron yana boye wani abu,” ta fada tana murmushi. “Amma zan jira, lokaci zai yi da zai fadi.”
××××
Bayan ya fice daga falon, Fawaaz ya nufi babban lambun gidan, inda iska ke kadawa da sanyi. Ya dafe goshinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi.
Bai san yaushe ya shiga irin wannan halin ba. Shi mutum ne mai matukar kwarjini, mai kamun kai, mai jan aji. Babu wanda ke iya cewa ya taba ganinsa cikin damuwa. Amma yau, sai gashi yana jin wani irin yanayi da bai taba fuskanta ba.
Ya jingina da wata bishiya, yana kallon sararin sama. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Me zai yi? Shin zai iya hana auren Nabeeha da Muhammsd? Shin zai iya cewa yana sonta? Idan ma ya fada, me zai canza?Ya runtse ido, yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa.
"Ko da na fada,” ya furta a hankali, “babu wanda zai saurare ni.”
Idanunsa sun kada, zuciyarsa ta gama hargitsewa. Amma abu daya ya tabbata, Bai shirya rasa Nabeeha ba. Fawaaz ya sake lumshe ido. Iskar da ke kadawa a lambun gidan ta bugi fuskarsa, amma ba ta iya sanyaya zuciyarsa ba. Gabansa na faduwa, tunaninsa a rikice, amma babu wanda ya fahimta sai shi kadai.
Ko da yana zaune a cikin falon tare da su Major General Dawud da Gwaggo Hafsatu da sauran iyalansu dazu, ya ji maganar aurar da Nabeeha kamar saukar aradu a kansa. Bai taba tsammanin cewa rana guda za a zauna a yanke hukunci a kan rayuwarta ba, ba tare da shi ya san komai ba.
Me zai ce? Ta yaya zai fada? Idan ya fada, ya san iyayensa ba za su fahimce shi ba. Saboda shi mutum ne mai taurin kai, wanda ba ya bayyana abin da ke zuciyarsa.
Ya sake sauke ajiyar zuciya.
"Nabeeha…”
Ya furta sunanta a hankali, yana jin wani nauyi a zuciyarsa. Tunaninsa ya koma lokacin da ya fara lura da ita. A lokacin tana da shekara goma sha biyar, tana da yarinta a idanunsa. Amma a hankali, sai ya fara ganin wani abu daban. Yadda take ladabi, yadda take biyayya, yadda take da nutsuwa, da hakuri.
Sai dai tun daga lokacin, bai taba nuna mata hakan ba. Bai taba barin ta fahimta cewa yana son ta fiye da yadda zai iya furtawa ba.
"Yanzu kuma za a dauke ta, ba tare da na ce komai ba?"
🎀🎀🎀
A cikin falon kuwa, bayan ficewar Fawaaz, zaman ya ci gaba. Kowa yana cikin nishadi, sai dai Gwaggo Hafsatu na kallon yadda Fawaaz ya bar wajen da hanzari, kamar wanda ke tserewa daga wani abu.
Nabeeha, wadda ke kusa da mahaifiyarta, ta dan sunkuyar da kai. Ba wai tana jin kunya ba, amma zuciyarta cike take da tunani barkatai data gaza amsar su...
A lokacin da za a rufe zaman, sai Gwaggo Hafsatu ta juya tana kallon Hajia Maijidda Hauwa.
"Ke kuma sai kin duba yaron nan naki. Yanzu haka na lura yana cikin damuwa.”
Hajia Maijidda tayi shiru tana duban Raudah da Humayrah, sai suka girgiza kai.
"Eh mana, ai duk muna ganin shi ya chanza,” Humayrah ta fada da fuskar damuwa.
Gwaggo Hafsatu ta dan yi murmushi, tana jin kamar ta gano dalilin.
"Idan da wata matsala, lokaci zai yi da zai fadi.”
"Hakane Kam gwaggo, Allah ya kawo masa sauki . Yanzu haka daga wajen aiki ne. Ko wani abun na daban ko bashi da lafiya me? Halin nasa ne sai shi. Inshaa Allah zan tuntube shi gwaggo..." Cewar hajia maijiddah hawwa..
Bayan ‘yan mintuna da kowa ya watse, Nabeeha ta fita zuwa lambun gidan don samun iskar sanyi. Sai ta ci karo da Fawaaz da ke jingine jikin wata bishiya, kamar wanda ke cikin duniyarsa.
Sai ta tsaya, tana kallonsa.zuciyarta ta dan buga. Bai taba yin irin wannan yanayin ba.
"Yaya Fawaaz…”ta kira sunansa a hankali.
Ya dago a hankali, idanunsa suka sauka a kanta. Sai dai da suka hada ido, nan take ya kauda kansa, kamar wanda ba ya son kallonta.
"Yaya lafiya kuwa?”
Zuciyarsa ta sake bugu. Ya yi kokarin hadiye wani nauyin numfashi. Bai san me zai ce mata ba. Idan har akwai lokaci da yake so ya gaya mata wani abu, to yanzu ne. Amma sai ya kasa.
Sai kawai ya juya, ya bar wajen ba tare da ya ce uffan ba.Nabeeha ta bi bayansa da kallo, zuciyarta na raya mata cewa akwai abu a zuciyarsa. Amma menene?ba ta sani ba. Amma tabbas akwai abu.Nabeeha ta tsaya cak, tana kallon bayansa yana tafiya. Daga yadda kafafunsa ke daukar matakai cikin gaggawa, da yadda hannayensa ke matse a gefensa, ta fahimci cewa yana cikin matsananciyar damuwa.
"Me ke damun Yaya Fawaaz?"
Tun da ta girma a gidan nan, ta san cewa mutum ne mai jan aji, mai yin nesa da kowa. Amma hakan bai taba hana shi kasancewa mai kwarjini da kamun kai ba. Yanzu kuwa, sai take ganin wani iri a tare da shi.
"Ko dai…”
Ta girgiza kai. Ba ta son tunanin wani abu maras tushe. Ta riga ta amince da zabin da aka yi mata. Idan akwai abu daya da take da tabbaci a kai, to shine cewa su Major General Dawud ba za su taba zabar mata abin da ba alheri ba.
Fawaaz ya nufi dakin sa da sauri. Bai tsaya ko ina ba, kai tsaye ya shiga ya rufe kofa.
Ya jingina da kofar, yana kokarin hadiye wani nauyin zuciya. Numfashinsa yana fita sama-sama, zuciyarsa na tafarfasa.
Wannan shi ne karon farko da yake jin yanke kauna sosai. A ganinsa, ya dade yana da iko da zuciyarsa. Bai taba tunanin cewa zai kasance cikin irin wannan yanayi ba.
Kullum yana ganin Nabeeha, yana jin sonta na karuwa. Amma saboda miskilancinsa da jan ajinsa, bai taba bari ta fahimta ba.
“Ko da na fada mata yanzu, me zai canza?”
Ya dafa goshinsa da hannunsa. Wani kunci ya tokare masa makoshi.
"Me yasa ban fada ba tun da wuri?”
Bai san lokacin da ya zauna a bakin gadonsa ba. Ya dafe kansa da hannuwansa duka, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da karfi.
"Ba zan iya rasa ki ba, Nabeeha.”
Sai dai magana a zuciya ba ta da amfani idan ba a furta a zahiri ba.....
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
...
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE:78_*
A cikin babban falon gidan Major General Dawud, Kamar yadda gwaggo hafsatu ta umarta. Falon ya kasance cike da sarauta, an shimfida manyan darduma masu launin ruwan madara, an jera kujeru masu matukar tsari, sannan an kunna kyawawan fitilu da suka ba dakin haske mai daukar hankali. Ga kamshin turarukan wuta na kamfanin YERWA INCENSE AND MORE sai busawa suke. Suna sake sanyawa dukkanin wadanda ke wajen wata ni'ima da farin ciki....
Duk wanda ke cikin falon yana a zaune yana sauraran Gwaggo Hafsatu, wadda ke zaune bisa babbar kujera mai matukar kyan gani. Fuskar ta cike da nutsuwa da kamala, idanuwanta na dauke da alamun hikima da natsuwa irin ta dattijan da suka san darajar duniya da lahira.
A gefe guda, Hajiya Zaytunah tana zaune cikin ladabi da jin nauyin irin wannan taron. Kasancewar su gata da kuma bango majinginar ta..Gefenta kuma akwai 'ya'yanta, Nabeeha da Hammad, wadanda suke zaune daidai, suna kallon Gwaggo Hafsatu cike da mamaki da kuma fargaba kan me take shirin fada. Hajiya Hawwa Maijidda, matar Major General Dawud, tana zaune a gefe tana kallon abubuwan da ke faruwa da fuskar da ke nuna rashin jin dadinta.
Duk da ba ta fada da baki ba, akwai wani abu da yake nuna cewa tana da damuwa da wannan taro. Dama ranta babu dadu. Har yanzu dangin mijin zaytunah wayar su bata shiga. Tundai da matar ta kirata da wani la na daban tace tabasu lokaci sunanan tafe. A gefe guda kuma akwai wasu manyan mutane da suka hada da manyan lauyoyi wadanda suke akan kadarorin gwaggo Hafsatu.
Maaikatan gidan suka kammala shirya dukkanin kayayyakin abinci dana Sha a makaken farfajiyar parlorn dake dauke da babbar ledar da ake ajiye kayan abinci akai... Sannan aka bude wannan taro ko ince zama da addua.
Bayan an gama shiryawa, Gwaggo Hafsatu ta dago tana kallon kowa da kowa, sannan ta daga hannunta sama tana karawa da tata,
"Ya Allah, Ka albarkaci wannan haduwa, Ka sanya adalci da rabo nagari ga kowa. Ka ba mu ikon yin abin da zai amfani rayuwarmu a duniya da lahira. Ka albarkaci zuri’armu, Ka yaye mana damuwa, Ka sa mu mutu da kyakkyawan karshe, amin."
Bayan an amsa da amin, Gwaggo Hafsatu ta bada umarnin aci abinci tukunna. Bayan an gama harkar ci da sha. Kowa yayi hani'an. Sai Gwaggo Hafsatu ta sauke numfashi, sannan ta yi gyaran murya.
"Na tara ku a yau ba don komai ba, sai don in fadi wani muhimmin batu da yake a cikin zuciyata tun tsawon shekaru. Domin ita zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri. A matsayina na dattijuwa, na ga rayuwa, na san darajarta, kuma na fahimci cewa lokaci yana tafiya ba tare da jira ba. Akwai abubuwa da ya dace mutum ya yi kafin lokaci ya kure. A yau, ina son in yi magana akan wasu na daga cikin kadarorin da na mallaka da kuma yadda zan raba su ga wadanda suka cancanta."
Ta kalli Hajiya Zaytunah, Nabeeha da Hammad, sannan ta ci gaba da cewa,
"Akwai abubuwa da dama da suka faru a baya, akwai gwagwarmaya da wahalhalu da ba kowa ya san su ba. Akwai irin hakurin da wasu suka yi, da irin gudunmawar da wasu suka bayar a rayuwata. Kuma akwai wadanda suka cancanta su samu gata saboda irin rayuwar da suka sha. A yau, ina so in raba wasu daga cikin manyan kadarorina ga Hajiya Zaytunah, Nabeeha da Hammad, domin su samu ci gaba a rayuwa, kuma domin su san cewa su ma suna da wani gata a wannan duniya."
Major general ya kada kansa cikin Jin dadin maganganun mahaifiyar sa da goya mata baya hadi da sakin murmushin sa mai kayatarwa yace,
"Wannan batu naki yayi gwaggo. Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa. Allah ya iya miki yayi riko da hannuwanki Amin. Ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka amin."
"Aameen" yan parlorn suka amsa gaba daya.
Banda hajia hauwa Maijidda da lamarin ya doketa sosai. Maganganun gwaggo sun matukar bata mamaki. Wasu daga cikin manyan kadarorin ta zata dauka ta baiwa zaytunah da iyalanta ita kadai? Nata jikokin na tilon dan ta fa su sun tashi kenan a tutar babu?
"Na yanke shawara cewa Hajiya Zaytunah za ta mallaki filaye biyu da na mallaka a cikin birnin Garin Zulfawa. Wadanda ke kan titin Tudun Kashiya da Bakin Maza. Wadannan filaye suna da muhimmanci kuma ina so su taimaka mata a rayuwarta. Na kuma ba ta wani gida mai girma a unguwar Tsamiya wanda yake da dakuna hudu, har da lambuna da wuraren shakatawa. Wannan gida zai zama tushenta."
"Ke kuma Nabeeha, zan baki wani kamfani mai suna Zaidau Agro-Allied Ltd., wanda yake a cikin garin Gidan Madawaki. Wannan kamfani yana harkar sarrafa kayan amfanin gona, kuma ina so ki cigaba da tafiyar da shi tare da kara bunkasa shi. Haka kuma zan baki wasu shaguna guda biyu da ke cikin kasuwar Tashar Maigobe, wanda suke bayar da babban riba. Wadannan shaguna na tabbatar za su taimake ki a nan gaba."
"Kai kuma Hammad, zan baka wani fili dake kusa da sabon titin Rafin Gwaska, kusa da gadar Takalmi Gora. Wannan fili zai zama naka, kuma ina fatan za ka yi amfani da shi don ci gaban rayuwarka. Bayan haka, Na baka daya daga cikin gidajen mai na, Mai suna Zaidau Oil & Gas Ltd., wanda yake a cikin garin Kwanar Buzu. Wannan gidan mai yana daya daga cikin manyan kadarorina, kuma ina fata za ka tafiyar da shi da hikima."
Daga nan sai falon ya dauki shiru! Mamaki ya cika kowannen su. Idan aka tsame major general dawud. Da shi dama tuni yasan komai. Kuma ya amince da shawarar da gwaggon tayi masa. Sauran kuwa kowa ya yi shiru yana kallon Gwaggo Hafsatu cike da mamaki. Hajiya Hawwa Maijidda ta girgiza kai, tana jin wani abu yana taso mata daga zuciyarta. Ita dai daman batasan adadin yadda Gwaggo Hafsatu ke da yawan kadarori ba, balle har ta raba su haka nan. Tasan tanada tarin arziki kam. Ashe har yawan su ya kai haka? Bugu da kari kuma ta kyautar da wasu daga ciki kadai gasu zaytunah?
Nabeeha da Hammad kuwa sun kasa magana. Idanunsu sun cika da hawaye, ba wai don farin ciki ba, sai don mamaki da kuma girmama wannan gata da Gwaggo Hafsatu ta musu... Hajia zaytunah kuwa bakinta yaki rufuwa tunda ta bude shi cikeda mamaki takasa cewa komai...
"Wadannan kadarorin ba wai kawai na raba su ne saboda in ba ku abu ba. Na raba su ne domin ku san cewa rayuwa tana bukatar jajircewa da hakuri. Ku yi amfani da wadannan kadarori ta hanyar da za su amfanar da ku da zuri’ar ku, da ma al'umma baki daya. Kada ku yi sakaci da rayuwar ku, ku kasance masu biyayya da godewa Allah."
Bayan da Gwaggo Hafsatu ta kammala raba wasu daga cikin kadarorinta, falon ya dauki shiru na sakanni, sai kukan farin ciki da aka ji daga gefen Hajiya Zaytunah. Ta sanya hannu a fuskarta, tana jin zuciyarta cike da motsin rai irin wanda ba za a iya bayyanawa ba. Duk nauyin da ta dade tana dauke da shi ya zama kamar an sauke shi daga rayuwarta.
Ta dube Gwaggo Hafsatu da idanuwanta masu cike da hawaye, numfashinta yana fita da kyar kamar wadda ta gagara furta magana. Kamar wadda aka dagargaza da annuri da farin ciki, ta mike da sauri ta durkusa a gaban Gwaggo Hafsatu, hannayenta suna rawa, tana kallon dattijuwar da ta fi kowa girma a wajenta.
"Gwaggo... Gwaggo na! Meye zan ce? Meye zan furta da harshena da zai isa godiyar da nake ji a cikin zuciyata? Meye zan iya bayarwa da zai mayar da irin wannan gata da kika yi mana? Gwaggo, ni fa ‘yar talaka ce, mara gata, Kuma marainiya. amma yau ga ni... kin daga ni sama, kin daukaka ni, kin sa ni da ‘ya’yana mun zama masu daraja!"
Hawayen da suka gangaro daga fuskarta sun jike bakinta, amma hakan bai hana ta ci gaba da magana ba.
"Shekaru da yawa na rayu cikin duhu da rashin tabbas, amma yau kin ba ni haske. Na sha wahala, na ci gaba da rayuwa da tunanin ko zan