Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 46

15K to 18K   out of 137.8K words

dosa, amma gudun ɓacin ransa ya sa suka ce masa a'a. Komawa ya yi wurin da ya bar su Shukura, ya dubi Hajiya Karima ya ce.

"Ke ki je ɗaki Hajiya, zan zauna da ita zuwa nan da sallar asuba." Da ido Hajiya Karima ta bi shi, saboda ɓacin rai ko tanka masa ba ta yi ba ta nufi ɗaki zuciyarta tana suya. Cikin ɗaki Shukura ta shiga, Daddy ya rufe mata baya. Suna shiga ta shige jikinsa, tana runtse ido alamun tsoro take ji. Sannu a hankali yanayin salon zaman da suke yi ya sauya. Shukura ta shiga aika masa da saƙonni masu birkitarwa, ko kaɗan Daddy bai yi niyyar biye mata ba. Amma yanayin saƙon da take aika masa ya sa shi yi wa zuciyarsa biyayya, ya shiga mayar mata da martani. Jin Shukura tana ƙoƙarin kai shi matsayar da bai yi niyya ba, ya sa shi ɗagowa cikin wani irin yanayi ya ce.
"Baby mu bari sai na dawo nan ko?" Cikin kissa Shukura ta fashe masa da kuka tana narkewa a jikinsa ta ce.
"Amma ai ni ba haramun ba ce a wurinka, wai dama haka za ka dinga wulaƙanta ni ban sani ba." Yadda ta ƙarasa maganar tana haɗe jikinsa da nata ya sa jin wani abu yana fisgarsa a kanta, ya sunkuya ya laso hawayenta cike da so ya ce.
"Ba na son kukanki baby."

"To ni idan ba ka so ka daina hana ni." Ta furta tana sake aika hannunta cikin jikinsa. Cikin kissa da kisisina Shukura ta cigaba da sarrafa Alhaji har sai da suka biyawa juna buƙata, sai daga baya duk ya ji bai ji daɗi ba. Ko babu komai ya san wannan lokacin na Mommyn Mami ne. Shukura da gayya ta fita ta ɗora ruwa a tukunya, tamkar rana haka ta dinga buga tukunyar lokacin da za ta ɗebi ruwa. Sai da ta ɗora musu sannan ta koma ɗaki ta narke a jikin Daddy.

Hajiya Karima tana shiga ɗaki ta haɗa kai da bango saboda damuwa, ba ta yi tsammani ba sai ji ta yi hawaye yana bin idonta. Babban abin da ya fi ɓata mata rai, yadda ake ƙoƙarin yi wa 'ya'yanta sharri amma ƙiri-ƙiri Alhaji ya turbuɗawa idanunsa toka ya bi bayan matarsa.

"Dama akwai ranar da Daddyn Mami zai fifita mace a kan 'ya'yan da na haifa? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ta furta domin ta samu zuciyarta ta yi sanyi. Kwanyarta ce ta tushe, zuciyarta duk babu daɗi. Don haka ta miƙe ta fita domin ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila ko ta ji daɗi a ranta, tana fita ta nufi banɗaki don ta kama ruwa a nan ta ji motsin ruwa alamun ana wanka. Tana shirin komawa ɗaki ta ga Shukura ta fito, hannunta riƙe da na Daddy daga shi sai towel a ɗaure a ƙugunsa. Wani abu ne ta ji ya daki zuciyarta, sai ta yi kamar ba ta gansu ba. Ta shiga banɗaki ta kama ruwa sannan ta ɗauro alwala, ta nufi ɗakinta tana jin wani irin ɗaci a ranta.

Shukura daɗi ta ji a zuciyarta, duk da ta ga Daddy duk ya birkice. Doguwar riga ya zura ya nufi ɗakin Mommy cike da sanyin jiki, a lokacin da ya je ta idar da raka'a ta biyu. Cike da borin kunya ya riƙo hannunta ya ce.

"Ai ɗazu da kika ganmu ruwa na watsa saboda zafi, kin san garin kwana biyu..."

"Ban tambaye ka ba Daddyn Mami. Ko wuta ka watsa wannan ba damuwata ba ce tun da kai da iyalinka ne, wannan sirrinku ne ba sai ka tona ba." Hajiya Karima ta katse shi cikin ɓacin rai, ganin yanayin da take ciki ya sa shi kama kansa. Ta sake tayar da sallah yana nan zaune duk jikinsa a sanyaye.
Har gari ya waye Hajiya Karima ba ta ba wa Daddy fuska ba, shi ma ganin haka ya sa ya fara nan-nan da ita, bini-bini sai ya tambaye ta ko tana son wani abu. A kwana na biyun Hajiya Karima Shukura ba ta yi komai ba, lafiya ƙalau suka kwanta har Daddy ya koma ɗakinta.

Sannu a hankali zamansu ya cigaba da tafiya, sai dai kusan kullum Mommy danne zuciyarta take yi. A ɓangare ɗaya kuma tana ƙara dannar Ruƙayya, don sautari ta sha cewa za ta tare da a kan wasu abubuwan da take yi a gidan ta mata magana. Amma sanin Shukura irin matan nan masu sharri ne ya sa take haƙurƙurtar da ita.
Duk da an raba girki, amma wani lokacin Shukura tana sani sai ta ce wa Daddy ba ta yi girki ba na Hajiya Karima za ta ci. Haka zai je har ɗaki ya saka Ruƙayya ta zuba mata, kuma duk wannan abin da take yi Mommy ba ta taɓa tanka mata ba. Da ta lura da hakan ba zai kawo fitin ba, sai ta tsiri duk ranar girkinta za ta kira Daddy ta ce masa ba ta da lafiya, ko kuma ta ƙirƙiro wani abin da ba za ta yi girki ba. Idan ya ce zai taho mata da abinci sai ta ce masa ya kira Ruƙayya ya saka ta girka mata, tun Ruƙayya tana yin kara har haƙurinta ya fara ƙarewa. Ana cikin haka watarana Shukura ta yi wa Daddy waya, ta ce za ta yi baƙi kuma a ƙaryarta ta ce masa ba ta jin daɗi. Ruƙayya tana tsaka da typing ɗin assignment a laptop ɗinta, Daddy ya kira ta ya ce ya ta je ta karɓi ATM ɗin Shukura za ta yo cefane ta mata girkin baƙi. A ranar cike da ƙosawa ta ce.

"Yanzu Daddy saboda Allah matar nan kullum lafiyarta ƙalau sai ta dinga ce maka ba ta lafiya, gaskiya Daddy ni na gaji."

Daga can ɓangaren Daddy ya ce.
"Mamana kina son na saɓa miki ko? Idan mahaifiyarki ce ta saka ki za ki faɗi haka? Daga yau idan na sake jin ta saka ki abu kin yi mata musu wallahi ranki zai ɓaci." Tana jin Daddy yana mata faɗa ta fara hawaye, ba don ta so ba ta je ta karɓa cike da raini Shukura ta faɗa mata duk abin da za a saya.

Ana cikin wannan yanayin Shukura ta fara laulayi, sai ta fara tsiro musu da tsirfa kala-kala. Watana rana Daddy yana dawowa da yake a ɗakinta yake, sai kawai ta fashe da kuka. A rikice ya riƙo ta ya ce.
"Me aka yi miki Shukura?"

Shukura ta share hawayen idonta ta ce, "Waɗancan kajin da Hajiya ta zuba wallahi cutata suke yi, kullum sai na yi amai ya fi sau biyar saboda warin kashinsu har nan yake zuwa. Kuma idan ina aman ji nake kamar ɗan cikina zai zube, gaskiya ni dai ka saka ta fita da su wallahi."
Hankalin Daddy ne ya tashi da jin furucinta, sai kuma ya yi shiru yana nazari saboda Mommyn Mami ta kusa shekara goma tana sana'ar kiwon kaji, kusan duk shekara sai ta zuba na sallah ƙarama, sallah babba da na maulidi. Kwantar da kai Daddy ya yi ya ce.
"Ai na ga a bayan gida suke Shukura, kuma duka kajin yanzu ko wata ɗaya ba su yi ba. Ga shi kin ga da yawa ta zuba su, a ƙalla za su kai guda ɗari ko fi ma. Zan sayo miki turarurruka..."

"Ka san dai ba na son ƙamshin turare tun da na samu ciki, wallahi ni dai idan ba za ta fita da su ba sai dai na bar maka gidanka ka sake ni. Dama ai ka fi sonta da ni, tun da ita ce uwar 'ya'yanka. Wa ya sani ma ko dama cikin jikin nawa ne ba ka so."
A rikice Daddy ya ce.

"Ba zan iya rabuwa da ke ba Shukura, bari na je na same ta." Daddy ya furta yana fita da sauri, Shukura ta faɗa kan gado tana sakin dariyar ƙeta.



Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

*ADVERT*
Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman


Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

SHAFI NA SHIDA

A lokacin da Alhaji ya shiga ɗakin Mommy tana zaune tana waya, gani ya yi ta yi rubutu a cikin littafin da take lissafi da shi.

"Eh rannan an kawo mini buhun dusa ashirin, wancan lissafin ai mun gama da shi. So nake a ƙaro mini buhu biyar, yanzu nawa zan ciko kuma?" Amsa aka ba ta daga can ɓangaren sannan ta ce.

"To shi kenan, zan turo da kuɗin."

Mommy ta ƙarasa maganar ta kashe wayar, jikin Alhaji ne ya yi sanyi. Duk sai ya ji fargaba ta cika shi, Hajiya tana ɗagowa ta sakar masa murmushi ta ce.
"Daddyn Mami ka shigo ina waya, wallahi lissafi muke da Halliru mai kaji. Ina tunanin ma zan ƙaro guda ashirin fa, saboda Ɗan Fulani suya sport ya ce yana kamun guda tamanin." Murmushin yaƙe ya yi ya ce, "Eh haka ne, dama zuwa na yi mu yi wata magana a kansu."

Amsa masa ta yi Alhaji ya zauna ya yi shiru, kallonsa ta yi ta ce.
"Ina jinka Alhaji."
Shiru ya sake yi gabansa yana faɗuwa ya ce, "To dama... game da kiwon kajin nan ne... to kin san Shukura ciki gare ta, shi ne..."

"Shi ne me?"

Mommy ta katse shi da sauri, saboda ta fahimci akwai abin da yake tafe da shi. Abba ya ce.
"Wai warinsu yana damunta, har tana jin kamar za ta yi ɓari idan tana amai." Wani kallo Mommy ta yi masa, wanda hakan ne ya sa shi yin shiru da bakinsa. A ƙufule ta ce.
"To yanzu me ta aiko ka a yi?"

"Nake ganin tun da sun kwana biyu, me zai hana ki fitar da su ai za a samu masu saye. Ko ni ina da mutanen da za su saya, saboda kin san me laulayi. Idan ya so bayan ta haihu..."

"Alhaji!"

Hajiya ta kira shi sunansa cikin ɓacin rai, a sanyaye ya ɗago ya ce.
"Ina jin ki."

Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun da nake da kai, ba na ja'inja a kan maganar da ka faɗa. Amma ka sani a wannan karon ba zan amince da maganarka ba. Ka sani na kai shekara goma ina sana'ar kiwon kaji, tun ina kiwo da kaji biyar har Allah ya sa na ci gaba. Amma yanzu rana tsaka ka zo ka ce wai matarka ba ta son warin ka ji, kajin da suke can bayan gida sune warinsu har..."

"Kina nufin ban isa da gidana ba kenan? Ko kina nufin kin fi ni iko da gidana?" Alhaji ya katse ta. Girgiza kai ta yi ta ce.
"Ba haka nake nufi ba, amma wallahi a wannan karon sai dai ka yi haƙuri." Cikin zafin rai Alhaji ya ce.

"To na dakatar da kiwon na ki ma gabaɗaya, saboda kawai na ce ki bari har zuwa lokacin da za ta haihu shi ne za ki faɗa mini magana." Baki sake Mommy take kallon Alhaji, ya miƙe ya nufi hanyar fita sannan ya waigo ya ce.

"Zuwa nan da gobe akwai mutanen da za su yi miki maganar kajin, idan kuma ba haka ba ni da kaina zan sa a fitar da su." Har ya saka ƙafa zai fita Hajiya ta bi bayansa da sauri ta ce.

"Ina mai tabbatar maka idan ka fitar mini da kaji wallahi-wallahi sai dai ka zauna da Shukura a gidah nan ba ni ba." Cak! Daddy ya tsaya, rai a ɓace ya waigo ya ce.
"Wato kaji sun fi maganata kenan? Me kike nufi?"

"Ina nufin zan bar gidanka?" Ita ma ta ba shi amsa kai tsaye.

"Saboda kina baƙinciki da abin da za ta haifa? Yanzu dama akwai ranar da za ki ƙi jinina Karima? Saboda kawai na ce ki yi haƙuri zuwa wani lokaci za ki faɗi haka? Wato kin fi son ta yi ɓarin cikin kenan?" Ahaji Ya furta, Mommy da ranta ya gama ɓaci ta ce.
"Idan duniya Shukura za ta haifa maka wallahi ba na baƙinciki ko ƙyashi, saboda na san na wuce ta har abada ni da 'ya'yana ne a gaba. Amma wallahi ba zan ɗauki kowanne irin cin kashi da yarinyar nan za ta yi mini ba."

Kamar Alhaji zai yi magana sai kuma ya fice daga cikin ɗakin zuciyarsa tana suya. Can ɗakin Shukura ya shiga, tana ganinsa ta tashi zaune ta ce.
"Ya ake ciki ne?"

Dafe kansa ya yi ya ce, "Wallahi ta ƙi amincewa, ni na rasa yaushe Hajiya ta fara musu da ni." Shukura tana jin haka ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya riƙo ta ya ce.

"Don Allah kada ki ɗaga hankalinki, wannan ba abin damuwa ba ne. Wallahi na yi bakin ƙoƙari don ta amince amma fir ta ƙi amincewa. Har tana ce mini za ta bar gidan nan idan aka fitar mata da kaji." Da sauri Shukura ta ɗago ta ce.

"To sai me? Ba sai ka sake ta ba tun da ba za ta bi umarninka ba. Daɗin abin ai ba ita kaɗai ce matarka ba." Da wani irin sauri Alhaji ya fisge jikinsa daga jikin na Shukura, har sai da ta tsora ta. Rai a ɓace ya nuna ta ya ce.

"Ko a mafarki kada ki sake tunanin zan iya rabuwa da Hajiya Karima, wannan matar da kike gani ita ce komai nawa. Kuma ban auro ki saboda na daina sonta ba, ina son matata domin ita ce rufin asirina. Duk wani mataki da kika ga na kai, wallahi ta silarta ce." Alhaji ya gama faɗa ya fita daga ɗakin a zuciye.

GIDAN HAFIZ

Bayan Hafiz ya watsa ruwa, zama ya yi daga shi sai kayan shan iska.A gefen Amina ya zauna, ya fara bin ta da wani irin kallo. Murmushi ta sakar masa, ya shafo fuskarta ya ce.

"Na yi kewarki Meena."

Cikin zolaya ta ce, "Ba wani nan ni ban ga alama ba." Matse ta yi a jikinsa tsam, ta saki 'yar ƙara kaɗan lokaci ɗaya suka saki dariya. Janye jikinta ta yi ta ce.

"Akwai tea akwai drink wanne za ka fara sha?"

Lumshe ido Hafiz ya yi ya ce. "Da ke zan fara mana." A ɗan shagwaɓe Amina ta ce.

"Habibi ka fiye wasa fa."

Sauka ya yi ƙasa, Amina ta zuba masa ruwan shayi a kofi, ta buɗe fulas za ta zuba masa abinci, daga bakin ƙofa suka ji Bilkisu ta zuro kwano cike da abinci ta ce.

"Idan har kin yi haka don ki kashe ni ko ki kashe 'ya'yana, In Shaa Allahu sai dai ki gani a kanki. Saboda kin ɗebi naki abincin da na Abban Sayyid shi ne mu za ki hala ka mu, ai shi kenan Allah Yana kallo." Daga haka Bilkisu ta bar wurin.
Kallon juna Hafiz da Amina suka yi, a sanyaye ta miƙa hannu ta ɗauko kwanon tana kallonsa, sai dai ko kaɗan ba ta ga komai ba. Abu ɗaya ta ji shi ne wari-warin fetir, Hafiz ya ɗauki abincin ya shinshina ya ce.

"Me kuma ya kawo warin fetir a abinci?" A sanyaye Amina ta ce.

"Wallahi ban san yadda aka yi ba. Lafiya ƙalau na yi girki na gama." Ajiye kwanon ta yi, ta fara zubawa Hafiz shi ma. Yana matso da plate ɗin gabansa ya ji warin fetir ya doki hancinsa, da sauri ya ɗago ya ce.
"Amina wai me yake faruwa ne? Wannan wanne irin wulaƙanci ne za ki saka mana fetir a cikin abinci? Ina ce galan ɗin fetir daban na mai ma daban?" Idanun Amina suka ciko da ƙwalla, ta saka hannu ta share hawaye murya tana rawa ta ce.

"Wallahi ban san komai ba, lafiya ƙalau na gama girki."

"Ƙafa gare shi man ko hannu da zai zuba kansa? Shi kenan sai ki san yadda za ki yi da shi." Hafiz ya furta cikin fushi sannan ya zura doguwar rigarsa ya fice. Bilkisu da ke ɗaki murmushin ƙeta ta saki, ta ɗauko waya ta kira shi tana ji ya ɗauka ta ce.

"Abban Sayyid yanzu ya zan yi da yara? Ga shi suna kukan yunwa."

"Ki dafa musu taliya mana." Hafiz ya faɗa a ɗan faɗace. Kwantar da murya Bilkisu ta yi ta ce, "Ai ina tsoron ko man ne yake da fetir kada na sake saka musu a koma 'yar gidan jiya." Shiru Hafiz ya yi sannan ya ce.

"Ki fara dubawa kafin ki zuba,

6 / 46