Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   26 / 46

75K to 78K   out of 137.8K words

faɗa ya sa kalmar ta ƙara ba ta mata rai, ta tuno boyis ɗin da ta saurara wanda ya yi wa Hafsa da ta ji yana cewa, duk duniya bai taɓa yi wa kowacce mace soyayyar da yake yi mata ba. Ganin ba ta za ta ba shi amsa ba, ya sa shi saurin karɓar jaririyar ya rungume a ƙirjinsa.

Kamar mutum-mutumi haka Maman Nana ta daskare a tsaye tana kallon Jafar har ya shige ɗaki, ita abin ma mamaki ya ba ta. Domin tun da suka yi aure ba ta taɓa amfani da gawayi ba, duk da a shekarun baya ƙarfin Jafar bai kai na yanzu ba. Rufa masa baya ta yi cikin ɗakin, yana ganin haka ya sake haɗe fuska.

"Abban Nana wai me yake faruwa? Me ya sa kake son cusguna mini? Me na yi maka duk ka canza kake ƙaƙalo abin da za ka cusguna mini?"
Maman Nana ta yi maganar muryarta tana rawa.

"Me kuma na yi miki?"

"Amma clinder fa ka ɗauke mini ka kawo buhunhunan gawayi ka ajiye mini."
Sai da ya ɗaura towel ɗin wankansa sannan ya ce.

"Su waɗanda suke amfani da gawayin mutuwa suka yi? Ko kuma taɓo ya yi musu a goshi? Am sorry to say na ga ke gidanku ma da itace suka amfani." Saukar kalaman Jafar a kunnenta ji ta yi tamkar an buga mata guduma. Maman Nana ta haɗiyi wani irin abu mai ɗaci a zuciyarta, idonta ya ciko da ƙwalla.

"Gori za ka yi mini Abban Nana? Ko dai ka daina ƙaunata ne? Wane ne yake zuga ka a kan iyalinka ne?"

Jafar ya matsi toothpaste kamar ba zai tanka mata ba, sai da ya je bakin ƙofa ya waiga ya ce.
"Babu ɗaya daga ciki, kawai ke kika yi zargin haka. Yanzun ba ni da ƙarfin saka gas ne..."

"Wallahi kana da shi Jafar, sai dai idan wani ne yake zuga ka kuma wallahi ba zan yi amfani da gawayi ba."
Maman Nana ta furta cikin kuka, jin hayaniyarsu ya sa Abdul ya rarrafa ya riƙe ƙafarta ya saka kuka shi ma. Ɗaukarsa ta yi tana hawaye ta ji ya ce, "Ke dai Sumayya wallahi ba matar rufin asiri ba ce, ban da haka saboda na kawo miki gawayi, za ki yi mini hayaniya har maƙota su ji."

Wani irin sak Maman Nana ta yi, tana jin wata irin juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwanta. Hawaye ya shiga kwarara daga kwarmin idonta, cikin ƙunan zuciya da sarewa ta ce.
"Yau ni kake kira da ba matar rufin asiri ba Jafar?" Cikin halin ko inkula Jafar ya ce.
"Mata nawa ne a nan unguwar suka amfani da gawayi? Su sun yi wa mazajensu irin abin da kika yi mini? Idan kina son rufin asirina ba hannu bibbiyu za ki karɓa ki sarrafa ba, mata ku dai halinku sai Allah. Da kun samu sake a gidan miji sai ku manta halin da kuke ciki a gidanku." Baƙaƙen maganganun Jafar suka sake baƙanta ranta, zama ta yi a wurin ta ci kuka ta more saboda ɗacin da zuciyarta take ciki.

Tana nan zaune har Jafar ya fito daga banɗaki, sai da ya gama shiryawa sannan ya ce mata.
"Idan kin gama ki miƙa su Nana makaranta ni ina da uzuri da wuri zan fita." Yana gama maganar ya fice.

Kamar ta ga sabuwar hallita haka ta bi bayan Jafar da kallo, zuciyarta ce ta shiga yi mata saƙa da warwara. Sai ta fita ta fara yunƙurin kunna kurfitin, amma ta ƙona ashana ta fi goma ba ta kama ba. Sannan ta ɗauki wata ledar pure water ta kunna da ita A nan ta samu wutar da kunnu, da yake tana da ruwan tea fulas sai ɗumame kawai ta yi, bayan ta sauke ta ɗora doyar su Nana ta makaranta.
Saboda rashin sabo Maman Nana ba ta gana suyar doya ba sai kusan ƙarfe tara na safe, da yake bayan su Nana sun gama breakfast shirya su ta yi ta miƙa su. Sai daga ba ya ta kai musu abin break, da ta koma ta ɗora abincin rana. Wuni ɗaya da ta yi gidan gabaɗaya ya ɓaci da toka, hannuwanta sun yi baƙi da gawayi. Sai kusan azahar ta gama girki sannan ta gyara gidan. Ranta ya ɓaci sosai da ta ga cikin faratanta duk baƙin gawayi, gyara gidan ta yi bayan ta gama ta faɗa wanka.
Sai da ta yi wa Abdul wanka sannan ta shiga gidan Maimuna, a harabar gate ɗin ta same ta sanye da hijabi ta ce.
"Sai ina kuma uwar Asiya?"

Maimuna ta gyara saka hijabin ta ce, "Wallahi almajirina ne bai zo ba, ga lokaci ya ƙure yara sun kusa dawowa kuma gawayina ya ƙare."

Maman Nana ta saki tsaki ta ce, "Hmmm wai kin san ni ma yau Abban Nana buhunnan gawayi ya dire mini? Wallahi namiji ɗan kunama ne. Kin ga cin zarafin da ya yi mini yau a kan na ce ba zan yi girki da gawayi ba?"

Maimuna har cikin zuciyarta ta ji wani irin daɗi, a cikin zuciyarta ta raya.
'Ƙaryar banza ashe ke marar kunyar ƙarya ce?'

Amma a fili sai Maimuna ta ce, "Ikon Allah, ni kam lamarin Abban Nana kullum ƙara gaba yake, wai ni ko dai neman aure ya fara ne? Maman Nana sai fa kin tashi tsaye, ba na son dai ki yi mini wata fassarar da sai na ce gaskiya sai kin haɗa da neman taimako."
Maman Nana ta yi shiru tana juya kalaman Maimuna a ranta.


Ummou Aslam Bint Adam🌚
+2347062062624
[17/02, 19:53] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.

SHAFI NA TARA

UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳

Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya

Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731

***

Ganin kamar tarkonta ya kama Maman Nana ya sa ta saki murmushin gefen baki, ta ɗan taɓo ta da tuni ta dulmiya kogin tunani.
"Na ga kin yi shiru Maman Nana, amma fa kada ki yi mini mummunar fahimta. Lamarin ne nake ganin kamar ba banza aka bar shi ba, tun da ke da bakinki kike cewa a duniya Abban Nana ba ya son abin da zai sa ki wahala ko ya ƙuntata miki. Kwanaki na ji kin ce har girki yake taya ki da rainon yara, shi ya sa na ce ko za ki haɗa da neman taimako."

Maman Nana ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan girgiza kai, don ko kaɗan ba ta da ra'ayin zuwa wurin malaman a kan duk wani abu da ya sha mata kai.

"Kai an ya kuwa Maman Asiya? Gaskiya ba zan iya ba, saboda malaman nan idan ka fara zuwa wurinsu sun fara kunto maka matsaloli kenan. Bari dai mu gani zuwa nan gaba."
Maman Nana ta ƙarasa maganar tana dafa ƙofar, ba haa Maimuna ta so ba. Don haka ta taɓe baki a fakaice ta ce, "To ai shi kenan, Allah Ya yi mana magani. Kin san akwai malamai akwai kuma muna malamai." Maman Nana ba ta tanka mata ba, suka fito ita da Maimuna. A madadin Maman Nana ta koma gida sai ta shiga gidan ɗayar maƙociyarsu da ke ɓarin hannun hagu, buga ƙofar ta yi babu jimawa Maman Sudais ta buɗe mata. Daga bakin ƙofa Maman Nana ta tsaya ta ce, "Maman Sudais kwana biyu."

Maman Sudais da ba ta cika shiga shirgin maƙotan ba ta taɓe baki ta ce, "Lafiya ƙalau, daga ina haka?"

"Gidan Maman Asiya na leƙa."

Maman Nana ta furta, nan take Maman Sudais ta haɗe rai sannan ta ce.
"Aminan juna kenan, ki gaishe ta idan kun sake haɗuwa."

Maman Sudais ta faɗa cike da ƙagauta, ganin haka ya sa Maman Nana ta fita ta wuce gida.
Maman Sudais ba ta da shige-shigen maƙota, idan har ta shiga gida to sai dai idan abin jaja ko murna ne ya kai ta. Ba wai dom mijinta ya hana ta ba, sai don tuntuni haka tsari da ra'ayinta yake. Koda cefane ta fita sai dai ta sayi abin da za ta saya, idan sun haɗu da maƙotan a bakin hanya sai su gaisa. Har gara idan ta ga an ɗauki kwanaki tana iya leƙawa a tsaitsaye su gaisa ta koma gida, dalilin da ya sa ba su cika ga maciji da Maimuna ba tun watarana da Maman Sudais ta kama Maimuna da ƙanwar mijinta suna gulmarta, da yake ko kaɗan dangin mahaifin Baban Sudais ba sa son ta. Yau da gobe shigar da take yi gidan Maimuna ya sa suka yi sabo har da ƙanwar mijinta, a ranar da za ta kama su bayan ƙanwar mijin tata ta fito da niyyar tafiya gida, sun yi sallama tun da jimawa sai ta faɗa gidan Maimuna. Ashe ita take ƙara hura wuta tsakanin Maman Sudais da dangin mijinta, duk wani sirrinta take kwashe take faɗa musu. Dalilin da yake da a kullin suke ƙara kafa nata ƙahon zuƙa, Maman Sudais ta fito sayen ashana ta ga Salma ta fito daga gidan Maimuna tana faɗin.

"Ai wallahi daga yau yaya ya daina saya wa mahaifinta maganin hawan jinin, gara da kika faɗa mini. Ina zuwa wallahi kamar Umma ta ji labari..."
Maganarta ta maƙale sakamakon ido huɗu da suka yi da Maman Sudais, murmushin takaici ta sakar mata ta ce.
"Maimuna kenan, na ba ki yarda da aminci ashe cin dunduniyata kike? Idan kuwa ni ce yadda Annabi ya bar duniya na bar ki kenan."
Cike da borin kunya Maimuna ta ce, "To zancenki ake yi da za ki faɗa wa mutane magana? Idan kin bar ni Baban Asiya ne ya bar ni ko me? Ai dama ba zamanki nake yi ba." A ranar haka suka rabu baram-baram dutse a hannun riga, tun daga wannan ranar idan ba abin jaje ko gaisuwa ba ne babu abin da yake haɗa su da Maimuna. Gaisuwar ma sai da Abban Sudais ya takura mata da yake ta sanar da shi komai, kuma shi mutum ne mai fahimta ya ce ta kiyaye zamanta da maƙota. Don haka take takatsantsan da gabaɗayansu, tsakaninta da su sai hirar duniya ko ta yara. Kuma tun daga lokacin ta rage ba su fuska, shi ya sa yawanci suka daina shigar mata sai Maman Nana da take leƙa mata sama-sama.
Sai da Maimuna ta sayo gawayi bayan ta ɗora girki, ta sake shiga ɗaki ta ɗauko sabuwar wayarta da Jafar ya aiko mata, dama tun bayan fitar Nazir ta ciro ta haɗe da saita komai ta yi masa Salam ta whatsapp. Saboda farinciki kamar Jafad zau taka rawa haka suka ɓa ta lokaci suna musayar kalaman soyayya, domin a ranar Maimuna ba ta yi aiki gida da wuri ba. Don haka a yanzun ma da ta koma ta kira shi voice call ta whatsapp da yake ta ga yana online, yana ɗauka suka dasa daga inda suka tsaya. Daga ƙarshe ya ce ta ɗauki hotuna masu kyau ta tura masa. Wannan ne ya sanyaya mata jiki, kuma tsoro ya kamata. Har ta shiga wasu-wasin kada ta zo tsautsayi ya ratsa Maman Nana ta gani, duk da ta ji ya ce mata zai ɓoye amma haja kawai ta ji tana tsoron tura hoton. A ɓangaren ɗaya kuma ta ji kamar ba ta kyauta masa ba, domin shi ya zuba maƙudan kuɗinsa ya saya mata wayar saboda haka. Jin ta shiru ba ta tura masa ba ya sa shi kiranta a waya ya sake tunasar da ita, sai da Jafar ya yi da gaske sannan ra iya tura masa tana sake jadadda masa da ya san yadda zai yi ya adana hoton ta yadda kwaɓarsu ba za ta taɓa yin ruwa tsululu ba.

Nazir irin bauɗaɗɗun mazan nan ne, kuma yana ɗaya daga cikin mazan da ba su damu da ba wa mace haƙuri ko lallaɓa ta ba idan ta yu fushi ko idan sun yi mata laifi. Idan har Maimuna ta ga ya ɗan sakar mata fuska to a ranar yana buƙatar kusantarta ne. Abin da ya fi ci wa Maimuna tuwo a ƙwarya bai wuce rashin ba ta kulawa ba, idan Nazir ya dawo gida ba shi da abokiyar hira sai wayarsa. Koda hira Maimuna ta zauna tana yi masa sai dai ya dinga ba ta amsa sama-sama, amma kaso casa'in cikin ɗari (90%) hankalinsa yana kan wayarsa. Da yake Maimuna tana da ɗan surutu ta dinga yi masa mita kenan, tana nuna ɓacin ranta. Hakan ne ya sa wani lokacin Nazir ba ya dawowa gida da wuri, sai ya gama uzurorinsa a waje. Ya kasance mutum mai takura, bin diddigi da rashin yarda. Don hatta maƙota ba ya barin Maimuna shiga, su ma kuma a ɓoye suke shigo mata bai sani ba. Duk inda Maimuna za ta je shi zai kai ta, kuma bai cika kai ta da rana ba har sai ya dawo daga kasuwa. Kuma idan ya kai ta duk taron da ake yi sai dai ya jira ta a ƙofar gida agama ya tafi da ita. Maimuna tun tana zama ta ci kuka bayan aurensu har abin ya zame mata jiki, kuma sannu a hankali Nazir ya aurensa ya sure mata har take jin Allah Ya kawo sanadin da za su rabu wala mutuwa ko sakin aure. Sakamakon halinsu da ya yi hannun riga da ita, tun da har babbar waya ya hana ta riƙewa a cewarsa duk wani abu da zai buɗe idonta ba zai lamunra ba. Tun da ai sai mace ta yi mu'amala da mutane ake ba ta munanan shawarwari, ko a zuge ta ta sauya halaye. Idan kuwa aka ɗora mace a doron da ya ɗora Maimuna, a ganinsa hakan ne zai daidaita mace ta zama kamila tun da idonta bai buɗe ba.

Tarihin Maimuna
Maimuna 'yar asalin garin Dutse ce da ke jigawa, mahaifi da mahaifiyarta duk 'yan can ne. Kuma su biyar ne a wurin iyayensu, yayanta Sadik shi ne babba sai ita take binsa ƙannenta mata uku suke biye da ita.
Maimuna ta yi karatunta na addini daidai gwargwado, ha boko kuma ta tsaya a secondary. Domin mahaifinsu mai sauƙin ra'ayi ne, idan yarinya ta samu miji zai aurar da ita ra'ayin mijinta ne ta cigaba ko ya hana ta. Idan ba ta samu miji ba kuma ta cigaba da karatu, kuma hakan ce ta faru da Maimuna.
Tun tasowar Maimuna 'yar gayu ce mai sosai, tana son ƙwalisa. Uwa-uba tana da wayewa, don ƙawayen da take hulɗa da su duk masu buɗaɗɗan ido ne. Maimuna tun tasowarta take da tsari, don ra'ayinta ne auren namiji mai kuɗi da iya soyayya. Kuɗin ma bai cika tasiri a ranta ba matuƙar namiji zai ba ta kulawa da soyayya koda mai rufin asiri ne za ta iya zama da shi. Dalilin haka ya sa ta gama tsara rayuwar da za ta gudanar a gidan aurenta, ita da mijinta.

Tarihin Nazir
Nazir haifaffan garin Kano ne, sai dai mahaifi da mahaifiyarsa asalinsu 'yan garin Katsina ne. Neman kuɗi ne ya kawo mahaifinsa garin Kano, a nan duk aka haife su shi da ƙannensa. Mahaifinsa yana da mata biyu da 'ya'ya takwas, ƙannensa da suke uwa ɗaya guda uku ne duka maza. Sai waɗanda suke uba ɗaya su shida kasancewar shi ne babba a wurin mahaifinsa. Nazir kasuwancin hulunan maza yake a kasuwar kwari, shagonsa babba ne kuma yana da rufin asiri bakin gwargwado.

Nazir ya haɗu da Maimuna ne a wurin dinner wani abokinsa da suka yi a garin jigawa, da yake tana daga cikin manyan ƙawayen amarya. Tun da Nazir ya ganta ya maƙale mata har aka tashi daga taron, amma kafin su a watse sai da suka yi musayar lamba sannan ya kai ta har ƙofar gidansu ya sauke ta.
Ko kaɗan Nazir bai kwanta a ran Maimuna ba, don tun daga yanayinsa bai yi mata kalar irin mijin da take burin zama da shi ba. Shi kansa Nazir ya fahimci haka, don ko kiran wayarta ya yi wani lokacin ba ta ɗauka. Da ya yi bincike a kanta, sai aka yi masa bayanin halinta tsaf da yanayin waɗaanda take mu'amala da su. Hakan ne ya sa Nazir ya lulluɓe kura da fatar akuya, sai da ya tabbatar da da ya siffantu da irin mijin da Maimuna take muradi sannan ya koma mata tsamo-tsamo. Tun Maimuna tana share shi har ya fara karkato da hankalinta kansa, don tuni ya saye zuciyarta ta hanyar ƙyale-ƙyale da kayan ƙawa. Ya shiga shayar da ita romon zallar soyayya tana sharɓa, har sai da ta dinga gina musu irin rayuwar da za su gudanar a gaba. Hakan ya sa Nazir

26 / 46