Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
da suka tsaya a kan kula da shige da ficen yaransu. Daga ƙarshe Fadil ya yi masa godiya, sannan ya wuce gida a gurguje saboda ya kusa makara.
Malam sule dama abin nema ne ya samu, saboda yana daga cikin malaman da suke hora ɗalibai. Yana shiga ya dubi Laraba ya ce ta je gaban allo ta tsaya, sannan ya ce mata idan ya gama biya musu darasi sai ta karanta masa abin da ya rubuta.
Laraba ta wurga masa harara a fakaice, ta koma ta tsaya ta haɗa rai domin ko kaɗan ba ta san raini. Tana daga tsaye wasu daga cikin 'yan ajin suka dinga yi mata gwalo, wasu kuma suna tsokanar dukan da aka yi mata. Malam Sule subject ɗin English language yake ɗaukarsu. Kuma a ranar Comprehension ya yi musu, sai ya rubuta musu short story mai taken 'Tortise and the goat' kasancewar duk cikin ajin babu mai textbook. Sai da ya karanta da turanci sannan ya fassara musu da hausa, ya dubi Laraba da tun da aka fara karatun hankalinta yana kan ƙofa, tana kallon dukan makarar da ake yi wa sauran ɗalibai. Don ko bayanin da ya yi da hausa ba ta gama saurare. Malam Sule ya haɗe rai ya ce.
"Maza biya mana, ki fara yi da turanci sai ki fassara."
Shiru laraba ta yi tana bin allon da kallon, don ta tabbata da allon yana magana ƙila zai iya baya mata kansa saɓanin ita da babu abin da ta gane sai baƙaƙen a b c d, su ma idan da za a saka mata wuƙa a wuya ko guda goma ba za ta iya karantawa ba.
Laraba ba ta yi tsammani ba ta ji ya zuba mata bulala a baya, don haka ta taƙarƙare ta fara yi masa wani irin yare wanda ita kansa ba ta san me yake nufi ba. Duk yadda Malam sule ya kai ga mazewa sai da ya kawar da kai ya saki murmushi, sannan ya ce ta fassara da hausa. A nan ma Laraba babu tsiyar da ta tsinana, sai sokiburutsu da ta dinga yi masa. 'Yan ajinsu kuwa suka shiga ƙyaƙyata dariya suna yi mata ihu, Laraba ta ƙulu sosai don haka ta yi kukan kura ta faɗa kan Suwaiba ta rufe ta da duka, don ta fi jin haushinta dama saboda har gwalo take mata tana raɗawa na kusa da ita abin da za su faɗa. Da sauri Malam Sule ya fisgo Laraba saboda ya yi mata maganar duniya ta ƙi ji, ya shiga dukanta da zafafe. Zuciya ta kuma ciwo Laraba ta sake cukumo Suwaiba, tana kai mata naushi a baki har sai da ya fashe. Malam Sule mari ya zabga kata, sai a lokacin Laraba ta ja da baya ta dube shi a haukace cikin ɓacin rai ta ce.
"Kai malam kada ka sake dukana, wai ba kai ne ɗan gidan Bala mai satar agwagwa ba ko an faɗa maka ba mu sani ba." Wani abu ne ya caki zuciyar Malam Sule, saboda bai taɓa tunanin za ta yi masa wannan bankaɗar ba. Cikin borin kunya ya rufe ta da duka, sai da ya zane Laraba sannan ya riƙe hannunta ya dinga bin ajujuwa da ita, yana saka kowanne prefect ya yi mata bulala biyar kuma 'yan aji su yi mata ihu. Ranar zuciyar Laraba ta gama dagulewa, don haka ta ci alwashin ko sama da ƙasa ce zaata haɗe ba za ta ƙara zuwa makarantar ba. Kuma sai ta hukunta iyaye da 'ya'yan da suka ci zarafin, shi kuma Malam Sule ta ci alwashin sai ya yabawa aya zaƙinta a wurinta.
Duk irin zaman doya da manjar da suke yi tsakanin matan Yaya Inu, sai da suka ji jikinsu ya yi sanyi a kan sakin da ya yi wa Abu. Duk da ba baƙon abu ba ne a wurinsu amma irin son da suka san Yaya Inu yana yi mata ne ya ba su tsoro domin ba su taɓa tsammani ba. Hansatu ta fi kowa shiga damuwa saboda duk matan da Yaya Inu yake saki, idan suna da yara ƙarƙashin kulawarta suke komawa, kasamcewar ita ce uwargida a wannan lokacin. Sun jima suna janjantawa da suka ji motsinsa sai kowacce ta shiga aikin gabanta.
A yanzu Indo ita ce matar Yaya Inu ta uku, ita ce take bin Larai. A ƙalla ta kai shekara huɗu a gidansa, 'ya'yanta uku duka maza. Babban ɗanta Uzairu bai fi shekara uku da watanni ba, sai mai bin sa Ya'u mai shekara ɗaya da rabi. Sai kuma jaririn da take goyo mai wata shida Hannafi.
A washegarin ranar da aka saki Abu akwai bikin da matar yayan Indo ta gayyace ta, a wani ƙaramin gari da ke gaban garinsu. Tun safe Indo ta katsa wanka ta ɗauko galleliyar atamfarta yadi ta saka, ta yi wa su Larai sallama tana jin kamar za ta je wata sabuwar duniya. Larai a ranta take jin dama ita ce take da 'yan uwa a birni, da suke biki har ake gayyatarta da ko babu komai ta samu abin yi wa su Hansatu gori.
A gidan kamun bikin da Indo ta je ne, ta tarar da wata mata da aka ɗauko Hajiya Zanni mai gyaran aure tana yin lecture ma'aurata. Matar irin masu safarar magungunan mata daga Kano zuwa Saudiyya ne, ita take koyar da su kissa da dabarun jan hankalin miji wanda zai mallake zuciyar miji. Saboda yadda take yin lacture cikin batsa ya sa mata sai shewa suke, mafi yawa daga ciki suka ƙuduri niyyar yi wa mazajensu daga ciki har da Indo, da take ganin kamar ta mallake Yaya Inu ta gama. Daga ƙarshe Hajiya Zanni mai gyaran aure ta ɗebo magunguna ta fara tallatawa.
Jikin Indo yana rawa ta zaro ɗan canjin jakarta ta sayi wani magani mai suna, kin yi wa kishiya fintinkau da idonka idona. Cike ɗoki Indo ta tafi gida, koda ta je gida haka ta dinga kallon su Larai a sheƙe tana yi musu kallon tausayi, mai tafe da izgilin na yi muki nisa don a yanzu sai yadda na yi da mai gida.
Daɗin sai ya haɗe mata biyu sakamakon ita ce da girki ranar, tun kafin magriba Indo ta gama komai. Ta caɓa wanka, ta ɗauko wani turarenta na Binta sudan, ta bulbule jikinta da shi kamar yadda ta ji Hajiya Zanni ta ce namiji yana son ƙamshi. Indo har ƙaguwa ta yi a idar da sallar Isha'i Yaya Inu ya shigo gida, sai ga shi a ranar ya yi jinkirin shigowa don har kusan goma saura. Haka ta zauna a gefen gado har ta fara gyangyaɗi, sannan ta ji shigowarsa. Da sauri ta ɗauko Hannafi ta kai shi gefen Uzairu ta kwantar da shi, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce ba a zuwa turaka da yara suna takurawa uwargida da mai gida. Turarenta na Binta sudan haɗe da jan miski ta ɗauko ta sake bulbulawa, ta janyo wani fakeken gajeren wandonta a drower shi ma ta shafe shi da jan miski. Ta nufi ɗakin Yaya Inu hannunta ɗauke da tiren abinci, dama daga ita sai ɗaurin ƙirji wanda hakan duk yana cikin lecture Hajiya Zanni. Tana shiga ta ajiye masa abincin a gefe sai kuma ta ja ta tsaya a wurin, Yaya Inu ya ɗago fitilarsa ya haske ta yana shirin yi mata magana sai ya ga Indo ta saki zanin jikinta ya faɗi ƙasa. Saboda duk huɗubar da Hajiya Zanni ta yi musu ta haddace ta kanta. Da mamaki Yaya Inu yake bin Indo da ke tsaye tumɓur sai ɗan kanfai, da wata sakakkiyar rigar mama a jikinta wacce suk ta zuge ta saki kamar gugar jan ruwa saboda yawan sakawa.
"Ke Indo lafiyarki kuwa?"
Yaya Inu tambaya a tsorace.
Indo ta ji daɗi har ranta, don ta ji Hajiya Zanni ta ce akwai wani shauƙi da miji yake shiga idan an yi masa haka. Indo ta fara harba ƙafa tana wani juyi ita a dole rawar India za ta yi a gabansa, Yaya Inu zai sake magana Indo ta wurga masa wannan burgujejen gajeren wandon da ta ɗauko, wanda ta jiƙe shi sharkaf da turaren miski da Binta sudan. Gajeren wandon ya sauka a saman fuskar Yaya Inu, ya yi sakatoto yana bin ta da kallon mamaki. Indo ta yi wani tsalle tana harba ƙafa haɗe da fisge rigar maman jikinta, kusan lokaci ɗaya ta kifar da kwanon miyar abincin Yaya Inu. Kuma a daidai lokacin rigar maman ta faɗa saman wuyan Yaya Inu da ya gama kai wa wuya.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[10/12/2024, 19:47] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA BIYAR
Ko kaɗan Indo ba ta damu da ganin ɓarnar da ta yi masa ba, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce duk cikin sirrikan da ta ba su babu na yarwa indai a ɓangaren mallaka da saye zuciyar miji ne. Don haka ta yi wata girgiza ta cake a wuri ɗaya, ta fara miƙa masa hannu ɗaya irin yadda jaruman india suke yi, idan za su miƙa wa masoyinsu hannu domin su yi rawa. Ta miƙe ƙafa gaba da zummar ta yi tsalle ta dira a gaban Yaya Inu, ta yadda za ta ɗago shi ta manna a jikinta kamar yadda Hajiya Zinni ta kwatanta musu, bisa tsautsayi ƙafarta ta harɗo labulen ɗakin ya faɗo a kanta. Kukan Hannafi ta fara ji sama-sama da alama ya tashi daga bacci, amma sai ta basar ta tunkari Yaya Inu da zuciya ta gama cika shi. Don yadda yake ji ransa ya ɓaci kamar ya tashi ya shaƙe Indo, saboda wannan sabon iskancin da take ƙoƙarin kawo masa. A gabansa ta tsaya tana wani rangaji, iska ta fara kaɗo cikin ɗakin saboda sanyin da ake busawa. Burgujejen gajeren wandonta ya fara kaɗo fuskar Yaya Inu, Indo ta yi masa wani far da idanu ta ƙanƙance murya ta ce.
"Taso mu yi rawa lantarkin zuciyata..."
Kalaman Indo suka katse sakamakon fisgowar da Yaya Inu ya yi mata, ta faɗi ƙasa daɓas! Gwiwoyinta suka bugu da ƙasa.
A tsammanin Indo shauƙin da Hajiya Zanni ta ce maza suna shiga ne ya fara kama Yaya Inu, don haka ta shanye zafin da ta ji ta sake wurƙila idanu da sunan fari tana wani banƙarewa kamar kazar mayu ta ce.
"Na jima ina alla-alla kwanakin girkina su dawo, saboda na shayar da kai romon soyayya..."
Takaici ya sake lulluɓe Yaya Inu, ya ɗaga hannu ya yi wa Indo mahangurɓa a fuska. Wani irin mummunan yanayi ya ratsa ta, don haka a gigice ta miƙe da niyyar ceton kanta. Yaya Inu ya shatalo ta da ƙafarsa ta faɗa kan miyar kukar da ta zubar.
A fusace ya ɗaga hannu ya zabga mata mari cikin fusata ya ce. "Wannan iskancin a gidan uban wa kika koyo shi? Wallahi ko kukar bulukiya ce a kanki sai na sauke miki ita."
Indo ta fashe da kuka tana jan jiki gefe ta ce, "Yanzu mai gida duk abin da na yi maka ban birge ka ba, saboda Allah duk wannan kissa da kisisinar..."
"Au to, sai yanzu na gano! Wato saken da kika samu na zuwa cikin gari, shi ne kika haɗu da siraran karuwai suka koya miki wannan karuwancin ko? To ba a gidana ba, tun wuri ki watsar da abin da yake kanki idan ba haka ba ki ƙara gaba." Shiru Indo ta yi tana share hawaye. Daga can bakin ƙofa Hansatu da Larai suka ƙaraso suna tambayar abin da ya faru saboda sun ji ihun Indo, Yaya Inu bai tanka musu ba saboda har lokacin haushin Indo yake ji. Ita ma Indo ban da hawaye babu abin da take yi, don haka kowacce ta ƙunshe dariyarta cike da ƙeta suka koma ɗaki. Saboda dama haushin Indo suke ji, a kan shan ƙamshi da kallon wulaƙancin da ta dinga yi musu.
A kunyace Indo ta tashi za ta fita Yaya Inu ya ce, "Kuma tun wuri ki gyara mini ɗaki tas, kika ɗebo siraran cinyoyi kamar tsinke ashana. Yo ni akwai wani iya shege da wata figaggiya za ta yi mini?" Takaici ya sake cika Indo, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zare rigar mamanta da ke saƙale a wuyansa. Ta ɗauki zaninta ta ɗaura sannan ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin, a cikin ranta ta shiga tsine wa Hajiya Zanni da miyagun shawarwarin da ta ba ta.
Washegari
Tun kusan kimanin ƙarfe huɗun asuba ya farka yake sharɓa kuka, tun yana yin na zuciya har ya dawo yin na sarari. Sautin sasshekar kukan da Baba Sale yake yi ne ya farkar da Uwale daga baccin da take. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, da sauri ta zaro ƙaramar wayarta a ƙarƙashin filo ta haske ɓangaren da Ɗan Bishir yake bacc. Ganin yana bacci cikin kwanciyar hankali ya sa, ta dubi Baba Sale ta ce.
"Me yake faruwa mai gida?"
A maimakon Baba Sale ya ba ta amsa sai ya sake kallon wurin Ɗan Bishir ya fashe da kuka. Jikinta ne ya yi sanyi don rabonta da ganin kukansa, tun wata rashin lafiya da Ɗan Bishir ya yi kusan shekara ɗaya da rabi kenan.
"Mai gida don Allah ka cire ni a cikin duhu, wallahi hankalina duk a tashe yake."
Uwale ta furta jikinta yana rawa, don ta ayyana abubuwa da dama a cikin ranta.
Baba Sale ne ya faɗa jikinta kamar wani sabon maraya, ya ja majina cikin kuka ya ce.
"Kamar kin manta yau ne za a yi wa Ɗan Bishir shayi! Yau ne fa wa'adin kwanakin da za a yi masa kaciya ya cika."
Baba Sale ya yi maganar yana share ƙwalla, haɗe da shigewa jikin Uwale kamar wani ƙaramin yaro. Ya ɗago murya a dashe saboda kukan da ya ci ya ce.
"Uwale hankalina a tashe yake, wallahi duk wani abu da zai taɓa lafiyar Ɗan Bishir ba na son shi..."
Kuka ya sake cin ƙarfinsa, takaici ya mamaye Uwale amma gudun kada su fara raba hali tun da asuba ya sa ta ce.
"To ya za a yi, ai dama kowa da haka ya fara. Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah na ji har an shiga masallaci."
A hankali Baba Sale ya fita yana jan majina, ya ɗauro alwala ya wuce masallaci. A lokacin da ya ƙarasa masallaci a raka'ar ƙarshe ake, bayan an idar ya tashi ya ciko raka'a ɗaya sannan ya yi sallama. Baba Sale hannu ya ɗaga ya fara zazzago addu'a, mutane ba su yi tsammani ba sai ji suka yi ya fashe. Sororo mutanen wurin suka yi, Yaya Ado har zai fita ya koma ya zauna. Duka mutane suka yi carko-carko suna kallonsa, Malam Rabe ne ya yi ƙarfin halin zuwa kusa da shi ya ce.
"Sale me yake faruwa ne?"
Baba Sale ya sharce majina ya fara wata shassheka kamar wanda uwarsa ta mutu ya ce, "Ina buƙatar addu'arku. Domin kowa ya san ɗana ɗaya ne a duniya wato Ɗan Bishir! Kuma ina fatan ya haifa mini jikoki ashirin da huɗu sai dai kash..."
Kuka ya sake cin ƙarfinsa. Gaban su Baba Labaran ya faɗi, don duk wanda ya ci karo da irin kukan da Baba Sale yake yi za ka ɗauka mutuwa aka yi masa. Cikin haɗin baki hankali a tashe duka mutanen cikin masallacin suka ce.
"Sai dai me?"
Baba Sale ya rungumo hannun Yaya Inu ya shiga goge fuskarsa da shi ya ce.
"Ku yi mini fatan a yi a gama wa Ɗan Bishir shayi, an jima Bala wanzan zai zo ya yi masa don ni ba zan iya ba. Ba ni da ƙarfin zuciyar ta guntule Ɗan Bishir."
Jin haka ya sa takaici ya mamaye su, a zafafe Yaya Inu ya fisge hannunsa ya ce.
"Kai dai ka zama gantalalle ɗan wahala. Yanzu shayin da za a yi wa Ɗan Bishir ne kake wannan iskancin, kai Allah Ya tsine iskanci da magoya bayansa. Shi ya sa ka sakar mana murya kamar an kunna generator kana ihu, Allah wadaran naka ya lalace."
Daga haka Yaya Inu ya fice daga masallacin rai a ɓace. Ɗaya bayan ɗaya haka mutane suka watse kowa yana mita, Baba Sale ya koma gida ya sake saka Ɗan Bishir a gaba yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki.
Tun da Ɗan Bishir ya tashi daga bacci Baba Sale ya ɗauke shi ya rungume, hatta abinci a baki ya dinga ba shi. Kimanin ƙarfe tara na safe Bala wanzan da yaransa suka ƙarasa ƙofar gidan, Uwale ce ta iya ɗaukar Ɗan Bishir ta miƙa masa. Domin Baba Sale uwar ɗaki ya shige ya haɗa kai da ƙarfen gado yana kuka. Saboda shekara ta uku kenan ana cewa za a yi masa shayi yana ɗagawa saboda soyayyar da yake yi masa. Yana nan zaune Inno ta aika kiransa, da ƙyar ya iya fita ya nufi sashenta fuskarsa ta kumbura saboda kukan da ya sharɓa. 'Yan'uwansa ya gani gabaɗaya a zaune, ya yi mamki matuƙa don haka ya zauna a gefe yana kallonsu. Inno ta dube su ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ta saki wani murmushi zuciyarta fes ta ce.
"Dalilin da ya sa na tara ku a wurin nan ba komai ba ne, illa na sanar da ku wani abin alheri kuma abin farinciki da ya tunkaro mu. Kuma na tabbata za ku ji daɗinsa, domin cigaba ne da zai iya kai ni aljanna da ku bakiɗaya."
Fuskarsu