Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
wayarta a caji, kallon-kallo suka shiga yi wa junansu. Mama ba ta taɓa tsammanin Mommy za ta kula Shukura ba, amma sai ta ga ta saki murmushi ta ce.
"Aunty yau baƙi ne a gidan namu?"
Mama ta ce, "Eh wallahi, Shukura ce ta zo wurin Daddyn yara. Wai Daddyn Mami ne a asibitu ba shi da lafiya." Ɗan taɓe baki Mommy ta yi ta ce.
"Oh dama fa haka ake ta fama, Allah Ya sawaƙe." Daga haka ta ɗauki waya ta nufi ɗakinta.
Baba malam ne ya shiga cikin falon, Shukura tana ganinsa ta cigaba da share hawaye cikin shasshekar kuka.
HAFIZ
Su Hafiz suna zuwa asibiti likitoci suka shiga yi wa Amina tambayoyi tana ba su amsa, gwaje-gwaje suka yi mata suka tabbatar da cikinta lafiya ƙalau yake ba su ga wani abu da yake damunta ba. Sai kuma jininta da ya ɗan yi ƙasa kaɗan, abin da suka ce sun gani a jikin Amina kenan. Gudun kada Hafiz ya gano Amina, sai ta ce musu tana ɗan yawan ciwon kai. A nan suka sake ba su shawarwari a kan ta dinga samun bacci wadatacce, ta kuma dage da cin abubuwa da ke gina jiki. Suna fitowa daga asibitin ya ga kiran mahaifinsa, sai da suka shiga adaidaita sahu sannan ya ɗauka cikin girmamawa. Bayan sun gaisa Baba ya ce.
"Hafiz kana ina ne?"
Hafiz ya ce. "Baba yanzu na fito daga asibiti."
"To idan ka gama ina son ganinka kai da Amina."
Baba ya furta a gajarce, sannan ya katse wayar.
Gaban Hafiz ne ya faɗi, don tun da ya ji haka ya san ba ya wuce Bilkisu ce ta kira ta faɗa masa wani abin. Ita kanta Amina sai da ta ji gabanta ya faɗi, da yake ba ta saba irin waɗannan ƙarairayin ba har gani take kamar idan suka je za a iya gano ciwon ƙarya take yi.
Lokacin da suka ƙarasa gidansu Hafiz, su Sayyid suna tsakar gida suna wasa. Oyoyo suka yi masa, bayan da suka gaisa da mutanen gidan sannan suka wuce ɗakin Mahaifinsa. Tun da ya ga su Sayyada jikinsa ya ba shi Bilkisu tana gidan, sai da suka gaisa sannan Baba ya sa aka kira Bilkisu. Fuska a haɗe ta shiga ta nemi wuri ta zauna, Baba ya dubi Bilkisu ya ce.
"Bilkisu maimaita mini abin da kika ce ya haɗa ku."
Kamar tana jira, Bilkisu ta shiga wassafa jawabin abin da ya faru. Baba ya dubi Hafiz ya ce.
"Shin abin da matarka ta faɗa haka ne?" Gyaɗa kai ya yi sannan ya cigaba da cewa.
"Baba ni ban hankaɗe Bilkisu, saboda wata manufa ko don na wulaƙantata ba. Yanzu Baba saboda kwananta ne, sai ta ce ba zan kai Amina asibiti ba don ba ta da lafiya? Ita Bilkisun sau nawa idan kwanan Amina ne, za ta kira ni ta ce yaro ko ita ba lafiya amma haka nake fita na ba su kulawa."
Ajiyar zuciya Baba ya yi ya ce.
"A gaskiya Bilkisu ba ki kyauta ba, ko Hafiz ba ya nan ai ke mai kai 'yar'uwarki asibiti ne." Baba ya nuna Amina, sannan da sake kallon Bilkisu ya ce.
"Ke Amina da Bilkisu na dawo gare ku, ku ji tsoron Allah a zamantakewarku. Ku sani duk wacce kuka cutar Allah ba zai bar ku ba, zan yabi Hafiz ba don yana ɗana ba. Amma ku sani yana ba kin ƙoƙarinsa a kanku, ku haɗa kanku ku rungumi mijinku ku zauna lafiya." Baba ya jima yana yi musu nasiha, har jikin Amina ya yi sanyi ta ji za ta watsar da duk wani zaman ƙarya da makirci da ta tsira. Ta saka wa ranta duk rintsi za ta cigaba da zaman haƙuri, da kyautatawa mijinta. Musamman da Baba ya nuna musu muhimmanci haƙuri da ladan da mace take samu ya yin ibadar aure.
A kwanaki biyun da suka biyo baya, gidan Hafiz suna zaune lafiya ƙalau. Saboda Amina gabaɗaya ta zubar da makamanta, ta cigaba da zama da Bilkisu da zuciyarta ɗaya tsakaninta da Allah kamar yadda ta zo tun farko. Ita ma Bilkisu a haka nunawa ta yi kamar komai ya wuce, don haka ta dinga kwantar da kai har Hafiz ya gama sakin jiki gidansa ya zauna lafiya.
Ana cikin haka kuma sai Bilkisu ta tsiro da wani sabon makircin, don har lokacin da cikin Amina ya tsufa ba ta cire rai da fitar da ita daga cikin gidan ba. Sabon layi Bilkisu ta saya ta saka a wayarta, idan Amina da Hafiz suna zaune sai ta tura mata saƙon soyayya. Idan ka ga irin saƙon za ka yi tsammanin saurayi ne ya turawa budurwrsa da yake tsananin so. Tun abin bai fara damun Amina ba, har watarana ta taɓa yin replay da cewar wrong number ne. Tun ana tura mata text har ta kai wani lokacin ana kiranta a waya, amma idan ta ɗauka sai ta ji an yi shiru. Tafi-tafi sai ya zamana idan ta ɗauka sai dai ta ji an ce ana sonta, ko an yi kewarta. Wani zubin har cewa ake yi an yi kewar ni'imarta. Tun da ta ji ire-iren miyagun kalaman, ba ta sake ɗauka ba. Kuma ba ta taɓa tunanin faɗa wa Hafiz ba. Ita kaɗai ta bar abin a cikin ranta, don ba ta ɗauka lamarin zai yi tsamari ba.
Watarana da daddare Hafiz yana ɗakin Bilkisu yana cin abinci, sai ji ya yi ana ƙwanƙwasa ƙofa. Miƙewa ya yi ya fita ya buɗe ƙofar, wani almajiri ya yi gani da wata leda a hannu. Almajirin bayan ya gaishe shi ya ce.
"Ai ko ni aka yi."
"Kawo saƙon, waye ya turo ka?" Hafiz ya furta yana kai hannu zai karɓa, da sauri almajirin ya janye ya ce.
"Mutumin ya ce kada na ba wa kowa sai Amina."
Da mamaki Hafiz ya ce.
"Wani ne ya turo ka? Wane ne shi?"
Almajirin ya ce, "Eh wani ne a mota, ya ce na kawo mata."
Zuciyar Hafiz ce ta fara tafasa, sai ya daure ya ƙwala wa Amina kira. Da ƙyar ta yunƙura ta taso, saboda yadda cikinta ya tsufa. Tana zuwa rai a ɓace Hafiz ya ce.
"Ga aikenki nan sai ki karɓa."
Da mamki Amina ta dubi Aljamirin ta ce, "Kai waye ya aiko? Daga ina kuma?" Almajirin ya waiga ya ce.
"Wani ne a mota ya ce na kawo miki, ya ce a ce miki wanda ya ɗauko ki daga asibiti ne rannan. Wai ki kira shi idan kin ga wannan saƙon." Cikin mamaki Amina ta sake cewa.
"Ni kuma? An ya nan aka ce ka kawo kuwa? Gaskiya ba nan ba ne."
"Ni dai nan ya ce na shigo na kawo wa Amina."
Almajirin ya faɗa, Amina za ta sake magana Hafiz ya ce.
"Yana ina mutumin?"
Almajirin ya ce, "Ai yana ba ni da ya ga na shigo ya tafi." Zuciyar Hafiz har ɗaci take yi ya kai hannu ya karɓi ledar ya ce.
"Jeka kawai." Yaron ya juya ya fita, Hafiz ya buɗe ledar yana leƙawa. Farin hanki ya gani da turare, sai zoben azurfa da aka ƙawata mai ɗauke da alamun gift daha masoyi. Sai ya ga wani ɗan memo mai kyau, yana buɗe ciki ya ga an rubuta.
' _Ga ɗayar numberta nan, idan kin nemi waccan layin ba ki samu ba. Daga masoyinki da ke burin kasancewa da ke koda bayan kin haihu ne._'
Nan take idanun Hafiz suka kaɗa jajir saboda tsananin kishi, kallon da ya wurga wa Amina ne ya sa cikinta ya karta.
"Ina wayarki take?"
Hafiz ya furta da wata irin murya, jikinta har rawa yake ta ce.
"Ta...tat... tana ɗaki."
Bai amsa mata ba ya wuce ɗakinta rai a ɓace.
In Shaa Allahu gobe za mu gama book 1💃🏻👌🏻
Masu son karanta book 2 za su biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA BIYAR
BABA MALAM
Da mamaki Baba malam ya dubi Shukura ya ce.
"Lafiya dai na ga kina hawaye? Hajiya ko wani abin ne ya faru?" Ya tambaya yana kallon Mama da ke zaune a gefe, girgiza kai ta yi ta ce.
"Babu abin da ya faru Alhaji, na ji dai ta ce Daddyn Mami yana asibiti babu lafiya. Ban sani ba ko jikin nasa ne, amma dai tun da ta shigo take hawaye."
Baba malam zai yi magana Shukura cikin kuka ta ce.
"Don Allah Yaya ku gafarce ni, ku yafe mini ku yafe wa Daddyn Mami. Wallahi yanzu haka yana can a asibiti rai a hannun Allah. Don Allah ka yafe mini Yaya, na san gabaɗaya kowa ya tsane ni saboda abin da ya faru."
Jin rashin lafiyar Daddy ya sa gaban Baba malam ya faɗi, amma gudun kada ya nuna wa Shukura damuwarsa sai ya ce.
"Tun daga haihuwar mutum dama ai ransa yana hannun Allah Shukura, Allah Ya ba shi lafiya. Batun tsana kuma da kika yi, duk cikinmu babu wanda ya tsane ki. Ƙarƙari dai abin da muka yi, mun dai tsani halinki ne."
Shukura a cikin ranta ta ce, 'Ko ni ɗin kuka tsana kun yi ta banza, yanzu ma so nake na yi amfani da ku kafin buƙatata ta biya.' Amma a fili sai ta ce.
"Dama na zo ne na nemi yafiyar Hajiyan Mami, wallahi na yi nadamar duk abubuwna da na aikata a baya. Don Allah Yaya ku yafe mana, wallahi sharrin shaiɗan da ruɗin ƙawaye ne." Shiru Baba malam ya yi ya ce, "Allah Ya yafe mana gabaɗaya, amma wannan ba magana ce da za a yi ta a taƙaitaccan lokaci ba. Muna buƙatar isasshen lokaci tukunna, idan ya so sai a tattauna abin da ya dace." Kamar mutuniyar kirki haka Shukura ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce.
"Na gode Yaya, Allah Ya ƙara girma." Ganin ya yi shiru ta sake cewa.
"Yaya don Allah ku taimaka ku leƙa a sibitin nan, Dadyn Mami yana jin jiki sosai." Karɓar adireshin asibitin ya yi, sannan ya ce ta wuce zai taho.
Bayan tafiyar Shukura Mama ta dubi Baba malam ta ce, "Alhaji wallahi ban yarda da makirar yarinyar nan ba. Haka kawai nake ji a jikina ba da zuciya ɗaya ta yi wannan zuwan ba." Miƙewa tsaye Baba malam ya yi ya ce.
"To ai kowa ya yi na gari kansa, idan ma da wata manufa ta zo Allah ya mayar mata da mugun nufinta kanta. Ki cewa su Mu'alim su shirya za mu je duba shi yanzu."
Mama ta amsa masa sannan Baba malam ya wuce ciki don ya shirya. Sai da ya kira 'yan uwansa ya sanar da su, sannan ya fito shi da su Haidar da 'ya'yansa suka wuce asibiti. Kusan lokaci ɗaya motar Shukura da ta su Baba malam ta shiga harabar asibitin, saboda Shukura ta biya ta store ta yi musu sayayyar abubuwan da za a buƙata. Ganin ta taho hannuwanta ɗauke da manyan ledoji, ya sa Baba malam ya ce su Haidar da Mu'allim su karɓa, babu yadda Haidar zai yi don dai ya san ba shi da damar musawa. Amma da babu yadda za a yi ya karɓi kayan hannun Shukura, suna shiga reception suka hango Inna tana zaune jigum. Shukura tana ganinta har za ta mata magana, cikin zafin nama Inna ta tsinke da mari. Ɗgowar da za ta yi ta sake tsinke ta da mari, da sauri Baba malam ya matsa ya ce.
"Subhanallah! Haba Hajiya ya da haka? Ba ki ga a yanayin da take ciki ba ne?" Inna ta fashe da kuka ta ce.
"Alhaji ka bar ni na kashe yarinyar nan na huta da ta kaicin da ta ƙunsa mini, ashe dama kishiyarta Hajiya ba ta gidan? Sai ɗazu da ta kira ni take sanar da ni abin da ya faru. Wallahi Shukura ke dai ba ki da mutumci, albasa ba ta yi halin ruwa ba." Inna ta ƙarasa maganar tana sake kai wa Shukura duka, da sauri Shukura ta yi bayan Baba malama tana kuka saboda marin da Inna ta yi mata ba ƙaramin shigarta ya yi ba. Baba malam ne ya kare ta cikin lallashi ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri hajiya, idan ka ce za ka biye ta halin yara sai ka nakasa su a banza."
Inna ta fyace majiya haɗe da rushewa da kuka sannan ta ce.
"Alhaji yarinyar nan so take ta ɓata mini suna? Me ta aikata haka? Wallahi kin ci sa'a da Alhaji Ya ƙwace ki, amma wallahi idan ba ki saka Alhaji ya mayar da matarsa ba babu ni babu ke. Mara mutumci ina zaman-zamana za ki ja wa zuri'ata zagi, ke dai ba ki ji daɗin halinki ba." Inna ta furta tana sake kai wa Shukura duka.
Da ƙyar Baba malam ya samu ya shawo kan Inna ta daina barazanar kai wa Shukura duka, haka a gaban kowa ta dinga jaddada idan Shukura ba tayi bakin ƙoƙari, ta saka Daddy ya mayar da Hajiya Karima ba za ta tsine mata. Wannan abin da ta yi ya sa mutane suka dinga yabonta, a ɓangare ɗaya suka dinga kallon Shukura a matsayin wacce take da uwa tagari amma ba ta yi koyi da ita ba.
Lokacin da suka shiga ɗakin Daddy yana kwance ya ƙurawa saman silin ido, har suka ƙarasa wurin bai sani ba. Baba malam ne ya dafa hannunsa ya ce.
"Sannu Umaru."
A hargitse Daddy ya ɗago ya ce, "Yaya kai ne? Don Allah tare kuke da Karima?" Shukura da ke gefe ta ji wani abu ya daki zuciyarta, don ko mai irin sunan Mommy ba ta son ta ji an ambata.
Baba malam ya ce, "Umaru ka nutsu don Allah, ba mu kaɗai ba ne a wurin nan. Ga yara ma sun zo duba ka." Sai a lokacin ya ɗago ya dubi su Haidar cike sa so. Su kansu ba ƙaramin kewar mahaifinsu suka yi ba, ganin ya rame sosai ya sa Haidar ya matsa kusa da shi jiki a sanyaye ya ce.
"Sannu Daddy ya jikin?"
Daddy da idonsa ya fara zubar da ƙwalla ya ce.
"Haidar! Haidar ina Mommynku ko ba ta zo duba ni ba?" Gyaɗa masa kai Haidar ya yi ya ce.
"Ta ce a duba ka, Mami ma ta ce gobe za ta zo duba ka."
"Ai na warke Haidar, Yaya don Allah ka taimaka ka ce Karima ta dawo. Wallahi ban san lokacin da na sake ta ba, wallahi sharr..."
Inna ta katse maganar Daddy sakamakon jifan Shukura da ta yi da takalmi ta ce.
"Munafuka kin ji abin da mijinki yake faɗa ko? An ya Shukura zuciyar musulunci gare ki, wallahi tun wuri ki je ki nemi yafiyar mijinki, kuma ki bi duk yadda za ki yi ki sa ya dawo da matarsa idan ba haka ba wallahi kada ki sake takowa inda nake."
Daddy har cikin ransa ya ji daɗin abin da Inna ta yi, Baba malam ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri haka, ba na jin daɗin furucin da kike mata."
"Alhaji haushin yarinyar nan da nake ji, wallahi ji nake kamar na maƙure mata wuya ta mutu. Ace ki zo ki samu mace da mijinta sama da shekara ashirin, ki ƙulla makircin da za ki sa mijinta ya sake ta. Alhaji ta kyauta kenan?" Inna ta furta tana kumfar baki.
Baba malam ya jinjina kai ya ce, "Ba ta kyauta ba, kin san ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba. Yanzu dai ki je gida ki huta Hajiya." Inna ta ƙarasa bakin gadon ta duba Daddy sannan ta yi musu sallama ta fita.
Su Haidar ne suka fita waje, Shukura ta maƙure a bango ban da hawaye babu abin take yi. Daddy ya sauko daga gadon, ya russuna a gaban Baba malam ya ce.
"Don girman Allah yaya ka taimaka ka dawo mini da Karima, wallahi tallahi ban san yadda aka yi na rabu da ita ba. Na yi rashinta a kusa da ni Yaya, don Allah ka tausaya mini."
Daddy ya ƙarasa maganar yana hawaye, jikin Baba malam ne ya yi sanyi, zai yi magana Shukura ta matsa ita ma tana sake ƙwaƙulo hawayen munafurci ta ce.
"Don Allah yaya ka taimaka mini, hankalina a tashe yake da jin furucin mahaifiyata a kaina. Don Allah yaya ka taimaka ka ba wa Mommyn su Mami haƙuri." Baba malam ne ya ce ta tashi ta zauna a kujera, saboda yanayin da take ciki tun da cikinta ya tsufa.
Daga Daddy har Shukura zama suka yi dirshen suna ba shi haƙuri, sai da ya gama sauraronsu sannan ya ce.
"Duk na ji maganganunku, to amma ku sani. Ba ni zan zauna da kai ba Umaru, Karima ce mai zama da kai, ita ta san irin zaman da ta yi da ku. Don haka sai da amincewar Karima sannan za a mayar muku da aurenku, idam ta yarda shi kenan idan kuma ba ta amince ba dole