Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   31 / 46

90K to 93K   out of 137.8K words

Kabir ya nuna yaransa ba za su yi talla ba sai ta kawo ido ta saka masa. Fauziya da karanbami har magana ta yi a kan su Salim, a nan ne Inna ta ce daga Kabir har ita ba su isa ba matuƙar ba mahaifinsu ne ya hana ba. Wannan dalilin ne ya ja wa Fauziya da yaranta baƙin jini a wurin Inna, ko fita suka yi tsakar gida wasa ta dinga zaginsu tana hantarasu wani lokacin har da duka.
Daga ɓangaren Kabir shi ma zamansa da ita tuni ya sauya salo, don babu abin da za ta yi masa haka kawai zai ɗauki fushi da ita. Ko kuma magana kaɗan za ta yi masa sai ya rufe ta da faɗa, daga haka ma sai ya ƙaurace mata. Domin a zaman da suke yi sun tafi kusan wata biyu ba tare da wani abu ya gifta a tsakaninsu ba.

Ana cikin haka watarana Kabir ya dawo da daddare a lokacin sha ɗaya saura, a zaune ya samu Fauziya ta yi shiru tana nazari. Tsakin da ya ja ne ya sa ta ɗago tana kallonsa, karaf idonta ya sauka a kan damɓareren jambakin da ke gaban rigarsa har zuwa leɓensa. Ta haɗiyi wani irin yawun takaici, amma ba ta tanka masa. Kamar yadda ta yi tsammani, buta ta ga ya ɗauka ya tafi banɗaki. Ba tun ranar ba, dama ta lura da shi kusan kullum idan ya dawo ya yi wanka ya fita, to bayan ya sake dawowa daga yawonsa sai ta ji ya ɗebi ruwa yana wanka. Ya tafi banɗaki ba jimawa ta ji kira ya shigo wayarsa, a kan windo ta hango wayar jikinta har rawa yake ta saka hannu ta ɗauka. Wannan ce rana ta farko da zuciya ta ingizata a kan ta ɗauki wayarsa, ƙirjinta yana bugu ta ɗauki kiran da ta ga an ributa 'Sec wf' Ɗauka ta yi sai ta yi shiru daga can ɓangaren ta ji an ce.

"Baby don Allah idan za ka yi wanka ka turo mini hoton lovely ɗina, ni ma na turo maka ina wanka ka duba whatsapp ɗinka."
Da sauri Fauziya ta katse, ta ci sa'a wayar babu key tana duba whtaspp ta ga sakon lambar da aka kira.
Ƙazantaccan hotun surorin jikin Surry ne, sai ta yi sama a nan ta ci karo da hotunan al'aurar Kabir ya tura mata hotuna. Sai kuma wasu hotuna da ta gansu rungume da juna hannun Kabir yana saman ƙirjin Surry. A yadda ta gani babu riga a jikinsa, ta ga kuma ita ma Surayyan ko ɗankwali babu a kanta. Amma sai ta lura wurin da suke kamar ba gida ba ne.

"Innalilla wa Inna ilahir raji'un."

Fauziya ta furta tana jin kanta yana sarawa, idabunta suka fara ganin dishi-dashi. Ɗakin da take ciki ta ga ya fara juya mata.

GIDANSU MAIMUNA
Saboda fushin da Nazir yake yi da Maimuna ya sa koda gari ya waye bai bi ta kanta ba, wanka kawai ya yi ya ɗebo shinkafa kofi huɗu ya tsiyayo mai wata 'yar roba ya ajiye mata sannan ya fice kasuwa. Maimuna tana kallonsa duk abin da yake yi har ya fita, da yake a lokacin tuni yaranta sun tafi makaranta, wanka ita ma ta shiga ta tsala a banɗaki. Bayan ta fito ta zaro wayarta ta ga misscall ɗin Jafar, goge hannunta ta yi za ta kira ta ga wani kiran ya sake shigowa. Tana ɗauka cikin zumuɗi ya ce.

"Baby ke fa nake jira."

Murmushi Maimuna ta yi ta ce, "Na gama komai kayana zan saka." Katse kiran ya yi. Maimuna ta jima a gaban drower kayanta, sai ta ɗauko wasu figaggun ƙananan kaya ta saka, ta zaro zumbulelen hijabinta ta zura. Ƙaramar wayarta ta gani Nazir ya mantata a falo, don ta tabbatar da ya yi nisa da gida sai ta kira shi. Har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

"Ina jinki."

"Na ga ka ajiye mana shinkafa, har dare ko iya rana."
Ta furta tana sauraron yanayin wurin da yake. Daga cikin wayar ta ji alamar yana cikin kasuwa, don ta ji ana tambayarsa hula lamba ashirin (Size 20).

"Har dare za ku dafa."

Ya ba ta amsa a zafafe yana katse wayar. Tsalle ta buga sannan ta ɗauko mukulli ta rufe gidanta, kamar yadda Jafar ya ce zai bar mata gidan a buɗe haka ta same shi. Duk da ta san Maman Nana ba ta nan, haka kawai ta ji gabanta yana faɗuwa. Tana shiga ciki ta hango shi daga shi sai gajeren wando, da sauri ya ƙarasa ya rungume ta yana zame hijabin jikinta. Wata irin kunyarsa Maimuna ta ji ta sunne kanta ƙasa, shi kuwa ya shiga laluben jikinta kamar waɗanda suka jima da sanin juna. A kan gadon Maman Nana suka yada zango, Jafar ya shiga rage mata kayan jikinta har ya raba ta da su gabaɗaya, ya shiga gwaɗa mata zafaffiyar soyayya. Abin da ya birge ta, ya kuma ba ta mamaki yadda ta ga Jafar ba ƙyamar komai na jikinta. Abin da Nazir bai taɓa yi mata ba, don shi ko kiss bai damu da ya yi wa mace ba. Sai da Maimuna da Jafar suka gigita juna sannan komai ya wakana a tsakaninsu, cike da so ya rungumo ta a jikinsa ya ce.
"Don Allah ki cigaba da ni haɗin kai zumata." Gyaɗa masa kai ta yi har lokacin hannun Jafar yana cikin jikinta.

Bayan gari ya waye sai da Maman Nana suka ci abinci sannan ta yi musu wanka, ta nufo hanyar gidanta. Mahaifinta ya yi mata nasiha sosai, ya sake tabbatar mata da zai kira Jafar ya yi masa faɗa. Da yake ita ma tana da mukulli a hannunta, tana zuwa bakin gate ta saka key ta buɗe jamlock ɗin. Ta yi mamaki da ta ga motarsa a gida har lokacin, amma sai ta yi tsammanin ko lalacewa ta yi bai fita da ita. Don haka ba ta yi wata-wata ba ta nausa kanta ciki, tun daga tsakar gida ta fara jiyo sautin dariya da wasannin da suke yi a cikin banɗaki da ruwa suna wanka.


AlhamduLIllah a nan ƙarshen free pages ya ƙare, ba sai na tsaya bayanin irin cakwakiyar da za a riska a gaba ba. Mai son cigaba zai biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
In Shaa Allah Jibi Asabar zan cigaba da posting a paid group

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[04/12/2024, 14:28] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA ƊAYA

Jar mota ƙirar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare ɗima-ɗiman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot ɗin motar a buɗe yake waɗansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu riƙe da jarkokin magunguna suna ɗagawa. Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ƙura da jar ƙasa. Mai maganin gargajiyar yana daga cikin motar, ya sake ƙara volum ɗin recording ɗin tallan magungun da yake yi.

"Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku dawo na ba ku kuɗinku. Ina mai fama da sanyin ƙashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka kallon cikakken namiji amma a baɗini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai maganin ya rage volum ɗin recording ɗin, sai ya zuro kansa ta window ganin ya ƙaraso wurin da jama'a suke zirga-zirga ya ce.

"Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma ɗan kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su."

Baba Inu da ke kishingiɗe a kan benci ya tashi zaune, ya ɗan ƙanƙance ido yana ƙarewa motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba baƙinsa ba ne, don yana iya tantance duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer.

"Kai mai magani, zo nan."
Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking ɗin motar yana kaikaitata a daidai ƙofar gidan.
"Babana da Innata ga ɗan baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo kada a yi wasa."
Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. Ƙuri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina amma dai kai baƙo ne a garin nan ko?"
Mai maganin ya gyaɗa kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai baɗi."
"Miƙo mini wancan maganin na jarka, nawa ne kuɗinsa?"
Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da jiƙaƙƙun itatuwa a ciki. Jarka biyu mai maganin ya miƙa masa yana faɗin.

"Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka ɗaga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka dawo ka ba ni bayani."

Baba Inu bai jira cewarsa ba ya ɓalle murfin robar, ya ɗaga ta sama sai da ya ga maganin ya ƙare sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana a wannan layin ko?"
Horn ɗin da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa.
"Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun ƙaraso."
Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya ƙarasa da ta shi motar ya yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya ƙarasa gaban Baba Inu ya shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya ɗaga ya shanye. Da sallama ya ƙarasa wurinsa haɗe da faɗin.

"Yaya barka da hutawa."

Baba Inu ya ɗan kalle shi a sheƙe ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?"
Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya ƙalau Yaya."
Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi? Ka saka ni a gaba ko kai ma a miƙo maka maganin ne?"
Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam."

Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace ɗaya har ya bugi ƙirji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke."
Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce.

"Yanzu Yaya hanyar da ka ɗauko wa kanka mai ɓillewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin shaye-shaye da jiƙe-jiƙen magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi a ƙofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci waɗanda kake sha babu wata ƙa'ida kai tsaye kake hankaɗa wa cikinka, kuma mafi yawa masu haɗa magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda za a yi mu ɗauki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba."

Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa.
"Yaya da ace kuɗaɗen nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ƙananan ƙwayayan ake sake ƙyanƙyashe maka."
Baba Inu ya ɗago fuska a haɗe ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka cigaba."
Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Na gama."

"To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin zaɓe ka zo ka tsaya mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda za ka yi domin ka turmushe mini ƙwaiƙwayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura baƙinciki da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin ƙwaiƙwayen haihuwa masu yawa da albarka kamar ni ba."

Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faɗa, yadda kake sakin jiki kai da matan da kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba."
A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce.

"Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faɗa kanka. Sai ja je ka yi ta fama da 'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba."

Ganin Baba Inu bai ɗauki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce.
"Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba.

Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa.

Komai baƙin cikin tsololon ƙato.
Wallahi sai dai ya yi ƙototo.
Na zama kainuwa a wannan loto.
Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina.

Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa.
Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan ya ce.

"Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!"
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace ya ce.

"Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar ka yi mini haɗin komai da ruwanka."
Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar motarsa da yake tallan magungunansa, ya buɗe ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin magani sannan ya rufe.

Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi sallama da mai maganin ta ce.

"Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan."
Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?"

"Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare Ɗahe ɗan gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa. Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin ɗan bokiti ban da son zuciya?"
Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suɗe hannunta da ya yi shanana da miyar ragadada.
Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta."
Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari.

Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan tabarmar fuska a haɗe ta ce.

"Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!"
Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?"
Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce.

"Ke Laraba waye wannan?"
Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban Ɗahe kamar ba ta gane shi

31 / 46