Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
Inna ta dubi farantin har Fauziya za ta miƙe Inna ta ce, "Au ashe fa ke ba ki san tsarin gidan nan ba ko?" Fauziya ta gyaɗa kai.
Inna ta saki murfin ya faɗi ƙasa a wulaƙance ta ce, "Abincin rana a gidan nan haɗa shi ake a yi girka gabaɗaya, girkin safe da na dare ne kowa yake yin nasa. Sannan daga yau kada ki sake zuba mini abinci a ciki shatalallan faranti, saboda mu a lokacinmu kwanon uwar miji daban ake yi mata don haka ki kiyaye wannan ma ai wulaƙanci ne." A sanyaye Fauziya ta amsa mata, ta koma ɗakinta. Tana shiga ta ga Zainabu, 'yar wurin Sadiya ta cika hannu da ƙatuwar lomar abincin su Na'ima ta tura a baki, tana ganin Fauziya ta sake kwasar ƙatuwar loma ta fita a guje tana dariya. Hidaya da Fatima suka saka kuka suna faɗin, "Ta cinye mana abinci, Mami tun ɗazu take kwashe mana abinci." Shiru Fauziya ta yi sai ta ji duk zuciyarta babu daɗi, buɗe tukunya ta yi ta ɗebo daga cikin wacca ta rage za ta ci ta zuba musu. Ta zauna gefen katifa ta janyo tukunyar ta fara ci a ciki, tana nan zaune ta ga Zainbu da ƙaninta Faisal ɗan shekara ɗaya da rabi suka dinga leƙensu sai su tafi da gudu.
Tun daga wannan ranar, zaman Maman Nana da Jafar ya koma irin zaman doya da manja. Sakamakon rashin kyakkayawar alaƙar da take shiga tsakaninsu. Kuma har kullum zaman nasu ƙara tsamari yake, don Jafar ya jima da ƙaurace mata. Idan dare ya yi sai dai ya ɗauki filo ya tafi falo ya kwanta, gari yana wayewa kuma ko breakfast ba ya yi yake fita. Idan ta ce abu ya ƙare sai dai ya ba ta kuɗi ta sayo kaɗan, saɓanin a baya da komai idan ya tashi dire mata yake yi mai yawa. Wani abu da Jafar ya tsiro mata da shi sai suna zaune ya ɗauki waya ya yi ta latsawa yana sakin murmushi, ita kuma da ta yi magana kamar jira yake sai ya rufe ta da faɗa. Watarana tana suna zaune da safe, da yake ranar ba ta ga alamar zai fita da wuri ba. Waya ta ga ya latsa yana kai wa kunnensa, tsam ya tashi ya wuce uwar ɗaki sai ta ji ya kashe murya yana faɗin.
"Barka da hutawa My Moon."
Ƙirjin Maman Nana ya buga da ƙarfi, don a yanayin maganar da ta ga yanayi ta fahimci da mace yake waya. Ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Wato duk wannan cin kashin da yake yi mini saboda mace ya yi mini fana? Ai kuwa ba zan lamunci ya dinga yi mini waya a ɗaki ba." Tuni zuciya ta ɗebe ta, ita ma ta faɗa cikin ɗakin a daidai lokacin ta ji ya ce.
"Wallahi tallahi Moon babu wata 'ya mace nake jin kewa da muradinta a yanzu, ganin hotunanki kaɗai suna iya hargitsa ni har na gagara gane kaina."
Tsaye Maman Nana ta yi hawaye ya gama wanke idonta, baki yana rawa ta ce.
"Abban... Nana... ashe a kan wata 'yar iskar kake wulaƙanta ni?" Ɗago kansa ya yi ya kalle ta, ga mamakinta sai ta ga ya ɗauke kansa gefe ya cigaba da cewa.
"Na rasa abin da zan yi miki don ki yarda da abin da nake faɗa, kin san Allah ke ta daban ce a cikin mata..."
Shiru Maman Nana ta yi tana ƙura masa ido cike da hawaye, har gani take kamar ba Jafar ɗinta ba. Domin a baya Jafar ba ƙaramin shakkarta yake yi ba, amma a yau wai shi yake yabon wata a gabanta. A haukace ta fisge wayar ta yi wurgi da ita, cikin matsanancin kishi haɗe da ƙaraji ta ce.
"Jafar ni za ka mayar mahaukaciya? Da wacce 'yar iskar kake waya a ɗakina..."
Maganarta ce ta katse sakamakon wani gigitaccan mari da ya sakar mata, idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai. Ya dube ta a hargitse ya ce, "Kada ki sake ce mata 'yar iska, idan kuma ba haka ba wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kanki." Wani irin sanyi jikin Maman Nana ya yi, sai kuma tsoro ya kama ta. Har take ganin kamar Jafar ba a hayyacinsa yake ba, ta sake matsawa gabansa ta riƙo rigarsa tana jijjiga shi, a ganinta ko hakan zai sa ya dawo hayyacinsa. Hawaye yana zuba ta ce, "Kana cikin hayyacinka kuwa Jafar? Ni kake mari saboda na cewa wata 'yar iska?"
Kamar yana jira ya yi saurin faɗin, "Na mare ki Sumayya, wallahi idan kika kuma faɗar mummunar kalma a kanta sai na yi miki abin da ya fi haka." Maman Nana ta ji kamar ya watsa mata ruwan zafi, zuciya a ƙeƙashe ta ce.
"Na faɗa 'yar iska karuwa don Allah ka kashe ni a wurin nan."
Kamar wancan karon haka ya sake tsinke ta da mari, sai dai a wannan karon tagwayen mari Maman Nana ta samu. Wayarsa ya ɗauka, da yake dama ya yi wanka sai kawai ya shiga ɗaki ya saka kayansa ya fice daga gidan.
A wurin Maman Nana ta durƙushe tana kuka kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta sannan ta sauya kaya. Ta ɗauki Abdul da yake bacci ta goya shi ta fito daga gidan, duk wanda ya ganta kallo ɗaya zai yi mata ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. Gidan Maimuna ta shiga ta same ta zaune a falo, Maimuna tana jin shigarta ta saki murmushin ƙeta saboda duk abin da suka yi a kan kunnenta, tunda wayar ba mutuwa ta yi ba a lokacin da ta yi wurgi da wayar Jafar. Amma a fili tana ganin Maman Nana ta dafe ƙirji ta ce, "Lafiya kuwa Maman Nana? Me ya samu fuskarki ta kumbure haka?" Da yake har lokacin da ɗacin abin a ranta, sai Maman Nana ta rushe da kuka mai cin zuciya.
'Na rantse da Allah kuka ma yanzu kika fara, mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura." Maimuna ta faɗa a ranta, amma a fili cikin ruɗewa ta ce.
"Maman Nana ki yi magana don Allah, kin ɗaga mini hankali. Daga gida ne aka kira ki wani abu ya faru, ko Abban Nana ne?"
Maman Nana ta girgiza kai, Sai Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"To mene ne? Don Allah ki yi mini magana, wannan kukan da gani dai ba na lafiya ba ne."
"Wai yau ni Jafar ya mara saboda wata maman Asiya, Jafar ya zama wani iri wallahi asiri aka yi masa, don Jafar ɗina ba ya cikin hayyacinsa."
Maman Nana ta yi maganar cikin kuka.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Kada ki ce mini tun yarinyar da muka yi magana da ke kwanaki? Ai kin ga sakacinki Maman Nana, tun wancan karon na ce ki ɗauki mataki amma kika tsaya sanya. Yanzu ai ga shi kina gani ƙarfi da yaji yarinya ƙarama ta shanye shi."
Cikin ƙaguwa da neman mafita ta ce, "Yanzu mene ne abin yi Maman Asiya?"
Shiru Maimuna ta yi kamar mai yin nazari, sai ta ɗago da sauri ta ce.
"Gidanku sun san abin da ya faru?" Girgiza kai Maman Nana ta yi, sai Maimuna ta ce.
"Yanzu abin da za ki yi kai tsaye ki wuce gida, ki sanar da iyayenki a san halin da ake ciki. Saboda wallahi matuƙar ba a ɗauki mataki ba abin ƙara gaba zai yi, kin san aka ce idan namiji ya ji daɗin dukanka ya samu wuri kenan. Kar ma ki faɗa masa za ki tafi, ki bari sai dai ya dawo kawai ya ga ba kya nan. Idan aka yi muku sulhu daga baya sai ku daidaita ki dawo, amma ina mai tabbatar miki da sai kin tashi tsaye." Shawarar Maimuna ba ƙaramin kwanciya ta yi a zuciyar Maman Nana ba, haka ta dinga ba ta shawarwari daga ƙarshe suka yi sallama ta fita. Da yake makarantar su Nana a bakin titi take, sai ta da ɗebi kayansu sannan ta wuce ta makarantar ta ɗauke su suka wuce gidansu da ke unguwa uku.
Tun bayan da Maman Nana ta yi wa Maimuna sallama da ta ji fitarta daga gida, ta kira Jafar ta kwashe ƙarya da makirci ta faɗa masa. Don har cewa ta yi Maman Nana tana ta zaginsa kuma ta ce ta tafi gidansu kenan, domin ta gama zaman aure da shi. Maganar da ta fi tsaye masa a rai da Maimuna ta ce wai Maman Nana tana kuka tana cewa, ta yi dana sanin haɗa zuri'a da shi, domin shi ba miji kuma uba nagari ba ne. Da irin waɗannan miyagun huɗubar, Maimuna ta samu yin galaba a kan Jafar. Har shi ma ya hau dokin zuciya da cewar ba zai taɓa nemanta ba, kuma ba zai je biko ba tun da ba shi ya ce ta tafi ba. Ya kuma ci alwashin ko a ranar ta nemi takardar saki, a shirye yake da ya miƙa mata kayarta. A ranar tun yamma ya dawo gida saboda ya san Maman Nana ba ta nan, kuma har cikin zuciyarsa da zai samu yadda yake so kuma da babu 'yan gulma tsaf zai ce Maimuna ta zagayo su sha soyayya. Amma da yake ya san akwai matan maƙota da suke kai kawo, sai ya haƙura da buƙatarsa. Ya shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa sannan ya jira Maimuna a waya, ya ce ta kunna data za su yi magana. Ita ma da yake ta gama girki ta kuma sheƙa wankan ƙananan kaya, sai wayar ta shi ta zo mata a daidai. Ta whatsapp ya kira ta video call, ta ɗauka a kunyace tana sunne kai ƙasa.
"Wai wai wai, wannan wankan duk ni aka yi wa? A gaskiya baby za ki hargitsa ni." Sai kuma Jafar ya shagwaɓe murya ya ce, "Don Allah idan babu damuwa ki zagayo mana Moon. Wallahi babu wanda zai gane, domin a cike nake da ƙishirwarki."Maimuna ta yi shiru tana nazari, domin ita kanta wannan lokacin ta jima tana buri da fata.
Tun da dare ya yi bayan ta kwantar da yaran ta yi shiru tana ƙare musu kallo, Na'ima da Fatima ne ta yi musu shimfiɗa daga ƙasan katifa. Hidaya da Humaira kuma ta yi musu shimfiɗa a kan katifa, tana nan zaune Kabir ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa ta yi ta mayar da kanta gefe, saboda haka kawai haushin Kabir take ji. Shi kansa shiru ya yi ganin yanayin kwanciyar da suka yi, sai kuma jikinsa ya yi sanyi tausayinsu ya kama shi. Kayan abincinsa ta ajiye a gabansa, ba tare da ta ce masa uffan ba. Shi kansa ya fahimci fushi take da shi, sai ya ɗan saki fuska ya ce.
"Haba Fauzina yanzu wannan fuskar da kika haɗe duk saboda za ki zauna da mahaifiyata ne, zaman nan fa ba na dindindin ba ne. Don Allah ki daina ɓata ranki ba na so." Fauziya da dama ciki take da shi ta ce.
"Ni ba ina fushi da zaman da zan yi tare da mahaifiyarka ba ne Abban Na'ima, domin Inna tamkar mahaifiyata haka na ɗauke ta. Kawai yanayin zaman ne bai yi mini ba, dubi a inda yaran nan suka kwanta. A gaskiya sam babu tsari wallahi, don girman Allah ka bari mu koma gidannmu idan ya so ko a hankali sai ka ƙarasa."
Kabir ya ɗan yi jim ya ce, "Ummu banat kin san dai muna da maƙiya, waɗanda suke son ganin cigabanmu, wallahi ba na son na koma a ga gidana ko fulasta babu. Kin san idan aka ce shago ba naka ba ne sai haƙuri, Oga ba wata kyakkaywar sallama yake mana ba. Kin ga Allah Ya taimaki Sani da yake shi kekensa ya kai shagon, shi yake cin gashin kansa. Sai dai ɗan kuɗin da yake bayarwa duk shekara, wanda Oga yake cikawa ya biya kuɗin shago. Ni ma kin ga da ina da keken kaina rufin asirin da zan samu sai ya fi haka."
Shiru Fauziya ta yi, ta kallo keken ɗinkinta da ke waje. Ta tuna ba wani ɗinki take samu ba, mafi yawa sai ɗan gyare-gyare da mata suke kawo mata. A yadda take jinta kamar kwance cikin ƙaya, babban burinta bai wuce ta ga sun tashi daga wannan gidan ba. Don haka ba ta yi dogon tunani da nazari ba ta ce. "Indai hakan zai sa ka yi ka ƙarasa mana, ga kekena nan ka ɗauka Abban Nana. Babban fatana Ubangiji ya rufa mana asiri." Tana gama magana Kabir ya rungumo ta jikinsa, sai ya shiga sakar mata kiss a duk ilahirin jikinta. Cikin wata irin murya ya ce, "I love you my Fauzee."
Fauziya ta saki murmushi ta ce, "I love you too Abi." Gani ta yi Kabir yana yunƙurin wuce gona da iri, don haka ta janye shi daga jikinta ta ce, "Ga abincinka fa." Kafaɗa ya maƙale mata yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Idan da ke abinci da komai ba ne." Tana shirin sake yin magana Kabir ya janyo ta jikinsa, ya shiga yawo da hannuwansa a cikin jikinta.
"Wallahi kunya nake ji, magana ta Allah ba zan iya wani abu a cikin ɗakin nan ba. Don gani nake kamar Inna tana jin duk abin da muke yi, tun da kaga ɗakinmu a jikin ɗakinta yake. Kuma ka dubi kusancin kwaniya da muka yi da yaran nan."
Kabir ya zame hannun rigarta ƙasa, ya ɗora kanta a saman cinyarsa cikin wata irin murya ya ce.
"Babu abin da za ta ji, don haka kada ma ki..."
"Kabiru! Kai Kabiru ashe kana ciki?"
Maganar Inna da bakaɗa labulen ɗakin da ta yi ne ya sa maganar da Kabir yake yi ta maƙale, cikin tsananin jin kunya Fauziya ta tashi tana jan rigarta sama. Inna ta saki baki haɗe da riƙe baki ta ce.
"Dole na ji ku shiru a ɗaki mana, ku dai wallahi an yi jarababbun yara. Don masifa tun a farkon dare? Ko tara fa ba ta yi ba, shi ne za ki saka yaro a ɗaki ki ƙadandane kamar alkaki."
Shi kansa kunya Kabir ya ji, ya ɗan sosa kai ya ce.
"Amma Inna ai da kin yi sallama kafin ki shigo."
"Ba zan yi ba, na ce ba zan yi shashashan banza da wofi. Ina ganin jarabar su Sadiya da duk asuba za ka ji su suna karafniya da ruwa kamar kifaye, ashe nasu shafar mai ne tun da ga ku; ku tun garin bai nausa ba. To idan ka gama shinshine-shinshinen sai ka zo ka same ni a ɗaki." Inna ta ƙarasa maganar tana sakin tsaki sannan ta wuce ɗakinta.
Bayin Allah na kusa kammala free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[19/02, 17:43] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA SHA ƊAYA
GIDAN INNA
Wani irin ɓacin rai ne ya lulluɓe zuciyar Fauziya, rai a ɓace ta miƙe tsaye tana ɓalle maɓallin rigarta. Shi kansa Kabir bai ji daɗi ba, cikin tausasa harshe ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri Fauziya." Fuska babu walwala ta ce, "Babu damuwa."
Ya ɗan leƙa fuskarta ya ga har lokacin babu alamar fara'a, duk sai ya ji babu baɗi.
"Kin san iyaye wani abin sai ana haƙuri da su." Ya furta a sanyaye.
"To ni me na ce Kabir? Ka je idan ka gama sai ka ci abincin."
Fauziya ta furta bayan ta zura doguwar rigar bacci, can gefen katifa ta koma ta kwanta. Kamar Kabir zai yi mata magaba sai kuma ya fasa ya nufi ɗakin Inna. A bakin gado ya samu Inna da alama ta gama cika, ya zauna a ƙasa ya ce.
"Gani Inna."
"Kai ma ashe sakarai ne Kabiru ban sani ba? Don Allah kai ba ka ji kunyar kanka ba, a ce tun farkon dare ka naniƙe 'yar mutane a ɗaki? Kai Allah dai ya sawaƙe da wannan jaraba ta 'yan zamani."
Shiru Kabir ya yi, sai ya ji kunya duk ta kama shi. Inna ta taɓe baki ta ce, "To dama kuɗinka na wurina nake son na ranta, idan ba amfani za ka yi da su ba. Na ji an ce barkono ya sauko a ƙauye zan saro na dinga ƙulla wa yaran nan." Da sauri Kabir ya ɗago ya ce, "A'a Inna, dama na ce ki adana mini su ne saboda ban samu ciko ba. Amma zaman da muka yi da Fauziya, yanzu ta ba ni keken ɗinkinta, idan na sayar da shi sai na haɗa kuɗin suka cike dubu ɗari. Idan ya so sai a tura su Yaya su kai kuɗin, don Allah Inna kada ki taɓa ko sisi, wallahi yayan yarinyar nan ne ya ba ni sati biyu. Idan ban tura ba zai iya aura mata wani."
Inna ta wara hannu ta ce, "Ai ka ga matar rufin asiri, wallahi da Sadiya ce sisi ba za ta ba shi ba. To idan an kai kuɗin auren wai a ina za ka saka ta,