samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
May Allah reward your efforts abundantly
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE: 73_*
Nabeeha ta daga Kai ta dan kalleshi ganin yayi shiru bai ce komai ba.... Alokacin Kuma Muhammad tsananin farin cikin Allah ya cika masa burinsa na yau gashi ga nabeeha ne yasa shi dan dakatawa da magana...
Ya danyi murmushi yana ganin ta kalleshi ta kauda Kai da sauri...ya kalli Nabeeha da idanunsa masu zurfi, yana jin zuciyarsa na bugawa da sauri. Ya daɗe yana ganin kyawawan mata, amma bai taɓa jin irin wannan ba. Wata natsuwa da shauƙi suka lulluɓe shi, yana jin tamkar an tsayar da duniya a wannan lokaci.
"Ina jin kamar na san ki tun daɗewa," ya furta cikin nutsuwa, yana kallon ta kai tsaye.
Nabeeha ta sauke idanunta ƙasa, ba ta san me za ta ce ba. Duk da cewa ba ita ce fara jin irin wannan furucin daga wani namiji ba, akwai wani abu a cikin muryarsa da yadda idanunsa ke kallonta da ya sa zuciyarta ke bugawa da sauri.
"Amma ba zan ce dole sai kin yarda da hakan ba," ya ƙara faɗa, yana murmushi. "
Nabeeha tayi murmushi kawai batace dashi komai ba. Muhammad Hammad ya sauke numfashi a hankali, yana kallon Nabeeha da idanunsa masu dauke da wata irin natsuwa. Idanunsa sun nuna cewa yana shirin bayyana wani abu mai muhimmanci, wani abu da zai iya sauya komai a tsakaninsu.
"Kin san yaushe na fara sonki?"
Nabeeha ta dan waro ido, zuciyarta na harbawa da sauri. Ba ta taba tunanin zai yi mata wannan tambaya ba, kuma yadda ya fada, cikin muryarsa mai cike da gaskiya, sai ta ji kamar numfashinta ya tsaya na dan lokaci.
Ta girgiza kai a hankali. "A'a," ta fada cikin kasalalliyar murya.
Ya dan murmusa, yana mai jin yadda zuciyarsa ke bugawa. Sai da ya gyara zamansa kafin ya cigaba da magana.
"Ranar farko da na ganki," ya fada kai tsaye.
Ta dan bata fuska da mamaki. "Ranar farko?" Ta maimaita, kamar ba ta yarda da abin da ya fada ba.
Muhammad ya gyada kai, yana kallon cikin idanunta. "Eh. Ranar da kika tsaya a gaban ajin Fahad.. malamin ku malam Fahad.. kina gabatar da presentation. Ranar da kika riƙe takarda a hannunki, amma ni kaina na san cewa ba takardar ce ke bayani ba..ke ce da kanki kika san abin da kike fada."
Ya sauke murya kadan, yana tuna yadda ya ji a ranar..
"Nayi shiru a inda nake zaune, amma a zahiri, zuciyata tana tafiya da ke. Lokaci guda kin shige min, kin zauna a zuciyata ba tare da izini ba. A wancan lokacin na gane cewa ba kawai kyawunki ne ya dauke min hankali ba, a'a, akwai wani abu a tattare da ke da zuciyata ta kasa watsi da shi."
Nabeeha ta yi shiru, tana kallonsa da idanunta masu dauke da mamaki. Bata taba jin irin wannan furuci daga bakin wani da namiji ba cikin nutsuwa, Har a lokacin da ta fara fahimtar maganganun da yake fada ba. , bata taba tunanin cewa soyayyarsa ta taso tun daga wancan lokacin ba.. wayaga batasan anayi ba. Sam bata tuna ma yaushe ne. Domin sunyiyyi presentation kala kala. Anatomy – Nazarin tsarin jikin mutum, gabobi, da yadda suke aiki. Da ,Physiology – Yadda jiki ke aiki (kamar yadda zuciya, huhu, koda, da kwakwalwa ke aiki). Bochemistry – Nazarin sinadarai da ke jikin mutum da yadda suke aiki..... Tabbas ta tuno tayi presenting paper work akansu...
"Ranar da kika tsaya kina bayani cikin natsuwa, cikin kwarjini, cikin sanin me kike fada... a ranar na kamu da sonki, Nabeeha."
Tayi shiru, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi. Wannan kalmomi nasa sun gama narkar da ita. Ba ta san ya akayi haka ba, amma tana jin kamar ana jefa ta cikin wani yanayi da ba ta saba da shi ba.
Shiru ya ratsa tsakaninsu. Ita kanta bata san abin da za ta ce ba. Duk da haka, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin cewa tabbas wannan kalmomi sun samu matsuguni a ranta.
"Duk da haka, zan so mu fi jin daɗin juna. Don haka... zan iya samun lambarki?"
Akwai wata nutsuwa da yake da ita da ta kasa fassara. Sai ta sauke numfashi a hankali, sannan ta dan ja baya kadan...
"Lambar waya?" Ta maimaita tamkar mai jin wani abu a karo na farko.
Muhammad ya gyada kai yana murmushi. "Ee, zan so na same ki a waya idan babu matsala."
Nabeeha ta dan yi shiru na wasu dakiku, zuciyarta na harbawa. A hankali, ta dauko wayarta da ke gefenta. Duk da cewa ba ta saba bayar da lambarta haka ba, wani sashi a cikin zuciyarta yana raya mata cewa Muhammad ba irin sauran mazan bane.
"Ki kirani kawai, zan riƙe lambar," ya faɗa cikin wata irin murya da ya sa jikinta ya ɗan yi sanyi. Yana kirawo mata lambobin .
Bata san lokacin da ta danna kiran lambar da ya nuna mata ba. Wayarsa ta ɗauki ringing, yana kallon sunan da ya bayyana a fuskar wayarsa—"Nabeeha U M". true caller ta nuna. Sai ya yi murmushi, zuciyarsa cike da jin daɗi.
"Nagode," ya faɗa a hankali, yana riƙe wayarsa.
Ita ma ta yi murmushi kadan, haka suka cigaba da yar hirar su kadan kadan. Duk da dai shi yaketa maganar sa nabeeha nata daga Kai kota jefa amsa kadan tayi shiru. Muhammad ya dan Sha lemon da aka ajiye ya Mike da robar ruwan daya dauka guda daya bayan sunyi sallama..
Muhammad ya sauke numfashi, ya san lokaci ya kure. "Za mu sake magana?" Ya tambaya.
"In shaa Allah," Nabeeha ta amsa a hankali.
Ya dubi malam Fahad, wanda ke sanye da murmushi a fuska, sannan suka yi sallama suka fice baki daya wajen harabar farfajiyar gidan..m
Bayan sun futa wajen sashen motoci inda Muhammad ya faka motar sa. Sai suka tsaya. Muhammad yana sake nanata number nabeeha har ya hardace akansa. Ya Kuma kirata din awajen ta daga wayar tana murmushi...
Fawaaz na tsaye a saman sashen sa, yana kallon komai daga nesa. Tun farkon shigowar Muhammad ya lura da shi, kuma yanzu yana kallon yadda yake magana da Nabeeha har ta ba shi lamba ya kirata ..
Zuciyarsa ta yi wani irin nauyi. Bai san me yake ji ba, amma ya san dai ba dadi bane. Wani abu a cikin sa yana raya masa cewa Muhammad ba mutum ne da za a yi wasa da shi ba.
Ya sake kallonsu daga saman sashen, yana jin zuciyarsa na cunkushewa... Bayansa yake hangowa da gefen sa. Tamkar Kuma ya San shi, ya manta a ainane? "Wane ne wannan? Me yake nema?" Ya furta a hankali, idanunsa suka kada da wani irin yanayi.
Zai jira... Zai ga inda wannan al’amari zai dosa.
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
A bangaren Muhmmad da abokinsa kuwa, suna tafiya suna tattaunawa.
"Wai dai kana nufin da gaske ne akan abin da ka fada min?" Fahad ya tambaya yana kallon sa.
Hammad ya sauke ajiyar zuciya. "Ba wasa nake ba, tun ranar da na ganta nake jin cewa ita ce macen da nake so... Kuma zan aureta da yardar Allah"
Fahad ya tabe baki. "Kasan dai ba abu ne mai sauki ba, ba kowane mutum zai yarda da haka ba."
Muhammad ya tsaya cak, yana fuskantar dr Fahad. "Duk wahalar da zan sha, ba zan bari ba. Ina son ta."
Fahad ya dafa kafadarsa. "Zan taimaka maka, amma fa dole ka shirya komai."
Hammad ya jinjina kai da tabbaci. "Komai zan iya yi domin ita."
Haka dai suka cigaba da hirar su. Har suka karasa gidan su fahad. Suka cigaba da tattaunawa. Aka kira sallah suka nufi masallacii sukayi. Suka koma sashen Fahad sunata hira. Sai da dare yaja sannan suka kwanta . Ranar Muhammad har bacci yayi da minshari saboda tsananin farin cikin ganawa da nabeeha...
Washegari ana idaar da sallar asubah kuwa bayan gari ya fara haske yayi sallama da ahalin gidan su fahad masu karamci da dattako ya dauki hanyar komawa garin su....
Dake titi ba motoci sosai kasancewar safiya ce ainun.. Yana kuma zuba gudu. Bai ja awanni da yawa ba ya Isa garin su cikin ikon Allah da qudirar sa.....
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
..
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE:74_*
Hajia Hauwa Maijidda tana zaune a dakin ta. kasancewar dare yaja ainun. Zuwa da safe kuma idan Allah ya nufa mai gidan ta washegari da safe zai dawo..
Sanye take cikin kayan bacci. Ta juya nan ta juya can. A babban king size bed dinta makeke royal daya kusa cinye dakin saboda tsananin girmansa. Komai na dakin samfarin royal ne kirar Italy. Lamarin sai sam barka kawai...
Mikewa tayi ganin bacci ya kaurawa cewa idanun ta...
"Kiri Kiri gasu Raudah nan. Amman ace dan abokin baban su yaga Nabeeha kadai yana so? Tsabar ya dauka yar dawud ce ta cikin sa ko? Kai! Kai! Kai!" Ta fada cikin tu'ajjabi. Ta cigaba da cewa,
"Wannan lamari na zaytunah da iyalanta ya isheni." Ta shiga zayage dakin . Hannuwanta a bayanta tanata kwafa hadi da cigaba da mita ita kadai. Da jera tsaki ba kakkautawa..
Dakin mijinta ta nufa ta tura kofar. Sai kamshi ne ke tashi dake tanada tsafta . Gidan baki daya ka qal yake. Gashi duk da mai gidan baya nan yayi tafiya. Amman kullum sai an gyara bangarensa an turare shi. Shi ya sa gidan ya kamu da kamshin turare. Ko da yaushe a kamsashe yake...
Ta zauna akan gadon tana dafe kanta.. can ta dauki wayar ta tana duban chatting dinsu da mai gidan nata. Gaba daya komai zaytunah tayi kanai kanai... Rabin maganar sa Allah yasa kowa kalau har wajen su hajia zaytunah da iyalanta?
Hannunta ta saka ta janyo bedside drawer... Wayar sa ta gani 'dayar da yake bari agidah Nigeria. Ta kunna ta tana sauke zuciya. Ta danna button kenan zata kashe sai Kuma ta fasa ganin message ya shigo..
"Ranka ya dade barka da rana... Ya iyali fatan suna nan kalau? Ya kuma aiki? Ubangiji Allah ya temaka Amin. Kayi hakuri dai dani kwana biyu. Wallahi jikin dan uwan namu ne wato shi miji ga zaytunan da muke neman ka temaka mana da binciko inda take a raye ko a mace? itada yaranta biyu ?Ya matsa jikin nasa wallahi. Dan Allah amana kokari. A Kuma yi hakuri da mu... "
Hajia hauwa Maijidda tana zaune sai ta mike da hannu a bakinta... Ta shiga scrooling din message din baya tana dubawa,
"Assalamu alaikum ranka ya dade sunana Amiru Muhammad . Dan uwa ga uzairu Muhammad . Ni ne Wanda nazo da dan wajena muhammad. Wannan daya number tache. Waccen ta samu matsala ne nace bara na maka magana da wannan kafin a gyara wancen"
"Ranka ya dade. Ina miko duban gaisuwa agareka da dimbin fatan alkhairi. Allah yayi riko da hannayen ka amin. Ranka ya dade dan Allah a temaka mana nasan Kai me temaka ne. Bamu da wani gata sai na Allah da gudunmawar sa. Sai ta hanyar ka da muka biyo. Dan Allah a duba mana"
"Ranka ya dade....Assalamu Alaikum, Yallabai. Ina fatan kana cikin koshin lafiya.? Na ga cewa duniya ƙarama ce! Ashe wannan yaron naka da yake son ‘yarmu yar wajen kaa, Muhammad Hammad dan waje na,? Kuma shi aboki ne ga Fahad, ɗan gidan Chief Judge Abdulfatah, wanda kuma abokinka ne. Mahaifin shi Fahad shi yayi gaba ya kiraka yace yana nemawa dansa izinin zuwa tadi/zance wajen yar wajenka daya gani a makaranta. Har ka amince. Sai da Muhammad din ya dawo yake sheda mun komai. Lallai rayuwa cike take da abubuwan mamaki. Sai da shi Muhammad ya dawo nema yake sheda mun, Na ji daɗin jin cewa an karɓe su hannu biyu, kuma na gode ƙwarai da karamcin da aka nuna musu. Allah ya saka da alheri.na kuma samu labari cewa baka kasar. Ina maka fatan alkhairi a tafiyarka, Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da kai gida lafiya. Ameen... Idan ka dawo ka huta inshaa Allah zamu shigo. Kan dai batun matar dan uwana, wato hajiya Zaytunah data bata shekarun baya da yaranta biyu zainab da Muhammad.. a huta lafiya"
Hajia hauwa Maijidda na gama karanta sakon ta sulale ta zube akan gado.