Dahuwar Kawo Book Compelet Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   22 / 46

63K to 66K   out of 137.8K words

kuɗin ta goge alert ɗin. Sai da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunnata, a gaggauce ta shiga kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira ta.

"Baby yanzu na ga kulin ya shigo."

Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har cikin zuciyarta ta yi. Ta ya ce, "Yanzu saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka." Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce.

"Ni fa na gagar haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna."
Maimuna ta ji daɗi sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano ta.
"To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..."

"Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa."
Jafar katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa.
"A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamat na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce.

"Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi."

Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake ɗamfare cikin zuciyarta, kalamasa suka yamutsa zuciyarta tana jin ɗacin yaudarar da Naziri ya yi mata a shakarun baya.

"Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci kawai nake jira my baby."

"Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?"

Tambayar da Jafar ya yi mata ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta tana ƙarewa kanta kallo.
"Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi duk wanda ya ganki ba zai cw kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan kasaran da ta yi shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma leda a ruwa."
Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta ce.
"An ya ba faɗa kake ba Baby, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana mayar da hankali wurin gyara."

Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan ba wa Maman Nana ta kawo miki gobe..."
Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faɗa kuwa Jafar?"

Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa maman Nana waya ta kawo miki har shi ne ya sa kike kiran sunanan gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan ce mata mijinki ne ya ba hi sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ya miƙo miki, amma sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?"
Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun ɗan ɗauki lokaci suna waya sannan sula yi sallama cile da kewar juna.

Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munaharinsa, wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin murya ta ce.

"Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini mijina."
A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta.
"Don Allah ki yi haƙuru Fauzina!"
Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa.

"Zuwa yanzu ya ci avw na haddace waɗannan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima zan yi sallah.
Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce.

"Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan ne ƙarshe."

"Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata magana da za ka faɗa mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su yi maka dole idan kai ma ba ka so ba."

Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallaahinta. Alwala ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daɗin baki ya ce.

"Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci."

Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa.

"Ragowar ta ce sai bayan kwana uku, an jima idan gari ya waye ta ce za ta zo da wanda zai ɗauka."
Kabir ya janye hannunsa daga kuɗin ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin gidan can, ka an rage. Idan ta kawo cikon kuɗin, kafin nan kai ma ka samu wasu sai ka haɗa da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a rage." Fauziya ta ɗan kalli ɗakinsu da shinfiɗar su Na'ima cikin damuwa ta ce.
"Na gaji da zaman da muke yi ɗaki ɗaya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana da su a ɗaki ɗaya zai iya haifarwa tarbiyyarsu da matsala." Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce.

"Haba ne Fauzina, amma kuɗaɗen da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan gaba."
Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta dube shi a sanyaye ta ce.
"Me kake gudu Abban Na'ima?"

"Ina gudun kada watarana abin abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ya yi ba, domin duk abin da take yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne domin a ganinta rufin asirinsa tamkar rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya gifa biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burun kawo wata ƙaddara da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bauta wato gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin tamkar bai ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce.

"Shi kenan tun da kai abin da ka ɗauka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka, tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro."

Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce.
"Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin na mene ne?"
Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana."

Hira suka yi ɓarke da ita har gari ya ƙaraaa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abim ya ce ta kai masa, har turare sayo mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin hannunta na kuɗin kitso ko gyaran tsumma da take yi sai da saya wa matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta komai ba da kuɗinta take ɗan saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba.

Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana bai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata da martanin baƙar magana.
Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan gabaɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba ma zai iya zuwa da ƙafa.

A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna Sadiya tana tsakar gida tana wanki, Inna kuma tana zaune tana ɗaurin tsintsiya. Sadiya ce ta faɗaɗa fara'arta ta ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana ɗa a titi?"

Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban ta tsugunna ta ce.
"Barka da hutawa Inna."
Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna domin irin matan nan ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata, amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawa da take yi mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta ɗan taɓe baki ta ce.

"Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi, Inna ta sake leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa.
"Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini garin tuwo da taliya. To dai nan ɗin da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni."
Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilim da ya sa ba sa son zuwa wurin Inna yawan faɗanta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta cw su zo su gaida Inna amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya.

"Ke Salim ku zo ku ɗauki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki ɗauka. Yau idan kika sake ki yar munnda kuɗi wallahi sai ubanki ya biya ni kuɗina."
Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da mahutan. Sadiya ko kaɗan ba ta jin daɗin tallan da Inna take ɗora mu, don dai babu yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace.

"Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa."
Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin tsintsiya sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuya ko ƙullin gishiri ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce, "To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da wuri za ku wuce ne Fauziya."
Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce. "Yanzu za mu wuce Inna, dana zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki." Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin.
"Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na yi mata."

Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?"
Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya, wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa."

"Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?"
Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen kuma su yi rayuwa kamar kowa."
Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar hankali.
"Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri ɗaya dama yana kawo haka, ki cigaba da addu'a sai ki ga watarana sai labari."

"Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a gidan."
Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abim da ya fi ƙarfin addu'a."

Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta.A tsakar gida ta samu mahaifinta yana ta bambamin faɗa a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu. Su Nai'ima kuwa dana tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu.


Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakim dandamalin rijiyar sannan ya ɗauka.

"Gimbiyar mata!"

Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce.
"An ya kana jin abin da nake ji kuwa?" Kabir ya sake kwantar da murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faɗin haka."
Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp ɗinka na turo maka da hotuna."

Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya.

"Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana."

22 / 46