Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   39 / 46

114K to 117K   out of 137.8K words

"Inno dama wata 'yar magana gare ni idan babu damuwa."
Daga can ɓangaren Inno ta ce, "Na taso ko za ka shigo ciki?"
Baba Ibrahim ya ji daɗi yadda ya ji muryar Inno wasai, don haka yake fatan Allah Ya sa ta ba shi haɗin kai a game da buƙatar da zai je musu da ita. Ya matsa bakin ƙofar sannan ya ce.

"A'a zan shigo ma, da yake maganar da ku duka za mu tattauna."
Sai da Inno ta amsa masa sannan ya shiga cikin ɗakin ya zauna daga gefe, ganin har lokacin Mai Yasin bai daina kuka ba ya sa mamaki ya kama Baba Ibrahim don haka ya ce.
"Inno lafiya? Me ya samu Malam?"
Inno ta ɗan canza fuska ta ce. "Wai fa don ya ji na ce ragon Inusa na saka aka gasa mana, shi ne yake taya shi kukan jimami!" Baba Ibrahim ya yi ƙuri yana kallon Malam, saboda haka kawai ya ji bai yarda da hujjar yin kukansa ba.

"Inno magana ta gaskiya ba a kyauta wa Yaya Inu ba, ina laifin ma ki sa a ɗebi kaji amma a ce rago guda ai kuma ya yi muku yawa."
Baba Ibrahim ya furta, don ya san fiye da jinya ma ɗan'uwan nasa yana iya yi saboda soyayyarsa da abin duniya.
"Mu ajiye wannan zancen a gefe Iro, yanzu me yake tafe da kai."
Baba Ibrahim ya yi jim sannan ya ce.

"AlhamduLillah! Haƙiƙa ina godiya ga Allah (S W.A) da Ya sa haɗuwarmu da kai Malam da zamo mana alheri. Tun da aka ce harka ta auratayya ta shiga tsakani, to kuwa ta wuce komai. Amma wani hanzari gare ni ba gudu ba Inno da kuma Malam!"
Baba Ibrahim ya ɗago ya ɗan dube su sannan ya cigaba da cewa.

"Dama maganar gwajin jinin da na yi rannan ita ce na zo zan sake maimaitawa. Don Allah ina son ka fahimce ni Malam, ba ina son a yi wannan gwajin don wata manufa ta ko saboda ba mu yarda da kai ba ne. A'a ina son a yi muku wannan gwajin ne saboda a tantance lafiyarka da ita Inno, saboda kada a cutar da ɗaya daga cikinku ko kuma gudun samun wata matsalar da ba ma fata a nan gaba."

Tun da Baba Ibrahim ya fara magana Mai Yasin ya haɗe rai, Inno ta dube shi sheƙeƙe ta ce.

"Kai Iro fita daga idona na rufe, yadda yahudanci ya ratsa ka so kake ni ma ka ribace ni ko? Wallahi tun ranar da na ji kana yi wa Inusa faɗa, a kan yawan haihuwa na fara zargin ka karɓo kwangilar yahudawa. Kai Iro ka ji tsoron Allah, yanzu lokacin da na auri ubanka akwai wani tsirfar gwajin jini kafin aure ne? Ni za ka haramtawa sunnar Annabi ina zaune ƙalau?"
Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin damuwa, don dama ya san za a rina an saci zanin mahaukaciya. Shi kuwa Malam zuciyarsa fes, duk da ya san lafiyarsa ƙalau amma shi kansa bai yarda da sabuwar al'adar da ta shigo ta gwajin jini kafin aure ba.

"Wallahi Inno ba ni da wata alaƙa da Yahudawa kamar yadda kuke zargi, shi wannan gwajin jinin yana bayyana rukunin jinin da kika ɗauke da shi. Gwari-gwari bari na yi miki bayani, nau'in rukunin lafiyar jini na gado shi ake kira da Genotype. To kamar yadda muka sani Inno kowanne ɗan'adanm da Allah Ya hallita, yana tare da wasu ƙwayoyin halitta da suke gudana a jikinsa, kuma waɗannan ƙwayoyin halittar gadonsu ake yi. Misali idan iyaye suna da nau'in jini mai kyau sai su haifi yara lafiyayyu, idan kuma aka samu akasin haka sai a haifi yara masu ɗauke da matsalar amosanin jini wacce aka fi sani da sikila. Bayan wannan gwajin akwai kuma wanda yake bayyana cututtuka da dama kamar: Ciwon hanta, hawan jini, cutar damuwa (Depression) sai uwa-uba cutar ƙanjamau (HIV/AIDS) da ragowar cututtukan da ban lissafa ba. A gwaje-gwajen da ake yi kafin aure akwai cutukan da idan aka same su, ake haƙura da auren. Akwai kuma wanda ake yin auren sai a bayar da shawarwari."
Baba Ibrahim ya faɗa cikin tattausan lafazi.

"Innalillahi wa 'inna'ilahi raji'un! Yanzu Iro ni ko Malam a cikinmu wa kake yi wa fatan ƙanjamu? Mu za ka mayar 'yan iska, masu yawon kwararo? Idan na ce kana ƙoƙarin raba sunnar Annabi ka ce ba haka ba. Yanzu tun da ubanku ya rasu akwai ƙaton da ya sake taɓa mini hannu? Ta shi ka fice mini tun raina bai ɓaci ba."
Inno ta faɗa a zafafe tana nuna masa hanyar fita.

"Don Allah Inno ki fahimce ni, ba ina nufin zarginku nake yi ba. Ita cuta mai karya garkuwar jiki, ai ba sai an sadu tsakanin mace da namiji ake samunta ba, ana iya ɗaukarta ta hanyoyi da dama kamar amfani da reza ɗaya, burushin wanke baki, kibiya wacce mata suke kitso, kilifa ta masu aski, askar wanzamai, wuƙa, abin yankan farce, allura ta asibiti da allurar ɗinki. Duk ana iya ɗauka da su matuƙar dai jinin mai ɗauke ita zai taɓa abubuwan da na lissafa, wanda ba shi da ita idan ya yi amfani da su to tabbas zai iya kamuwa shi ma. Inno hanyoyin suna da dama fa, kuma gwajin jini na genotype yana bayyana rukunin jinin da ya dace su haɗu wurin aure da waɗanda ba su dace ba. Kin ga mai rukunin jinin AS ba zai yiwu ya auri mai irin nasa na AS ba, haka zalika mai jinin SS ba zai auri mai SS ko mai AS ba saboda gudun kada su haifi yaran da za su zo da lalurar sikila, su yaran su wahala haka su ma iyayen su wahala wurin ɗawainiya."
Kallon da Inna take jifansa da shi ya sa ya tsahirta sannan ya ce, "Inno na ga kamar ba ki gama fahimtar bayanina ba. Ana sanin genotype idan anyi gwajin jini, kuma daga gwajin ake samun genotypes a jikin mutane cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS da SS.
AA sune masu cikakkiyar ƙwayar halitta, AS kuma su ake cewa carrier, akwai ɗan rauni a cikin ƙwayar halittarsu, sai kuma na ukun sune SS masu ɗauke da amosanin jini wato sikila. Saboda raunin ita wannan ƙwayar halittar ya kai maƙura.
Shi ya sa muke yawan jan hankulan mutane, da su tabbatar da sun yi gwaji jini tun kafin soyayya ta yi ƙarfi. Muke kuma hankaltar da muhimman abubauwan da ya kamata a lura kafin aure, idan an duba genotype din sune kamar haka:

Rukunin farko yana nufin mijin, ba biyun kuma yana nufin matar, sakamakon kuwa irin yayan da za a samu ne.

1. AA +AA = AA, AA, AA, AA (Za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya.)

2. AA + AS = AA, AS, AA, AS, (Shi ma aure ne mai kyau, kuma babu matsala a lafiyar 'ya'yan da za a haifa, amma bai kai na saman ba.)

3. AA + SS = AS, AS, AS, AS, (Shi ma wannan auren ana iya yin sa, duk da akwai 'yar matsala kaɗan a kan 'ya'yan da za a haifa. Za su zama AS ne duka, ma'ana carriers)

4. AS + AS = AA, AS, AS, SS, (Akwai matsala, domin za a samu ɗa ko 'ya mai cutar sikila)

5. AS + SS = AS, SS, SS, SS (Akwai matsala sosai domin kusan kaso tamanin 80% na 'ya'ya za su zama masu cutar sikila)

6. SS + SS = SS, SS, SS, SS, (Akwai matsala mai muni, domin dukkan 'ya'yan da iyayen sikila ne, za su ƙare cikin tsanani da wahalar rashin lafiya..."

A zafafe Mai Yasin ya katse shi, "Kai Iro ka kiyaye ni, kai yanzu mu za ka zaunar kana nusar da mu gaibu? Waye masanin gobe idan ba Ubangiji ba? Yanzu zurfin da ka yi a yahudancin har ya kai ka fara ja da hukuncin Ubangiji, kana yi masa shisshigi a kan halitar bayinsa? Wane ne kai ban da gajiyayye wanda fushin Allah kaɗai zai iya tarwatsawa, wallahi ka dawo cikin hayyacinka, don ba abin mamaki ba ne yanzu Ubangiji ya mayar da kai ragon sallah. Sakarai dube ka a ido kamar mutumin kirki, amma dai kai an yi zindiƙin bayahuɗe."
Inno da takaici ya gama cika ta, ta nuna masa hanya rai a ɓace ra ce.

"Fice mini daga ɗaki Iro!
"Don Allah Inno..."

"Na ce ka fita ko!"
Ta katse shi a zafafe.
"Shashasha, kai ni dai kam ban san ƙaddarar da ta saka na yarje maka ka yi karatun nasara ba tun asali, idan abin da ka faɗa haka ne me ya sa ku duk ban haife ku a nakashe ba?"
Inno ta faɗa cike da masifa, babu yadda ya iya haka Baba Ibrahim ya fita jiki a sanyaye don ba haka ya so ba.

Ko kaɗan auren Inno da Malam bai ɗaɗa Laraba da ƙasa ba, saboda mutuminta ne tun zuwansa gidan yake faran-faran da ita. A cewarsa 'ya'ya da jikiokin Inno tamkar nasa haka ya ɗauke su, dalili kenan da ya sa ya sake mamaye zuciyar Inno tun bai furta mata kalmar so ba. Laraba ganin Inno ta tafi ɗakin Mai Yasin ya sa ta yi zaraf ta ɗauki hijabinta ta nufi wurin mai daban-daban, a lokacin da ta je ya gama gashe mata zabin sun yi jar suya gwanin birgewa. Laraba ta basar kamar gaske ta ce masa.

"Mai daban-daban Inno ta ce na tambaye ka, nawa ne kuɗin aikin naman sai a biya ka."
Mai daban-daban ya washe baki cikin jin daɗin ganin Laraba tana sakar masa fuska ya ce.
"Haba Laraba, yanzu saboda ni na fi kowa rashin kara sai na karɓi kuɗin Inno don na yi mata aikin zabi, ai a kanki Laraba babu abin da ba zan iya sadaukar miki ba." Laraba ta fakaice shi ta ɗan taɓe fuska sannan ta ce.
"Ashe haka kake sona ban sani ba Mai daban-daban?"

Mai daban-daban ya miƙa mata ledar da ya zuba zabin a ciki ya ce, "Tun farko dama ai ke ce kika ƙi ba ni haɗin kai Laraba, amma bakina ai ba zai iya furta irin soyayyar da nake yi miki ba."
Laraba ta yi masa murmushi sannan ta tafi gida, sai dai fargaba ce fal a ranta tana tunanin me za ta ce wa Inno, idan ta tambaye ta a inda ta samo nama mai yawa haka. Tun da ta doshi kwanar layinsu ta ga wani matashin saurayi yana biye da ita, ita mamaki ma abin ya ba ta don idan aka cire Mai daban-daban babu namijin da ya taɓa cewa yana sonta, saboda duka mutanen garin kallon marar hankali suke yi mata.

"Yan mata, don Allah ki tsaya ina da magana da ke." Matashin ya furta yana shan gabanta, Laraba ta ɗan haɗe fuska kamar ba ta fahimci me yake son faɗa mata ba ta ce.

"Malam lafiya kuwa?"
Sai da ya gyara gaban rigarsa ya saki murmushi sannan ya ce.

"Tun ɗazu da kika wuce na ji kin kwanta mini a zuciyata, to na ga bai da ce na tsayar da ke a can ba shi ya sa na biyo ki zan ga gidanku."

Laraba ta ɗan maƙale murya ta ce, "To gaskiya ni dai ina da masoya da yawa, amma ka san dai an ce mace allurar cikin ruwa ce. Kuma yanzu aike na aka yi, sai dai idan na kai aiken ka tsaya na fito."
A fili ta lura da yadda matashin ya ɗan tsora ta jin ta ce tana da masoya, amma da ya ga ta ba shi dama sai ya sauke ajiyar zuciya. Laraba zuciyarta ƙal, don ita ma so take ta gwada yadda ta ga su Bushira yayyanta da suke uba ɗaya suke yi kafin su yi aure ko ta ji abin da ake ji. A ƙofar gida matashin ya tsaya Laraba tana shiga cikin gida ta zura da gudu ta nufi sashen Inno, har a ranta tana fargabar kada ya gudu kafin ta shiga ta fito. A uwar ɗakin ta ajiye ledar ta sake zurowa da gudu ta koma, sai da ta je soro sannan ta tsaya ta ɗan daidaita nutsuwarta tana mayar da numfashi.

"Ɗan samari na dawo!"
Laraba ta furta tana wani kanne ido.
Martanin murmushi ya mayar mata ya ce, "Barkanki da dawowa sarauniyata, ni dai sunana Habu kuma ba a ƙauyen nan nake ba. Na zo ne daga maƙotan garin nan, ban sani ba ko kin san gidan Malam Lado mai itace?" Laraba ta yi murmushi ta ce.

"Wallahi na gane shi, sam-sam ba shi da mutumci. Sau ɗaya na taɓa tsinkar masa mangwaro ya kai ƙarata har gaban mai gari, kawai dai na raga masa ne saboda na ga ƙafa ɗaya gare shi."
Habu ya saka hanu ya rufe bakinsa ya ce, "Yayan mahaifina ne fa!"
Cikin halin ko'in kula Laraba ta ce, "Ita gaskiya ai dama ɗaci gare ta." Shiru ya yi yana tsoron kada ya sake wata maganar ta ce ta fasa son shi, don ya lura kamar ba ta rufa-rufa. Don haka ya basar ya ce.

"Na tambayi sunanki an ce sunanki Laraba, amma Laraba ai ba sunan ainahi ba ne."

Laraba ta yi fuskar tausayi ta ce, "Sunana Aminatu, sunan mahaifiyata na ci kasan tana haihuwata ta mutu. Ana kirana da Laraba ne saboda ranar Laraba aka haife ni, ga kuma sunan Innata da na ci." Cike da tausayawa ya yi wa mahaifiyarta addu'a, sannan suka ci gaba da hira duk da mafi yawan hirar da Laraba take yi masa shirme da shirirta ne, amma haka kawai ya ji tana birge shi.

Tun da ya shawo kwanar layin hasken fitilar motarsa ta haske su Laraba da ke tsaye a ƙofar gida, suna hira ita da Habu tana ta sheƙa dariya. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cike da ɓacin rai ya ja dogon tsaki har sai da matarsa Nabila da ke gefe ta kalle shi ta ce.

"Baby lafiya?"
Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Nothing!"

Shiru suka yi har suka ƙarasa ƙofar gidan, sai da ya fita ya buɗe gate ya koma cikin motar ya shiga da ita cikin harabar gidan, sannan ya yi hanyar fita a zafafe. Saboda ya lura koda Laraba ta gan shi babu wani tsoro ko shakku a tattare da ita.

"Baby ina za ka je kuma?"

Nabila ta furta, don ta lura da sauyinsa.
"Get inside, i am coming back righ now."
Bai jira cewarta ba ya fice. Shiru ta yi tana nazari, haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga da wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri ta ce.

"No! It can't be happen!"
Ta buɗe motar ta ɗauko lapcoat ɗinta da jaka ta rataya sannan ta shige sashensu.

"Shiga gida!"
Dr Fadil ya furta wa Laraba a tsawace, ta wani kwaɓe fuska ganin zai yarfa ta a gaban saurayi ta ce, "Zance fa nake yi Ya Fadil."
Ɗan zaro ido waje ya yi jin abin da Laraba ta faɗa masa babu ko shakku.
"Idan na sake magana ranki zai ɓaci."

Laraba ta fara hawaye rai a ɓace ta ce, "Wallahi Ya Fadil ka fiye shiga haƙƙina, kai lokacin da kake soyewarka wa ye ya hana..."
Marin da ya sauke mata ne ya sa ta katse ragowar kalamanta, gefen bakinta ya fashe ganin irin ƙasƙancin da ya yi mata ya sa ta fashe da kuka tana faɗawa cikin gida da gudu.

"Haba Malam wannan wane irin abu ne haka? Mene ne aibu a maganganun da ta yi da za ka mare ta..."
A fusace Dr Fadil ya ɗauke Habu da mari, ya nuna shi da yatse cike da masifa ya ce.

"Dama ku ne irin 'yan iskan samarin da suke hurewa ƙananan yara kunne ko? Idan na sake ganinka a ƙofar gidan nan, sai na karairayaka na watsar a ƙasa." Daga haka Fadil ya shige gida ya bar Habu riƙe da kunci, ƙwafa ya yi ya ja ƙafafuwansa ya bar ƙofar gidan, a ransa yana jin idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai daina zuwa wurinta ba saboda soyayyarta ta yi masa mummunan kamu.

A harabar gidan Laraba ta yi zaman 'yan bori ta fasa ihu, kamar wacce ake ƙwaƙwalewa idanu. Mutane suka shiga fitowa daga ɓangare-ɓangare ciki har da su Inno, takaici ne ya cika Fadil ya yi tsaye ya harɗe hannuwa a ƙirji yana kallonta.

"Ke Laraba lafiya kike ihu da daren nan kamar wacce ta taka 'ya'yan shaiɗanu?" Inno ta faɗa a ruɗe. Laraba ta sharce majina da ɗan kwalinta fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce.

"Ba Ya Fadil ba ne ya koro ni ina zance da saurayina, haka kawai ya dinga falla mini mari duk ya zubar mini da aji a gabansa."
Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe rai ta ce.

"Kai Boka ka fita idona na rufe, Larabar ce ba ta isa zance ko mene ne nufinka? Ina ce saba'ar watannan ta cika shekara goma sha biyar? Ga Lantan nan sa'arta ce haihuwa biyu za ta yi a ɗakin miji."

"Wallahi idan na sake ganin Laraba a ƙofar guda sai na ci mutumcinta, dama duk iskancin da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata Inno. Ni da ita za mu ga mai taurin kai."
Dr Fadil ya furta a

39 / 46