Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   43 / 46

126K to 129K   out of 137.8K words

ba, ba za ki sakar mini yaro ba."
Inno ma ta yi maganar tana ƙarasawa wurinsu. Mai Yasin ya gimtse dariyar ƙetarsa, saboda dama a ciki yake da Yaya Inu. Kuma ya san fiye da haka ma 'Yar gwal za ta iya aikatawa.
Ganin da gaske 'Yar gwal ba za ta sake shi ba, ya sa ya tattare iya ƙarfinsa da niyyar ya warɓo ta ƙasa, sai ta maƙale shi ƙam a madadin 'Yar gwal ta faɗo sai wata wawiyar tusa ce ta ƙwacewa Yaya Inu.

"Subhanallahi! Inusa mene ne haka da sakin tusa?"
Mai Yasin ya furta, sannan ya ce. "Ke yarinya kanki ɗaya kuwa? Kamar muna ƙasar kafirai za ki ƙadandane mutumin da ba muharraminki ba." 'Yar gwal ta ɗago tana bin sa da wani irin kallo, sai kawai suka ji ta saki jiki ta faɗi yaraf a ƙasa. Sai a lokacin Yaya Inu ya ja gefe yana kaɗe riga, ya cigaba da wurga mata kallon tsana kamar zai mata duka.

"Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?"
Furucin Baba Ɗanladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, Ɗanladi ya ɗago ya dubi Yaya Inu ya ce.
"Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." Ɗanladi ya ƙarasa maganar yana ɗaukar 'Yar gwal ya shige ɗaki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce.

"Inusa yaushe ɗan'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?"

Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin ƙiri-ƙiri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce. "Inno kin fi kowa sanin wane ne Ɗanladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba."
Daga cikin ɗakin Ɗanladi ya ce.

"Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini ƙage, kuna cewa ina lalubar yaran mutane a chemist ɗina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke ƙyashi na raya?"

'Haƙiƙa na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tirƙashi, wannan Ɗanladin ai ya gama tashin kaina.'
Mai Yasin ya raya a ransa.
Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta.
"Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta ɓaci a banza. Yanzu mu je ciki ni ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun nutsuwa."
Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga ɗaki.

"Inno ɗazu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..."

"Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga haihuwar yarinyar za ta ɗauko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?"
Inno ta katse shi tun bai ƙarasa magana ba.

"Don Allah Inno ki bari na dire maganata."
Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta ɗora daga inda ta tsaya.
"An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce, saboda kowa shaida ne ban taɓa haihuwar zabiya ba."
A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan ta ce.

"Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama saɓon Allah sannan za ka same ni kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka ɗauki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi maganar tana miƙewa, har za ta shige uwar ɗakinta ta waigo ta ce.
"Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin da kuka kwaso Allah Ya jarabce ni da shi." Tana gama maganar ta shige ciki. Kamar Yaya Inu zai ɗora hannu a ka, haka ya fice daga sashen Inno abin duniya ya haɗe masa.

Yamma ce sakaliya, sanyin la'asar tuni ya riga da ya sauko. Fadar Mai gari cike take da mutane ana zaune ana zaman fada. Mafi yawan mutanen da suke zaune gulma ce ta kawo su, a kan abin da ya faru da Mai gari. Shi ma da yake ya fahimci haka sai ya tsuke fuska, ya dubi su Mahmud da suke takure kamar zakarun da aka tsamo daga ruwa ya ce.
"A madadinmu da na talakawan yankinmu muna yi muku barka da zuwa. Muna buƙatar ɗayan bayan ɗaya, ku gabatar da kanku a gaban mutane. Mudassir ne ya ɗan muskuta zai yi magana, Mai gari ya yi wa Mahmud ƙuri da ido ya ce.

"Kai yaro, kamar na san fuskar nan taka?"

Cikin Mahmud ya karta, amma sai ya yi ta maza ya ce. "A'a ranka shi daɗe, sai dai idan mai kama da ni ka sani. "
Jin Mai gari ya yi shiru ya sa Mudassir ya furta, "Ni dai sunana Mudassir Najib, ɗaya daga cikin ɗaliban da aka turo daga babbar Jami'a yin bautar ƙasa (NYSC)." A fili Mai gari ya faɗaɗa fara'arsa yana jinjina kai, saboda ya ji ya ce bautar ƙasa suka zo don haka sai ya ci banza. Har ya fara lissafa kansa, a sahun mahajjatan da za su sauke farali a bana. Duba da irin aikin gonar da ya ayyana zai jibga wa su Mudassir. Shi ma Mahmud ya gabatar da kansa, sannan Mai gari ya fara baza babbar yana haɗe rai ya ce.

"Tun da har Gwamnati ta aiko ku garin nan, na tabbata babbar Masarauta ƙasar nan ta san irin gudunmawar da nake bayarwa a ƙasata. A don haka, ya zame muku wajibi ku zage damtse ku yi mini noma yadda ya kamata." Mai gari ya zaro ido waje cike sa barazana ya sake dubansu ya ce.

"Ku dube ni nan, bautar ƙasa ba wasa ba ce yara ina fatan kun gane. Domin shinkafar da kuke miƙe ƙafa kuke ci, ita ma sai da aka gama bauta mata sannan ta bauta muku a cikinku.

"Ammm amma ina ganin kamar ba ka fahimce mu ranka shi daɗe. Service muka zo fa, ga wannan takardar za ka iya karantawa." Mahmud ya ƙarasa maganar yana miƙa masa takardar.

Gaban Mai gari ya faɗi, da ya ga ya miƙa masa wata zungureriyar takarda mai cike da rubutun turanci. Sai da ya fakaice su ya sharce gumin fuskarsa, sannan ya riƙe takardar yana ɗan matse idanu ya fara karantawa.

"Assalamu Alaikum. Ni Mai girma gwamna, na aiko waɗannan jajirtattu kuma haziƙan ɗaliban nan, domin su zo garin nan su taya Mai gari aikin gona wanda muke kira da bautar ƙasa. Kuma a don haka, muke jan kunnensu domin su jajirce wurin yin aiki tuƙuru. Idan ba haka ba, za mu zartar musu da mummunan hukunci." Mai gari ya ɗago yana muzurai, daga can ƙasa ya ga wani rubutu da lambar waya har da saka hannu, sai ya ce.

"Ga lambar wayata nan ni mai girma gwamna, duk wani ƙorafi da kuke da shi kai tsaye za ku iya tuntuɓa ta. Kuma duk wanda ya yi ba daidai ba a cikinsu, muna bayar da umarnin Mai gari ya saɓa masa. Idan da hali ma ya ci tararsa."

Tun da ya fara jawabin Mahmud da Mudassir, suka yi zuru suna kallonsa cike da mamaki. Mutanen da ke wurin suka ɗauki sowa cikin kambaba Mai gari suka ce. "Allah Ya ja zamaninka mai martaba. Haƙiƙa gado ba karanbani ba, duk wanda ya san gidanku ya san mane ne mulki." Mai gari ya fara zuba doro yana kalle-kalle cikin izza. Hambali da yake gefe cikin tsananin jin kunya ya ce.
"Allah Ya taimake ka, idan na fahimce su fa kamar ba haka suke nufi ba. Duk da dai ni ma ba karatu na yi mai zurfi ba, iya ka ta diploma. Idan aka ce an tura ɗalibi NYSC wato bautar ƙasa, ana nufin ya hidimtawa ƙasa ta hanyar bunƙasata da ciyar da ita gaba. Kuma kamar wani ƙarin horo ne, da ɗalibai suke sake gogewa; domin su zama shugabanni ko al'ummar da za a yi alfahari da su a gobe. Amma a gafarce ni ranka shi daɗe, idan na faɗi ba daidai ba."
Tun bai gama magana ba Mai gari ya fusata. Rai a ɓace ya nuna Shazali ya ce. "A kanannaɗe shi a hukunta shi, mu zai kawowa raini a gaban fada? Shazali, yaron nan yana nufin fada ba ta san me take yi ba ne?"

"Allah Ya taimake ka, abin da bawan Allahn nan ya faɗa fa haka ne. Ba aikin gona muka zo ba, kamar yadda ka faɗa..."
Da sauri Mai gari ya katse Mahmud.

"Kai yaro ka iya bakinka. Shin ya bari mun gama fesar da maganganun bakinmu ne? Ko numfashinmu ya tara? Abin da muke shirin faɗa kenan ya yi mana katsalandan, don haka dole a hukunta shi." Kallon tsaf Mahmud ya yi masa, yana jinjina ƙarfinsa. Bayan Mai gari ya sallame su, suna tafe a hanya ya ce.

"Na lura da Mai garin nan tsaf, ashe duk burgagin banza yake yi. Ba abin da ya sani wallahi, kawai su yake naɗewa."
Mudassir ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa sai dai su ya naɗe su, don idan ya shiga tawa gonar sai na yi masa naɗin da ya fi na huhun goro." Gabaɗaya suka saka dariya.

Baba Sale shi da Uwale ba su suka dawo daga asibiti ba sai yamma liƙis, saboda bayan likita ya gwada Ɗan Bishir sai da aka ba shi gwaje-gwaje. Bayan sakamakon ya fito aka yi masa dressing, sannan aka rubuta musu magungunan. Duk soyayyar da Baba Sale yake yi masa haka ya danne shi da ana wanke masa, saboda likita ya tabbatar masa da matuƙar bai samu kyakkyawar kulawa ba komai zai iya faruwa, tun da har wurin ya fara ruwa yana ɗan wari. Likitan ya gargaɗe su sosai, wurin kula da tsaftar sabon gyambo koda ba na kaciya ba ne, sannan ya ce bayan kwana uku su koma a sake duba jikin nasa. Bayan sun koma gida, ko zama bai yi ba ya nufi gidan Bala wanzan. A ƙofar gida ya tsaya ya ce a yi masa sallama da shi, yana nan tsaye yaron ya dawo tare da wani ɗan matashin saurayi.

"Kai Tasi'u, ina mahaifinka yake?"

Baba Sale ya furta fuska babu walwala. Matashin da ba zai wuce shekara goma sha uku ba, ya rausayar da murya cike da neman tausasawa ya ce.

"An tafi da Baba ofishin 'yan sanda ɗazu."

Da sauri Baba Sale ya ce, "Ofishin 'yansanda fa? Me ya yi aka kai shi can?"

"Ban san takamaiman abin da ya yi ba, amma an ce wai Idi Naira ya yi wa aska, kuma wai ana zargin yana da cutar ƙanjamau!"

"La'ilaha'illa'illahu Muhammadur Rasulillahi, Sallallahu alaihi wasallam. Ɗan Tasi me kunnuwana suke zuƙo mini? Kada ka ce mini Ɗan Bishiriri ya kamu, wayyo Allah Tasi riƙe ni da ƙarfi duhu nake gani."

Baba Sale ya yi maganar yana jin wata irin hajijiya tana yin ɗiban karan mahaukaciya da shi.
Da sauri Tasi'u ya riƙe shi yana kiran sunansa da ƙarfi, "Baban Ɗan Bishir lafiya." A hankali Baba Sale ya ɗago duk da ba ya gane abin da Tasi'u yake faɗa sosai ya ce, "Tasi'u maza kai ni ofishin 'yansandan."
Kamar sabon ɗan maye haka suka tafi Tasi'u yana riƙe da shi, don har suka ƙarasa wani irin layi yake yi idanunsa suna yi masa gizo. Su Baba Sale suna zuwa, suka samu Bala Wanzan a tsaye yana bayani.

"Wallahi tallahi yallaɓai ban taɓa sanin Idi Naira yana da cutar abar nan ba, ni ko sunanta ba na son faɗa. Kuma babban tashin hankalina yaran da na yi wa shayi, a ranar da wannan tsautsayin ya afku. Domin su ne masu tasowa ba su mori ƙuruciya ba..."
Wata irin ƙara suka ji gijiiiiiif Baba Sale ya faɗa ta saman kanta, saboda tun a bayanin farko da ya ji Bala wanzan yana yi, ya ji ƙafafuwansa ba za su iya ɗaukarsa ba. Kalaman Bala na ƙarshe suka sa ya ga wani baƙin duhu ta lulluɓe idonsa, numfashinsa ya ɗauke.

"Subhnallah! Waye wannan? Lafiya?"

Wani kurtun ɗansanda ya ƙarasa kansa yana tambaya. Tasi'u ne ya yi musu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Baba Sale, har zuwansu cikin station ɗin. Ruwa aka ɗebo aka zuba masa, a hankali ya farfaɗo yana daga kwance yake kallon mutane ɗaiɗai. Ya yunƙura a hankali ya zauna sai a lokacin komai ya shiga dawo masa.

"Yallaɓai Ɗan Bishir, kun bincika mini Ɗan Bishiriri."

Wani Sergent da ya fahimci Baba Sale, ya dubi Bala Wanzan ya ce, "Kai Wanzan ka yi wa yaron wannan mutumin kaciya ne?"

Da yake a lokacin an mayar da Bala cikin cell, yana daga ciki ya ce. "Eh na yi masa yallaɓ..."
Tun Bala bai gama magana ba Baba Sale ya sake sumewa a wurin, haka suka sake zuba masa ruwa ya sake farfaɗowa. Sai dai su kansu abin da ya fi ɗaga hankalinsu, yadda Baba Sale yana farfaɗowa zai sake suma. Har sun lura ko ya farfaɗo ba ya zama cikin hayyacinsa. Don haka suka tattarashi hankali a tashe suka yi asibiti da shi, sai bayan sun je suka saka Tasi'u ya yi musu rakiya har gida aka sanar da Uwale da su Baba Ibrahim halin da ake ciki.

Tun da suka fito daga asibitin yake zabga sauri, cikin sassarfa ta rufa masa baya ganin ya fara yi mata nisa ya sa ta fara ƙwala masa kira.

"Masoyi! Masoyi don Allah ka jira ni saurin me kake yi kamar za ka tashi sama."

"Ya muke da jirgin sama? Na ce ya muke da shi?"
Baba Labaran ya furta a zafafe.
Sororo ta yi tana kallonsa don har tsoro-tsoro ta ji, ganin yana yi mata faɗan da ba ta saba gani a tattare da shi ba. Hasali ma ba ta ga abin faɗa a maganarta ba.

"Asibiti na uku kenan a yau muna zuwa suna yi miki gwaji, amma duk maganarsu ɗaya kamar haɗin baki. To magana ta gaskiya na fi son mace a haihuwar fari, saboda magaji nake nema. Haka kawai duka asibitocin sun ce mace suka gani. Wallahi da sake an ba wa mai kaza kai." Da mamaki ta dube shi ta ce.
"Da sake fa ka ce Masoyi? Shin butulci za ka yi wa uabangiji ne? Mutane nawa ne suke neman haihuwar ba su samu ba, mace ko namiji mai albarka ya kamata ka roƙa."
Maimakon ya ba ta amsa sai kawai ya saki tsaki ya yi gaba yana faɗin.
"Kanki ake ji, ni na gama faɗar ra'ayina."
Daskarewa Rahinatu ta yi, ta ɗora hannunta a kan ƙaramin cikin jikinta da bai fi wata uku da satika ba. Cikin sanyin murya ta ce. "Dama duk soyayyar da mutumin nan yake yi mini ta fatar baki ce? Haƙiƙa Labaran ya cika butulu."
Daga haka ta fara takawa a hankali, ta rufa masa baya tana jin zuciyarta na suya.

Damuwa haɗe da tarin ayarin tunaninnika ne suka cunkushe masa kwanya, saboda Indo da su Hansatu sun nemi mayar da shi kamar mahaukaci. Don da sun kalle shi sai kowacce ta gimtse fuska, yana bada baya sai su kwashe da dariya. Rumfar Tsalha mai kayan miya nufa, yana zuwa ya yi sallama amma babu wanda ya amsa masa. Kamar haɗin baki, lokaci ɗaya mutanen cikin rumfar suka watse . Turus Yaya Inu ya yi, yana shirin magana ya ji Tsalha ya ce, "A gaskiya malam Inusa ka dakata da zuwa cikin rumfata, saboda ka da ka kawashe mini albarkar cinikayyata. Ba zan ɓoye maka Inusa ka san dai ni abokinka ne, maganar haihuwar zabiyar nan fa ya karaɗe ciki da wajen garin nan don haka ka yi hattara." Daga haka Malam Tsalha ya koma kujera ya zauna yana haɗe rai, don kada Yaya Inu ya samu fuskar zama.

Kamar zakaran da aka tsamo daga cikin ruwa haka Yaya Inu ya fito ya nufi hanyar gida, tunanin Zuly matashin kai ce ta faɗo masa. Ya saki murmushi ya nufi ƙofar gidansu. Ƙaramar wayarsa ya ciro ya kira ta, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana taunar cingam.

"Haskena ashe kaine da yamma haka?"

Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Takanas na shiryo na zo na ganki domin na huce takaicin zuciyata, saboda ke kaɗai ce hasken da ke yaye duhun da ke ɗanfare a ciki."
Sai da ta hura kwai da cingam ta ce, "Wani zance nake ji yana tashi, wai an haifar maka zabiya 'yan gidanmu har sun fara bala'i. Ni kuwa na ce duk bala'insu ba zabiya ba, ko rabi mutum rabi aljan aka haifa maka babu wanda ya isa ya han ni aurenka." Farinciki ya sa ta Yaya Inu ya zaro rafa kuɗi har dubu goma ya miƙa mata.

"Ki sha lemo da wannan, masoyiyata kuma

43 / 46