KIRJIN MAI HANKALI BOOK COMPELET PDF 1 BY MX.txt

Author :  ms xoxo Category :  Arewa Pen

Chapter   11 / 34

30K to 33K   out of 102K words

ji kake timm......
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: 37...


Malam Nata'ala ya doka tsawa,

"Kai mu gangara can"

Matan suka dare suka bashi wuri. Ya ke tare ya wuce cikin dakin na ciki kuma suka futo waje. Bai wata wata ba ya sanya hannu ya dauke fuskar gwaggo haire da mari tas Zatayi magana Ya sake daga hannu ya dauketa da wani marin.

"Nata'ala...k

Ai bata karasa ba ya sake zuba mata wasu gigitattu har uku... Yana ajiye hannunsa yalwaji tace,

"Kuma malam kar na katse ka sai yanzun ta saki wuyan rigar abule. Dakyar ta ringa kakarin mutuwa saboda numfashinta baya fita. Haire ba karamin riko ta mata ba. Saboda yarinyar nan zaytunah tazo tana rokon ta sakar mata mahaifiya bayan batada lafiya. Shine ta keta dirkata da kasa. Karo na biyu kenan"

Malam Nata'ala ya girgiza kansa cikeda takaici Ya dubi gwaggo haire daketa faman huci kaman zakanya yana karkada hannu yace

"Metayi miki? Me sukayi miki? Me suka tsare miki? Tunda halinki ne kin Saba. Saboda Allah ba zaki iya dannewa koma menene ba ki bari na karaso gidah idan da wani abunne babba! A bainar jamaa. Ranar da ake farin ciki ana wasa da dariya kika rikida ranar ta koma ta bakin ciki ta zubar da hawaye. Saboda Allah akan abunda bai Kai ya kawo ba? Akan wane dalilin zaki dau mataki da hannun ki? Ina ruwanki ki?"

"Saboda na Isa ne na dauka ko kana nufin ban Isa ba. Ko zaka nunamun isata ne ai ba yau ka fara ba sullutun kawai

Daga hannu yayi ya sanya yatsan sa saitin fuskarta yana karkadawa na kashedi,

"Kinga haire kinga ki ji tsoron duniya. Ki kuka da kan ki. Kuma naji na amince abunda kike son na fada zan fada ni tunda naga ke kin cire rigar mutinci data zumunci kin ajiye agefe, matan nan duk ba bare bane. Domin duk Wanda aka gayyata an san su. Kai Wanda ma bai sani ba gara ya sani din. Waɗannan Yara kamar yadda kikace din na Isa dasu ne, na Isa,,’yaya na ne daya yar ciki nace rumanah daya yar kanina ce itama yata ce....ba yayan ki bane. Ki rubuta ki ajiye. DUK abunda kike son sani zaki sani, aure ne an daura babu fasawa, sai kibi limamin da waliyyan da sukayi kuskuren ki dakesu"

"Yo ai ba yin Kansu bane, asiri ne. Na subutar baki. Ai ba yau suka fara daura aure ba ehe"

"Dadi na dake kwakwalwar kifi ce dake wallahi. Allah wadaran naka ya lalace wallahi Sam albasa batai halin ruwa ba. Tir da halayen ki munana haire. Bantaba Dana sanin kasancewar ki yar uwataba irin yau wallahil azim"

"Ba lefinka bane An wanke an baka kasha ne Kai ma shiyasa kake fadar haka. "

"Mtcwww Shashasha sakarai, wadda addini bai isheta ba Kije ki cigaba da bin sakararru kina kin yarda da hukuncin da Allah ya zartar. Wannan aure Allah ne ya hada ya Kuma aura ba mutum ba. Daga samun auren har maganar auren ya zuwa kawo kayan auren da daurin auren. Kai tundaga kawo yaran ma sukayi karatu daga birni zuwa nan marayar bokezuwa aure ne dai ba zaa warware shi ba. Ince dai yar da akai auren da kike wannan hura hancin kike fiffika kamar tantafara ince yata ce bataki ba?"

Gwaggo haire tayi shiru tana wulwulga idanuwa, malam Nata'ala ya daka mata tsawa,

"Yata ce ko yarki ce?"

"Yar kace"

"Toh alhamdulillahi tunda yata ce. Don da ban bada auren ba ma ba zaa daura ba. Idan nace ni yau naji na amince ma rumanah ba zatai aure ba wallahi ta zauna. Don mahaifinta ne ni. Ko ince ga Wanda naga damar aura mata wallahi ta zauna kenan babu Wanda ya Isa ya canza Tunda nine mahaifinta nine dolenta, Baki Isa ki tsayar da abunda zai wakana ba. Bare ke Karan kada miya da har zaki kokarin ja da ikon Allah, Tirr da halin ki aure ne dai babu fashi an daura kenan Kuma ya dauru Kafin ma na amince mahaifin shi yaron daya auri zaytunah din shi ya fara cewa abari hakanan ai duk aure ne yaji ya amince dansa ya zauna da wadda aka aura masa wato rumanah... Kafin ma mahaifin shi uzairu ya amince. Sannan waliyyai sukace suma sun amince kana ni ma na amince. Don haka aure ya dauru da iznin Allah Kuma mutuwa ce zata rabasu . Rumanah sun daura auren ta da Amiru da yardar Allah mutuwa ce zata raba su. Haka zaytunah an daura aurenta uzairu mutuwa ce zata raba su da yardar Allah.............
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _38..._

Gwaggo haire ta fashe da kuka tana nuna kanta da yatsanta

"Nata'ala ni kake Wa gori ko? Ni kakewa gori a bainar jamaa? kake fadawa maganganu haka akan zaytunah?"

"Kina bani mamaki haire wallahi, gori ? Fadar maganganu a bainar jamaa? Sannan akan zaytunah wato zaytunah ba wata aba ba ko? Ni bansan rashin basira ne ko rashin tunani da sanin yakamata ne yake damun ki ba. Na kasa ganewa, Amma ya kamata ace waɗannan abubuwan duk kin wuce su,Idan ma magana zaki gayawa mutum ya kasance wadda take Mai hankali Wanda idan wani yaji ma zaiyi duba na tsanaki sannan. Da fari kince wai nayi miki gori.wanene ya janyo akayi masa gorin. Sannan gorin me nayi miki?Yadda kike nuna banbanci da son zartar da hukunci a hannun kine ya wuce mizanin hankali,abu na biyu..a bainar jamaar ke kika jawo fadan nan. Da ace baki kawo shiba Da duk haka bata faru ba,Tun awajen gangare ake tarata ana gayamun abunda yake wakana agidannan,Tun daga hayin rigau ake jiyo kurarin maganganun ki kefa macece Sam bakida SIRRI bakuma ki iya magana ba,Mata da aka sansu da tausasa harshe da iya magana Amman ke haka kawai baki tambayi ba’asi ba baki nemi Karin bayani ba kin dau hukunci kin yanke da hannun ki kawai saboda Neman bala’i irin naki. Zaytunah Kuma idan mantawa kike bari na tuna miki, da rumanah da zaytunah duk Yaya ne awajen ki,Yadda rumanah take awajen ki haka zaytunah take awajen ki Babu Wanda yafi wani acikin su awurin ki sai wata kaida ta daban da kika dauka kika aza abirnin zuciyar ki. Mahaifin yarinyar nan uwar ku daya uban ku daya dukan mu tsatso daya ne ya samo su. Da ni da ke da shi mu uku Allah ya albarkaci iyayen mu da su. Amman kike nuna ba haka ba..kike kyamatar iyalan sa. Sannan wace irin musiba ce? Dan Allah ku temaka mun akama yarinyar nan akaita asibiti. "

Ya karasa fada yana duban zaytunah da yalwaji ta rikota tana rungumar tah.

"Cigaba da mun gori... Saboda bani da 'ya mace. Ai Allah ne ya kadarta Hakan"

"To kaji wata magana ta daban. Waye yake miki gori saboda baki haifi ya mace ba? Ba Allah ne me bayarwa ba? Da matan da mazan ai duk daya ne. A wannan zamanin ma anfi kaunar samun albarkar mazan ma. Don haka wannan zance naki Neman magana ne kawai."

"Malam akwai abun Hawa ne?"cewar yalwaji

"Eh akwai mutane waje saboda Halliru ma naga hayis dinsa a kofar gidan nan. Sai muje duka Ku dakkota Ubangiji Allah yasa bataji wani raunin ba na daban aciki Kai ko jikin ma bashi da dadi. Allah ya kiyaye ya tsare gaba."

"Aameen " matan wajen suka hada baki wajen amsa addu‘oinsa

"Kuyi hakuri fa,dan Allah hankali na ne a tashe wallahi. Inata zantuka, kuyi hakuri. Mungode fa Allah ya Saka da alkhairi ga duk wadanda suka halarci wannan Taron biki, Allah ya mayar daku gidajen ku, unguwannin ku, garin ku lafiya. Allah Kuma ya kawo na yan gaba Su Kuma Allah ya saka musu alkhairi a auren su. Wadanda suka fito Allah ya basu nagari. Na ciki Allah ya zaunar dasu agidan su lafiya Komai ya wuce Dan Allah. Acigaba da hidimar biki kamar yadda aka fara. Akwai sauran abinci da dangin ango suka kawo na walimar daurin aure. Yayi ragowa,Zaa aiko dashi sai ku rarraba ko gidah ne kwa tafi dashi. Allah yasakawa kowa da alkhairi. Yadda kuke kokari da tsayin daka akan hidindimu dakan taso na wanna maraya tamu Allah ya biyaku da aljanna ya biya bukatu "

"Aameen .. Yaa Rabb. Mungode malam "Matan suka hada baki wajen amsa shi.

Aka dauki zaytunah aka kaita cikin mota, sai wayyo Allah na takeyi Suka shiga mota suka tafi...Yan biki sai tu'ajjabi akeyi kowa jikinsa a sanyaye…..
[12/2/2024, 1:32 PM] Hafsaat🧕💞: _39..._

_MAWII AVENUE..._


Hajia zaytunah tanata tunanin shekarun baya da suka shude.. Ta juya nan ta juya can.Tashiga salati tanayi tanayi dakyar Bacci ya dauke ta kanta na mata azabar ciwo tamkar zai fadi kasa...

Tana cikin baccin ta da Allah ya temaka ya dauketa dakyar. Sai shaaaa kamar a mafarki Irin ana zuba maka ruwan nan ta farka gigice tana salati.

Tsaye suke akanta. Wannan da bokiti na roba waccan da katuwar buta kowacce cike da ruwa Sai da suka juye shi tas a kanta.

"Innalillahi Wa inna ilaihir rajiun..." ta fada tana kokarin mikewa tsaye.

"Eh zaki abunda ya fi salati ma. Wato saboda tsananin iskanci da tsantsar wulakanci sarai kinsan Yara ga lokacin da suke zuwa makaranta ba sai an gaya miki ba Ki tashi ki shirya su ki dafa musu abunda zasu Saka a lunch boxes dinsu Amma baki tashi ba,Saboda tsabar renin hankali zaki zauna kina bacci mtcww" cewar hajiya Ladii kishiyar ta..

"Rabu da malalaciya, Yar renin hankali kawai. Kasa uwar bacci.."

Da sauri hajiya zaytunah ta mike jikinta sai rawa yake. Ga sanyin gari ga jikon da kayanta sukayi lunqum da ruwa..


"Kuyi hakuri.... Dan Allah"

"Kiji fa Yaya wai muyi hakuri"

"Zaki wuce kije ki karasa aiyukan da baki ba ko Sai ranki ya baci?"

"Zanje... Zanje Ina zuwa gani nan"

"Minti biyar idan kika Dara haka zaki Sha mamaki"

"Sai kache mayya Mtcwww"

Fita sukayi daga dakin bayan sun gama gasa Mata maganganu.

Jikinta na bari ta sanya bayan hannunta tana katse hawayen da ke sharara daga fuskar ta. Har wani rawar dari take saboda tsananin sanyin dake dukanta.

Ta yaye zanin gadon da suka jikata dashi,Ta futa tsakar gidah ta shanya shi

Ta koma daki ta dauki katifar dakyar ta futar da ita can wajen corridor inda akwai winduna da iska ke shiga sosai ta jingina ta awajen saboda ta bushe.

Ta koma ta dakko mopper ta goge ruwan wajen ta tsane sannan ta shanya ta.

Bandaki ta shige da sauri ta dauraye bakinta tayi brush Ta zame kayanta ta cire. Ta dauki wata riga ta Saka ta daura dankwali ta zura hijabi tanata sauri karta gota lokacin da aka bata ta fita..

Kanta a kasa ta nufi babban parlour gidan inda Mai gidan nasu yake zama safe da daddaren Kuma yakara parlor a sashen sa daban. Amma wannan anan yake zama yayi Karin kumallo,Ko ya zauna da iyalansa su gaysa.

"Barka da safiya... An tashi lafiya?" Kanta a kasa ta durkusa ta gayshe da Mai gidan nasu

"Alhamdulillah..... Meya hadaki da su Ladi? Kinga zaytunah banason waɗannan hakayen naki Shekara da shekaru kin kasa denawa ya ilahi kullum abu daya ? Ke kenan kowa yayi Kuka da ke saboda wani kuduri na daban da kika sanya a zuciyar ki? Wanne irin banzan hali ne dake?"

Sadda kanta tayi a kasa. Yau Kuma wane tuggun suka hada mata? ta runtse idanunta Hawaye na zuba daga idanunta Batace komai ba tayi shiru.

Hajiya ladi na gefensa dake kujera ce Me cin mutum uku wato three seater ce ta kada Kai tana duban Mai gidan nasu tache,

"Abinci gashi nan kana gani.... Foodflask har biyu ana buga dakinta ana Kai mata taki budewa bare tayi magana a Saka ran zata ci? Duk abunda zamuyi mata agidan nan bama burgeta,Yanzu ma ni da aunty karama sai da mukaje dakin nata muga ko lafiya saboda bamuga ta tashi ba tin dazun ta dan Saka abu acikin ta..... "

"Yaya... Yaya zaytunah. Kici abincin kinji?"cewar hajia karama cikin kissa da makirci

Hajiya zaytunah ji take inama ta rufe idanu ta bude taga komai mafarki ne kawai. Ace tana bokezuwa duk waɗannan abubuwan basu faru ba,Tunda take bata taba ganin masu tuggu da munafurci irin abokan zamanta ba da suka hade mata Kai suke cin xarafinta suna hadata da mijinta da yan uwan sa da danginsa Ba inda ta tsira.

"Suna magana kinyi shiru. Saboda kawai renin hankali zaytunah? Shikenan tunda wannan halayen naki marasa kyau ba zaki dena su ba,likita zai zo anjima zai miki ragowar allurori da magunguna ... Matsa na wuce"

Alhaji uzairu ya fada Wa hajiya zaytunah data zauna a gefen kujerar sa dayake a zaune daga kasa

"A.... Alha....alhaji.." ta kira sunansa dakyar a rarrabe kamar Mai koyan magana.

"Ya akai?" Ya tambayeta Hadi da juyawa yana dubanta.

Batace komai ba sai ma mayar da kanta tayi kasa. Yaja dogon tsaki yana duban hajia ladi yache,

"Maganar ma‘aikata masu girki. Har yanzu ba‘a samu ba ta yarda..ku kukeyi?"

"Mu mukeyi. Nayi da safe da rana, aunty karama tayi da daddare tayi abincin ka.sai zaytunah Da asubah Kuma muna tashi ni da ita muyiwa Yara abun kumallo. "

"Har yanzu zaytunah bata Saka hannu a taykn aikin gidah kafin asamu yar aikin Bata tayaku komai har yanzu?"

"Batayi Ba abunda take daga bacci sai kallo“

Hajia zaytunah ta daga Kai tana duban hajia ladi dake sakar mata karya gashi ta rasa ma yadda zata bude bakinta ta sanar masa komai....

_40..._


*MX*


Alhaji Mohammed ya dubi hajiya zaytunah. Ya girgiza Kai kawai yana sauke numfashi yace,

"Kuma har yanzu taki amincewar a dakko masu aikin ko?"

"Eh gatanann dai ai tana jinka. Taki harda bataso. "

'zaytunah kalle ni nan."

Hajia zaytunah ta sadda kanta kasa. Juyin duniya yayi yayi ta kalle shi.. Tana jiyo ladi da karama sunata tuntsiririn dariya..

  Tana kallo ya sanya kafar sa ya fice daga gidan. Hajia ladi da hajia karama suka rakashi har wajen mota driver ya ja shi suka fita daga gidan...

Cikin gidah suka koma sunata tuntsiririn dariya...

"Wai baki kama aiyukan ba ? Inada baki yau Dan haka kiyi girki da yawa Wanda zai ishi kowa yaci. Kajin banason suyi yaji irin na rannan. Gashi zaki ma su dadi. " Hajia ladi tace da hajiya zaytunah

"Toh..."

"Idan kin gama ni Kuma doya nakeson ci. Soyayyyiya Mai sauce din hanta. Amma kinsan ni maabociyar yaji ce don haka ki Saka mun isasshhen yaji da tafarnuwa"

"Toh"

"Yaya ladi bari na koma na kwantar sai zuwa anjiima"

"Toh aunty karama. Nima kwanciyar zanyi. Kinga idan kin gama ki kankwasa mun kofa nazo nagani. Amma ki bari ki dan Kara minti ishirin da gamawa haka. Zanyi bacci Nima"

"Toh" hajiya zaytunah tace kanta a kasa. Hawaye na Diga daga fuskar ta.

Kowanne yakewayeta ya ketare ya shige sashensa.

Hajiya zaytunah ta mike jikintava sanyaye ta nufi kitchen. Kacha kacha kitchen din yake. Duk sun bata komai na kwanukan. Kamar ko da yaushe din Kuma idan tsautsayi yasa su sukayi girki da safe to ko karfe nawa zatakai idan ma bata gidan data dawo za ace mata to aiyukan gidan suna jiranta. Ko da kuwa daga asibiti ta dawo Dan babu inda take zuwa. Batada Wanda zataje wajensa. Ita kadai ce bata da kowa.

Wanke wanken ta dauraye. Nan da nan ta hada ruwan kumfa Dana daurayata soma wanke su. Tanayi tana runtse idanunta, hawaye masu matukar dumi na zuba daga idanun ta

"Ya Rabbi ka kawomun dauki ... Rabbi ka kawomun sauki... Rabbi ka yafemun idan wani laifin na maka. Allah ni baiwar ka ce Mai rauni.. Mara karfi kuma. Allah Dan ikon ka da qudirar ka Allah ka iya munka cece ni Yaa Allah. Na fada hannuwan Wadanda suke sun su hallaka ni..."

Tana Kuka tana kaiwa Allah halin da take ciki. A haka ta karasa wanke wanken. Nan da nan Kuma ta shiga kokarin sarrafa girkunan da suka sakata.

Kujera ta janyo ta zauna acikin kitchen din. Ta daga kanta sama tanata tunane tunane..

Haka kawai gidah da maaikata masu girki ma akwai kuku har uku. Banda masu shara da masu wanki da masu dawainiya da harkar shuka na gidan ciki da wajen sa.

Amma saboda tsabar tsana da akayi mata. Kishiyoyon ta biyu suka hada baki wajen korar maaikatan dake girki da sauran su.

I take musu girki ko da kuwa yayi kadan. Sai ta sake Dora tukunya ta girka wani. Su da yaran su. Dake it'a bama me cimar abinci bace. Kadan takeci shima sai likita ya tsawatar yace lalle ta riqa cin abinci.

Mikewa tayi ta nufi sashenta ta dakko yar rediyon ta da take jin Shirin yau da kullum.

Rediyon ta na debi mata kewa ainun. Saboda ba inda take zuwa inde ba asibiti ba. Shima kaita ake a dakkota. Wani lokacin Kuma likitan ne kan zo gidah yayi mata abunda ya kamata

Karfi da yaji an rabata da mutane., an hanata ziyartar mutane. Ta fiya waje ma Tasha iskar duniya an Hana. Ance idan taga mutane bata sukuni. Bata da samun nutsuwa. Hankalin a tashe.. Tanaji tana gaji aka Dora mata lalurar kin mutane da kin kasancewa acikin su. Bayan mutum Rahama ne. Rediyon da take sauraro kadai tana Jin muryoyon masu shirye shiryen sake gudanarwa, suna debe mata kewa sosai

Don haka ta rage rediyon ta katse Dede sauraron kunnenta. Ta saka tana Jin Shirin da sukeyi...

Ta dau tsawon lokaci a kitchen din. Don sai data koma daki tayi sallar shabiyu da rabi da ake kira ta azahar. Sannan ta koma kitchen din da sauri sauri ganin Yara sun kusa dawowa daga makaranta. Sai data jara minti ashhirin yana duban agogon dake sakale ajikin bangon kitchen din sannan ta nufi dakin ladi. Kamar yadda ta umarceta idan ta kammala ta kwankwasa mata kofa.

Ta nufi dakin ta, gabanta nata harvawa, Sam batason tashin hankaki. Ta Saka hannu,

"Ya akai?"

"n gama..."

"Ok ki debi naki. Ki Saka fika fiki daya... "

"Na koshi da naman"

"Wannan matsalar ki ce.. Bar mun bakin kofa"

Hajia zaytunah ta koma kitchen ta samu plate ta debi Dan kadan. Ta zauna a kitchen din taci ta Sha ruwa ta dauraye plate din ta kife ta koma bangaren ta.

Tana zuwa ta rufe kofa, ta jingina da kofar ta sauke katuwar bahaguwar ajiyar zuciya Mai dauke da dimbin damuwar da take ciki marar misaltuwa ..

[1/13, 8:59 PM] Hafsaat🧕💞: KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞

*PG :41*

*AREWABOOKS VVIP:👇*

https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb

Ayi following yerwa incense and more TikTok account:

11 / 34