Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   44 / 46

129K to 132K   out of 137.8K words

hasken zuciyar Inusa."

Alewa ta buɗe ta wurga a baki ta tsotsa, sannan ta zaro ta miƙa masa cike da kissa. Cikin so da ƙauna Yaya Inu ya karɓi alewar, ya jefa a baki ya yi mata sallama. Yana gab da shiga gida ya hango wani mai magani, yana tafe da wata ƙatuwar Mp3 da wani faffaɗan kwando mai ɗauke da magungunan maza a ciki.

"Ina mai matsalar kuzari? Ina namijin da ya rako maza? To ya hanzarta ya zo ga adamalmala. Maganina rabo ne, maganina sa'a ce. Alhaji sai mai tsananin rabo ne zai dace na ba shi, ina mazan da basir ya jima da yi musu illa? Alhaji ba ka nisan zango wurin tuƙa sitiyarin mota? Don Allah ka zo, ga mai adamalmala ya dawo. Idan na bar garin nan ba zan dawo ba, maza kaɗai nake ba wa magungunana domin na fi kishinsu a kan mata. Alhaji ko Malam kada ka ji kunyar karɓa, indai matsalarka a ɓangare iyali ne ta kau. Sabon aure za ka yi ne? Ko kuwa ka rasa gane kan matanka ne? To maza gangaro ka karɓa sadakar ƙalilance, ni dai ba na rowa domin burina na kankaro mutumci a wurin maigida."
Yaya Inu ya tsaya a jikin bishiya ya yafito shi da hannu, Mai maganin ya ƙarasa wurinsa adaidai lokacin Na Balaraba ya ƙarasa ta wurin zai wuce.

"Kai wa nake gani kamar Gambo, ko idanuna ne?"
Cewar Gambo.
Mai maganin ya ɗago yana kallon Na Balaraba da sauri ya ce, "Kai! Wa nake gani kamar Na Balaraba? Dama rai kan ga rai?"
Yaya Inu ya washe baki, "Na Balaraba ka san shi ne?"

Na Balaraba ya furta, "Na san shi farin sani, yanzu ne dai zumunci ya zama yanda ya zama, shekara biyar zuwa shida rabona da shi."

Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Ka ce faɗuwa ta yi daidai da zama, dama kiransa na yi zan sayi magani."
Mutumin tun da ya yi tsaye yake ƙarewa Yaya Inu kallo, har sai da gabansa ya faɗi. Amma jin Na Balaraba ya ce ya san shi ya sa ya saki jikinsa.

"Haba ba ka da damuwa Inusa, ka sayi maganinka wannan da kake gani ba na shakku a kansa."

Yaya Inu ya nuna wani magani ya ce yana son saya, Mai maganin ya yi zaraf ya ce. "A'a mai gida bari na ba ka wannan, ai wannan shi ne gagara-badau an buga da kai an barka." Ya ƙarasa maganar yana miƙa masa wata roba ƙarama ya ɗora da cewa.

"Yanzu kana komawa gida tun da magariba ta ƙarato ka shafa shi, sai bayan minti talatin ka wanke da ruwan ɗumi. Ka zuba wa sarautar Allah ido za ka ba ni labari idan na sake dawowa."
Jiki yana rawa Yaya Inu ya zaro kuɗi ya biya. Bayan Mai maganin ya tafi Baba Ado da yake gefe ya ce masa.
"Yanzu Allah Yaya, ba za ka raba kanka da gabzawa kanka waɗannan magungunan barkatai ba? Haka kawai maganin kare da doki kowa na ka ne, ba ka duba inganci ko ka je wurin masu magungunan gargajiya waɗanda suka san kansu ka saya..."
A sheƙe Yaya Inu ya katse shi.

"Kai dakata kada ka yi mini rashin kunya, tuzurun banza da wofi. Wai har da su kaza a cin danƙo? Kai da ko arzikin auren ba ka samu ba, shi ne har za ka zauna kana yi mini fi'ili? Tun da kai 'yan mata aljanu sun gama tsuƙe jijiyoyin jikinka, ai sai ka bar masu raya sunnar Annabi su yi. Da uwar kuɗina nake saya babu wani ƙato da yake saya mini, don haka kada ka sake shiga hurumina."

Yaya Inu yana gama magana ya shige gida a fusace.
Yana zuwa ɗakinsa bayan ya huta ya shafa man kamar yadda Mai maganin ya faɗa masa, bayan kamar minti biyar da shafa man ya ji wani irin zafi yana ratsa shi. A ɓangare ɗaya kuma ya fara jin kamar ana tsoma wurin a ruwan zafi, ba shiri ya tashi ya rage dogon wandon jikinsa. Ya ɗauki muhuci yake firfita, jin azabar ta yi yawa ya sa yaYaya Inu ya faɗa banɗaki a guje har yana ɓari da kwanuka. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, bayan ya shafo jikinsa ya ji tamkar ba na shi ba. Yaya Inu yana kai kallonsa, ganin sauyin hallitarsa ya sa wani wawan kuka ya kwace masa.


Saura na ji wani ya yi wa Yaya Inu dariya.😂

Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[05/01, 19:31] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd

Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻

SHAFI NA SHA BIYU

Indo tana daga bakin murhu ta fara jiyo numfarfashin Yaya Inu da shasshekar kukansa, da farko ba ta yi tsammanin shi ba ne. Saboda hayaniyar yaran da ke kai-kawo a cikin gidan, sai da ta kasa kunne sosai sannan ta fahimci kukan babba ne. Mamaki ne ya kama ta, don su Hansatu gabaɗaya suna nan ballantana ta ce wata daga cikinsu ce. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar banɗakin tana zuwa ta ji yana faɗin.

"Kaico wannan wanne irin tsinanna magani da mai maganin ne? Ai kuwa ni da magani irin wannan har abada."

Sai ya sake ɓarkewa da kuka. Ƙirjin Indo ya buga da ƙarfi, ta ɗan buga ƙofar banɗakin ta ce. "Mai gida lafiya kuwa? Me yake faruwa?"

Daga can cikin banɗakin Yaya Inu ya ja majina ya ce, "Shigo ciki Indo."

"Cikin banɗaki fa Mai gida?"
Ta tambaya da mamaki.

Yaya Inu bai sake tanka mata ba saboda yadda abin duniya ya dame shi, tambayar Indo ma haushi ta ba shi, don haka ya ja baki ya tsuke. Jin Yaya Inu ya yi mata shiru, ya sa Indo ta faɗa banɗakin gabanta yana faɗuwa musamman da ta tuna bai taɓa yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a ɓanɗakin ba ta sani ba.

"Mai gida lafiya kake kuka a banɗaki?"

Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne.
"Indo na haɗu da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana."

Muryar Yaya Inu kaɗai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Me ya faru dai yanzu?"

Yaya Inu ya zauna a kan wani ɗan dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce.

"Ku je ku kori yara ɗaki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni ɗakina. Saboda su kansu jijiyoyin ƙafafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba."

Jin haka ya sake ɗaga hankalin Indo, ta ja ƙafafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke ɗinkin mahuci ta furta.
"Mai gida fa babu lafiya Hansatu."
Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawaƙe, kowa ma fama yaka da rashin lafiya."

"Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara ɗaki mu je mu ɗauke shi mu mayar da shi ɗakinsa."
Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu ɗauka mu kai ɗaki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"

Da sauri Hansatu ta miƙe, kowacce ta shiga ƙoƙarin tura yaranta ɗaki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya haɗa kai da gwiwa. Abin da ya sake ɗaga hankalin matan nasa, ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa yana ambaliya.

"Mai gida! Wai me yake faruwa haka?"

Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta shaƙe can ciki ya ce.
"Ku yi tara-tara ku kai ni ɗaki. "

Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai ƙiba ba, ya sa su ukun suka haɗu suka ɗaga shii suka yi ɗaki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana saƙa da warwara a cikin ranta.

"Ɗazu gabanin zan shigo gida na haɗu da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!"
Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana bankaɗe zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa.

"Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?"
Hansatu ta faɗa a ruɗe.
Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi."

Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya ɗauka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can ɓangaren ya ce.

"Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai."
Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa ƙarfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zuƙe?"

"Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa."
Kalaman mai maganin kenan da suka ɗan ƙara wa Yaya Inu ƙwarin giwa.

Larai da ke riƙe da haɓa ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya."
Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?"

Larai ta murguɗe baki gefe ta yi ƙasa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. Ƙila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta saɓon Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..."

"Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa."
Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji.
Kalaman su Larai ba ƙaramin ɗaga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune ƙirjinsa yana bugawa ya ce.
"Na rantse da girman Allah ban taɓa aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi."
Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron taɓa ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta.

Kuka Yaya Inu yake iya ƙarfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ɗago mata hannu. Ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba ƙaramin tashin hankali ba ne.

A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?"
Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu."

Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani ɓangaren ya fara ba ta tsoro.
"A'a kai ne mai faɗa aji ai, tun da kai rana ta ƙwacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya faɗa."
Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya riƙo hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke kaɗai ce ba ki guje ni ba a cikinsu."
Hansatu ta yi wa Yaya Inu ƙuri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce.
"Ai wannan kalaman da kake faɗa na fatar baki ne ranka shi daɗe, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka taɓa sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida."
Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lulluɓe shi, Hansatu ta cigaba ɗebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce ɗakinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da ƙyar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara daɗi yana miyagun mafarkai kala-kala.

Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga halin da Ɗan Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye ƙaramin asibitin gwamnati ƙauyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa ƙarin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya buɗe idonsa.

"Sannu Sale, ya jikin naka?"

Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?"

Ya gyaɗa masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai kai musulmi ne, ka yarda da ƙaddara mai kyau da akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka Ɗan Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar ɗauke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ɗungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga faɗar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba."

Da sauri Baba Sale ya riƙo hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona."
Baba Ibrahim ya sake haɗai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan."
Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su kuɗin ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station.

Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya ɗora da cewa.
"Yallaɓai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gabaɗaya."

Sergent ɗin da ke tsaye ya buɗe wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo ƙarar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ƙofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case ɗin zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana ɓa ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan ɗin?"

"Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." Ɗansandan ya furta.
Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ɗari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi ƙarar Malam Shehu zai ɓata masa suna.

Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a ɓangare ɗaya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar Ɗanladi a

44 / 46