Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
Amin.
SHAFI NA SHA BIYU
GIDANSU MAIMUNA
Ganin irin miyagun ɗabi'un da Maimuna ta ɓullo wa Nazir, ya sa shi tattara ta gabaɗaya ya yi watsi da ita. Dama can ba ya dawowa gida da wuri, don haka ko da ya kai dare idan ya ci abinci hakan ba ya hana shi ya sake fita. Har mamakin Maimuna yake, saboda gabaɗaya halayenta sun sauya. Maimunan da ya sani a baya ko kara ya ajiye ba ta isa ta ƙetare ba, duk da taurin zuciya irin nata sai da ta kai ta kawo ya sa ta yi laushi, ta yadda ko musu ba ta isa ta yi masa ba. Amma a yanzu Maimuna ta yi masa rainin da ko ƙannensa ba su yi masa ba, ya hana ta shiga mutane ya hana ta hulɗa da maƙota. Ya hana ta riƙe babbar waya, ya hana ta shige cikin danginta sosai. Ya hana ta cigaba da karatu duk don kada ta saba da shiga jama mata su zuga masa ita. Amma sai ga shi a rana tsaka tana shuka masa rashin mutumci son ranta, don a yanzu ba ta shakkun idan ya faɗi magana ta mayar masa. Dalilin haka ne ya sa ya tsiri zuwa majalisar gaban gidansa, da yake wasu maƙonsu suna zama shi ma ya bi sahunsu.
A ɓangaren Maimuna kuwa hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, saboda tana jin fitarsa take yin zaraf ta ɗauko wayarta ta kunna data su fara shan soyayya ita da Jafar. Maimuna bayan whatsapp har sabon Acc na facebook ta buɗe, amma ba da sunanta na ainahi ba sai kawai ta rubuta 'Matar Mai Rabo' ta cigaba da fantamawa tana harkokin gabanta.
Zaman Nazir a majalisar kenan, ya samu maƙocinsa Adam yana nuna wa ɗayan maƙocin wani rubutu da ya ga an yi posting ya ce.
"Ni ban san me matan aure suka ɗauki aure ba, bini-bini za ka ga rubutu ace wai a bata shawara ga halin da take ciki. Don Allah dubi wannan, wai mijinta ya hana ta cigaba da karatu bayan an yi yarjejeniya a ba ta shawara."
Lawan ya saki tsaki ya ce, "Sakarcin fa, ai mata wasu a cikinsu mahaukata ne. Na tabbata a nan wasu za su zuge ta har ta kashe auren."
Haruna ya ce, "A'a ba lalle ba, ka san wasu matan suna jin nauyin tambayar 'yan'uwansu neman mafita. Sai suka zaɓi a ɓoye sunansu tun da ba wani ne zai gane su ba."
"Kai wannan fa ba magana ba ce, shi ya sa tun matata tana budurwa na ce mata ban yarda da wannan hawa soshiyal midiyar ba."
Adam ya faɗa cikin ɓacin rai. Jin haka ya sa Nazir ya yi zaraf ya ce, "Ai wallahi tun farko shi ya sa na datse duk wata alaƙa da za ta sa a hurewa iyalina kunne, ba sai ta fita ko tana hawa soshiyal midiyar kanta zai sake wayewa ba? Don lalacewa kwanaki haka na ji ana maganar wata matar aure tana soyayya da wani matashi. Shi ma kuma a onlayin ɗin suka haɗu." Haruna ya yi dariya ya ce, "Wallahi ina faɗa muku mace fa kariyar Ubangiji ce, wallahi duk kaffa-kaffarka idan mace ta so ninke ka a baibai wallahi ba za ka taɓa ganewa ba. Kai tsanani fa ba shi ne ba, ka yi ƙoƙari iya iyawarka a kan kula da iyalinka. Kada ka saki gidanka sakaka, kuma kada ka tsananta. Sauran sai ka bar wa Allah, shi zai tsare maka su."
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa, sai sauran ma suka miƙe. Nazir ya kaɗe rigarsa ya ce.
"Ai wallahi wannan zance ne, kai dai kawai kowa ya ji da gidansa. Amma ka saki mace take walwalawa ai ka riga da ka daɓa wa kanka wuƙa, musamman ma ace ka bar ta tana aiki ko sana'a kuɗi yana juya mata. To kuwa sai abin da ka gani, don matan auren yanzu wallahi mafi yawa sun gama lalacewa."
"A'a gaskiya Alhaji Nazir, waɗannan zantukanma bai kamata mu dinga danganta su da iyalanmu ba, Allah Ya nesanta mana su da dukkan wani abin ƙi."
Adam ya furta, sannan suka yi wa junansu sallama.
Gida Nazir ya nufa sai kuma tunanin Maimuna ya faɗo masa, don haƙurinsa yana gab da ƙarewa. Tun da ta yi watsi da shi, a duk lokacin da ya neme ta sai kawo masa wani uzurin.
Maimuna tana kwance ta ji motsin shigowar Nazir, da sauri ta ɗauki wayar ta ɓoye ta koma ta kwanta. Haka kawai ya ji kamar ba bacci take yi ba, don haka ya zauna agefenta yana bubbuga hannunta.
"Maimuna! Maimuna."
A yatsine ta tashi tana faɗin, "Ya aka yi?"
Mamaita kalaman ya yi yana jin ɓacin rai, ya ɗan haɗe fuska ya ce.
"Ki tashi mu yi magana."
"Ni bacci nake yi sai da safe ma yi maganar."
A ɗan tsawace ya ce, "Ki tashi na ce, yanzu nake son mu yi maganar." A hankali ta tashi yana sakin guntun tsaki.
"Me ya sa kike ƙaurace mini, me ya sa duka kika canza kin raina niMaimu kada ki bari ki kai ni bango."
Murmushi ta saki cikin halin ko inkula ta ce, "Wane kalar ɓacin ranka ne bn sani ba Nazir? Ai sai dai ka faɗa wa wata macen idan ka sake aure."
Idanunsa suka kaɗa jawur saboda ɓacin rai, ya matso kusa da ita ya damƙi hannunta yana faɗin.
"Uban waye yake zuga ki da yake hure miki kunne har kika raina ni?"
Ido cikin ido ta kalle shi ta ce, "Sai ka fara sanar da ni wanda ya zuga ka har ka tauye ni, ka kuma dakushe burikana saboda zalinci ka ƙuntata mini ta hanyar tsauwalawa. Sannan ni kuma na sanar da kai wanda ya zuga ni."
Shiru ya yi yana kallonta kamar a ranar ya taɓa ganinta, cikin rashin damuwa ta ce.
"Idan kuma ba ka da abin magana sai na yi kwanciyata."
"Ni kike faɗa wa haka Maimuna."
Nazir ya tambaye ta a zafafe, sai kuwa ta mayar masa da martani cikin sauri kamar tana jira.
"Na faɗa maka Nazir, na fa jima ina tara ka a zuciyata. Wlalahi-wallahi daraja ɗaya kake ci a wurin, wato mahaifina. Da ace mahaifina ba ya raye, wallahi da na jima da datse alaƙar auratayyata da kai."
Tas! Ta ji ya sauke mata mari a fuska, zuciyarsa tana suya ya nuna ta da yatse.
"Duk rashin mutumcin da kike tunƙaho da shi, wallahi daidai nake na sauke miki su. Kin san wane ne ni sarai, ba zan ɗauki wannan iskancin ba." Maimuna ta dafe kumatu tana bin sa da kallon tsana, har zai fita ta ce.
"Allah Ya isa ban yafe maka ba, kuma wallahi indai ni ce ba zan taɓa komawa yadda nake a baya ba."
Nazir bai kula ta ba ya fita, kai tsaye cikin store ɗin ta ya shiga. Ya ɗauko wani ƙaramin mukulli ya rufe shi, sannan ya ɗauke ƙaramar wayar Maimuna da ke falo ya koma ɗakin.
Duk abin da yake yi tana jin sa, don ba sabon abu ba ne idan sun yi faɗa ya rife store ɗinta na kayan abinci. Sai dai kullum idan zai fita ya ɗebo mata wanda za ta dafa. Fulo ta ga ya ɗauka ya tafi falo, ta taɓe baki tana nuna ko a jikinta. Don ta sake ɓa ta masa rai sai ta furta.
"Ko a jikina, wai an tsikari kakkaura."
Ta gyara kwanciyarta, tana ayyana irin abin da za ta yi wa Nazir don ta huce takaicin marin da ya yi mata.
GIDAN INNA
Tun bayan fitar Sadiya gidan Inna ya kacame da iface-ifacen kukan yaranta, Inna ban da kyara da hantararsu ba abin da take yi. Fauziya ce ta janyo su ta rarrashe su, da ƙyar Zainabu ta ta yi shiru. Zazzaɓi ne ya rufe Fauziya, saboda duk cikin matan 'yan'uwan Kabiru Sadiya ce ta hannun damanta, suna ba wa junansu shawara musamman da ya kasance Sadiya ba ta da kowa a garin. Sai su rufe su binne ba tare da wani ya ji labari ba, domin dama Kabir da Yaya Nura sune masu ƙaramin ƙarfi. Gudun raini ne ya sa su Fauziya suka kama kansu, don haka ma ya sa matan su Yaya Tasi'u ko gidansu ba sa zuwa.
Abincin kari Fauziya ta haɗa gabaɗaya har yaran Sadiya, bayan ta gama ta zuba wa yaran. Suka fara ci, sai dai ta lura har lokacin sun gagara sakin jikinsu.
Kabir kafin ya tafi sai da ya kira Mai adaidaita sahu ya fita da keken ɗinkin Fauziya, kai tsaye shagonsu ya wuce da shi. Ya yi sa'a Ogansu yana nan, yana ganinsa ya washe baki ya ce.
"Allah Ya taimaki Oga"
Oga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce, "Kb namu."
Janyo keken ɗinki ya fara yi har ya samu ya shigar da shi cikin shagon, sai ya ce, "Oga ya ka ga keken? Ay na faɗa maka sabo ne bai ji jiki ba."
Tasowa ya yi daga mazauninsa ya sake leƙa keken ya ce, "Gaskiya ne kuma na ga butterfly ne. A ajiye shi a gefe, zan sa a yi masa service sai ku cigaba da amfani da shi."
Kabir ya matsar da keken ciki, sai kuma ya saki murmushi ya ce.
"To Oga cittar fa?"
"Idan za ka tafi an jima ka yi mini magana, zan ba ka rabin, rabin kuɗin kuma sai zuwa nan da rana ita uku."
Ba haka Kabir ya so ba, ya so ace duka kuɗin ya samu. Amma duk da haka ya san idan ya karɓi kuɗin, za su cika a haɗa a kai gidansu Surayya.
Tun daga wannan ranar zaman Fauziya da Inna ya fara ɗaukan sabon salo, sai dai Fauziya tana bakin ƙoƙarinta don ganin wani abu bai haɗo su ba. Duk safiya idan ta yi abinci tana bakin ƙoƙarinta, don ta ga ta ba wa su Zainabu abinci ko yaya ne duk da ciyarwarsu ta koma hannun Inna kacokam.
Kwana biyu da tafiyar Sadiya, har gida Yaya Tas'u ya zo ya ƙarewa Yaya Nura faɗa a kan sakin da ya yi wa Sadiya. Don wani lokacin idan suka yi faɗa tana zuwa ta kai ƙararsa wurinsa, shi kuma sai ya je ya yi masa faɗa. Idan aka yi haka sai Sadiya ta samu sassaucin rashin mutumcinsa, bayan kwana biyu kuma ya ɗora daga inda ya tsaya.
Duk aikin da Sadiya take yi wa Inno sannu a hankali ya dinga dawowa kan Fauziya, lokaci ɗaya ta yi wani irin duhu ga rashin hutu daga wannan sai wannan. Murmurewar jegon da ta yi duk sai ta zuge, a ɓangare ɗaya ga tunanin halin da gininsu yake ciki. Saboda halayen Kabir sun dawo mata sababbi, don tana yi masa magana yake rufe ta da faɗa. Idan Inna ta jiyo sai ta ƙarasa bakin ƙofa ita ma ta cigaba da tofa albarkacin bakinta.
Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta lura da take-taken Inna tana son fara ɗora wa su Na'ima talla ba. Duk da ba ta fito ta faɗa ba, amma ta lura da yanayin shaguɓen da take yi. Hakan ne ya sa ta shiga takura wa Kabir a kan ya saka su a makaranta, amma sai dai ya ce mata ba shi da kuɗi. Kuma ta rasa wurin da yake zuwa, a kullum ya dawo gida da wuri haka zai buga wankan ƙananan kaya ko manya ya fice daga gidan. Wani lokacin ma sai ta yi bacci yake dawowa, saboda gajiya ta sa ana yin sallar Isha'i take yin bacci.
Watarana suna zaune bayan magriba yana tsaka da shiri ta ce.
"Abban Na'ima!"
"Ina jin ki."
Ya amsa mata yana saka belt ɗin wandonsa.
"Wai kasuwar ɗinkin ce yanzu ba a samu ko yaya? Zaman yaran nan babu makaranta baya zai mayar da su, don Allah ko Islamiya ce ka saka su."
Sai da ya ƙarasa komai sannan ya ce, "Islamiyyar ma ai ba kyauta ake zuwa ba, ki bari idan na samu kuɗi zan saka su. Kin san dai yadda abubuwa suke ƙara tsada."
Saboda takaici ba ta tanka masa ba, ya gama shiryawa yana fesa turare, a daidai lokacin wayarsa ta kawo haske da yake a silent take. Da sauri ya ɗauke wayar ya saka a aljihu har zai fita Fauziya ta ce, "Abban Na'ima ni fa ban gane wannan shige da ficen nan da kake yi ba. Ina za ka je ne da daren nan?"
"Haifata kika yi da za ki tsare ni da tambaya, ina ruwanki da wurin da za ni? Kin san dai yanzu na daina shaye-shaye ballanta ki kafa mini zargi."
Sai kawai ya saka kai ya fice daga ɗakin, shiru Fauziya ta yi tana nazari.
"Tabbas ruwa ba ya tsami banza, wallahi akwai abin da Abban Na'ima yake ƙullawa." Ta faɗa a sanyaye, tana jin nadamar ba shi kekenta. Saboda ta san da ko da kuɗin gyaran da take yi ne za ta iya samu ta biya musu kuɗin makaranta, a nan take tunani ya faɗo mata a kan ta fara yin wankau tun da yanzu Sadiya ba ta nan. Sai kuma ta ga sam ba za ta iya wankau ba, don wani lokacin ko wankin yaranta ta yi wuni take bayanta yana ciwo. Sai kuma dabara ta faɗo mata a kan ta fara yin kitso, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta a kan idan gari ya waye za ta shiga maƙota duk ta faɗa musu.
Kabir yana fita daga gidan ya ciro wayarsa ya latsa lambar Surayya yana faɗin, "Na fito fa baby."
Surayya ta akashe murya ta ce, "Tun ɗazu fa nake ciki da muradin son ganinka gwarzona."
Amsa mata ya yi sannan ya kashe wayar. Adaidaita sahu ya tara kai tsaye ya wuce unguwarsu Surry, waya ya ciro ya kira ta sannan ta fito. Kamar kullum idan za su yi zance a soron gidan suke yi, hakan ce ta sa yanzu ma ta shimfiɗa musu dadduma a soro.
Rungumo Surayya ya yi, ita kuma ta kamo bakinsa ta fara sakar masa kiss. Nan take Kabir ya fara birkice mata, ya shiga kai hannunsa cikin sassan jikinta. Jingina suka yi da bango, ita ma Surry ta fara sarrafa shi da hannunta tamkar ƙwararriyar matar aure.
"Baby na gaji fa!"
Kabir ya furta cikin wani irin yanayi.
"Kamar yau ne fa, ba yanzu saura wata goma ba. Ni fa ba don 'yan gidanmu ba, da ko ba lefe tsaf za a sha biki. Don tun lokacin da aka tsayar da rana na so a saka wata shida."
Janye kansa ya yi daga cikin ƙirjinta ya ɗago yana kai hannunsa ciki jikinta sannan ya ce, "Amma kafin lokacin me ya sa ba za ki ɗan dinga rage mini zafi ba dear?"
Surry don ta zolaye shi sai ta ce, "Ba kana da mata ba, ya kake abu kamar wanda bai taɓa aure ba."
"Mtswww."
Ta ji Kabir ya ja dogon tsaki sannan ya ce, "Ana maganar matan da suka cika cikakkun mata, kina sako mini zancan waccan abar. Don Allah ki taimaka mu dinga zuwa gidan can kina yi mini dabaru." Wani irin daɗi Surry ta ji, saboda ta jima da fahimtar matarsa ba komai ba ce a wurinsa. Ta sake maƙale shi ta ce.
"Shi kenan my love, zan yi ƙoƙari na dinga yi wa su Yaya dabarar fita, kasan tun da aka saka ranarmu yake saka mini ido sosai."
Sake haɗe bakinsu Kabir ya yi sai da suka ji alamar motsin za a fito, da sauri ya sake ta yana sauke numfashi, Surry ta wayance da cewa.
"Hasko nan mu ga ko can azurfar taka ta yi."
Wayarsa ya zaro ya fara haska mata, kamar masu neman azurfar gaske. Suna cikin haka Yaya Umar ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Ya so sake yamutsa Surry ta nuna masa ya yi haƙuri za ta dinga zuwa can gidan, saboda tana tsoron kada yayanta ya sake dawowa ya kama su.
Cike da kewar Surry Kabir ya fito daga soron gidan, yana fitowa babu jimawa ya zaro wayarsa. Misscall ɗin Farha ya gani har sau uku, ya latsa layin nata yana karawa a kunne ya ce.
"Ina fatan sarauniya ba ta yi fushi da ni da."
"Idan na yi ma ai ka saba kanainaye zuciyata har ta yi maka afuwa."
Farha ta furta cikin shagwaɓa. Murmushi ya yi yana jinjina baiwar da yake da ita. Kabir irin mazan nan ne masu iya tsara zance da kanainaye zuciyar 'yanmata. Ya ƙwarai sosai wurin iya yaudara da kife mace, kuma yana ɗaya daga cikin maza masu kule-kule da ƙoƙarin dandanlar arzikin jikin budurwa.
"To yanzu dai ayi mini afuwa cajina ya ƙare, zan kira ki da asuba. Ina fatan za ki yi bacci da ni a zuciyarki."
Kafin su yi sallama sai da suka yi musayar kalaman soyayya sannan ya katse.
Lokacin da ya ƙarasa gida tuni Fauziya ta yi bacci, don haka ya ɗauki buta ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa sannan ya koma ɗaki.
Sannu a hankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya watanni suna shuɗewa, Fauziya ta fara kitso babu laifi tana samun ɗan kuɗin kashewa. Da kanta ta saka yaran a wata makaranta da ake yi boko da Islamiyya, sai dai duk da hakan ba su tsira ba sai da Inna ta fara ɗora musu tallar barkono ranar Alhamis da Juma'a. Tun Fauziya tana kara har ta gagara haƙuri ta yi wa Inna magana, a lokacin faɗa ta rife ta da shi amma da shi ma