bin ta dasu ladi da karama suke da makirci da tsibbu komai tarwatsewa yakeyi.
Gashi Alhamdulillah Allah cikin ikonsa da kudirar sa.. Allah ya azurta hajia zaytunah da juna biyu.. cikin ikon Allah tafara laulayin cikin tana renonsa. Har Allah ya amince ya shiga watan haihiwar sa..a Kuma watanne hajia zainab mahaifiyar su alhaji uzairu ta dawo gidan alhaji uzairu da zama gaba daya saboda an kammala sashen da zata zauna tuni..
A ranar da ta diro garin. Asibiti ta wuce inda aka kwantar da hajia zaytunah zata haihu.
Allah cikin ikonsa da kudirar sa Allah ya azurta hajia zaytunah da samun yarinya mace sankaceciya tamkar yar larabawa. Ta dakko kyawun mahaifinta da mahaifiyarta. Sumar gashin kanta tamkar ta budurwar balarabiya. Kyakkyawaa mashaa Allahu. Tubarkallah Allah yayi halitta.
A Kuma lokacin alhaji uzairu ya dauketa yayi mata huduba. Ya sanya mata sunan mahaifiyar sa zainab. Yarinyar taci suna biyu. Sunan marigayiya gwaggo abule. Da sunan mahaifiyar sa zainab. ..
Kwanan su uku likita ya tarkataa ya sallamesu. Hajia zaytunah ta koma gidah dajego ga uwar mijinta dake sonta ga mijinta da yan uwansa da shima abun ya Karye suna kaunar yarinyar baby zainab nan nan yakeyi da ita. Kowa sonta yake yana Kuma San ya dauketa....
A haka har ta cika shekara daya da wata shida. Dake tana surutu tana Kuma tafuya tayi gudu. Hakan yasa hajia zainab mahaifiyar alhaji uzairu ta dauketa ta kaita wajenta ta Kuma yaye ta mashaa Allahu... Ashe rabon wani cikin ne baa dade da yaye baby zainab ba hajia zaytunah ta sake haihuwa, wannan karon da namiji aka samu. Suka sanya mishi Muhammad wato sunan marigayi alhaji muhammad mahaifin su alhaji uzairu...
A haka hajia zaytunah tacigaba da kula da baby zainab da Kuma baby Muhammd cikin koshin lafiya, lumana da kuma kaunar juna...
×ZURI'AR ALHAJI MUHAMMAD+
marigayi alhaji muhammd. shine asalin sunan mahaifin su alhaji uzairu. Mahaifiyar su Kuma hajia zainab.
Allah ya azurta marigayi alhaji Muhammad da hajia zainab da albarkar yara gudu hudu... Mata biyu Maza biyu..
Alhaji uzairu. Da alhaji Amiru da hajia habiba da Kuma hajia Layla.. dukkaninsu kowanne yayi aure Alhamdulillah
Kafin rasuwar alhaji muhammd. Sanaar sa itace kasuwanci. Yana da katafaren kudi, yanada kamfani kala kala . Yana Kuma sanaar safarar Kai dabbobi zuwa kudu. Baanan kadai ya tsaya ba. Yanada manyan shauguna a manyan kasuwanni na kasa baki daya. Inda ake sayar da kayan sawa na atamfofi, leshika da sauran su.
Ya na Kuma da asibitoci na kudi nasa na kansa. Yana Kuma da kamfani babba da share holders Wanda matarsa hajia zainab itama babbar shareholder ce wato tanada babban hannun jari a kamfanin bayaga yayansa yana da dukiya sosai don har gidajen Mai yake dasu. Da gonaki na kiwo Dana nomada sauran tarin dukiya Masha Allah. Sannan wannan dukiyar tashi bata sakashi dagawa ba ko kyamatar talakawa. Haka zalika bai manta da talakawa ba yayinawa talakawa sosai da makotansa. Bayaga yan uwa da abokan arzuka. Sannan yanada ilimin addini sosai. Shi yasanya. Sai da yaransa suka kammala allo sukayi suaka. Sannan ya kai su boko sukayi boko gar suka Kai matakin da suke ayanzu...
Alhaji Amiru yanada mata biyu hajia Bilkisu. Tanada yara hudu. Hadiyya, Hattuna, Ilham, da Kuma rabia.. sai daya matarsa hajia rumanah tanada yara uku. Rumaisa, Hadiza, da kuma Hammad..
Alhaji uzairu yanada mata uku.. hajia ladi tanada yara hudu Yasmin, tasnim, eeman da Kuma Aysha. Sai hajia karama tanada yara uku. Haifa, Saleema, sadiya. Sai Kuma hajiya zaytunah tanada yara biyu. Zainab da Kuma Muhammd...
Sai kanwar su hajia habiba tanada Yara biyu. Umar da Ayaan. Sai Kuma hajia Layla bata taba haihuwa ba...
Alhamdulillah duka wannan zuriyah. Zuriyar alhaji Muhammad ne marigayi mahaifin su alhaji uzairu. Gashi suma har sun hayayyafa sunyi zuriyah...
××××××
To haka zaman ya kasance...hajia zaytunah ta zama tamkar KIBIYAR AJALIn datake tarwatsa duk wasu sharrin masu sharri da mugayen halayen su...
......
Rannan...bayan ta gama yiwa baby Muhammd wanka. Ta samu kantada shirya shi. Ta Saba shi a baya. Ta shirya baby Zainab. Ta diba musu kaya a yar jakar su .
Ta ajiye wayar da alhaji uzairu ya saya Mata sabuwa kwanaki. Ta zare mukullin sashen da take ta ta ajiye akan gado tare da wayar..
Ta rike hannun Zainab. Ta zura hijabinta ta fice daga gidan, ba kowa a babban tsakar gidan. Sai Mai aikin da tace mata
"Hajia fita zaki?"
"Eh"
"Sai kin dawo"
Ina bata samu damar amsa Mai aikin bama. Ta fuce da sauri. Tayita nausawa. Ta samu kanta da zuwa tasha. Ina zataje oho? Ta manta ma inda zataje ..
Anata lodin mota itama ta shiga. Allah yaso da da yan kudi a hannun ta. Tashiga mota ta zauna..motar ta gama lodi, suka dau hanya...
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/22, 11:05 PM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_57_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Kwandastan ya gyara zamansa akan maneji yana kirga yan cannin hannunsa yana hadasu. Ya daga muryarsa ya kwarara kara yace,
"Na baya ku harhado naku.. ku hado kudaden ku"cewar kwandastan motar..
"Baba dan Allah nawane kudin motar Ina Kuma zamu?"hajia zaytunah ta tanbayi wata yar tsohuwa dake kusa da ita tanata cin goro..
Tsohuwar ta dubeta sosai ta mayar da kanta kan goran da take ci kafin tache,
"Bakisan inda zaki je ba kika hau mota baiwar Allah?"
"Wallahi bansani ba" hajia zaytunah ta amsa ta cikin karshen gaskiyar ta.
Tsohuwar ta dubeta sosai. Sai Kuma tace
"Burnin Noka...kudin mota Kuma dubu uku ne "
"Ku kawo naku nan..." Kwandastan ya zura hannunsa saitin su hajia Zaytunah
"Ni sai munje Tasha... Zaazo abaka" tsohuwar ta fada tana mayarda kanta kan window
Kwandastan yaja mugun tsaki yana buga jikin motar,
"Karki renamana hankali mana iya. Ya za'ai kice wani sai anje zaa bada kudin Mota. Aina aka taba haka? Kawai zaki shafemu ne ki arwace.. "
"Allah ba shirya zance nake ba. Yaro kasan wacece ni?"
"Waceece kuwa ke Banda tsohuwar data shigo mota batada kudin motar. Tsaya na nan mu sauke gyatumar nan" ya fada yana tabo kafadar direban
Direban ya bude baki zaiyi magana. Zaytunah ta Miko dubu shida da sauri,
"Gashi ni da ita"
Duk yan motar suka juya duna dubanta . Tsohuwar ma ta dubeta sosai tace,
"Kinsanni ne kika biyamun kudin mota yar nan?"
"Baba ai kowa zai iya tsintar kansa ahalin da kika shiga. Fata dai Allah ya saukemu alfiya"
"Aameen Yaa rabbu nagode miki idan Allah ya yarda bazaki taba Dana sanin wannan abun alkhairi dakikai mun ba... Daga Ina kike baiwar Allah? Wacece Kuma ke? Ya kuma sunan waɗannan jikokin nawa?"
Hajia zaytunah tayii shiru. Dan hawayen da take rikewa ta zubo dashi tache,
"Bansan inda zani ba iya .. ahalin yanzu Kuma bansan wacece ni bama. Ga SIRRINa a dankare a KIRJI na Amma na Gaza furta komai."
Tsohuwar tayi shiru can ta nisa kafin tache
"Kinyi gaskia .. KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA ne) waɗannan SIRRIKA naki ki bar su a KIRJIN ki. Idan da Rai da rabo. Allah zai bayyana gaskia. Domin komai nisan dare gari zai waye. Allah zai bayyana gaskiar komai ya ta....Rike SIRRI yana da matukar muhimmanci a Musulunci, domin yana daga cikin halayen kirki da aka kwadaitar da su. Addinin Musulunci ya bayar da muhimmanci sosai wajen rike SIRRIN mutum da na wasu, saboda yana da alaka da gaskiya, amana, da kare mutunci, Rike Sirri Alama ce ta amana da Mutunci
"Manzon Allah (SAW) ya ce: "idan mutum ya fada maka magana kuma ya kalle ka, to wannan magana amana ce." (Abu Dawud)
Wannan yana nuna cewa rike SIRRIN wani yana daga cikin abubuwan da ke nuna amana, domin amana tana daga cikin siffofin mumini nagari.Rike sirri yana kare mutuncin wanda ya fada maka sirrin., yana tabbatar da cewa kai mutum ne mai amana wanda ake iya dogaro da shi....yake baiwar Allah, musulunci ya yi hani da tonon asirin wani ko bayyana SIRRIN mutane da zai iya bata musu suna ko jawo musu kunya. Allah ya ce:
"Kada ku yi leken asiri, kuma kada ku bata wa juna suna." (Suratul Hujurat: 12). Karki ji komai, Wanda ya rike sirrin wani zai sami kariya daga Allah a lokacin da yake bukatar taimako. Don haka karki damu da komai, Bayyana SIRRIN ba tare da izini ba na iya haifar da matsaloli, fitina, ko keta hakkoki. Musulunci ya yi hani da abin da zai kawo barna tsakanin mutane. Don haka, Allah Ya ba mu ikon zama masu rike amana da SIRRI acikin hikima da tausayi. Allah ya miki albarka ya raya miki zuriah .. ni nasan inda zanje. Idan Kuma har kin aminta dani zan je dake inda nake ki zauna Dani har sanda Allah zai yanke komai kinji?"
"Inshaa Allah.... Nagode kwarai Allah ya Saka miki da alkhairi...zamu iya kiran yarinyar nan da NABEEHA.. yaron Kuma sunan sa Hammad"
"Mashaa Allahu. Allah ya raya mana NABEEHA da Hammad. Irin sunanki irin kyawun ki tubarkallah NABEEHA... Take naji kaunar ki tashiga Raina..itada Dan kannin nata Hammad."
Hajia zaytunah tayi murmushi. Tanaji Wata nutsuwa ta dabaibayeta, ta wannan tsohuwar har takejinta tamkar ta santa..
"Sunana Hafsatu zaki iya kirana da gwaggo... Gidan dazamuje gidan 'da na ne. Sannan banason ki nuna musu kedin babu sanayyaa a tsakanin mu kinji? "
"Toh gwaggo inshaa Allah. Nagode da kyautata warki gareni Allah yasaka miki da alkhairi "
"Toh aameen ya rabbii....godia ma tana gaba.. ban miki komai ba yanzu. Toh Wanne suna zan kiraki dashi yanzu Wanne zan dinga kiran ki?"
Hajia zaytunah ta sakeyin shiru. Can ta nisa tace,
"Sunana zaytunah... Sunana zaytunah.. Amman zaki iya kirana da kowane suna kike so gwaggo."
"Masha Allah sunan ki kenan na yanka? Shi kin tuna?"
"Eh"
"Mashaa Allahu zaytunah.. Allah ya sauke mu lafiya"
"Aameen"
Haka dai suka cigaba dazama. Hajia hafsat ta dauki baby Zainab wadda ta zama NABEEHA a yanzu ta Dora akan cinyarta ta riketa. Yayinda hajia zaytunaa kuma ta rike baby Muhammad.
A haka har Allah ya saukesu a burnin Noka..
*FEDERAL CAPITAL TERRITORY*
MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE:
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/22, 11:15 PM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_58_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Babban gidah ne Wanda ya amsa sunan gidah. Gidah ne Wanda kallo daya zakayi masa kasan gidane na masu farcinnan suna. Wato attajirai da suka shaki iskar kudi suka Kuma Tada Kai da ita.
Gida ne Wanda duk yanda alkalami zai bayyana muku adadin kyawunsa. To tabbas bakomai zai zayyana ba. Don kalamai sunyi kadan wajen bayyana muku tsaruwar sa. Haka baki yayi kadan wajen furta muku irin tasa kalar. Idanu ba yadda zasu fasalta muku gidan ku tabbatar
Gidah ne aljannar duniya. Kunsan Kuma dik abunda zaace dashi aljannar duniya. To yakai matukar kololuwa a kyau da ya wuce duk wani tunanin Mai tunani..
Gidah ne Wanda tun daga farkon titin layin sunan gidan yake arubace a wani tafkeken signboard an rubuta. Major general dawud mafia avenue..
Saanan tun daga farkon layin katangar gidan ta fara, dauke da wayar wuta Mai shocking... An zubawa katangar wayar shocking ta wuta. Data karfe. Gashi katangar doguwaa ce Mai matukar tsayi tamkar ta prison.
Ga shuke shuke nan tun daga wajen gidan zuwa cikin sa... Katotan mamakeken gate ne daya gaji da haduwa. Jijjigagge Wanda masubudewa sai sun hada da Nishi. Amman dakee na masu arziki ne. Gate din da remote yake amfani. Daka doso inde motar gidah ce zai bude da kansa. Idan Kuma bata gidan bace zai fara horn da kansa kamar mota. Sai a danna permit button sai ya bude da kansa.
Cameras ne samfurin cctv duk tundaga katangar farko zuwa karshe ta gidan. Ga wasu manyan street lights da suka haskake layin gaba daya sai kache a turai.
Layin kansa gidaje uku ne kawaii. Kuma gidan major general dawud ne na farko dayacinye kusan rabi da kwatan layin sai wasu manyan gidah suma guda biyu. Ko baa gaya maka ba kasan na masu kudine suma..
Ba abunda kakeji a layin sai kukan kanaru. Sai Kuma karar gen babba irin mikano achan achan dai lamarin baa magana. Masu gadin gidajen suna waje akan wata babbar tabarma gabansu kuwa dauke yake da mangal na wuta. Sun Dora katuwar butar shayi akai irin ta buzayen nan sai kofuna yan kanana a gefe. Jira suke ruwan ya tafasa su sauke shi..
Mai karatu kofar jikin gidan an rubuta masa wasu manyan rubutu na larabci.. na tsari adduoi ne da akayi su da wasu irin design Masha Allah na kariya..
Ga Kuma tankakemen wani signboard din an Saka kifiya wato arrow tana nuni da gidan.. an rubuta..
*MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE*
Kana shiga zaka tarar da wani katon kewayen gidan. Dake dauke da wawakeken wajen faka motoci. Idan kayi gaba Kuma wani katon wani wajen ne na volley ball wato ball din da ake cillawa a Raga.. kana gaba kadan Kuma wurine sosai an Saka grass carpet dauke da raga guda biyu wurin yin football ne wato kwallon kafa.
Daga can gefe Kuma wani wajen ne katoto. An rubuta gymnasium wurin motsa jiki ne. Babu irin injinan motsa jikin da babu. Cike yake da kayan aiki..
Can daga gefe Kuma wata kofa ce.. garden ne katoton waje ne. Bayan wajen akwai fulawoyi sosai mashaa Allah awajen da suka Kara kawata gidan sosai.
Can gaba kadan aciki Kuma akwai swimming pools har kashi biyu daya babba daya karami. Kana gaba kadan daya na Yara ne dayan Kuma na manya ne. Daga can ciki Kuma wata kofa ce daban an kewaye wajen da tsaunuka na waya. Kiwo ne awajen. Sanyiyoyi,raguna zomaye, akuyoyi, tunkiyoyi da kaji fal..
Sai Kuma wani bangaren daban babba shima. Islamiya ce da kayan karatu an zuba na ibadah... Akwai Kuma wawakeken masallaci shima da kofunan sa biyu daya awajen gidah daya ta ciki. .
Sai kuma wasu dakuna jere... Su Kuma na maaikatan gidan ne Maza. Daga can baya idan ka shiga babbar kofar itama wani sashen ne babba Masha Allahu...
Boy squatter ne.. Shima na baki ne gashinan a gyarre a Kuma tsare shima.
Da ka Dan matso gaba Kuma wani gidan me sosai sama da kasa. Na mazan gidan ne samari akayi musu shi. Duk kuwa da basu wani Kai girman da zasu ware waje ba. Kasancewar basu girma ba, Yara ne. Dubada inda iyayen sukema babban waje ne da ya isheshi su har yaran ya Kuma ma musu yawa. Amman duk da Hakan anwa yaran Maza bangaren su idan sun Kara tasa sosai..lamarin sai Wanda ya kalla kawai..
Sai Kuma main kofar babba da akayi kaman wani mini gate. Babbar kofa ce da zata sadaka da katafaren ainihin idan major general dawud yake da iyalansa. Gidah ne Wanda sai ka masa kallo sau nawa kana sumbatu saboda tsananin tsaruwar su..
Daga can gefe Kuma shima wnai flat ne gidah.. bungalow marar bene. Shi Kuma sashen masu aikine matan awadace Kuma a mutince. Don wani gidan zakaga maaikata mata baa dauke su da muhimmanci ba. Sai a basu daki a wajen gidan. Ko akai su kusada na na maaikatan Maza. Ko Kuma su zama dakunan sune afarko ainihin gidan yana ciki.
Amman waɗannan saboda Kara. Flat dinsu acikin bangaren su major gegenal yake daga farko. Sai kuna sashen babba wato main house. Main the main kenan...
Gidah ne 6d. Wato hawa uku... Ya hadu karshen haduwa. Tsayawa bayyanawa bata lokaci ne. Amman duk inda haduwa takai to wannan karshe ne. Kamar irin tsanukan hotels dinnan na burj arab dake daular larabawa ta Dubai. Saboda tsananin haduwar sa. Mai karatu harda lift agidan
Dakuna da faluka da bandakuna kacha kacha. Ma'ana akwai wadatar su sosai. Kitchen ma kala uku ne a sashen da stores biyu. Sannan abayan bangaren maaikatan matan ma akwai babban kitchen da ake girki. mashaa Allahu kawai zaace domin babu ce kawai babu agidan tubarkallah..
Major general dawud mafia.. babban maaikacine na khaki. Tsohon soja ne sosai. Kafin ma ya zama soja. Tare yake da iyayensa akasar waje suna united state of america. Acan ya girma sai daga bayan suka dawo kasar su. Ainda yayi aure yake Kuma zaune a babbar birnin dake kasar..
Babban soja ne dayakai matakin major general. Bayaga haka haka ya rike ministan tsaro na kasa, yayi jakada babba, sannan babban dan kasuwa ne Mai kudi sosai. Wanda yanada arziki dama tun kafin ya zama general na soja. Dubada tsananin tulin dukiyar da yake dashi.. shi yasa ake masa lakabi da "Mafia". Don shi kudaden salary na da da ake biya baya karba ca yayu atemakawa talakawa. Asibiti Kuma file dinsa yace aga talakawa. Maaikatan sa duk can suke zuwa. Ba karamin Mai kudi bane sosai... Allah ya masa arzikin da yana cikin jerin masu kudi na fadin nahiyar afirka Kai harda ketare...
Yanada mata daya da yara guda hudu mashaa Allah... Fawaaz ne na farko, Sai Hashim, Raudah da Kuma auta Humayrah.
Masha Allahu, dukkanin yaran ba wasu manya bane can. Dan babban dannasa yana matakin furamari ne Wanda shine babba yana primary 5 zai shiga jjs. Yayinda Hashim yake primary 3. Sai Raudah tana primary one. Sai auta humayrah bata shiga makaranta ba an dai kusa sakata...
××××××
Wata zungureriyar mota ce a parke a tashar tana tsaye. Baka sidin tinted glasses. Sai Nishi take. Hadaddiyar mota ce da zaka dauka wani gwamnan ne aciki ko shugaban kasa...
Gwaggo Hafsat ta fito daga cikin bus da hannun NABEEHA rike a cikin nata..yayinda hajia