mahalicci daya shiga cikin dukkanin lamuran sa, munsaman wannan lamarin na sa da gimbiyar da zuciyar sa ke bege wato nabeeha....
Bayan ya idar da sallolin ne ya dade yana kwarara adduoi. Yana ambatar sunayen Allah kyawawan mafi girma da Allah yafi so.
Ya nufi gadonsa ya kwanta bayan ya karkade da basmala. Bakinsa dauke da adduar bacci wato azkhar na kwanciya. Ya kwanta yana lunshe idanunsa. Idanuwansa na nuna masa hotunan fuskar nabeeha inda take murmushi yayinda kyawawan hakoranta dake jere reras a bakinta suka bayyana a tsadadden murmushinta Mai matukar sanyaya zuciya. Ya samu kansa da sakin murmushin shima tamkar itan yake gani a gaske. Kasan makoshinsa. Bakinsa ya furta,
"Yaa Allah ka mallakamin NABEEHA...." Da wannan bacci mai dadi cikeda mafarkan nabeeha ya kwashe shi...
×××××
Dake kasancewar weekends ne. Kuma duk ranakun karshen mako a sashen kakarsu gwaggo Hafsatu suke wuni..shine ma baya zama da sun gaysa zai tashi. Saboda kowa yasan halinsa. Shiyasa baabi ta kansa. Don da zamansa da kin zamansa awaje duk daya ne. Har gwara ma ya bar wajen dan zamansa awajen, wadanda kan iya bude baki suyi magana saboda zamansa awajen yasasu shiga karsashi na kwarjininsa. Su kasa magana..
Bandaki ya shiga yayi wanka. Ya shirya cikin kananun kaya da suka amshi kirar zatin halittar jikinsa. Da sukayi matukar masa kyau.
Ya dakko brush ya taje tsaftacciyar sumar kansa. Bata cika yawa ba dai. A kwance take luf a Kuma gyare. Yanada saje((side burns) daya lullube gefe da gefen fuskar sa. Ga gashin baki shima duk kuwa da ya aske shi. Amman akwai kadan . Sai gemun sa shima da bai cika yawa ba ya zauna gam awajen.
Turarukan ya dauka ya feffesa ajikinsa ya dauki na kaya ma ya bi lungu da Sako ya fesa sosai. Ya dauki wayarsa da mukullin mota ya fita daga bangaren..
Kai tsaye ya nufi sashen da su gwaggo Hafsatu suke. Ya kwankwasa babbar kofar sashen kafin bakinsa dauke da sallama ya tura kofar ya shiga...
Duk suna zaune... Gwaggo hafsatu akan doguwar kujera hannunta dauke da charbi tana ja. Sai hajia zaytunah dake kasa kusa da gwaggon tana matsa mata kafafuwa.
Sai Raudah tana kujera mai cin mutum daya daga gefe tana danna ipad din hannunta. Can daga gefen kujerar da take Kai itama Mai cin mutum daya humayrah ce akai tana danna wayarta.
Sai mahaifiyar su hajia hauwa maijiddah tana zaune akan kujera Mai cin mutum biyu ita kadai..
Yayinda makekiyar tv dake parlorn tanata futar da sautin karar maganar labaran da ake yadawa na tashar aljazeerah..
Duk suka juya suna amsa sallamar tasa. Ya samu kansa da rashin samun nutsuwa ganin tagaban zuciyar tasa batanan wato nabeeha. Don haka ya karasa shiga cikin tsakar parlorn ya zube..
"Granny barka da rana..... An tashi kalau?"
"Kalau Alhamdulillah ranka ya dade! Ga irin ta ka" gwaggo hafsat ta daga hannu tana masa jinjina.
Dan murmushi yayi yana sosa keyarsa cikin sauri yace,
"Tuba nake granny. Wane mutum?"
Sai Kuma ya juya ya fuskanci mahaifiyar sa,
"Barka da safiya Maa... Aunty barka da safiya" ya Kuma juya bangaren hajia zaytunah yana gayshe da ita..
"Alhamdulillah fawaaz."
"Alhamdulillahi. Sannu da kokari" cewar hajia zaytunah
Nan da nan daya bayan daya su Raudah suka shiga gayshe da shi. Ya shiga amsa musu kasan makoshi. Basu damu ba don kowa yasan halin miskilancinsa. Don haka kowacce ta cigaba da sabgarta..
"Ka zauna mana ranka ya dade. Yau anyi mutumin naka fa. A zubo? "
So yake yacewa gwaggo Hafsatu a'ah. Amman Kuma zuciyarsa da gangar jikinsa dama idanuwansa suna son kasancewa da Nabeeha. Don haka ya dan murmusa yana daga kansa sama..
"Yauwa ko kai fa... "Gwaggo hafsat ta fada tana kokarin mikewa tsaye
"Bara a debo masa gwaggo"
"Aa na hutassheki zaytunah. Tun dazu kike aikin matsa kafafun nan ba gajiyawa inata ki huta, baki huta ba. Bari na Dan shiga kitchen din Nima na motsa kafafun nawa. Sannu da kokari nagode miki Allah ya Saka da alkhairi Amin"
"Aameen gwaggo" hajia zaytunah ta amsa.
Hajia hauwa Maijidda ta dube su ta gefen idanu tana tabe Baki. Gabanta nata wutar ruruwa na takaicin haushin zaytunah da ahalin ta datakeji . Haka kawai sunzo sun kankame musu agidah. Kayi magana yanzu karamar magana tazama babba.
Gwaggo ta mike ta shiga kitchen.nan da nan ta fito da kofi Mai matukar kyau da cokali. Dauke da kunun gyada sai kamshin kayan kamshi yakeyi da gyada mashaa Allah.
Ta karasa kusada fawaaz tana mika masa. Ya karba cike da girmamawa ya koma ya zauna yana juya kunun da cokali... Ya lunshe idanunsa yana bude kofofin hancin sa hadi da shakar niimataccen kamshin da kunun yakeyi..
"Sha kar ya huche..." Gwaggo tacedashi tana murmushi..
Kada Kai yayi. Ya Kai cikolin bakinsa yana kurba. Ya dubu gwaggo yana murmushi,
"Da dadi ko?"
Ya sake kada kansa alamar eh...
Gwaggo Hafsatu tayi murmushi tana girgiza kai Kai tache,
"Kasan waye yayi? Chanki?"
Fawaaz ya daga Kai tamkar Mai tunani can ya sauke yana murmushi. Ya sanya yatsansa daya yana nuni da mahaifiyar sa hajia hauwa maijiddah.
Gwaggo hafsatu ta girgiza masa Kai tana cewa,
"Ba ita bace..... Sake chanka dai"
Ya nuna hajia zaytunah. Nanma gwaggo Hafsatu ta girgiza masa Kai alamar aa.
"Duk basu bane...."
Ya daga kafadarsa irin bai gane kowaye yayi ba toh. Ya kurbe duka ya a jiye kofin akan center table...
"Ka bani gari na amsa ka?"
Ya sake kada kansa sama eh. Gwaggo Hafsatu ta kyalkyale da dariya kafin ta girgizia Kai tache,
"Kafin na amsa dai. Ina rokon Allah ya bude maka wannan bakin naka ka dinga magana sosai kamar kowanne Mai baki a doron duniya. Wannan miskilanci naka sai Kai.. ace mutum dan adam ba zai dinga bude baki yana hria kamar kowane mutum ba. Sai kache mutum mutumi? Sai ka dinga amsawa da kai kana kadawa kamar wani kadangare?. "
Yan parlorn suka Saka dariya baki daya. Gwaggo Hafsatu ta girgizaa Kai tana murmushi tana duban fawaz da shima murmushin yake, bayan ya juya ya zabgawa su humayrah harara, yana kokarin mikewa tsaye tache,
"Nabeeha dai kanwar ka ita tayi... "
Ai fawaaz bai San sanda ya koma ba ya zauna... Gabansa ya tsananta bugawa. Lokacin daya jiyo sautin takun takalmanta tana dakkowa daga sama. Ya samu kansa da satar kallon kafar benen yana binta da kallo.
Sanye take cikin doguwar riga ta abaya baka ta ya ne kanta da mayafin abayar. Hannunta rike da wayarta. Tana Isowa parlorn ya Mike tsaye yana karasa zura takalmansa..
"Ba dai tafiya ba?" Gwaggo Hafsatu tace da shi ganin yana kokarin gita.
"Eh zan dan futa ne..."
"Ba zaka tsaya kaci abincin rana ba? An kusa saukewa"
Ya girgiza kansa yana duban screen din wayar sa..
"Ina kwana ya fawaaz?" Muryar Nabeeha ta doki kofofin kunnuwan sa.
Fawaaz ya samu kansa da kin amsawa. Bakuma wai shareta yayi ba. Aa labbansa ne suka yi masa nauyi saboda sanyin jiki da muryar Nabeeha ta saukawar dukkanin gabobin jikinsa.. gashi muryar tata tamkar ana busa sarewa don dadi ...
"Ana gayshe ka fa. Sarkin sarakan miskilai na nahiyar afirka da ketare. Ka amsa dai tunda gaysheka akayi ko?" Gwaggo Hafsatu ta ceda shi cikin fada...
"Lafiya" ya amsa murya kasa kasa yana satar kallon ta ta gefen idanun sa.
Yayi hanzarin ficewa yana Kara waya a kunnensa. Nabeeha jikinta a sanyaye ta nemi gefen humayrah ta zauna.
Ita kuwa hajia hauwa Maijidda dadin Hakan taji. Don batasan wannan Shirin da yaranta suke dasu Nabeeha. Shi yasa fawaaz yafi burgeta rashin jituwar da basayi da yaran zaytunah. Musanman Nabeeha. Don aganinta kusantakar shirin yaran nasu tayi yawa. Har tana kokarin ta koma wani shakuwar ta wuce ta mizanin hankali.
Mikewa itama tayi bayan ta dan sunkuya saitin sirikarta gwaggo Hafsatu,
"Gwaggo bara naje akwai wani abu da kike bukata na daban a dafa idan zan dawo?"
"Aa Maijidda. Sannu da kokari kinji?"
"Tohm gwaggo a huta lafiya" ta mike
"A huta lafiya hajia" hajia zaytunah taceda ita.
"Yauwa.. sai na dawo" hajia maijiddah ta amsa ta.
Ta fice daga parlorn bayan ta zubawa su Raudah uwar harara. Ba shiri suka mike suma suka bi bayanta bayan sunyiwa yan parlorn sai anjima...
Tun a hanya kafun ta karasa sashenta take jera tsaki a jere ba kakkautawa. Ta shiga bangarenta tana buga kofar ji kake garammmm
Yaran suka shiga suma bakunansu dauke da sallama. Ta dube su ta tabe baki tana wurga musu wani kallo.
"Sai kache marasa zuciya. Tun safe kuke can a zaune. Ko waiwayo gidah bakwayi, sakarkaru kawai. "
"Yi hakuri maa" suka hada baki wajen amsa ta.
Ta sake dubansu tana hararar su tamkar idanuwanta zasu fado saboda fada tache,
"Har ita wadda kuke bi tamkar itace asaman ku tashi taje tayo wankan ta sauya kaya Kuna zaune kamar an dasaku"
"Kiyi hakuri maa" Raudah ta fada kanta a kasa.
"Kiyi hakuri" humayrah ta amsa ta.
Hajia maijiddah ta mike ta bar parlorn tana sauke wani tsakin a karo na ba adadi...
Kai tsaye ta nufi parlorn Mai gidan nata. Tunda yayi tafiya bata shiga ba sai ranar.
Ta zauna akan kujera tana Mai sauke katuwar ajiyar zuciya. Can ta sanya hannu ta janyo drawer dake jikin center table.
Takardu ne fal. Ta sanya hannu tana kokarin mayarda locker din data janyo ta hango wata yar farar takarda janyota tayi tamkar ba zata duba ba sai Kuma ta fara karanta abunda ke jikin ta... .
*HGL CHARITY FOUNDATION*
(Feed a fasting soul/ Helping the needy/ Charity foundation)
_Assalamu Alaikum Wa Rahamatullah Wa Barakatuh... Kira zuwa ga al’umma:_
Muna kira ga dukkan wadanda Allah ya horewa. masu son lada da su shiga cikin aikin alkairi na ciyar da masu azumi ko bayar da kayan abinci ga mabukata. Wannan taimako zai rage wahala ga mabukata a watan Ramadhan, da kuma bayar da damar samun ladan wannan aiki mai girma. Inshaa Allah kamar yadda mukayi a wancen azumin Alhamdulillah..
Abubuwan da za a iya bayarwa ga wadanda suke son bada kayan masarufi:
1. Kayan abinci:
Wake don yin kosai.
Shinkafa don yin waina ko tuwo.
Gero ko dawa don yin kunu.
Da Duk wani nau'in kayan abinci da ya dace.
2. Abincin buda baki:
Kosai, waina, shayi da biredi. Da duk abunda Allah ya hore .
Kunu mai zafi ko ruwa da kankara.
3.Ruwan sha:Pure water ko ruwa na roba ko lemo da ake hadawa na sachet...
Hanyoyin Bayar da Tallafi:
1. Ta hanyar kudi:
Asusun Banki: 9044191709
Sunan Banki: Opay
Sunan Asusu: HGL Charity Foundation
Zaku iya bada Kayan Abinci: Zaku iya kawo kayan abinci kai tsaye zuwa inda muke a Kano, Unguwar Tarauni.
3. Akwai masu tambayar to zamu iya bayar da abincin a dinga dafawa a madadin mu don ladanmu? Kwarai a madadinku: Idan kuna son mu yi amfani da tallafin ku wajen dafawa da rarraba abinci, za mu yi hakan a madadinku. Sai a Aiko da kayan abincin na adadin kwanakin da akeso sai ayi sai a raba ..
Tuntube Mu:
Lambar waya: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Ziyarci Shafukanmu:
Instagram: @hglcharityfoundation
https://www.instagram.com/hglcharityfoundation?igsh=OWltMzE2dWgyYWFk
TikTok: @hglcharityfoundation
https://www.tiktok.com/@hglcharityfoundation?_t=8sdPaqY4bMT&_r=1
Facebook: @hglcharityfoundation
Ƙarin Taimako:
Ga masu son tallafawa da ayyuka na musamman:
Ciyarwar Fridays: Wannan tana gudana kowace Juma’a don taimakon mabukata. Duk sanda halin ya kasance. Wanda ke so sai ya bayar ayi masa akwai masallatai da makarantun almajirai sosai da mabukata a yankin da muke..
Rijiya ko borehole: Masu son tallafawa da rijiya suna iya tuntubarmu; akwai kauyuka masu bukata da suka kawo koken su.
Taimakon mabukata na gida: Duk wanda yake da kayan da zai iya bayarwa, muna maraba da shi.
Manufar Gidauniyar:
Manufar mu ita ce taimakawa mabukata da ciyarwa da masu azumi, don samun lada mai yawa a wannan wata mai albarka.
Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da lada irin na mai azumin, ba tare da ladan mai azumin ya ragu ba.” (Hadisi)
Ku kasance cikin masu taimako. Allah Ya saka da alheri kuma Ya biya mana bukatunmu na alkhairi. Amin
Allahumma ballighna Ramadan bil amni wal iman.
HGL CHARITY FOUNDATION
"Feed a fasting soul this Ramadan!"
We invite you to join us in providing meals and support to those in need during this blessed month of Ramadhan. Your contributions, no matter how small, can make a big difference.
How You Can Help:
1. Donate Food Items:
Beans (for kosai), rice (for waina or tuwo), millet or guinea corn (for kunu), etc.
2. Provide Ready-to-Eat Meals:
Kosai, waina, bread and tea, kunu, or chilled water.
3. Financial Donations:
Bank Name: Opay
Account Name: HGL Charity Foundation
Account Number: 9044191709
Contact Us:
Phone: 09044191709 / 09134848107 / 08021481240
WhatsApp: 09044191709
Let us come together to bring smiles to the faces of those fasting. Your support can also help fund Friday feeding programs or even build wells for villages in need.
"Whoever feeds a fasting person will receive the same reward as the fasting person, without diminishing their reward."
May Allah reward your efforts abundantly.
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_*BOOK ONE/LITTAFI NA DAYA:*_
*_PAGE:69_*
"Alhaji Amiru Muhammad. Dan uwa ga Alhaji uzairu Muhammad. Iyalan Hajia zainabu. Mawii crescent... suna neman yar uwarsu data bata da yara biyu..."
Jujjiya takardar tayi tamkar me kokarin gano wani abun na cikin ta. Musanman sunayen data ga kamar ta San su. Names din sounds familiar. sai Kuma ta mayar drawer cikin inda ta dauka ta mike ta fice daga parlorn....
Gaba daya ranta a dagule yake. Zuciyarta na mata Kuna da raɗaɗi. Baki daya akan kasancewar zaytunah da iyalanta ne....
Tana tafe tana kokarin tuno lissafin mutanen data karanta a takardar dake a rubuce da sunayen su ..
"Itama zaytunah ai yaranta biyu dasu tazo ko?" Ta tanbayi kanta tana sauke ajiyar zuciya da tsaki ta sake cewa
"Ai ita ba bata tayi ba. Sannan yar uwar su gwaggo surukar tane. Data jajujo bosu daga wani waje gashinan sun zaman musu karfen kafa...
Mikewa tayi tana sake hararar parlorn ita kadai Kai kache mutum ne awajen take Jin haushin sa.. Tanata kwafa tana jera tsakin takaici.
Sai data huta sosai ta yo wanka harda bacci tukun sannan ta sauya kaya zuwa doguwar riga mai mayafin babba. Samfarin Dubai
"Raudah.... Humayrah " ta kira sunayen su.
Shirun dataji ne ya tabbatar mata da sunyi wanka sun sake koma can bangaren. Cikeda kifulewa da kololuwar takaici marar iyaka tace,
" Ba zata sabu ba wallahi. Zaytunah ba zaki rabani da uwar mijina ba. Kina kuma kokarin raba ni da mijin ma gaba daya, abu kadan yace kanwar sa zaytunah waye waye. . Sannan Kuma ace yayan cikin nawa ma sun tare awajen ki? Wannan wacce iriyar lukutar masifar kaddara ce haka? Allah idan wani lefin na maka kake hukunta ni da haka rabbi Dan tsarkakkun kyawawan sunayen ka casssain da tara.. Allah ka yafemun, wannan mata Allah Kai qasa qasa da ita sharrin da take tafe dashi yasa ya kare haka yanzu.m wannan wace iriyar musiba ce? Kowa zaytunah. Lamarin harda masu aiki jikinsu na rawa idan zasu bangaren hajia zaytunah... Gaskia da sake. Don na Kai kololuwar karshe " tana magana tana karasa rufe kofar sashenta da mukulli . Ta nufi sashen hajia..
Ta kofar parlor kujerar da Raudah take akai suka hade idanu ta zunduma musu hararar irin Kun kyauta da baku jirani ba
"Maa sannu da dawowa" Nabeeha ta gayshe da ita
Sai data dau mintina kafin tana yatsina tace..
"Yauwa"
Yaran nata ma suka shiga yi mata sannu da zuwa.. Ta amsa su suma a kufule saboda tanajin haushin su...
Wajen gwaggo zainabu ta nufa. Ta durkusa ta sake gayshe da ita. Suka gaysa da hajia zaytunah ma sannan ta nemi waje ta zauna. Parlorn sai karar TV suna kallon wani Turkish drama early birds..
🎀🎀. 🎀🎀. 🎀🎀.
Shi ko Fawaaz yana futa motar sa ya shiga ya fice daga gidan gaba daya ya nufi headquarter dinsu. Office dinsa ya shiga juniors dinsa nata kamewa suna kwasar gaisuwa.
"Morning sir .. " Hadi da saluting/Sara masa..
Kada Kai kawai yayi musu ya bude ofishin ya shiga ya zauna akan kujera tana dafe kansa . Wani junior dinsa ya kwankwasa sannan ya shiga,
"Sir akwai wani abu da kakeso ayi?" Cikin harshen turanci..
Nanma ya girgiza masa Kai alamar a'ah... Junior din ya fice da sauri yana sake saluting nasa.
Yana futa, fawaaz ya sauke katuwar ajiyar zuciya Mai tattare da dimbin damuwar da yake ciki....
"The girl named Nabeeha....... My mystery girl. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun Allah ka kawo mun dauki .. Yaa Allah ka bude mun bakina ka kawo ranar da zan bayyanawa yarinyar nan irin tarin kaunar da nake mata. Godd I love nabeeha madly.. Kai na shiga uku." Ya karasa fada yana jera tsaki Hadi da Saka hannu ya dafe kansa..
Wayar sace tayi kara ya sauke zuciya, kafin ya zura hannu ya ciro ta agaban aljihunsa.. mahaifin sane mai kiran sa don haka da sauri ya dauka,
"Morning sir" ya fada cikin girmamawa. Tukun sannan ya Kara da,
"Barka da rana Babaa... Da fatan kana cikin koshin lafiya?"
"Captain fawaaz"
"Yes sir"
"Allahumma Barik"
"Wa iyyakum Babaa"
"Mashaa Allah. Komai kalau, da fatan kowa da komai na gidah yana lafiya ba damuwa?"
"Alhamdulillah Babaa.. Ba komai" ya karasa fadin bakomai din a sanyaye. Cuz shi deep down he's totally gone. Asin he's insanely in love. A kama kamar me HANKALI da nutsuwa. Amma ina KIRJIN sa tattare yake da SIRRI. SIRRIN ma na kauna... Kaunar ma ta wadda bazai taba iya samu ya gayawa ba. Shi kansa yakan yi mamakin kansa. Izza da miskilancinsa sunyi yawa. Gashi yayi kokari ya dena amma Ina. It's in him. Like nature ne haka Allah yayi masa tasa halittar. Zai ga kamar yayi kasa ne idan ya nuna son wata ya mace. Bare shi da mata ke binsa. Bayabi takansu. Sai gashi haka kawai ya tashi da renon kaunar Nabeeha. Yarinyar daya fara Jin yana kaunarta a ransa. Tun ranar daya fara tozali da ita shekarun baya da suka dawo gidan su da zama...
"You sounds down.... Son! Kanada damuwa ne? Ko akwai wani mai damuwa acikin gidah? Look karka boyemun komai. You dare not. Ka sanar dani."
"Ba komai Allah ... Everything is going on smoothly .komai yana tafiya yadda ake so. Alhamdulillah!"
"Toh mashaa Allah. Dama zance maka ne jibi idan Allah ya kai mu kazo ka dakko ni a airport as early as 7 inshaa Allah. Saboda banason direbobin nan suzo sunada iyali tashin sassafe ba dadi."
"Toh shikenan Babaa Allah ya dawo da Kai lafiya amin"
"Aameen Yaa Allah Captain. Ina da wani conference ne later... Oh wait wait. Hello baka kashe ba ko?"
"Eh inaji baba. I'm all ears..Babaa. Allah ya temaka ya Kara riko da hannuwanka Amin"
"Aameen Aameen, Yarinyar