Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
idan kin dafa kuma ki zuba mini ni ma a cooler ina dawowa." Daɗi ne ya cika Bilkisu, ta amsa masa sannan ta kashe wayar.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA BAKWAI
AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*
***
Bilkisu drower kayanta ta buɗe, ta jima a tsaye tana nazarin waɗanda za ta ɗauka. Wata doguwar riga shara-shara ta ɗauko ta zura, ta shiga ɗakin yaran ta same su har sun fara bacci da yake an yi sallar Isha'i. Shimfiɗa ta yi musu ta ɗauko net ta saka musu, ta koma ɗaki sannan ta ɗauki ragowar taliyar da suka ci ita da yaran wacce ta zuba a cooler ta ajiye. Motsin Amina ta ji, don haka ta yi zaraf ta fito ta ɗauki buta ta yi kamar banɗaki za ta shiga. Amina ta gani ta fito da abincin ta saka a kicin, murmushin ƙeta Bilkisu ta yi ta shiga banɗaki bayan wani lokaci ta fito har za ta shiga ɗaki ta ja tsaki ta ce.
"Aikin banza, haka kawai a jaza wa mutum ɗora girkin dare. Ai shi ma Abban Sayyid ɗin maganinsa kenan, kana tare da matarka cikin rufin asiri ka ci ba ka ci ba babu wanda ya sani. Amma haka kawai rana tsaka a ɗauko maka baƙar ƙaddara ta addabe ka, tun da nake a gidan nan 'ya'yana ba su taɓa kwanciya ba su ci abinci ba sai yanzu."Ta gama faɗar haka ta faɗa ɗaki. Amina da ke durƙushe tana juye abinci a tukunya ta share hawayen idonta, saboda ta yi tunanin duniya ba ta tuna a lokacin da ta zuba fetir a madadin mai a abinci ba. Kuma ko da ta gama girki ba ta ji warin komai ba, a sanyaye cikin damuwa ta koma ɗaki ta zauna. Waya ta ɗauka ta kira layin Hafiz ta ji bai ɗauka ba, abin duniya duk ya dame ta don bai taɓa yin fushi da ita irin haka ba.
Bilkisu tana daga ɗaki wani tunani ne ya faɗo mata, da sauri ta ɗauki waya ta je bakin ƙofa yadda Amina za ta ji ta ce.
"Hello Abban Sayyid, na ce ka haɗo mini da tsiren jiya da ka sayo mini. Amma dai yau kada a cika albasa, sai kuma su Sayyada yogot ɗin nan za ka taho musu da shi." Sai Bilkisu ta yi shiru kamar ana ba ta amsa sannan ta sake cewa.
"A'a ba sai ka sayo mini kifi ba, kai dai ka sayo wanda za ka ci taliyar da shi." Ta sake yin shiru sai daga ƙarshe ta ce.
"A'a ai abin da Amina ta yi maka bai kai ka ce za ka ƙauracewa kwanan ɗakinta ba. Ba a yi haka ba, gaskiya kada kasa ta ƙulla ce ni. Sai dai ka shigo kawai." Bilkisu ta lallaɓa ta koma kan kujera tana ƙunshe dariyar ƙeta, saboda ta san babu tantama Hafiz ba zai shigo ba sai da kifi. Ɗabi'arsa ce indai ta yi shinkafa ko taliya fara da mai to ba ya taɓa ci sai ya sayo kifi ya ci da shi, ita da yara kuma sai ya sayo musu balangu ko tsire.
Amina tana daga ɗaki wani irin takaici ya lulluɓe ta, musamman da ta ji wai Hafiz yana faɗa wa Bilkis zai ƙauracewa kwanan ɗakinta. Kiransa ta gani, saboda haushi kawar da kai gefe ta yi ba ta ɗauka ba. Miƙewa ta yi ta shiga uwar ɗaki ta cire kwalliyar atamfar da ta yi, ta ɗauki wasu riga da wando marasa nauyi na bacci ta saka, sannan ta fita ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah.
Tana nan zaune ta ji sallamar Hafiz, mamaki bai gama kashe ta ba sai da ta ga Hafiz ya nufi ɗakin Bilkisu. Bai wani jima ba, ta ga ya ɗawo ɗakinta ya zauna, sai dai har lokacin fuskarsa a haɗe take. Kifin da ta ga ya fito da shi ya sake tabbatar mata da wayar da ta ji Bilkisu tana yi, Hafiz bai kalli ɓangaren da take ba ya ce.
"Idan za ki ci ki sauko."
Haushi ya kama ta da jin abin da ya faɗa, zuciya ce ta ciwo ta ta ce.
"Na ƙoshi."
Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, bai tanka mata ba ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama ya tura mata ledar wani ƙunshin kifi gabanta ya ce.
"Ga shi nan ki tashi ki ci."
"Na ƙoshi ka cinye."
Amina ta faɗa a karo na biyu, ransa ne ya ɓaci don ya san ba ta ci abinci ba. Cikin faɗa ya ce.
"Wai saboda na yi miki faɗa shi ne za ki hau ɓata rai? Wani sabon hali za ki tsiro mini Amina? Kin san asarar yawan abincin da kika yi mini?" A ɗan zafafe ita ma ta ce.
"To yanzu me nace maka? Kawai don na ce na ƙoshi sai ya zama abin faɗa? Idan ba da son ranka ka dawo za ka kwana a nan ba, ba sai ka koma can."
"Me kike nufi Amina?"
Ya jefa mata tambaya rai a ɓace. Shiru Amina ta yi, cikin hawaye ta miƙe ta shiga ɗaki tana kuka. Kukan da Amina ta yi shi ya sake harzuƙa Hafiz, don gani ya yi bai ga abin fushi da kuka ba saboda kawai ya nuna mata kuskurenta. Hafiz yana gama cin abinci kallo ya kunna, don ba ya son ya sabarwa kansa da zaman majalisa. Yana nan zaune har ya ji bacci don haka ya kashe ya shiga ɗaki, a lokacin da ya shiga Amina ta yi bacci. Rage kayan jikinsa ya yi sannan ya haye gado ya kwanta.
Duk abin da ya faru tsakanin Amina da Hafiz, Bilkisu tana laɓe tana jin su. Daɗi ne ya cika ta, cikin farinciki ta koma ɗaki ta buɗe ledar kifin da Hafiz ya ajiya mata. Sai da ta cinye shi tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta haye gado ta kwanta hankali kwance.
WASHEGARI
Washegari koda Amina ta tashi yanayinta babu yabo babi fallasa, haka shi ma daga wurin Hafiz. Sai da ta zo yin wanke-wanke ta juye shinkafar a leda, saboda ko akuyoyi ba za su iya ci ba. Bilkisu ce ta sharo ɗakinta a lokacin tuni Hafiz ya jima da fita, da gayya ta sharo wata ƙatuwar takardar tsire wacce take sharkaf da mai, ƙuli da albasa. A yatsine ta sharo takardar da ta yi fakaka a saman makwashin shara ta ce.
"Shi ma Abban Sayyada na faɗa masa ya cewa mai tsiren nan ya rage zabga mana albasa, amma kullum sai ya manta." Ta gefen ido Bilkisu ta kalli Amina da ke wanke-wanke, sai da ta je wucewa ta gabanta sannan ta saki takardar ta faɗi ƙasa da gayya don ta gani. Tsugunnawa Bilkisu ta yi ta share ta saka a shara, sannan ta wuce ɗaki tana murmushin mugunta. Wunin ranar haka Amina ta yi shi cikin damuwa, zuciya ta raya mata munafurcin da Hafiz zai tsiro mata. Har take ji a ranta da ya san ba zai yi musu adalci ba, da ba ta aure shi ba. A yammacin ranar sai da ta yi wanka sannan ta ɗora girki, bayan ta gama ta ɗebi nata ita da Hafiz sannan ta ba wa Bilkisu da yaranta. Kuma a wannan ranar lafiya ƙalau suka ci abinci, har Hafiz yana janta da hira saboda girkin da ta yi ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Hakan ne ya sanyaya zuciyar Amina har ta sauko daga fushin da take yi, ta so ta yi masa magana a kan rashin adalcin da ya fara yi amma sai ta ƙyale shi don kada ya ga kamar ta cika ƙorafi.
Sannu a hankali rayuwar gidan Hafiz ta cigaba da tafiya, da daɗi babu daɗi haka suke rayuwa. Saboda kusan kullum da abin da Bilkisu take tsiro da shi, musamman idan Hafiz yana ɗakin Amina. Sautari idan yana ɗakin Amina sai dare ya yi za ta buga masa ƙofa ta ce ɗaya daga cikin yaran babu lafiya, ko kuma ta ce ya fito ya duba mata ɗakinta ta ji motsin wani abin. Tun Hafiz bai fahimta ba, yana biye mata. Har ya fahimci kamar da makirci a cikin lamarinta, saboda idan yana ɗakinta lafiya ƙalau suke kwanciya su yi bacci.
Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri idan Hafiz yana ɗakinta sai ta fice ta koma cikin yaran ta kwanta, a ranar farko da ta yi da ya tambaye ta sai ta ce ita ta fi jin daɗin kwanciya a cikinsu. Da ya nemi kasancewa da ita nan ma sai ta ce ba ta buƙata, daga haka sai ta koma idan ya dawo ɗakinta sai dai ta zauna ta yi ta rusa kuka ko ta ce ya sake ta. Hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya yi ba, da ya tambaye ta sai ta ce masa idan yana ɗakinta ji take kamar ta kashe shi. Kuma sai jikinta ya ɗauki zafi kamar ana dafa namanta ko ana tsira mata allura. Wannan lamarin ne ya ɗaga hankalin Hafiz, ya shiga nema mata maganin aljanu a tsammaninsa ko su suka fara shafarta. Watarana da safe Hafiz yana shan shayi, ta fara shara, da gayya Bilkisu ta sharo ƙarƙashin kujera sai ga wata ƙatuwar laya ta fito. Da mamaki ta ɗauki layar ta ce.
"Abban Sayyid kai ne ka ajiye ta." Yamutsa fuska ya yi ya ce
"Ni kuwa me zai haɗa ni da laya Bilkisu? Miƙo mini na gani." Ƙin ɗauka ta yi ta janye gannu gefe ta ce.
"Cab wallahi ba zan taɓa ba, haka kawai ban san ta mece ce ba zan taɓa ina zaune ƙalau." Miƙewa ya yi ya ƙarasa wurin ya yi bismillah ya ɗauka. Ya shiga warwarewa yana buɗewa sai ga wani busasshen ɗanyan nama, da ƙananan allurai a ciki. Wata takarda ya gani ya buɗe ta, a ciki ya ga an rubuta sunansa da na Bilkisu na farraƙu. Daga ƙasa kuma an saka sunansa da na Amina an yi rubutun mallaka." A firgice ya ɗago yana bin Bilkisu da kallon tausayi, sai a lokacin ya fahimci irin abin da ta ce masa tana ji a cikin jikinta. Kamar Bilkisu ba ta san da komai ba, ta matsa kusa da shi ta ce.
"Me aka rubuta a ciki, ba ni mu gani." Naɗe takardar ya yi, don ba ya son ta gani ya cusa a aljihu ya ce.
"Ƙarasa shararki babu damuwa." Haɗe fuska Bilkisu ta yi ta ce.
"Kamar ya babu damuwa Abban Sayyid? Ya za a yi a ga laya a ɗakina kuma a ce ba zan gani ba, salon haka kawai a ce asiri na yi tun da dama yanzu ni ce mai lefi." Rasa abin da zai faɗa mata zai yi, sai kawai ya fice daga ɗakin ya shiga ɗakin Amina. A lokacin da ya shiga tana kwance, saboda a kwana biyun gabaɗaya ba ta jin daɗin jikinta. Kullum cikin tashin zuciya da kasala take, tana ganinsa ta tashi zaune a hankali. Cikin zafin rai Hafiz ya miƙa mata ya ce.
"Mene ne wannan? Me kika aikata haka Amina?"
Ita warin busasshen naman ma tayar mata da zuciya ya yi, ta ɗan yamutsa fuska ta ce.
"Kamar ya ya? Mene ne wannan kuma" Takaici ne ya kama shi, rai a matuƙar ɓace ya shaƙo wuyanta yana jin kamar ya zabga mata mari ya ce.
"Ina tambayarki mene ne wannan kina tambayata? Baƙar munafuka algunguma, ashe dama haka kike ban sani ba?" Hankali Amina ba ƙaramin tashi ya yi ba, duk sai ta birkice jikinta ya fara rawa saboda Hafiz bai taɓa birkice mata irin haka ba.
GIDAN ALHAJI UMAR
Alhaji yana fita Shukura ta yi shiru, don ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba. Bata taɓa tsammanin har kawo wannan shekarun yana son Hajiya Karima haka ba, ta shi ta yi ta buɗe drowerta ta kwaso kayanta da duk wani abu da za ta buƙata ta saka a akwati. Tana shirin saka mayafi ya dawo ɗakin. Da mamaki yake bin ta da kallo, har lokacin fuska babu walwala ya ce.
"Ina za ki?"
Kuka Shukara ta saka, ta ce.
"Wurin mahaifiyata zan tafi, gara na je can tun kai da matarka ba ku kashe ni ba. Idan na haife maka ɗanka sai ka je ka ɗauka ka kawo mata." Hankalin Alhaji ne ya tashi, cikin sauri ya riƙo hannunta ya ce.
"Haba Sjukura, kawai saboda wannan maganar za ki yi fushi ki tafi gida? Tun da haka ne to zan kai ki ɗaya daga cikin gidajena na bayan gidan nan ki zauna. Haka ya yi miki?" Girgiza kai Shukura ta yi ta ce.
"Salon idan ba ka gidana wani ya haura mini kafin ka zo duk abin da za a yi an gama ko? Wallahi ba zan iya zama a wani gidan ba. Ni kawai ka bar ni na tafi, idan ta fitar da kajin na dawo."
Duk yadda Daddy ya so Shukura kar ta tafi fir ta ƙi amincewa, don haka ya ce zai kai ta ta yi kwana biyu idan ta ji daɗin jikinta sai ya dawo da ita. Hajiya Karima tana gani Shukura ta shirya ta fita, aka ɗauki ƙatuwar akwatinta aka fita da ita. Sai daga baya Alhaji yake ce mata ta je gida ta kwana biyu saboda ba ta jin daɗin jikinta.
Bayan da Daddy ya tafi, Shukura tana shiga gida ta wassafa wa mahaifiyarta abin da ya faru. Bayan ta gama sauraronta ta ce.
"Shukura abin da na fahimta ko za ki yi kissa fa dole sai mun haɗa da neman taimako. Don gaskiya na lura ba za mu cimma manufarmu ba, har sai mun kawar da hankalin mutumin nan. Saboda na lura ba ƙaramin so da shakkar tsohuwar guzumar nan yake yi ba, kin ga kuwa zama bai kama ni ba. Yadda ubanki ya mutu ya bar ni a talauci, na sha wahalar kula da ku tun kuna ƙanana ke da ƙannenki. Dole yanzu mu tara dukiya mu huta, tun da lokacin hutun ne ya zo." Shukura ta yi zaraf ta ce.
"Ai Inna shi ya sa na kafe kai da fata na ce sai na zo gida, wallahi na tsani matar nan da 'ya'yanta. Komai za ki ji ya ce Hajiya, komai Mamana yadda kika san na shaƙe shigiyar yarinyar nan haka nake ji." Taɓe baki Innar Shukura ta yi ta ce.
"Wannan ƙaramar alhaki ce, ki bari mu gama da ubanta na ta mai sauƙi ne." Ajiyar zuciya Shukura ta sauke ta ce.
"Ai ita mun ma kusa rabuwa tun da aurenta bai fi wata guda ba yanzu, don ma saurayin ne ya ce a ƙara masa sati biyu saboda uzurin gabansa. Yanzu ya za a yi Inna?" Miƙa hannu Innarta ta yi ta ce.
"Kawo kuɗi, ni kuma yanzu na bazama sha yanzu magani yanzu." Jaka Shukura ta zuge ta ɗebo kuɗi masu kauri ta miƙa mata. Nan take Innarta ta ɗauki mayafi ta fice ba ita ta dawo ba sai dare, don su Shukura har sun yi bacci suka ji motsinta. Sai da safe Inna ta fara yi wa Shukura bayani.
"Wannan baƙar ledar da kika gani, a yadda ya ba ni a haka ya ce mu binne ta. Mai binnewar yana yi yana ambatar sunan Alhaji Umar, sai kuma wannan ruwan rubutu ne da za ki sha ki yi wanka da shi." Murmushi Shukura take yi tana gyaɗa kai,