KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   30 / 34

87K to 90K   out of 102K words

taba samun mafita, amma yau Allah Ya bayyana ki a matsayin mafi girman alkhairin da Ya ba ni! Gwaggo, ki dube ni... ki dube ni da idanuwanki masu cike da hikima, ki fada min wane irin gata ne zan iya mayar miki da shi?" Ta fashe da kuka, tana sunkuyar da kanta kasa.

"Na gode Gwaggo! Wallahi na gode! Allah Ya albarkace ki! Allah Ya kara girma da daukaka a gare ki! Allah Ya albarkaci ‘ya’yanki da jikokinki! Allah Ya sa ki shiga Aljanna ba tare da hisabi ba! Allah Ya sa ki gamu da Manzon Allah S/A/W. A ranar gobe kiyama!" Ta cigaba da jujjuya kai tana hawaye sosai, Ta dago kanta da sauri, tana kallon Gwaggo Hafsatu cikin shauki tacigaba da cewa,

"Gwaggo, Narasa bakin godia, gwaggo bansan ma mai zan cigaba da ce miki ba, gwaggo dama waɗannan tarin arzika sune maganganun da kika fadamun a shekarun baya? Subhan'Allah. Gwaggo da me zan Saka miki? Banida bakin godiya, Ni da ya’yana za mu gaba da yi miki addu’a har abada! Allah Ya saka miki da gidan Aljanna!"

Bayan ta gama magana, ta sunkuya ta rungumi kafafuwan Gwaggo Hafsatu, tana cigaba da kuka. Gwaggo Hafsatu kuwa ta sanya hannu a kanta, tana shafa mata goshi da murmushi mai cike da kauna da tausayi.

Nabeeha da Hammad kuwa sun kasance cikin tsananin shauki. Nabeeha ta rike hannun Hammad gam, tana jin zuciyarta tana bugawa da karfi. Baki ya mutu a gare ta, ta kasa magana. Cike da mamaki da farin ciki, ta matso kusa da Gwaggo Hafsatu, jikinta yana rawa saboda tsananin motsin rai.

Ta durkusa a gaban Gwaggo Hafsatu, idanuwanta cike da hawaye, tana kallonta kamar wata baiwar Allah da aka aikowa da albarka daga sama.

"Granny.. granny" Ta furta da wata murya mai nuna tsananin shauki.

"Ni Nabeeha ce! Ni ce yarinyar da ba ta da komai, wadda bata san mecece rayuwa ba. Amma yau kin sauya min labarina! Kin cire ni daga sahun marasa gata, kin ba ni suna, kin sa na zama wata a cikin wannan duniya!"

Ta kara fashewa da kuka, tana girgiza kanta.

"Granny, ba zan taba manta wannan rana ba har karshen rayuwata! Wallahi, duk wanda ya yi min alkhairi a duniya, babu wanda zai kai wannan da kika yi min! Yanzu ba zan sake jin tsoro ba, ba zan sake jin bakin ciki ba, saboda kin karfafani, kin mallaka min abin da zai amfanar da rayuwata!"

Ta dago hannayenta sama, hawaye na gangarowa daga idanuwanta.

"Ya Allah! Ka saka wa Gwaggo Hafsatu da alkhairi! Ka tsawaita rayuwarta cikin lafiya da albarka! Ka sa ta gama duniya da imani! Ka sa dukan ahalinta su zama masu albarka! Ka sa su zama masu arziki da rayuwa mai kyau! Allah, Ka sa ta shiga Aljanna Firdausi ba tare da hisabi ba!"

Bayan ta gama, ta durkusa ta rungume kafafuwan Gwaggo Hafsatu kamar yadda mahaifiyarta ta yi.

Hammad,Wanda ya kasance Kani ga Nabeeha. Kuma marar magana acikin su gaba daya. Sai kawai ya fashe da kuka kamar karamin yaro, yana jin wani abu mai karfi yana taso masa a kirji. Ya matso kusa da Gwaggo Hafsatu, ya durkusa a gabanta kamar yadda Nabeeha ta yi, sannan ya dora kansa a kan cinyarta yana kuka sosai.

Bayan wasu mintuna da ya kasa cewa komai, sai ya dago, yana share hawaye, sannan da wata murya mai rauni ya ce,

"Granny... Ni ba zan ce komai ba sai dai in ce na gode. Kuma wallahi har karshen rayuwata ba zan manta da wannan gata da kika yi min ba. Yanzu na zama namiji mai gata, na zama wani a duniya! Kin dade kina kokari a kanmu, amma yau kin kawo karshen shakkan da ke zuciyata."

Ya dago hannuwansa sama kamar yaro mai neman wani abu daga mahaifiyarsa.

"Ya Allah, Ka albarkaci Gwaggo Hafsatu! Ka kara mata lafiya, ka tsawaita rayuwarta! Allah, Ka sanya zuriyarta su zama masu alkhairi, su zama tsani na jin dadi gare ta! Ya Allah, Ka saka mata da aljanna!"

Bayan ya gama, ya sunkuya yana goge fuskarsa, zuciyarsa tana cike da godiya marar misaltuwa.

Gwaggo Hafsatu kuwa, tana zaune tana kallonsu, zuciyarta tana cike da farin ciki da annashuwa. Bata taba jin irin wannan jin dadi ba. Ta shafa kan Nabeeha, ta shafa kan Hammad, sannan ta kalli Hajiya Zaytunah cikin kauna da girmamawa.

"Allah Ya saka muku da alkhairi. Allah Ya albarkaci rayuwarku. Ku ci gaba da rayuwa da hakuri da biyayya, domin rayuwa tana da SIRRIN ta. Ku kasance masu godewa Allah a ko da yaushe, kuma kada ku manta da cewa gata ba zai iya dorewa ba sai da adalci da biyayya ga Ubangiji."

Barrister Lukman shi ya fara daga hannu yana tafi. Bayan sunce Ameen gaba daya . Hajia zaytunah ta juya wajen major general zuciyarta ta cika da.......

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.


📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.


📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00




🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_


*_PAGE: 79_*

Ta cika da tsananin farin ciki da godiya. Duk da cewa tun farko Gwaggo Hafsatu ta nuna mata gata da kulawa fiye da yadda take tsammani, amma wannan gata da aka yi mata yau ya fi duk wani gata da aka taba yi mata a duniya.

Tayi ajiyar zuciya mai nauyi, tana jin yadda hawayen farin ciki suka cika idanuwanta. Ta mike tsaye daga inda take zaune, ta juya zuwa ga Major General Dawud, wanda yake zaune cikin natsuwa da girmamawa.


Ta karasa gabansa cikin girmamawa, sannan ta durkusa, hawaye na zuba a fuskarta.

"Yaya dawud.. ya zan fara? Ya zan iya bayyana irin alkhairin da kuka yi mana? Ta wane harshe zan gode maka, kuma ta wane harshe zan gode wa mahaifiyarka, wannan baiwar Allah mai zuciya mai kyau, mai imani da tausayi?"

Ta runtse idanuwanta, tana jin yadda zuciyarta ke tafasa da tsananin godiya.

"Ka tsaya a gare mu a lokacin da ba mu da mafaka. Ka kare mana mutunci da daraja lokacin da duniya ta juya mana baya. Ka rufe asirinmu, ka hana kowa ya san SIRRIN mu. Babu abin da na isa in ce sai dai Allah Ya saka muku da Aljanna! Allah Ya tsawaita rayuwar mahaifiyarka! Allah Ya ba ta lafiya, ya kara mata imani da kwanciyar hankali!"

Ta share hawayenta, sannan ta ci gaba da cewa,

"Yaya dawud, kai mutum ne na kwarai! Kai namiji ne nagari! Idan ba kai da mahaifiyarka ba, wane ne zai tsaya a gare mu? Yanzu ga irin gatan da mahaifiyarka ta yi mana! Ta mallaka mana kadarori da ba mu taba tsammanin za mu mallaka ba! Ya Allah! Wannan gata ya fi komai girma!"

Ta kara durkusawa, ta dago hannuwanta sama cikin tsananin godiya...

"Ya Allah! Ya Ubangiji, Ka albarkaci wannan bawan Naka! Ka kara masa lafiya da kwanciyar hankali! Ka sanya shi cikin kariyarka a duniya da Lahira! Ya Allah, Ka biya masa dukkan bukatunsa na alkhairi, Ka ba shi nasara a rayuwarsa, Ka sa dukkan hanyarsa ta zama mai albarka! Ua Allah, Ka tsare shi daga sharri da makiya! Ka sanya shi ya rayu cikin aminci da kwanciyar hankali! Ka albarkaci zuriyarsa, Ka sanya su su zama nagartattun bayinka! Ka tsawaita rayuwarsa cikin lafiya da arziki! Ya Allah, Ka saka masa da Aljanna! Ka sa rayuwarsa ta cika da ni’ima da daukaka! Ka kare shi daga hassada da mugunta! Ka biya masa dukkan bukatunsa! Ya Allah, duk wata nasara da yake nema a rayuwa, Ka bashi!"

"Ameen zaytunah. Ta Isa haka godiyar nan. Ta Isa haka." Major general ya shiga dakatar da ita shima idanuwansa na kokarin kawo ruwan tausayin kalaman ta... Ya tuno labarin ta da gwaggo ta bashi sai yaji itada iyalanta sun sake dulmiya shi a duniyar tausayin su. Ya jiyo ta cigaba da cewa,

"Ranka ya dade, ba zan taba mantawa da wannan gata ba. Kunyi mana gata fiye da yadda muke tsammani! Ku ne ginshikin rayuwarmu, ku ne ahalin da Allah Ya aiko domin mu sami sabon fata a rayuwa! Ku ne silar da muka tsaya tsayin daka a duniya! Allah Ya kara maka nasara, ya kara daukaka matsayinka! Allah Ya cika maka burinka na alkhairi, ya baka farin ciki da kwanciyar hankali a duniya da Lahira!"

Major General Dawud ya sauke numfashi a hankali, yana kallonta da murmushi mai dauke da kwanciyar hankali. Ya girgiza kai sannan ya ce,

"Hajiya Zaytunah, ai ba wani abu na musamman na yi ba. Wannan gata da kuka kira haka, wallahi ba wani abu ba ne. Mahaifiyata ce ta ga dacewa da haka, kuma ina alfahari da wannan hukuncin da ta yanke."

Ya kalli Nabeeha da Hammad, sannan ya ci gaba,

"Ku sani, duniya tana tafiya ne da addu’a da rikon amana. Kada ku bari wannan gata ya canza muku hali, ku zama masu tsoron Allah da rikon amana. Idan Allah Ya hore wa mutum alkhairi, sai ya yi amfani da shi domin taimakon wasu."

Ya kalli Zaytunah da idanuwansa masu cike da tausayawa, sannan ya ce da ita,

"Allah Ya albarkaci rayuwarki da ta ‘ya’yanki. Allah Ya sa ku yi amfani da wannan gata ta hanyar da ta dace. Allah Ya yi muku jagora. Kiyi hakuri, wannan abu ba wani abu bane da za ki sa a rai sosai."

Ta gyada kai cikin tsananin jin nauyin godiya, tana jin cewa ba za ta taba mantawa da wannan rana ba har abada.

A gefe guda, Hajiya Hawwa Maijidda tana zaune tana kallon komai da idanunta masu cike da tsantsar bakin ciki da takaici. Ta kasa dauke idanunta daga yadda Zaytunah ke nuna tsananin farin ciki da godiya.

"Yanzu haka kawai za a mallaka musu dukiya mai yawa haka? Yanzu haka kawai za a fifita su fiye da kowa a gidan nan? Ai wannan wuce gona da iri ne!"

Ta hade rai, zuciyarta cike da kishi da takaici. Ta mike tsaye a fusace, sannan ta fice daga falon ba tare da ta yi wa kowa sallama ba... Gwaggo Hafsatu na hankalce da ita tayi murmushi kawai. Haka ma major general mai gidan ta. Shima bin ta yayi da kallo ya sauke katuwar ajiyar zuciya yana girgiza kansa cikin takaicin abunda ta aikata..

Bayan addu’o’i sun kare, kowa ya mike cike da farin ciki da jin dadi. Zaytunah, Nabeeha, da Hammad sun ji kamar sun sami wata sabuwar rayuwa. Kowa na gidan ya ji mamakin yadda aka yi wannan rabon kadarori, amma babu wanda ya isa ya canza hukuncin Gwaggo Hafsatu...

Wannan rana ta kasance rana mafi girma a rayuwar su Zaytunah da ‘ya’yanta, kuma ba za su taba mantawa da ita ba har abada!

🎀🎀🎀🎀

Hajiya Hauwa Maijidda ta kasa kwantar da hankalinta gaba daya.. Tana zaune a falonta, zuciyarta cike da dacin rai da mamaki. Ta riga ta san cewa Gwaggo Hafsat tana da kyauta da tausayi, amma bata taba zaton cewa har kadarorinta zata baiwa wata da ba yar data haifa acikin ta ba. Ji tayi zuciyarta ta kadawa, domin abin da ke faruwa yana nufin cewa hajia zaytunah da ‘ya’yanta sun samu matsayi irin na ‘ya’ya a gidan!

Shiru tayi na wasu lokuta, tana nazari. “Meyasa Gwaggo Hafsat zata yi haka? Me yasa ba a yi wa su dawud ba, sai wannan matar da ni bansan ta inda suka hada jini ba?” Tambayoyin sun yi mata yawa. Ta san cewa Maigidan ta, Major General Dawud, yana da matukar biyayya ga mahaifiyarsa, kuma yana mutunta duk wani hukunci da ta yanke. Amma ta kasa daukar wannan hukunci da sauki.

A karshe, ta tashi ta nufi sashen maigidan nata. Ba ta so ta yi masa magana da bacin rai, don haka ta nutsu, sannan ta fara magana cikin sigar girmamawa.

“Alhaji.. ba don komai ba, amma gaskiya wannan abin da aka yi ya fi karfina. Ba na jin daɗi. Har kadarorin gidaje an baiwa wata ba tare da mu da muka dade muna yi wa gidan hidima mun sani ba?”

Major General Dawud ya dago daga takardun da yake dubawa, yana kallon matar tasa da tsantsar nutsuwa. Bai yi gaggawar magana ba, sai da ya tabbatar da cewa ya fahimci ainahin abin da take nufi.

“Hajiya Hauwa, na fahimci damuwarki. Amma kada ki manta cewa kadarorin da Gwaggon ta bayar nata ne. Ba wani ne ya bata ba, kuma ba wani ne ya hana ta amfani da su yadda take so ba. Hakkin ta ne, kuma idan har ta ga dacewar taimakawa da su, to ai wannan alheri ne, ba abin damuwa ba.”

Hajiya Hauwa ta hade rai. “Amma fa hakan yana da tasiri. Yau idan aka ce an bai wa Hajiya Zaytunah wani abu, gobe fa? Ta zama jinin gidan ne? Ko kuma an fara kafa mata tushe ne har ta gaji kadarorinmu gaba daya?”

Major General Dawud ya ajiye takardunsa, sannan ya gyara zama. “Ki ji tsoron Allah, Maijiddaa. Dukiyar da mutum ke da ita, idan bai yi amfani da ita wajen alheri ba, to a ranar da zai mutu, za ta zama fitina a gare shi. Dukiya amana ce, kuma idan Gwaggo ta yanke shawarar amfani da tata don ta taimaki wacce take bukatar taimako, ba ke ba ce za ki tare ta.”

Ya dauki tsawon lokaci yana yi mata bayanin mahimmancin kyauta da sadaka a addini, yana jaddada cewa dukiyarsu ba za ta ragu ba saboda sun taimaki marayu da matan da ba su da kowa. “Abin da kika gani a matsayin cuta, wata kila alheri ne da ke kunshe da rahamar Allah.”

Daga nan sai ya kara da cewa, “A matsayinki na uwar yayana, dole ne ki koyi yin biyayya ga zuriya ta. Duk wani abu da kika ji kunya a kansa, ki sani cewa idan Allah Ya yanke hukunci, ba za ki iya hana sa faruwa ba. Abin da na ke bukata daga gare ki shi ne ki tafi ki nemi afuwar Gwaggo, domin abubuwan da kika fada dazu a taro ba su dace ba.”

Hajiya Hauwa ta ji kamar kasa ta tsage ta shige! Bata taba zaton cewa maigidan nata zai matsa mata kan wannan ba. Amma ta san halinsa, idan ya yanke hukunci ba ya sauyawa. A ranta tana jin haushin yadda ya sa ta gaba, amma dole ta tashi ta je sashen Gwaggo Hafsat.

Bayan da ta isa, Gwaggo Hafsat ta karbe ta da fara’a, kamar wacce ba ta ji komai a taron dazu ba. Hajiya Hauwa ta daure, sannan ta fada mata cewa ta zo ne domin neman afuwa kan yadda ta nuna rashin jin dadinta. Gwaggo Hafsat ta kalli Hajiya Hauwa tare da sakin murmushi, sannan ta ce,

“Babu komai, Hauwa. Duk mu mutane ne, kuma ba za mu kasance da ra’ayi daya koyaushe ba. Amma ina fata ki fahimci cewa abin da na yi ba da gangan na yi ba, sai don neman alheri a rayuwar Zaytunah da ‘ya’yanta..."

"Hakane Kam gwaggo. Toh Allah ya biyaki da gidan aljanna .. Ya Saka miki da alkhairi Amin"

"Aameen. Allah ya miki albarka..."

Hajiya Hauwa ta yi murmushin dole, sannan ta bar sashen. Amma daga wannan rana, zuciyarta ta kara cika da kiyayya ga Hajia Zaytunah.

Zuciyarta cike da tunani. Tana jin cewa idan har aka bar Hajiya zaytunah a haka, to wata rana ba shakka za ta gaji dukiyar gidan gaba daya. Ta dauki wayarta, ta nemo lambarta ta musamman – wacce take amfani da ita don wasu aiyuka na SIRRI – sannan ta aika da sakon da zai tabbatar da cewa ta dauki matakin da ya dace.

"Ki tabbatar da cewar kinyi duk abin da zai yiwu, amma kar a gane cewa ina da hannu a ciki.”

Ta gama rubuta sakon, ta danna send. Wata irin annashuwa ta ratsa ta, zuciyarta na jin dadi da cewa ba za ta bar Hajiya Zaytunah ta ci galaba akanta ba. Wannan yaki ne, kuma ita ba ta da niyyar shan kaye...

🎀🎀🎀

Zuciyarsa cike take da raɗaɗi. Kamar ana huda ta da ƙaya. Kamar ana hura masa wuta a KIRJI, har ta hana shi numfashi yadda ya kamata.

Akwai soyayya, akwai ƙauna, akwai buri, akwai fata. Amma duk a zuciyarsa suke. Ba ya iya furtawa, ba ya iya bayyana komai. Sai dai ya yi shiru, yana ɓoyewa tamkar mai dauke da wani babban SIRRI da ba za a iya faɗa wa duniya ba.

Fawaaz yana zaune a ɗakin sa, hannunsa dafe da goshinsa. Ya lumshe ido, amma ba ya iya jin sauƙi. Duk inda ya juya, hoton Nabeeha yake gani. Murmushinta, yadda take magana da saurayinta ba tare da jin kunya ba. Yadda take dariya, tamkar ba ta san cewa wani yana kwance yana juyawa kan matashin gado ba, yana jin kamar zuciyarsa za ta tarwatse.

Ya san cewa shi mutum ne mai nutsuwa. Ba ya yawan magana. Ba ya yawan nuna halayensa a fili. Amma wannan karon zuciyarsa ta kasa. Ita kanta jinin jikinsa ba ta iya daukar kaunar Nabeeha da ta cika shi har KIRJIN sa yana jin tamkar ya fashe.

"Na gaji." Ya furta cikin sanyin murya, yana mai jin tsananin raɗaɗi.

Ya san cewa dole ya ɗauki mataki. Idan ya ci gaba da zama a cikin wannan gari, ba zai iya jure ganin Nabeeha da wani namiji ba. Duk ranar da ya kalle su tare, yakan ji tamkar wani yana tafasa masa zuciya da ruwa mai tsananin zafi. Duk da cewa bai taɓa nuna wa Nabeeha soyayyarsa ba..

KIRJIn sa na radadi. Idanuwansa na zugi. Zuciyar sa na zillo da tsananin bugun kaunar Nabeeha. Ya dauki wayar sa

30 / 34