"Ai dama Dr yace ba wani matsala . Kawai dai trauma ne. At first Nima ban yada ba. Amma bansan meya sameni ba haka kawai yau na samu kaina da tabbatarwa da tasamu lafiya. Bari na biya office gidah nakeson zuwa “
"Ya batin zuwan hajian Kuma?"
"Kamae yadda muka tsara din... Nanda 8months ko"
"To Masha Allah. Allah ya Kai mu"
"Madame sai wani lokacin"
Rumanah tayi kasa da Kai tana murmushin yake..
"Sai wani lokacin"
Alhaji uzairu na tafiya. Hajiya Rumanah ta Mike tsaye..
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/22, 10:13 PM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_51_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Ta daga Kai ta sauke akan alhaji Amiru Mai gidanta da ke ta murmushi yana daddana wayar hannun sa...
Taja dogon tsaki... Hade da yin kwafa tana karkada kafafuwan ta. Alhaji Amiru ya lura da yanayin ta don haka yayi shiru bai ce da ita komai ba..
"Iska na wahalar da me kayan kara."
Ajiye wayar sa yayi ya dubeta tana wani tattabe baki
"Da akayi me kenan?ke wai Dan Allah bakyason zaman lafiya ne? Yanzu meya faru Kuma?"
Tamkar dama jira take ya tofa albarkacin bakinsa ta Mike tsaye tana hayayyako masa,
"Saboda Allah. Shekaru nawa yanzu? Ace kakasa cire ta acikin ranka? "
"Bangane me kike fada ba rumanah. Kinga ko na haneki irin waɗannan maganganun naki marasa Kai. Yanzu wacece aka kasa cirewa arai meya faru anan?"
"Alhaji ka dena wani boye boye. Kowa ya sani inaga harta yayan cikin kaa ma sunsan akwai abunda yake kunshe acikin ranka ka kasa mantawa dashi. Wannan abu inaga da shi zaka mutu. Koma menene dai ai sai ka dinga sayawa. Tunda Nima dai dolen nan akai mun ba wai naga ni inaso bane"
Alhaji Amiru sai ya Mike tsaye. Ya daga yatsantsa yana Mai nuni da ita. Ta kaishi karshe don haka ya fara fada sosai,
"Me kike nufi rumanah? Me kike nufi? Fito ki Kalli tsabar idanuna ki gayamun abunda kike nufi"
"Yo ai Kai ma kasani. Amma bara na sake maimaitawa don ka sake tabbatarwa da kunnuwan ka. Ina sane da Kai Ina hankalce da lamuran ka. Alhaji har yanzu kakasa cire zaytunah a ranka. Har yanzu kana kaunar zaytunah . Ji kake dama da yarda zakayj zaytunah ta zama itace mata ag....
Ai bata karasa ba alhaji Amiru ya dauke ta da wani gigitattan marika har kala biyu... Duka kuncinanta... Zatayi magana ya sake sauke ta da wani akaro na uku.
Ta rike kuncinta tana duban sa baki bude. Agigice tace,
"Ni ka mara Amiru?"
"An dakeki rumanah. Ko zaki ramane? An dake ki. Ni kike kallon tsabar idanuna kike gayawa waɗannan maganganun haka? Lalle yau na sake tabbatarwar bakida HANKALI bakisan me kikeyi ba. Matar kanin nawa kike cewa inajin dama ita ta kasance mata agareni bake ba? Shekarun ma nawa dake? Duk a baya baki fada haka ba sai yanzu? Meya ke damun ki ne ehye?"
Rumanah da hawaye ke zuba a fuskarta ta daga kanta tana dubansa tache,
"Ko da dan uwanka yazo. Baka nuna alamun farin ciki ba sai da ya nuna maka ai zaytunah ta samu lafiyaa. Baka taba shiga cikin nutsuwa da kwnaciyar hankali ba irin yadda kake a yanzu. Haba Amiru ba yanzu na Saba rayuwa dakai ba. Shekarun mu nawa atare? "
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun.. lalle rumanah ban Kara gasgata lamuranki ba wallahi sai yanzu. Wallahi ban Kara tabbatarwa da ke din kwakwalwar kifi ce dake ba sai yau. Na Kuma tabbatar kinada karancin ilimin addini. Wanda ke dinnan zaki iya aikata komai. Ki shirya zance ki tabbatar cewa anyi shi bayan baayi dinba wannan wannan baki dakko halayen mahaifan ki ba Allah ya kyauta"
"Ya kyauta abunda yafi haka Amiru. Idan ma zaka musa ne kayita musawa daganan har tatar sara. Amma wallahi baka dena kaunar zaytunah ba kana sonta har yanzu"
"Dama zan dena kaunar zaytunah ne? Ai kauna daga Allah take. Sai dai kinyi kuskure a irin kaunar dake kwakwalwar ki da idanuwan ki suke duba Muki. yayinda akwakwalwar ki take shirya miki... Ina kaunar zaytunah Kam Amma kaunar da nake mata bata aure ba. Saboda babu aure atsakanina da ita. Bazan taba iya auren zaytunah ba. Ina dubanta amatsayin yar uwata Kuma kanwata. Saboda ko da aure bai hadamu dake ba, gaba daya ba. Ku kannena ne . Saboda mahaifan ku sun rike mu tamkar yaran da suka haifa daga cikin su. Abu na biyu zaytuna matar Dan uwana na ce. Ko babu kusanta dake. Zaytunah matar Kani Kuma Dan uwa nace. Mun rigada mun hada zuriya. Dole munada alaka. Ko aina na shiga a doron duniya zan nunata nace yar uwata ce. Abu na uku koma wanene ko da baisan zaytuna bah ba Kuma ba su da wata alaka kwata kwata. Ace ya ganta asibiti ko abashi labarin ta koyasan Wanda yasanta.. tabbas idan aka sanar masa ta samu lafiya yanzu. Kowannene dole yayi farin ciki. Dole yayi murna dole ne ya tayata murna Kuma shima yayi murna..
"Kuma wannan murnar da nayi. Da farin ciki Dana shiga. Da fara'ar data wanzu a fuskata. Kamata yayi ke kika rigani yi. Kamata yayi ace naki farin cikin da faraar ya wanzu fiye dani. Saboda kuwa ke kunfi kusantaka Dani. Ko ba komai yar uwar kice tare Kuka tashi, tsatson ku daya, garin ku daya , gidan ku daya, karewarta iyayen ku tsatso daya suka fito. First cousin dinki ce. Bakida wani daya fita. Sannan yanzu bakuda wasu yan uwa da zaku nunawa juna a manya dai irin kowannen ku. Kannen ki Maza ne. Kowa Kuma ya kama gabansa. Dama namiji ba a sanshi da zama ba. Na menene zaki dau wata al'ada ta daban ki aza abirnin zuciyar ki? Ko an gaya miki bana lura da ke bana fahimtar ki tun shekarun baya zuwa yanzu? Ai ko na karya ne sai ki kwakwalo farin ciki ki nuna agaban mijinta na ganin kinyi farin ciki da farfadowar yar uwarki daga lalurar data tsinci kanta aciki. Haba rumanah kina wani abu kamar wadda batada imani. Don haka ni nabar maganar. Ruwan kine ki dau duk abunda na fada ki ajiye shi a mizanin basirar ki ,ki auna shi da hankali, ruwannki ne kiyi fatali da maganganun da nayi. Ruwan kine duk abubuwan Dana fada ki sauya su zuwa taki fahimtar da sigar tunda naga ke duk abunda aka nuna miki kallonsa kike awani mahangar. Don haka ba abunda zan sake gaya miki duk abunda kikaga damar yarda ki yarda dashi...yar uwarki ce. Ku duniya zata zaga bani ba. Don haka ni babu abunda ya dameni. Zumunci Kuma da zaytunah ba ke kika hada mu ba. Don haka baki isa ki rabamu ba. Ba Kuma zan yanke zumuncin mu saboda wasu dalilai naki ba. Bakuma zan tirsasa ki ba akan kudirar ta akan ki. Ai ba yarinya bace ke kinada yara kin mallaki hankalin kanki kinsan dai dai kinsan abunda yake na daga bai dai ba. Toh duk abunda kika ga dama kiyi. Ni na fita"
Ya Saka hannu ya dauki mukullin motaa akan center table ya fice daga gidan baki daya. Yana juyawa tana jera tsaki. Girgiza kansa yayi. Ya shiga mota ya tayar yabar gidan gaba daya...
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/22, 10:23 PM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_52_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Hajia rumanah ta jera tsaki yafi a kirga. Ta zauna akan kujera cikin fushi da takaicin maganganun Alhaji Amiru Mai gidanta,
"Na tsani zaytunah... Duk abubuwan da zaytunah tamun Amman ita takecin galaba akai na? Har yan zu itace a samana? Har yanzu ita tauraruwar ta ke haskawa? Magana ta gaskiya hakuri na ya Kuma Kai karshe. Zan nunawa mutane gaskiar kalata. Zan nuna musu zaytunah ita ke zalunta ta. Itace azzalamu..Kuma annnamimiya. Munafuka Kuma wadda ba Allah a ranta"
Mikewa yayi fuuuuu tamkar jirgin da zai tashi sama. Daki ta shiga ta dakko wayarta ta zauna a bakin gado.
Ta danna sunayen su hajiya ladi da kishiyarta ta hadasu conference call. Sai huci take tamkar bajimar zakanyar data kamo abun farauta..
"Assalamu alaikum.... "
"Ah waalykm Salam hajjaju"
"Hajiya tahh. Yau kin kwace zumuncin"
Suka amsa sallamarta kowacce tana tsokanar ta. Hajia rumanah ta danyi murmushin yake tana furzar da iskar bakin ta tache,
"Da zuwa zanma... Toh Kuma yara zasu dawo daga makaranta. Ba Kuma zan iya jure har Su dawo ban sanar daku ba"
"Toh fa meke faruwa?"
"Wani abunne?"
Ta sake sauke nannauyar ajiyar zuciya tana jera kwafa har uku...
"Banason ma aji zancen nan a baki na ne. Zance ne na makirci da annamimanci."
"To fa meyafaru?"
"Ke da waye hajjaju?"
"Ni da abokiyar zaman ku... Kunsan kuwa abunda ya faru? Kaca kacha mu Kai da abban su yanzu yabar gidan nan bayan ya jeramun marika sama da biyu. Bamu rabu ta dadi ba ya gaggasa mun maganganu marasa dadi"
"Toh fa Subhan'Allah. Wai meya faru ne Dan Allah ki sanar damu"
"Ai shine ki gaya mana abunda yake faruwa. Koma menene babban abune. "
"Wannan abun ya wuce duk yadda kuke tunani. Wato makiyinka ba zai dena bibiyar ka ba. Wannan fadan da mukayi sai bayan Mai gidan ku yazo ya tafi mukaiyi shi. Duk da shima daya fada maganr kanzil bance ba wallahi. Sai shi ne ya yi mun ma sallama da zai tafi. Dan takaici wallahi ko na amsa shima oho. Ai ko yana fita fada muka fara yi da abban yaran na. Ta inda nake shiga batanan nake futa ba. Wallahi abu ta kaiga dai sai daya mareni ya gaggasa mun maganar da har na mutu banajin ni rumanah zan taba mancewa da su. Sannan abun yamun ciwo. Wannan abu ya dameni. Wallahi ku na fara kira yanzu na gayawa. Dan yanzun nan yaja motarsa ya tafi"
"To ai rumanah. Ni gaba daya kin lullube mu. Na kasa gane inda zancen ki ya dosa. Kina nufin kice waccen ragowar hankalin itace ta hadaku rigimar ko kwa Yaya? Ko kuwa shi baban yaran nan nan shine ya hadaku? Eh dan Allah ki sanar mana"
"Ragowar hankali kikace?
"Naga dai tayi wanke wanke fita ta dana yi dazu. Ta gama komai. So nasan tana daki tana haukanta mana"
Hajia rumanah ta barke da dariya tana tafa hannuwa. Dariyar ma irin mai ciwo dinnan datafi zubar da hawaye.
"Kai ba lafiya ba. Menene rumanah?"
"Yo ai gani nai kina kokarin ki manna mata wani haukan bayan akan rashin haukan nata aka faffaskamun Mari ba daya ba. "
"To fa.... Me Hakan ke nufi. ?"
"Da farko dai tun kafin ma na sanar da komai. Shin kunsan zaytunah nada waya a hannu?"
"Waya Kuma? Wayar hannu?"
"Kai zaytunah batada wata. To da Wa zatayi waya? Ai ko likitan ta sai dai ya kirani ko yakira aunty karama ko baban su."
"Toh tanada waya. Dan agaban mu shi Yaya uzairu ya kira zaytunah a waya. Har yana wani cemata tayi hakuri bayasan ya tashe ta a bacci ne yaga tana bacci shiysa...."
Ladi da hajia karama dake zaune a parlor dik sai suka tashi a tsaye a tare. Bakinsu a bude ..
"Zaytunah fa. A waya?"
"Shine ai. Zaytunah tayi waya da baban yaran nan?"
"Kwarai kuwa. Waya sosai tamkar dai shekarun baya da Kuka sani. Suna magana cikin annushuwa da farin ciki da kwanciyar hankali marar yankewa. Kai na dade banga Yaya uzairu acikin wannan farin cikin da nutsuwa ba irin na yau. Fuskar sa kadai zata tabbatar muku da adadin murnar da yake ciki. Har da ce mata sai ya dawo yana nan dawowa gidah.. hmm" ta karasa magana ta na kwafa..
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun"
"To munafuntar mu suke ko kuwa gaba daya tunani nama ya dauke"
"Dayan biyu. Inma dama can zaytunah lafiyar ta kalau. Ko Kuma malamun da aka Saka aiki karya suke basuyi aiki akanta ba. Inma Kuma dai lafiyar tasamu yanzu. Don maganar gaskia sai mun tashi tsaye. Don Baku kadai lamarin nan ya shafa ba Nima harda ni. Don wannan lafiya data samu ta jefani cikin musiba. Amiru fita yayi daga gidan nan da fushi na. Kuma bakuga yadda yake farin cikin samuwar lafiyar taba. Shima na dade banganshi a wannan sukunin ba. Don Ina mataarsa na bude baki nayi maganar rashin dacewar hakan nayi lefi?"
"Baki lefi ba wallahi"
"Gaskia dai babu lefi a maganar da kikai. Amma kai sunbani mamaki ko da yake.. ke da kawun Yara ba wani abu bane babba kamar na mu."
"Wane irin ba babba bane. Mijinta ne shi!? Kada ku manta na sanar muku abubuwan da duka faru a shekarun baya lokacin aurena da shi. "Rumanah ta katse hajia ladi tana huci
"Eh kuma Hakane gaskia"
"Gaskia ne. Baki lefi ba. Kuma ya cancanta kiji haushi" hajia karama ta fada
"To ni dai anawa bangaren kunga har sabani na samu da maigidana. Da nawa bacin ran Amma Kuma ai tayaku kishi ne ya jan yo Hakan"
"Hakane gaskia. Ai ke ta musamman ce"
"Samun ki sai an tona wallahi. Yanzu ya ake ciki"
"Ni dai anawa bangaren zan cigaba da Mai yiwuwa, ragi Kuma ya zaka namu. Sai ku tashi tsaye Kuma marar hankali zata rabaku da Mai gidan ku wallahi. Munyi wasarere ganin hankalinta ya gushe to gashinan ta samo wani salon. Nima anawa bangaren ban dena ba. Zanyi da baki na da jikina zan Kumayi da kudina. Bazan zauna haka ba. Kuma Kuma sai ku duba"
"Ai yanzu kuwa yar uwa.. zama bai ganmu ba. Zata gane shayi ruwa ne."
"Maganar ki kusa. Yanzu da muka zauna ba munga zama ba? Ai tashi zamuyi tsaye. Sai inda ruwanmu ya tsaya. Duk abunda zai faru sai dai ya faru"
"Yauwa yan gari. Mu taru mu hada karfi da karfe mu nemar wa kawunamu yanci. Shi ne magana kawai"
"Inshaa Allah"
"Wannan ya zama dole"
"To bari na barku haka. Abunda ya rage ya zama a hannuwanku. Idan mun sake haduwa sai mu zanta wasu abubuwan da suka dache.. kunji Kuma wai hajiya zata dawo ko?"
"Haba? wata lukutar masifar Kuma"
"Ai yau dai batayi dadi ba wallahi"
"Hmm Ashe ku gwara Dana kira ku. Wallahi dai abubuwan da suka faru kenan. Hajiya ma zata dawo nanda wani lokaci kankani. Sai musan abubuwan yi. Sai anjina dai kar na cika ku da surutai"
"Mungode da sanarwa. Sai kin jimu"
"Mungode hajjianmu... "
Hajia rumanah ta katse Kiran tana sakin munafukin murmushi . Ta wancakalar da wayar Hadi da mikewa ta futa daga cikin dakin....
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/22, 10:29 PM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_53_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Hajia zaytunah bayan ta kammala kintsa bangaren alhaji uzairu ta rufe sashen da mukulli. Tarike mullulin tana duban mukullin da kallo. Yaushe rabon ta shiga sashen bare har ta kullo ya bar mata spare key din. Ta saki murmishi tana damtse mukullin a tafun hannunta tamkar zaa kwace mata shi..
Kai tsaye ta nufi kitchen..ta fara tanadar abunda zata Dora na rana. Tana tsaye tanata tunanin abunda zata Dora sai ga shigowar su hajia ladi kitchen din.
"Yauwa.... Dama... Daman "
"Daman me bakar munafuka? Me raba aure Mai shiga tsakanin aure. Ke dai Allah wadaran waɗannan halayen naki wallahi. " Hajia ladi ta fada tana huci
"Ai wallahi badan tsagwarar makircin taba wallahi zama zanyi akanta na mata Dan banzan dukan da zata kasa tashi. Idan kina Neman algunguma bakar makira datayi matashin Kai da asiri kika samu wannan matar kin gama" hajia karama ta fada tana dingurewa zaytunah Kai
Zaytunah ta bude baki tana duban su. A iya sanin ta batasan abunda tayi ba. Sai idan Kiran da alhaji uzairu yayi mata ne take wajensa har suka raya Sunnah. Sai dai idan shi suke dauka a wata mahangar ta daban.....
"Bangane ba"
"Ai dama ba zaki gane ba...... Tunda ke ba Allah a ran ki. To ki sani wannan karon ba zakici galaba akan mu ba wallahi"
"Subhan'Allah.. ni wallahi waɗannan maganganun da kike fada na kasa gane inda suka dosa... "
"Ahap zance ya tabbata.har kinyi hankalin da kike iya mayar wa magana dukkanin abubuwan da muke fada? Wato wiyan ki ya Isa yanka. Kina ganin kanki daya damu ko?"
Hajia zaytunah ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza Kai tache,
"Ni dai bansan meyake faruwa ba. Amma koma menene naji na dauki lefin na dorawa Kai na. Allah yabaku hakuri..."
"Munafukar banza munafukar wofi. Duk munafucin da kike motsawa yana dawowa bayan kunnenmu. Koma atafin hannuwan mu yake. Mun san komai sarai. Kuma kinsani mun Saka kafar wando daya dake."
Hajiya zaytunah da gaba daya sun sake dulmiyata acikin duniyar tunani tache,
"Banda masaniya akan dukkanin abubuwan da kike ikirarin nasani. Yanzu ma abincin rana nazo na dora. Ina tunanin abunda zan dafa sai ga shigowar ku. Na safe Kuma zaku gani tunda asubah na kammala zuwa futowar rana na karasa komai"
"Dallacan yi mana shiru. Ai duk takun Saka ne gudun karmu San abunda kike aikatawa. To kisani wallahi kinyi kadan