zaytunah ke dauke da baby muhammad..
"Yauwa. Yazo da wuri kenan direban......' gwaggo ta fada
Ai kafin hajia zaytunah ta fada wani abun. Direban ya fito mota da sauri yana dunkule hannunsa yana dagawa gwaggo irin jinjina gareki dinnan yayi hanzarin karbar kayan hannunsu ya Saka a booth. Ya bude bayan motar ya durkusa. Cikeda ladabi da girmamawa yace,
"Barka da rana gwaggo.. kinzo kalau? Barka da rana ranki ya dade. Yar baby ya sunan ki?"....
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/23, 12:44 AM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_59_
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
Hajia zaytunah ta saki baki kafin tayi saurin rufewa. Don gaba daya sai ta nemi rudewa, ita dai tunda take bata taba ganin irin wannan motar ba. Tasan tabbas itama ta zauna agidan masu hannu da shuni. Tunda Mai gidanta yanada kudi. Kuma yan uwansa duk sunada hali suma. Kaf dangin su mijin maa ba fatarrarre sai dai na nesa.
"Alhamdulillah.... Harisu. Munzo kalau.. sunanta NABEEHA... Itama jikata ce"
Muryar gwaggo hafsat data amsa gaysuwar direban ce ta dawowa da hajia zaytunah tunanin data tafi tayi saurin amsa shi itama
"Alhamdulillah..."
"Ahh mashaa Allahu. Ai kuwaa ta debo kamanni dasu junior.. "
"Ai fawaz? Kai tafi shi kyau tubarkallah. Duk tafi su kyau harisu."
"Tohm Jine ne Kam. Amma ga kama nan"
Sukayi murmushi gaba daya. Harda hajia zaytunah da ta kara yaba kyautatawa da mutuncin irin na gwaggo hafsat...
Suka shiga motar atare. Gwaggo hafsat ta shiga owners corner . Sai hajia zaytunah data zagaya tashiga daya barin da harisu direba ya bude mata..
Malam harisu ya tashi motar yana karo sanyin ac.
"Hajia akara ko sanyin yayi haka?"
"Barshi haka. Ai saboda Yara ko?"
"Tohm.hajia"
Suka dau hanyar babbann titi. Hajia zaytunah sai kalle kallen titin takeyi tunda take bata taba zuwa nan haka ba. Bata ma taba tafiya Mai nisa ba inde ba kasar waje da sukaje kasa Mai tsarki ba... Amma futa tabar gari bata tabayi ba. Amman yanzu tasamu kanta da barin gidah ko waiwayen shii har abadah bataso..
"Harisu..." Gwaggo Hafsatu ta kira sunan direban
"Naam hajia?"
"Bakade sanar musu zanzo ba ko?"
"Ban fadaba hajia..."
"Yauwa saboda banason su sani... Sai dai su ganmu kwatsam"
Harisu yayi dariya yana murmushi yace,
"Toh Kuma hajia. Dan abinci da abubuwan motsa baki haka da baabu?"
"Kakka damu. Idan naje sayi. Kuma nasan ba zaa rasa abubuwa ba. Sannan banki basu tashi ba ko?"
"Basu tashi ba hajia. Sun dai kusa"
"Yauwa to akwai biro nan a hannun ka? "
"Yauwa nayi saa. Gashi kuwa"
Ya zaro biro a cikin Dan gidan motan nan na gaba ya mika mata... Gwaggo hafsat ta zura hannunta cikin riga. Tanada dan tofi aciki, wanda manya kan Saka goro ko kudi. Dan karamin littafi ta dakko. Da tanbarin giwa na bank ajiki..
Tayi rubuce rubucen da zatayi ta mikawa harisu. Ya karba yana zurawa a aljihunsa
"Check ne ko hajia?"
"Eh mana harisu... Tunda kasan ba yawo nake da kudi ba. Kudin da na rubuta idan suka baka. Yankan zaka dauka ka Sayo mana kaji gasassu. Ka yo order abinci na hotel dinnan. Sai ka hado da gasasshen kifi. Ka sayowa yarannan kayan wasa Dan Allah..."
"Ah gwaggo harda wahala?"
"Wahala? Dan nawa,Yaya da jikokina hidima shine wahala? Idan ma wahalar ce ataki hausar Wanda ni atawa hidima ce. Ai ke kika fara mun zaytunah. Allah dai ya miki albarka"
"Aameen... " suka amsa baki daya harda malam harisu. Dake lekensu ta mudubin gaba...
"Hajia na sawo yanzu ne ko sai dawo?"
"A'a harisu. Yadda mika gajin nan.... Ai mun gaji. Idan ka saukemu agidah sai kaje. Kakka dau lokaci Kuma dan Allah"
"Inshaa Allah hajjaju""
"Aamin. Ka dauki biyar Kai ma"
"Kai hajia. Wallahi wadanda kika bani wancen ma basu kare ba Allah kuwa"
"Ai badan sun kare na baka ba. "
"Nasani hajia. Wallahi hidimar yayi yawa. Baki gajiwa. Gidan marayun nanma wallahi bakiga godiyar da suke ba hajia. Sunata Allah ya shi miki albarka sunason su ga kyakkyawar fuskar dake dawaniya dasu. Hakama kauyen nan da akayiwa borehole da rijiyoyi da Kuma cikin gari da kika yiwa masallaci. Sunata godia. Hajia ki bari dan Allah suga fuskar ki"
Gwaggo Hafsatu tayi murmushi tana girgiza Kai tache,
"Allah ne ya azurta wasu suci ajikinn mu. Kuma ita dukiya ta Allah ce. Sannan duk Wanda yake kyauta don San asani batada maraba da riya ko riba. .. ka bada kyautada damanka hagunka bata sani ba haka ake fada. Ni nayi ne dan Allah. Badan su sanni ko Dan suga fuskata ba. Allah ya hadamu a ladan duka. Ya Kuma horewa kowa Amin"
"Aameen"
Hajia zaytunah ta fada. baki daya mamaki ma ya cikata ya gaurayeta. To ita wannan tsohuwar wacece ita? Gata da kyauta ? Amman yanda tayi kama a motar hayan nan Kai kache batada ko kwandala. Sannan inda kudi yayi batasan hanyar bama bare ilimi. Sai gashi tiryan tiryan harda rubutu na check din kudi. Lalle tsohuwace Mai ran karfe Mai kyautatawa da Kamala da Kuma dattako da mutintaka. Yanzu dubi batasanta ba Amma ta dauketa zata kaita gidan iyalanta.
Suka karasa unguwar suka shiga cikin layin, tun daga farkon layin zaytunah take leken window. Ji take tamkar kasar waje. Wani katon gidah da azatonta ma hotel ne Ashe shine inda suka dosa .
Gate din ya wangale da kansa. Motar ta kutsa Kai suka shiga. Zaytunah ta sake wangale baki tana duban ko'ina. Har sanda malam harisu ya karasa parking din motar awajen adana motoci..
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/23, 12:46 AM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_60_
Malam harisu ya fito da sauri ya bubbude musu kofar. Ya koma booth ya fito da kayan ciki...
Ai da sauri maaikatan gidan suka tattaso a sikwane. Suka daddauki kayan sunata zuba mata gaisuwa da kirari. Sai Kuma su juya su dubi zaytunah suna gaysheta itama tana gayshe da su..
Suka shiga damfareren gidan ta wata kofa da nakeda tabbacin babban sashe ne shima daban sama da kasa babu abunda babu kusan girma daya yake dana su major general dawud mafia. Malam harisu ya Saka mukulli ya bude maaikatan suka shiga da kayan
Matan suka shiga dakuna Dan fara gyaggyarawa. Da gani sun San aikin su
"A gyare koina.. sama da kasa" gwaggo hafsatu ta fada
"To ranki ya dadi" cewar wata maaikaciya. Duk sun Saka uniform da hula..
"A kira su hajia ne ?" Malam harisu ya tanbayi gwaggo hafsat
"No .. zamuje. Zaytunah zo muje ku gaysa da su ko"
"Tohm gwaggo"
Futa sukayi. Gwaggo hafsatu na gaba. Hajia zaytunah na biye da ita a baya. Ta wata kofar suka shiga cikin gidan.
Malam harisu ya Saka hannu yana knocking harda da danna door bell yana murmushi,
"Ko suna sama baaji"
"Kila" gwaggo hafsatu ta fada tana kamewa..
Ba jimawa kuwa wata maaikaciya tazo ta bude kofar. Tayi baya da sauri tana zubewa a kasa. Malam harisu yayi musu sallama kan ya tafi yaje aiken ya dawo..
"Sannu da zuwa hajia. Barka da rana kinzo lafiya?"
"Alhamdulillah karime...."
"Granny.... Granny" yaran suka taho da gudu su uku suka rungumeta..
Gwaggo hafsat ta rungume su itama tana shafa kansu daya bayan daya..
"Hmm.. Ina miskilin nan yana Ina Dan nema yanzu haka yana daki ko?"
"Tun dazu ya shiga daki yace kar Wanda ya tashe shi"
"Kai wannan yaro. Allah ya kawo ranar da Zai koyi zama cikin mutane. Kankaninsa dashi sai miskilanci. "
Tana rufe bakinta. Hajia Hawwah ta sakko daga kafar bene sanye cikin doguwar riga ta leshi tasha stones .
Ta durkusa har kasa tana kama hannun Kujera,
"Gwaggo sannu da zuwa. Barka da rana... "
"Yauwa barkan mu. Zagayo ki zauna mana zaytunah. Zo nan NABEEHA. " Gwaggo hafsat ta fada tana riko NABEEHA ta zaunar daita akan cinyarta. Haka kawai Allah ya dora mata San yarinyar sosai...
"Ina wuni hajia?" Hajia zaytunah ta gayshe da hajia hawwah dake binta da kallon rashin sani
"Lafiya Alhamdulillah. Kai Dan samari kana hannu?" Hajia Hauwa ta amsa tana tsokanar baby Muhammad dake hannun hajia zaytunah
"Hammad.... Tundai dazu da yayi dan kukansa. Bashida rigima Maijidda. wannan sunanta hajia zaytunah... Ya take awajen na. Waɗannan Kuma jikoki nane na wurinta. NABEEHA da hammad. "
"Allah sarki... Sai dai bansan su ba" hajia hawwah ta karasa fada tana mutstsika hannuwa.
Gwaggo Hafsatu ta mike kafafu tana kallon hajia hawwa tache,
"Ya tace kamar yadda na fada da Hausa. Waɗannan jikokin nawane. Na gaya miki sunayen suma duka. Sannan zasu zauna nan waje na. Har lokacin da zamu kammala abubuwan da muke yi da ita. Ta iya yiwuwa nan kusa ko nan da wasu shekaru ko illa Masha Allah ma. Daga yau banason a dauketa a matsayin bakuwa. Ko wata daban. Yar gidah ce kaman kowa itama. Sannan maaikatan nan tanada hakki akan kowanne. Zata sashi aiki da sauran su"
Hajia hauwa ta kada Kai. To me zatace sirikarta, uwar masu gidan ta Kara maimaita kusantakar matar awajen ta da muhimmancin su. .Duk yadda akayi babbar bakuwa ce ma'ana yan uwan juna ne na kusa. Gashi ba alamar yar kauye ce. Don kayan jikinta kadai zai sanar maka tafuto daga babban gidah itama. Don haka hajia hauwa tayi hanzarin cewa,
"Inshaa Allah ba matsala gwaggo. Sai dai baa Fadi zuwan ku ba baai muku wani abun na munsamman ba ... Sai dai yanzu a Dora idan akwai abunda kikeso. Already dai akwai abinci sai Kuma pepper soup na kaji... "
"Ba damuwa harisu na aikeshi ya kawo. Amma kafin ya dawo azubowa zaytunah da NABEEHA... "
"Toh shikenan gwaggo.. "
"Ki kira mun sarkin sarakan miskilanci. Nan ko ki Kai masa gaisuwata kice nache ransa ya dade"
Hajia Hauwa tayi murmushi tana rufe baki,
"Ah kunfi kusa hajia da dan gidan naki. Shine fa na gaban goshin ki.. bari na kira shi ai baaji kanku ba. Baisan kinzo ba. Yana daki"
"Ai wannan koyasan nazo ba zuwa zaiyi ba.. tunda shi halayansa daban dana sauran.. zo nan Hashim ga kanwa namu ku. Kai da Raudah da Kuma humayrah ita kaman zasuyi sa'anni ma ko"..
"Eh zasuyi Kam Masha Allah . NABEEHA ga kawa na miki humayrah. Humayrah zo ga Kawa"
Yaran din suka nufi wajen NABEEHA. Dake tanason Yara ta mike da sauri daga cinyar gwaggo Hafsatu ta nufi wajen su humayrahh suka fara wasa..
Nan da nan saiga maaikatan sunata ajiye kulolin abinci da tray dauke da ruwa da kofuna da lemuka, Can sai ga saukar wani yaro ya dara suaran yaran da alama shine babban su .
Yana tafe tamkar wani matashin saurayi. Yanada tsayi . Ya Tara gashi. Hannuwansa acikin aljihu. Kaikache wani saurayi ne..
Ganin mutanen da yawa, zai juya da sauri. Gwaggo Hafsatu ta kira sunansa da karfi,
"Zo nan fawaz"
Ba shiri ya juya yana sosa keyarsaa. Ya karasa kusa da gwaggon kansa akasa ya durkusa tamkar wani babba,
"Gwaggo sannu Da zuwa. Barka da rana! Ya hanya?"
"Alhamdulillah...."
"Barka da rana.. Ina wuni?" Ya juya yana gayshe da hajia zaytunah
"Lafiya kalau Alhamdulillahi" hajia zaytunah ta amsa shi
"Alhamdulillah sarkin miskilai sai danasa aka kirawo ka zaka sakko kenan ko? To ranka ya dade ga irin taku" Tayi masa jinjina da hannu tana murmushi
"Tuba nake gwaggo wane mutum"
"Ga Babar ku zaytunah. Ga kannen kunan. Hammad, Sai macen Kuma NABEEHA "
"NABEEHA..." Ya maimaita kasan zuciyarsa yana duban yarinyar yana dauke kansa da sauri
"Okay. Masha Allah" ya fada yana lankwasa hannuwansa .
"Eh samu wuri ka zauna"
Ya shafa keyarsa yana kallon bene yace
"Ina assignment ne gwaggo"
"Hakafa, Tashi ka tafi. Dan sarkin rashin son surutu..."
Bai ce komai ba yayi shiru yana mayar da kansa kan tv. Dama tasan ba magana zaiyi ba. Da aka samu ma yayi yar doguwar hira bai yi shirun nasa ya bata kunya agaban mutanen ba..
"Je ka"
Mikewa yayi ya haye sama da sauri..gwaggo Hafsatu ta girgiza Kai kawai .
Ba dadewa bayan gwaggo hafsat ta Saka maaikatan sunyi serving nasu abinci. Sai ga malama harisu ya dawo ya Sayo komai..
Gwaggo tasaka ya shigo dasu . Aka zuzzubawa zaytunah komai da sauran yaran suna dan cin abincin gwaggo sai Janta take da hira. Zaytunah tana kokarin biye mata..
Suna nan zaune har suka kammala sukayi sallah. Sai kuma suka dunguma suka koma sashen gwaggo hafsatun...
Ba dadewa Kuma bayan magriba. Sai ga dawowar major general dawud. Aka sanar masa zuwan gwaggon sa. Wajenta ya wuce ya kwashi gaisuwa. Take sheda masa ga zaytunah yar uwarsu. Bazai iya ja da zancen gwaggo ba don kilan yar uwace dake wani garin ko Dan haka shima ya saki jiki suka gaysa da hajia zaytunah tamkar sun San juna, Ya jima wajensu. Don Anan yaci abinci. Yaje yayi ishai anan masallacin dake cikin gidan daganan ya koma suka cigaba da gwaggo bashi yabar sashen gwaggo ba Saida yaga tana hamma zatayi bacci...
Gwaggo tace Wa hajia zaytunah taje sama ta biyu su zauna ko na ukun din Wanda ta zaba. Dakuna uku ne da parluna biyu kowanne kuma an saka masa kaya. Gwaggon tana kasa saboda ciwon kafa. Lamarin dai gwanin ban shaawa wallahi..
DUK yarda hajia zaytunah taso ta sanarwa gwaggo hafsatu wani abun daga labarunta. Gwaggon tache mata ta dakata ba yanzu ba tukun. Zata tanbayeta tane lokacin da ita taga ya dace awajenta ita gwaggon.
×××
Sannu ahankali haka rayuwar ta cigaba da garawa mashaa Allah.. aka sanya NABEEHA a makarantar su Raudah itada humayrah.
Yayinda fawaz ya kare primary Kuma. Mahaifinshi ya duake shi bisaga yarjewar gwaggo hafsatu. Aka kaishi army school dake united state of America tunda citizen ne shi na can...
Gidan ya zama sai su gwaggo sai su Raudah da Hashim da su NABEEHA da baby hammad. Suna zaune cikin lumana da kaunar juna da kwanciyar hankali.......
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACCOUNT NAME/SUNAN DAKE ASUSUN BANKI: MARYAM SANI GUMMI*
[1/23, 12:47 AM] Hafsaat🧕💞: *KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_PAGE:61_*
🎗️°🎗️°🎗️°🎗️°🎗️
*ALH UZAIRU MUHAMMD RES..*
Duka zazzaune suke a parlor. Alhaji uzairu har wani rama yayi tamkar Wanda yayi shekaru a kwance.. ya rame ya jemee tamkar an canza masa hallitta . Yayi kamar bashi ba.
Mahaifiyar su hajia zainab tana zaune itama akan doguwar kujera Mai cin mutane uku daga gefenta a kasa alhaji Amiru ne a zaune ya zabga tagumin shima..
Sai hajia rumanah dake gefe a zaune itada hajia ladi da hajia karama da hajia bilkisu..
"Kuma ko'ina an sake bincikawa ko? Oh hukumullahi min zalika. Wannan abu da daure Kai yake" hajia zainab tafada tana sauke ajiyar zuciya..
Alhaji Amiru ya nisa shima kafin yace
"Ko'ina gwaggo. Dik wasu kakafe na sadarwa na zumunta. Da gidajen talabijin Dana rediyo da newspapers duk an faffada. Kuma lokaci sai Kara ja yake amman ba wata magana mai kyau."
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun..gwaggo ya zanyi da raina? Zaytunah Amana ce agareni gwaggo, batada kowa. Ga yaran nan gwaggo. Duka duka nawa suke? Abu tamkar almara. Gwaggo zaytunah tamun nisa. Na rasa zaytunah gwaggo. Na shiga uku"
Hajia zainab tayi shiru can ta sauke ajiyar zuciya. Cikin muryar ban lallashi tache
"Kayi hakuri uzairu. Inshaa Allahu za agan su cikin koshin lafiya"
"Toh gwaggo yaushe? Gashi kwanaki suna ta tafiya?"
"Inshaa Allah nan kusa. Da yardar Allah duk ainda suke fatana sun fada hannun nagari. Cikin koshin lafiya . Allah yasa arike su da aminci Allahumma Ameenn ALLAH Kuma yasa munada rabon ganawa..Rabbu ya bayyana su. Rabbi ya bayyana su. Rabbi ya bayyana su"
"Allahumma Aameen" suka hada baki.
Banda su hajia rumanah da sukayi amin din kasan makoshi Kuma bata Kai zuciya ba..
"A cigaba da cigitawar Amiru kar a yi shiru. Acigaba sannu ahankali sai kaga Allah ya nufa"
"Inshaa Allah Rabbi. Kaf garin nan dai astagfirullah lungu da sako ko'ina an dudduba. Har cikin dajika masu farin kaya sun cigita mana"
"Toh inshaa Allah khair. Allah ya amince mana yasa adace. Kuma dai ba hannun miyagun nan bane da tuni sun kira waya suna neman wani abu. Sannan Kuma ba wai cikin gidah akazo aka dauke su ba. Wai futa tayi. Kai innalillahi Wa inna ilaihi rajiun"
"Wallahi shine abunda yafi dagamun hankali gwaggo. Rashin masaniyar ahalin da suke ciki. Suna Raye a'a suna mace ba Wanda ya sani gwaggo. Idan ma basa Raye gwara asanar mun na sani. Amman Shirun nan gwaggo Shirun nan yana bani tsoro"
"Inshaa Allahu sun fada hannun nagari. Da yardar Allah Kuma suna cikin koshin lafiya. Inshaa Allah Kuma zasu waiwayi gidah"
DUK sukayi shiru,Tamkar ruwa ya cinye su. Gidan Baki daya kullum da kaje kamar anyi mutuwa.. ba wasa ba dariya ba wata walwala musanman awajen alhaji uzairu. Sam ya rasa kuzari da nutsuwar sa. Shi dai yana rayuwa ne kawai gashinan ...
"Inaso nayi magana ma da major general. Amman samun sane baayi sosai. Yana ma amurka ance. "
"Wa kenan dawud mafia?"
"Eh shi.. kasan manyan mutanen nan"
"Kai rabu dashi. Shi dama rayuwar sa rabi awaje yayita. So yanzun ma Ina tunanin so yake ya tattara ya tafi. "
"Eh Amma idan ya Saka baki a maganar nan Ina tunanin zaa iya dacewa. Nasa na kusa dashi