Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   15 / 46

42K to 45K   out of 137.8K words

ko an so dole a zauna da ni."

Bilkisu tana rufe baki Amina ta saki dariyar rainin hankali sannan ta ce, "Ai duk na banza ne, tun da kika kasa riƙe shi har ya fita waje ya nemo ni domin ya samu kwanciyar hankali. Da kin isa da isarki ai da kin dakatar da shi daga aurena, ba ki san sakaci na rashin gamsarwa da kulawarki ne ya sa shi auro ni..." A zuciye Bilkisu ta kai wa Amina mari, a daidai lokacin Hafiz ya kawo kai ganin haka ya sa shi shiga ɗakin da sauri ya ce.

"Ke Bilkisu ba ki da hankali ne? Mace da ciki a jikinta kike marinta."

"Na mara ɗin, ko za ka rama mata? Ni ka san irin magamganun da ta furta mini..."
Tas! Ita ma Hafiz ya ɗauke fuskarta da mari. Amina da ke kwance a ƙasa ta saci kallon Bilkisu ta sakar mata gwalo, sai kawai ta fashe da kuka ta ce.

"Wayyo Allah cikina za ta kashe ni."

A hargitse Hafiz ya ɗago ta ya ce, "Sannu Amina, za ki iya tashi mu tafi ko na ɗauke ki." Kamar tana jira ta ce.

"Jiri nake ji ba zan iya tashi ba, ga shi dukan da ta yi mini cikina ciwo yake mini." Hafiz ne ya ɗauki Amina cak zai fita cikin sauri Bilkisu ta tare ƙofar ta ce.
"Wallahi babu inda za ka kai munafukar nan, kuma wallahi tun da ka mare ni sai na nuna muku ɗanyan kai."

"Ki matsa na wuce Bilkisu kada ki ɓata mini rai."

"Ba zan matsa ba." Bilkisu ta ba shi amsa kai tsaye, rai a ɓace ya sake cewa.
"Ki matsa na wuce Bilkisu, wallahi idan kika bari raina ya ɓaci ba za ki ji da daɗi ba."

"Wallahi sai dai ka yi duk abin da za ka yi amma ba za ku fita ba, saboda yau ranar girkina ce babu karuwancin da za ta nuna mini..." Bilkisu ba ta rife baki ba Hafiz ya hankaɗe ta ya wuce, daga can baya ta faɗi ƙasa warwasa don ba ƙaramij buguwa ta yi ba. Hafiz ya wuce da Amina ƙofar gida ya saka ta a Adaidaita sahu, sai da ya koma ya ɗauko katin asibitinta ya rufe ƙofar ɗakinta sannan ya fita suka wuce asibiti.
Bilkisu ta jima a wurin tana kuka, sai da ƙyar ta yunƙura ta shiga ɗaki. Ta sauya kayan jikinta, sannan ta shirya yaranta ta tasa ƙeyarsu gidansu Hafiz.

ALHAJI UMAR
Da mamaki Daddy ya dubi Baba malam ya ce.

"Yaya ina da Karima bayan wacce ka sani?"

Fuska a tamke babu alamun wasa Baba Malam ya ce.
"A da dai na sanka da Karima, amma a yanzu Karimar da na sani ba ka da hurimi da ita."

"Don Allah Yaya idan wasa kake yi mini ka daina, wallahi tallahi hankalina a tashe yake. Ina son na ganta, saboda mummunan mafarkin da na yi a kansu." Daddy ya furta a hargitse. Kallon da Baba malam ya yi masa ne ya sa shi shiga hankalinsa. Ya nuna shi da yatsa ya ce.

"Ni na yi kala da sa'anka ko wanda zai zauna yin wasa da kai? Kai Umaru! Kada ka raina mini hankali, Karima ba matarka ba ce. Ka koma can gidanka ka cigaba da zama da matarka, a yanzu haka tana gab da ɗaura aure. Idan kuma 'ya'yanka za ka karɓa, a yanzu zan shiga na taso maka su ka tasa ƙeyarsu a gaba ka tafi da su." Kafin Baba Malam ya gama magana tuni gumi ya wanke fuskar Daddy, hankali a tashe ya zube a gabansa ya ce.

"Don girman Allah kada ka yi mini haka Yaya, wallahi ni ban saki Karima ba. Yaya ka yi mini rai, wallahi ji nake ba zan iya rayuwa idan babu ita ba."

"Idan ka mutu kwananka ne ya ƙare Umaru, kada ka manta; a yanzu ba ni da uwa ba ni da uba. Don haka babu numfashin wani da zan rasa a yanzu, har ya ɗaga mini hankali. Ruwanka ne ka cigaba da rayuwa, ruwanka ne kuma ka zaɓi mutuwa. Amma ina me tabbatar maka, idan ka sake zuwa da maganar Karima gidan nan wallahi zan ba wa securities umarnin kada su bari ka sake shigowa." Baba malam yana gama magana ya shige ciki, da sauri Daddy ya bi bayansa sai dai kafin ya ƙarasa ya datse ƙofar. Daɓar! Daddy ya zauna a wurin yana jin duniyar gabaɗaya ta yi masa zafi. A nan barandar da Daddy ya zauna, yana nan zaune har aka kira sallar asuba, Daddy yana nan zaune Baba Malam ya fito zai tafi masallaci. A sanyaye Daddy ya ɗaura alwala ya bi shi suka wuce masallaci, sai dai kallon fuskar Baba malam da ya yi ya ji fargaba ta sake mamaye shi. A haka suka yi sallah suka dawo cikin gida, Baba malam yana gab da shiga cikin gida Daddy ya ce.

"Don Allah yaya, don zatin Ubangiji ka..."

"Umaru ba na son damuwa don Allah, yanzu haka kaina ciwo yake tun tashin da ka yi mini ina bacci. Ka je wurin matarka idan na yi nazari zan neme ka." Daga haka Baba malam ya wuce ya bar shi a tsaye. Kamar zai ɗora hannu a ka, haka Daddy ya wuce ya shiga mota ta nufi gida zuciyarsa a dagule.

Lokacin da ya je gida gari har ya yi haske, a lokacin da ya shiga Shukura tana zaune a takure cikin damuwa. Tana ganinsa ta miƙe zumbur kamar marar gaskiya ta ce.
"Baby ina fatan ka dawo lafiya?"

"Eh."
Kawai ya furta a taƙaice ya wuce ɗakinsa. Da sauri Shukura ta bi bayansa har ta shiga rai a ɓace ya ce.
"Get out please, ba na buƙatar hayaniya."

"Wai me kake nufi ne Alhaji? Ya za a yi a kan tsohuwar matarka ka dinga wulaƙanta ni. Wallahi ba zan ɗauka ba, idan ba za ka iya ba ka sallame ni sai ka dawo da ita."
Shukura ta yi maganar cikin tsiwa, saboda sabon da ta yi. A fusace Daddy ya ɗago ya ce.

"Idan haka kika zaɓa ki wuce gidanku, amma ki sani idan har bakinki ya sake furta magana marar daɗi a kan matata wallahi a bakin aurenki." A razane Shukura ta dube shi, jiki yana rawa ta ja ƙafa ta koma ɗaki. Sai da ta saka sakata sannan ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, a hankali ta janyo wayarta ta latsa lambar mahaifiyarta. Tana jin ta ɗauka cikin kuka ta ce.

"Inna don Allah ki yi wani abu, wallahi da matsala." Daga can ɓangaren Inna ta ce.
"Tun tasowa ta ban taɓa cin karo da matsala ba, don haka a yanzu ma ba zan ganta ba. Tun bayan sallar asuba na fito zuwa wurin malam, yanzu haka zan haɗa ki da shi a waya ki masa cikakken bayani." Bakin Shukura har rawa yake ta ce.

"Ba shi Inna, maza ba shi don Allah."
Tana faɗar haka ta miƙe ta shige banɗaki, don kada Daddy ya jiyo wayar da suke yi.


Littafin kuɗi ne 500 idan ya kammala 800 ne. Za a turo a acc Aisha Adam 3090957579 First bank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624.


Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA SHA HUƊU

Daga can ɓangaren Inna ce ta ba wa Malam waya, yana karɓa ya ce.
"Yarinya faɗi buƙatarki." Kamar Shukura tana jira ta ce.
"Malam duka aikin da ka yi mini a wancan karon ne ya lalace."

"Yarinya aikinmu ba ya buƙatar garaje, ki yi mana bayani dalla-dalla ta yadda za mu san yadda aka haihu a ragaya."
Malam ya faɗa a ɗan tsawace. Ta cikin wayar ta ji Inna tana faɗin.
"Ke Shukura ki shiga nutsuwarki mana, ki yi masa bayani dalla-dalla yadda zai fahimta." Tsawa ta ji Malam ya buga wa Inna ya ce.

"Tun kafin ki zo, muka san abin da yake tafe da ke. Kada ki sake cewa za a fahimtar da mu, domin mu masu sani ne. Kawai dai muna son ji daga gare ta ne, kin san waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi." Baki yana rawa ta ji Inna ta ce.

"Tuba nake malam, a yi mini aikin gafara."
Amsa mata ya yi, sannan ya sake yi wa Shukura magana. Tiryan-tiryan Shukura ta yi masa bayanin abin da ya faru, tun daga tashin Daddy daga bacci har zuwa dawowarsa. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce.

"Haƙiƙa kishiyarki ta tashi tsaye ba da wasa ba, kuma wannan birkicewar da kika ga mijinku ya yi asiri ne ta yi masa." Shukura ta yi zaraf ta ce.
"Ai wallahi na zargi matsiyaciyar nan."

"To wannan ba damuwa ba ne, tun da kayanki suka tsinke a gindin kaba. Za a yi miki aiki iya aiki, amma fa sai kin zubar da kuɗi. Saboda aikin za mu yi da baƙaƙen aljanu, kuma su kansu za mu zubar musu da jini. Ragowar kayan aikin ma idan muka faɗa miki su, idan za ki shekara ɗari ba za ki same su ba." Ta ji malamin ya yi mata bayani. Cikin sauri ta ce.

"A'a Malam, gara dai ka sayo da kanka. Ni kuɗi ba matsalata ba ne, nawa kake ganin za a bayar?"

"Zan sanar da mahaifiyarki, domin ita ya kamata ta damƙa mini hannu da hannu." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama, sai bayan ta gama sannan ta fito ta koma kan gado ta kwanata. Tana jin damuwar da take ciki kusan kaso casa'in ta tafi, don haka ta samu bacci ya yi awon gaba da ita.

ALHAJI UMAR
Abin duniya ne ya haɗe wa Daddy, gabaɗaya komai ya fita daga rayuwarsa. Har ji yake yi, a kan Mommy matuƙar bai same ta ba zai iya rasa rayuwarsa. Babban abin da ya ɗaga masa hankali, har kawo wani lokaci mai tsayi Baba malam bai sake bi ta kansa ba. Idan kuma ya kira shi a waya ba ya ɗauka, haka ita ma layin Hajiya Karima ya kira babu adadi ta ƙi a ɗauka. Daga ƙarshe ma sai ya ji wayar ta daina shiga, da Momny ta ga ya ƙara sauya layuka yana kiranta da su, sai ta saka wayar a DND sannan ta samu lafiya da shi.

Da Daddy ya ga ya bi duk wata kafa da zai samu Mommy bai samu ba, sai ya koma kiran ragowar 'yan'uwansa yana kai kukansa wurinsa. A ranar da ya kira yayansa Baba Yunusa ya gama zayyane masa damuwarsa, ba ƙaramin tausayinsa ya yi ba. Saboda ya san duk abin da ya yi a baya ba yin kansa ba ne. Cike da tausayin ɗan uwansa ya ce.

"Umar wannan matsalar taka tana hannun Baba malam, saboda ni da 'yan'uwana ka san ba mu da hurumi a kan wannan maganar. Yanzu dai ka yi haƙuri, In Shaa Allahu zan gwada sa'ata na kira shi na ga ko zai saurare ni." Jiki a sanyaye Daddy ya taso daga gidan, bayan kwana biyu a tsakani Baba Yunusa ya kira shi ya ce Baba malam bai saurare shi ba.
Tun Daddy yana ganin abin kamar wasa har aka sake shafe watanni a haka, duk wanda ya kira ya je wa da ƙorafin maganar Mommy sai dai ace masa ya bi ta wurin Baba malam. Wannan yanayin ya sake birkita shi, har zamansa da Shukura ya koma irin zaman doya da manja. Kwata-kwata ba ta ganinsa a gida idan ba dare ne ya yi ba, idan gari ya waye zai fice. Idan kuma ta matsa sai ya zauna a gida, ba shi da magana sai ta Mommy da iyalanta. Ga kaɗaici da ya dame ta, saboda gidan ya yi mata girma wani lokacin har tsorata kanta take yi. Musamman idan zuciya ta fara yi mata ayyane-ayyane, ga shi duk kuɗaɗen da suke kashewa a wurin malamai babu aikin da yake ci. A kan haka har faɗa suka taɓa yi da mahaifiyarta, saboda Shukura gani take kamar cinye mata kuɗi Inna take yi. Ita kuma Inna ganin bakin ƙoƙarinta take faɗi-tashi wurin bin malamai sai ya abin ya ɓata mata rai. Sai daga baya suka daidaita, ta cigaba da bata miyagin shawarwari amma babu wacce take mata amfani.

Bayan kwana biyu da faruwar al'amuran, watarana da safe ciwon hawan jinin Daddy ya tashi. Hankali a tashe Shukura ta fita wurin mai gadi cikin kururuwa ta sanar da shi, da sauri ya shiga ɗakinta ya riƙo Daddy da ya fara fita daga hayyacinsa ya saka shi a mota. Da sauri Shukura ta shiga mazaunin direba ta tuƙa shi ta nufi asibiti da shi, cikin kulawa likitoci suka karɓi Daddy suka shiga ba shi agajin gaggawa. Sai da ta ga ya ɗan dawo hayyacinsa, sannan ta zame jiki ta fice daga ɗakin, ta latsa lambar Inna ta kira ta sanar da ita. Sai da ta gama sauraronta ta ce.

"Wai Shukura me ya sa ba ki da wayo ne wani lokacin? Dama kin san haka jikinsa ya yi zafi shi ne ba ki sanar da ni ba? So kike mu gama ƙarar da gishirinmu a dahuwar ƙaho, ba tare da ya amfane mu da komai ba? Ko so kike mu yi wahalar hura wuta, zafin hayaƙi ya gama kashe mana idanuwa ba tare da mun sharɓi romon ƙahon da muke dafawa ba?"

"To Inna ya kike so na yi? Ba fa ni na ɗora masa ciwon nan ba, duk ta sanadin tsohuwar matar nan yake neman kassara rayuwarsa. Wallahi ba na son na rasa Alhaji, saboda ba ƙaramin so nake yi masa ba." Shukura ta furta muryarta tana rawa.
Dogon tsaki Inna ta ja sannan ta ce.
"Wallahi kin ba ni mamaki Shukura, au ke da soyayyar gaskiya ce ta kai ki gidan? To ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni."

Murya a sanyaye Shukura ta ce, "Ina jin ki Inna."
"Har yanzu ba ki ci adadin kwanakin da na ɗebar miki a gidan Alhaji ba, duka-duka yaushe aka yi abin da mutuwa take ƙoƙarin hana mu rawar gaban hantsi? Ko fa haihuwar fari ba ki yi ba, idan ya mutu yanzu ribar me muka ci?" Inna ta furta cike da damuwa, kamar Shukura za ta yi kuka ta ce.
"A'a Inna don Allah ki daina zancan mutuwa, ni dai tsakani da Allah nake son shi wallahi. Ina laifin abin da muke samu yanzu ma."

"Shashasha! Ana nuna miki gabas kina cewa kudu ce. Yanzu dai abin da nake so da ke, ki shirya ki tafi gidan yayansa Baba malam ɗin, ki sanar da su rashin lafiyarsa. Sannan ki fashe da kuka ki nemi yafiyar Hajiyan da 'yan'uwansa, ni kuma duk abin da na zo asibitin na aikata a kanki kada ki tuhume ni. Duk a cikin plan ne, ke ko dawo da itan ne ki tsaya tsayin daka a dawo ita ai ribarmu ce."

"Haba Inna, me kike faɗa haka? Gidan Baba malam fa? Kin san yadda suka tsane ni kuwa?"
Murmushin manya Inna ta yi ta ce, "Yaro man kaza, kin san dai ba na ƙwaina ai sai da zakara. Kuma banza ba ta kai romo kasuwa. Tun da kika ji na faɗi haka ki bar ni mu tafi a haka, idan hagu ta ƙi ai sai mu koma dama. Tun da asirin ya ƙi ci, sai mu gwada kissa mu gani."
Cikin damuwa Shukura ta ce, "Gaskiya Inna hankalina bai kwanta da wannan shirin ba, yanzu sai mu bari ya dawo da Hajiya ana zaune..."

"Shukura kin san dai ba zan saka ki a hanyar da ba za ta ɓille mana ba. So nake mu dafa ta da ruwan jikinta, ta yadda za ta gwammace zamanta a waje saɓanin cikin gidan." Inna ta furta cike da kwantar da hankali. Murmushi mai sauti Shukura ta yi, sannan ta ce.
"Allah Ya bar mini ke Innata." Inna ta amsa sannan suka yi sallama.

Shukura tana shiga ta tarar har lokacin Daddy bacci yake, da yake allurar da suka yi masa mai ƙarfi ce. Kuma a wannan asibitin Daddy yake ganin likita, nurses ɗin ta samu ta ce musu za ta je gida ta dawo. Amsa mata suka yi, sai da suka kira wasu daga cikin ma'aikatansu suka zauna a wurin Daddy sannan ta wuce gidan Baba Malam.

Shukura tana zuwa gidan Baba malam ta yi horn a bakin gate, mai gadi ne ya tambaye ta wurin wanda ta zo. Bayan ta sanar da shi, sai da ya ɗaga waya ya kira Baba malam ya sanar da shi sannan ya buɗe mata ta shiga.
Duk da Baba malam ya ji ɗacin zuwan Shukura, amma ya bar ta ta shigo ne albarkacin tana auren ɗan'uwansa. Uwa-uba kuma ya sa an buɗe mata ne, don ya ji abin da yake tafe da ita. Shukura ta yi mamakin yadda mutanen gidan suke ta karrama ta, duk sai ta ji ta tsargu. Tana nan zaune Haidar ya shiga falon, wani mugun kallo ya wurga mata. Da sauri ta kawar da kanta gabanta yana faɗuwa, buɗe firji ya yi ya ɗauki ruwa ya yi gaba. Fitarsa babu jimawa Mommy ta shiga da niyyar cire

15 / 46