fata. Tana jujjuya kalmomi cikin zuciyarta, tana ƙoƙarin bayyana musu cewa ba su da wani abu. Cikin murya mai rauni, Hajiya Zaytunah ta fara magana,
"Don Allah, kuyi hakuri. Ga yara tare da mu, Ga mahaifiyata nagaya muku da batada lafiya wajenta zamu a asibiti. wannan ba hanyar da za ku bi ba ce. Ku kyale mu, mu tafi lafiya. Zamu iya bayar da kudi idan har hakan zai taimaka. Amma muna roƙon ku da ku kyale mu, ku bar mu. Dan Allah "
Hajiya Zaytunah ta kara da cewa,
"Wannan ba zai zama da amfani ba gare ku. Don Allah, kuyi hakuri. Zamu bi duk abin da kuke so, amma ku kyale mu ku sake mu dan Allah.. Na san ba ku son haifar da wata matsala."
Wannan magana ta fito daga zuciya, tana ƙoƙarin nuna wa ‘yan fashin cewa ba su da wata bukata ta aiyukan da suke yi. Amma ɗaya daga cikin ‘yan fashin, wanda yake riƙe da makami mai ƙarfe, ya kalli Zaytunah cikin ƙanƙanin lokaci sannan ya daka musu tsawa cikin ƙarfin murya.
"Shut up dalla malama!" ya fadi cikin zafin rai, yana juyawa cikin gaggawa yana buga tsaki ya cigaba da cewa,
"Kada ki sa na daka miki kulqin nan akai, idan ba ku bar magana ba, zan yi muku mugun abu., ku mana shiru! Ku daina magana!"
Hajiya Zaytunah ta ji tsoronta na ƙara ƙaruwa, amma ta ƙi amincewa da nuna musu ta razana, musanman agaban yaranta kar su Kara dimaucewa suma. Tana ganin tsoro cikin idanuwansu sosai, Nabeeha da Hammad sunyi shiru, kowane daga cikinsu yana jin tsoron wannan ƙalubale mai girma.
Hajiya Zaytunah ta ƙara roƙon su cikin kwanciyar hankali, tana ƙoƙarin guje wa fushin ɗayan daga cikin ‘yan fashin. Cikin muryar roko da lallami ta ce,
"Don Allah, ba mu da wani abu a hannunmu. Zamu bi ku duk yadda kuke so. Amma ku bar mu mu tafi, mu duba lafiyar Gwaggo na. Dan Allah ku sake mu"
Sai dai, ƙarshen ƙoƙarin rokon Zaytunah ya zama ruwan dare, wanda ya ƙara tayar da hankali ga ɗayan ‘yan fashin. Ya daka musu tsawa da karfi, yana yi musu jan kunne mai ƙarfi, yana cewa,
"Ki ci gaba da roƙon, Bama ki da masaniyar inda kuke ba. Idan har kuna son ku zauna lafiya da idanuwan ku, da kafafun ku da hannuwan ku batare da mun rage muku wani abu daga ciki ba , Toh kuyi shiru! Idan ba haka ba, Ku kuka dagaa abin da zai biyo baya."
Hajiya zaytunah ta rufe bakinta da sauri, tana jin cinyoyinta suna rawa, Bakinta ya shiga motsawa tanada adduar Allah ya kawo musu sauki da rangwame.. Ta dubi Nabeeha da Hammad cikin idanu masu cike da damuwa. Kowannen su a tsakure fargaaba ta gauraye su. Nabeeha ta takure kanta ta sunkuya tana kokarin kashe wayarta sakon message sai shigowa suke ta private number a jere. Nan take kuma signal din wayar ya dauke ba network kwata kwata. Gabanta na tsananta bugawa ta fara karanta sakon,
Zuciyarta na dukan uku uku yayin da take kokarin karanta sakon. hawayen da take kokarin dannewa sun fara zuba daga idanunta. Ta fara karantawa cikin damuwa, a hankali da kuma hankali mai zurfi.
"Nabeeha..."
Hannunta yana rawa yayin da ta dade tana kallon kalmar sunan da ya rubuta. Duk da tsoron da ta ji, zuciyarta ta fara jin dadin kalamansa. Ta kara tisawa bayan ta karanta da fari,
“…You are the unspoken poetry in my heart, the melody that soothes my soul, the warmth I never knew I needed…”
Tana jin muryarsa yana karanta sakon a cikin zuciyarta, tamkar yana zaune a gabanta yana fadin wadannan kalmomin da kansa. Zuciyarta na bugawa da karfi, yayin da ta cigaba da karantawa da kyar.
“…I see you in every beautiful thing, in every sunrise and every gentle breeze…”
Wannan yana kara saka hawaye masu daci zuba daga idanunta. Amma a cikin zuciyarta, tana jin wani nutsuwa mai sanyi.
A hankali, ta karasa karanta sakon har zuwa karshe, zuciyarta na tafarfasa da son zuciya.
"Fawaaz."
Tana karanta sunansa, zuciyarta ta fara karkarwa. Kamar a mafarki , amma gaskiya ce. Zuciyarta ta fara bugawa sosai, tana jin dadin jin wannan kalamai daga Fawaaz kuma...
Ta rufe wayarta da sauri, tamkar zata iya rufe zuciyarta daga jin nauyin soyayyar da sakonnin suka lullube ta da shi. Amma ba ta iya rufe idonta daga ganin kalmomin da suka gama shigewa cikin zuciyarta ba. Kamar a mafarki, tana jin kamar tana jin muryar Fawaaz tana maimaita mata kalmomin da ya rubuta, Kalmomin da suka girgiza ta fiye da duk wani abu da ta taba fuskanta.
“Ban san ya aka yi kika mamaye zuciyata haka ba, Nabeeha. Amma da zan iya cire ki a cikinta, da tuni na yi. Na yi kokarin yin shiru, na yi kokarin gujewa soyayyarki, na fake da miskilancina, amma hakan bai hana ki zama numfashina ba. Kin mamaye tunanina, kin mayar da zuciyata ba ta da iko a kaina. Idan sonki laifi ne, to na san babu kotun da zata iya yanke min hukuncin da ya fi abinda zuciyata ke min.”
Ta kara jan numfashi da kyar, zuciyarta na bugawa da sauri. Idan hannunta na rawa ne, ba laifinta bane. Idan kwakwalwarta ta kasa tsara abin yi, ba laifinta bane. Wannan abu ne da bai taba faruwa da ita ba. Ita ce Nabeeha, mai juriya, mai iya sarrafa tunaninta, amma yau ta rikice, ta yanke jiki.
Hawayenta suka soma gudu a kan fuskarta, amma ba hawaye na bakin ciki ba ne. Hawaye ne na rudani, na tsananin jin daɗi da kuma firgicin wannan sabon abu da ke neman birkita mata rayuwa.
Amma sai kuma zuciyarta ta daka mata wata tsawa..Maganar Muhammad fa?
Gaba daya ta saki jiki, ta jingina da bango, tana jin yadda nauyin tunanin ke kokarin ruguza duk wani shaukin da sakonnin suka jefa ta a ciki. Muhammad. Wanda aka riga aka tsara rayuwarta da shi. Wanda take kokarin tilasta wa zuciyarta yarda da shi. Wanda iyayenta suka amince da shi.
Shin, me yasa Fawaaz ya bari bai sanar mata ba sai yanzu? Me yasa ya bari har ta amince da Muhammad kafin ya fito da wannan soyayyar da take jin tamkar zata ruguza duk wani shirin da aka mata? Anya kuwa Fawaaz ne ya rubuta wannan sakon? Ko wani wasa ne ake mata?
Zuciyarta ta kasa amincewa da tunanin cewa hakan ba gaskiya bane. Domin ita kanta ta san Fawaaz ba mutum bane da zai iya wasa da irin wannan abu. Idan yana cewa tana zuciyarsa, to gaskiya ne. Idan yana cewa ya kasa cireta daga tunaninsa, to ba karya bane.
Amma ita fa? Shin zata iya jurewa auren Muhammad alhali tana sane da cewa zuciyarta na dukan wani suna daban? Shin zata iya cigaba da rayuwa da wannan sabon zargi a zuciyarta?
Tana jin yadda jikin ta ke daukar wani irin radadi mai dadi, radadin son da ta jima ba ta san yana cikin zuciyarta ba.👀
Sai dai a wannan lokaci, lokacin da take sha'awar ci gaba da jin dadin sakon, sai ta ji wani karfi daga cikin motar. Daya daga cikin barayin ya kwace wayar daga hannunta.
'Tas' ya haska ta da mari yana murde hannunta da karfin tsiya...
"Ke! Me kika dubawa? Kai wallahi waya ce a hannunta. Dama ba'a karbe wayoyin su ba?" Wani daga cikin barayin ya daka musu tsawa, yana zaro idanu.
Suka kwakkwace wayoyin hannuwansu gaba daya. Suka kashe. Agaban su bayan sun karasa cikin duhun daji da wata wuta ke ci da karare. Dayan ya zuba wayoyin acikin wutar suka kama da wuta lokaci daya...
Hawaye ne suka shiga zuba daga idanun Nabeeha. Ba wai hawayen bakin cikin yadda aka zuba wayoyin nasu acikin wutar bane suka babbake. Aa hawaye ne na farin cikin sakonnnin data karanta.
Tana jin yadda hannunta ke rawa yayin da ta sake kunna wayarta, zuciyarta na bugawa da sauri kamar zata tsinke kirjinta. Ta kara hasaso sakonnin Fawaaz da idanuwan ta ke nuna mata hotunan tar tar na sakonnin ta rike komai akanta, Yayinda zuciyarta na kokarin amsa tambayoyin da ta kasa samun mafita a kansu.
Shin hakikanin gaskiya ne? Fawaaz ne ya rubuta wadannan sakonnin?
Kamar mai jin iska a kunne, sai ta rufe idonta tana tuna yadda Fawaaz yake. Yadda yake miskili, ba ya wasa, ba ya son surutu. Idonsa na da wani irin zurfin da idan yana kallonka, zaka ji kamar yana karanta zuciyarka. Amma ita fa? Tana masa kallon dutse ne. Mutum mai sanyi, wanda ko yana jin wani abu, ba ya bari a fahimta.
Amma yanzu ya bude zuciyarsa a gabanta. Ya fasa shingayen da ya dade yana gina wa, ya shafe duk wani tazara da ke tsakaninsu da wadannan sakonnin da suka fi karfin kwakwalwarta.
"Ki ce min wani abu, Nabeeha. Kar ki bar ni cikin duhu. Na dade da sanin cewa na rasa ki, amma zuciyata ta kasa yarda da hakan. Ina son ki."
Kalmar karshe ta sake tunota da fargaba, numfashinta na daukewa. Ina son ki.
Fawaaz ne ya rubuta hakan? Wani irin Fawaaz ne wannan da yake iya fadar wadannan kalmomin?
Tana jin yadda wani irin zafi ke tasowa daga kirjinta zuwa makoshinta. Sai ta rufe bakinta da tafin hannunta, zuciyarta na kokarin karasa furta abinda take jin ta kasa fada da kanta. Abinda ya jima yana bacci a cikin zuciyarta ba tare da ta san da shi ba.
Ita ma tana sonsa....🥲
Hawaye suka kara cika idonta, amma kafin zuciyarta ta rude gaba daya, wata murya a cikin kwakwalwarta ta tuno mata da abu daya da ta ke kokarin gujewa.
Muhammad.🥹
Tana jin kamar ruwan sanyi aka watsa mata. Tana da shi. Tana da Muhammad. Kuma ba soyayyar wofi bace. Magana ce da manya suka sani. Magana ce da ta riga ta amince da ita, ko da kuwa zuciyarta ba ta dauki hakan da gaske ba.
Shin yanzu me zata yi?🤭
Zata iya musanta Fawaaz, ta ci gaba da rayuwa kamar ba ta san da sakonnin ba? Zata iya rufe zuciyarta ta dauki soyayyar Muhammad da karfi? Zata iya daukar wannan abin a matsayin mafarki ne kawai?
Amma zuciyarta ta riga ta gano gaskiya.
Kuma da zarar zuciya ta gano wani abu, to ko da mutum ya so ko bai so ba, ba zai iya boye ta ba.
Sai dai bata karasa tunanin da take ba muryar daya daga cikin yan fashin da suka kama su ta doki kunnuwanta,
"Ku zauna anan... Kai da wo nan"
"Dan girman Allah kannena kuyi mana hakuri ku sake mu. Wallahi Indai don kudi ne da yardar Allah zaa baku. Dan Allah nawa kuke bukata?" Hajia zaytunah ta shiga rokon su.
Dan daban dake kusa dasu da katotuwar bindiga a hannun sa, Yayi murmushi yana busa tabar sigari a fuskar Nabeeha yace,
"Hajia kenan. Indai don kudi ne ai da an wuce wajen tun dazu. Bakiga wayoyin ku ma mun zuba su a wuta ba sun babbake? Ai da kudi mu ke nema awajen ku da tuni mun ce ku bamu number da zamu kira na dangin ku. An bamu isashhshen kudin aikin mu an sallamemu. Idan ma zaku dangana ku dangana kawai. Domin sakon umarni nake jira aturo yanzun zamu raba ku da iska ku shallara lahira"
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun... Allahumma Ajirniy Fi Musibatiy Wakluf Li Khairan Minha... Nabeeha, Hammad mu cigaba da addua muna neman Allah ya kawo mana dauki. Dukkan wani tsanani yana tare da sauki Inn shaa' Allah. Idan kuma tamu ce tazo, Allah kasa mu cika da Imani Amin"
"Aameen Aammi" Nabeeha ta fada tana goge hawayen dake tsiyaya daga idanunta..
"Aameen. In shaa Allah" cewar Hammad dake cen gefe an daure hannuwansa da kafafunsa da wata igiya..
Hajiya Zaytunah ta kasa tantance abin da ke faruwa. HANKALIn ta ya cunkushe, zuciyarta na bugawa da sauri fiye da kima. Ta dubi yankin da aka ajiyesu, hannayenta daure, Nabeeha da Hammad dake gefe suna ta rarraba ido cike da tsoro.
Waye? Waye ya sa aka kamo su?.. su waye ke da hannu aciki?
Wane ne ya yanke hukuncin cewa dole su hallaka? Me suka tare wa wanda ya aikata hakan? Me ya sa har aka yanke hukunci na kisa a kansu?
Idan akwai abu 'daya da ta fahimta a rayuwa, to babu shakka AKWATIN SIRRIN na mai hankali ba ya buɗuwa sai lokacin da abin da ke cikinsa ya zama dole a bayyana. Kuma SIRRIN nan da ke cikin wannan lamari ko KIRJI ba karamin abu ba ne...
Ta lumshe ido, hawaye na kokarin cika su. Shin wannan ne ƙarshen rayuwar su? Ko kuwa akwai wanda zai buɗe AKWATIN SIRRIN da ke ɓoye gaskiyar wannan mummunan shiri?
Amma waye ne ko su waye suka shirya hakan? Kuma me zai faru idan aka gano gaskiya?
Hajia zaytunah ta daga kanta sama tana mai cigaba da rokon Allah daya kawo musu sauki. Ya kuma bayyana gaskiar lamarin. Duk me hannu aciki Allah ya mayar masu da mugun nufin su......
-----
_1-Me zai faru da da Hajia Zaytunah da iyalanta da aka sace? Sannan wane SIRRI ke cikin wannan sacewar? Zai yiwu su Hajiya Zaytunah su tsira ko kuwa wannan zai zama sabon tashin HANKALI? Me zai faru idan wannan lamari ya isa gasu Major General Dawud?_
_2: Ga Fawaaz ya dakko hanyar dawawo gida, ya zai yi da Nabeeha idan da rabon ganawar su agaba? Shin zai ci gaba da guje mata ko kuma zuciyarsa za iya yarda ya fito mata a mutum? Ko akwai wani SIRRI ko al'amari da zai kawo canji cikin soyayyar su?_
_3:Me zai faru tsakanin Fawaaz da Muhammad ?sabuwar alaka ko rashin fahimta? Za su iya zama abokai ko kuwa soyayyar Fawaaz da Nabeeha zata raba su? Wane bangare zai fadi idan soyayya ta taso?_
_4: Gwaggo Zainabu da iyalanta sun dakko hanyar zuwa birnin Noka, ta yaya ganawarsu da Major General Dawud zai kaya? Shn akwai wani SIRRI ko hadari da za a gano a cikin wannan ganawa? Me zai faru idan Major General Dawud yayi idanu hudu da Alhaji Amiru?_
_5:Ancewa Alhaji Amiru cewa an ga su Hajia Zaytunah a gidan Major General Dawud? Shin wannan sanarwa za ta jawo karshen zaman Hajiya Zaytunah agidan major? ko zai kawo wani sabon rikici na daban? Me zai faru idan Alhaji Amiru ya dauki mataki mai tsauri?_
_6:Nabeeha da aka sace🥹Me zai faru da ita?Za a samu mafita ga Nabeeha ko kuwa wani sabon hadari zai sake zafafa mata rayuwarta? Shin zata iya rayuwa cikin hadari ko za a sami daukaka a nan gaba?_
_7: Me zai faru da Fawaaz da Muhammad idan soyayya ta taso? Wa zai hakura ya bar wa wani? Wane sakamako zai biyo bayan soyayya da rashin fahimtar juna? Soyayya ko hasara - a ina za su dosa cikin wannan tafiyar?_
_8: Haajia Hawwa da Hajiya Rumanah.. Za su hadu ko kuwa za a samu sabani?Shin za su yi aiki tare ko kuwa wani SIRRI zai kawo gajeriyar hanya da sabanin ra’ayi? Wane abu zai faru idan suka hadu?shin da sa hannun kowannen su a kamun su Hajiya Zaytunah? Ko kuwa wata sabuwar barakar ce ta kunno kai?_
_9: Ya zata kaya ga bangaren su Major general da Gwaggo Hafsatu dake jiran isowar su hajia zaytunah don su sanar musu lamarin daya kunno kai gaban su?.. Gashi an sace su hajia zaytunah ta ya ya su gwaggo zasu karbu wannan mummunan labari?_
_10: Shin su Gwaggo Hafsatu zasu ba wa Muhammad Amiru Muhammad auren Nabeeha Uzairu Muhammad? Ko kuwa sarkin sarakan miskilai na nahiyar afirka da ketare zaa bawa?🤧 ... Wato fawaaz Dawud Mafia?"_
_Duka wadannan tambayoyin da ma wasu, Kai da dukkanin ma amsoshinsu na ɓoye ne a cikin AKWATIn SIRRIN littafi na biyu. Ku tsayar da HANKALIn ku, ku shirya KIRJIN ku, domin gaskiya na tafe…Kuma wane irin rufi aka yi wa SIRRIN da har ba wanda ya fahimta?_
_Wayyo, KIRJIN MAI HANKALI ya fara nauyi da abin da ke cikin sa. Amma shin, zai iya riƙe wannan SIRRIN har zuwa ƙarshe?🤭_
_Ku jira littafi na biyu, wanda zai zo muku bayan Ramadhan, In shaa Allah!_
_ALHAMDU LIL LAAHI HAMDAN HAMDAH!!_
_Duka duka anan karashen LITTAFI NA DAYA (BOOK ONE) ya kare. Sai Kuma book two idan Rabbana ya kai mu. Rabbana ya hadamu a ladan dake ciki. Kurakuren ciki Allah ya yafemun da ku baki daya. Nasan mai karatu zuciyar sa na dabaibaye da kaunar son karance yadda karashen wannan labari zai kasance. Gashi ko wane bangare ya dau zafi, musanman yadda zata kaya da captain fawaaz, Air captain Muhammad da Dr Nabeeha 🥳 sai kuma book two idan Rabbana ya kai mu. Don baki daya ainihin gundarin abunda littafin ya kunsa ma a book two yake . Book one shimfida ce kawai.. Ainihin labarin ruguntsumin mai dauke da kauna tacacciya marar gauraye yana book two💃Wannan tafiyar mai zafi ce.. 🥳 . Book two shine inda dadin yake....._
_Toh Allah Ubangiji yasa muna daga cikin yantattun bayinsa. Allah yasa muna daga cikin wadanda zasu yi azumin wannan wata mai albarka tun daga farkon sa har karshen sa.. Allah Kuma ya amshi bukatun mu Amin. Ya yafe mana lefukan mu amin_
_Dan Adam tara yake bai cika goma ba. Dan Allah idan da akwai wanda na batawa farawar littafin nan zuwa karshen sa. Ya yafe mun dan Allah. Ina neman afuwar dukkanin ku. Haka zalika bangaren rashin posting, gajerun pages, ko wani wuri dana manta ban saka ba. Ko wanda na saka bai dace ba da sauran su. Afuwan! afuwan! afuwan!!!_
_Mu sanya juna a adduoin mu. Allah ya karba mana Amin . Kofa a bude take ga masu son temakawa kamar wancen ramadhan din. Na TALLAFIN abincin azumi. Kudi, kayan abinci, da sauran su zuwa ga HGL CHARITY FOUNDATION dake nan garin Kano. Unguwar tarauni 9044191709 OPAY. Allah yabada ladan temako ya biya bukatu na alkhairi amin_
_Amaren bayan ramadhan... Masu san turarukan wuta na kamshi. Da uwayen gidah da masu son fara sana'a sai ku garzaya YERWA INCENSE AND MORE. 08095215215 don mallakar naku_
_Sai book two wato kashi na biyu na littafin KIRJIN MAI HANKALI. idan Allah ya kai mu bayan sallah da rai da lafiya. Allah yasa a yi ibadah karbabbiya Allah Kuma yasa muna daga cikin yantattun bayinsa..Allah yasa mu dache da daren laylatul qadr amin._
_Taku: Nana Hafsatu bnt H😍_
09134848107