Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
ya katse kalaman da take yi, cikin jin azaba ta dafe kumatunta. Kafin ta ɗago Ruƙayya ta sake ɗauke fuskarta da mari har sai da kanta ya bugu da bango. A razane Shukura ta ja da baya, ta saka hannuwa biyu ta dafe kumatunta cikin tsoro ta ce.
"Ni kika mara Mami?"
Cikin zafin zuciya Ruƙayya ta sake yin kanta gadan-gadan ta ce, "Na mare ki, wallahi idan kika sake furta kalma mara daɗi a kan mahaifiyata sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Annoba makira, In Shaa Allahu da sannu za ki girbi abin da kika shuka."
Shukura ta sauke hannunta, ta nuna Ruƙayya da yatsa ta ce.
"Wallahi za ki san kin kai hannunki saman kumatuna, na rantse da Allah sai na rama a kan wannan tsohuwar kilakin." Tana ganin Ruƙayya ta yo kanta, ta fita da gudu haɗe da fashewa da kuka. Lokacin da Shukura ta fita harabar gidan, Alhaji Umar ya shiga mota kenan zai fita. Tana zuwa jikin motar ta sake rushewa da kuka tana riƙe cikinta, da sauri Daddy ya fito jikinsa har rawa yake yi ya ce.
"Me ya faru Shukura? Mene ne ya samu cikin naki?"
Durƙushewa Shukura ta yi cikin kuka ta ce. "Kawai daga kai wa Hajiya takarda, shi kenan ita da Mami suka rufe ni da duka. Hajiya har tana dukan cikina, wai gara na rasa cikin kowa ya huta. Ni gaskiya ba zan cigaba da zaman gidan nan ba, wallahi ko dai su fice su bar ni ko kuma ni na fita bar su, don wallahi ba zan zauna su kashe ni ba."
Cikin kumfar baki Daddy ya ce.
"Ita Hajiyan saboda ba ta da hankali ta dake ki a ciki? Wato saboda na sake ta sai ita da Mami su huce a kanki ko? Bari na shiga gidan." Yana gama faɗar haka ya shige da sauri, har babbar rigarsa tana shirin kayar da shi. Shukura miƙewa ta yi tana sakin murmushin ƙeta, sannan ta rifa masa baya. Maigadi shiru ya yi cike da jimami, don duk da 'yan gidan ba shiga huruminsa suke yi ba amma ya fahimci zuwan Shukura bai kawo komai a gidan ba sai sharri.
Lokacin da Shukura ta fita da faɗa Mommy ta tari Ruƙayya tana faɗin, "Ruƙayya kanki ɗaya kuwa? Kin san me kika aikata? So kike ki janyo wa kanki masifa kina zaune ƙalau?" Hawaye yana zuba daga idonta ta ce.
"Mommy ba ki ji abin da take faɗa ba? Duk wannan maganganun sai na yi mata shiru, yanzu saboda Allah ban da Daddy ya ba ta fuska ta isa ta faɗa miki haka?"
"Tun da mahaifiyarku ta ɗaure muku ai dole ku yi rashin mutumcin da kuka ga dama." Daddy ya furta a zafafe, cikin sauri Ruƙayya ta waiga ta ce.
"Daddy ka ga..."
Tas! Daddy ya ɗauke fuskarta da mari, kafin Ruƙayya ta yi motsi ya sake sauke mata wani. Rai a ɓace ya ce.
"Don ba ki da mutumci matar tawa uwarki za ta saka ki daka? Ni za ku wulaƙanta saboda rashin tarbiyya."
"Ai ba ita ba ce har da Hajiyan, kuma wallahi sai ka rama mini ko ni na rama." Shukura ta faɗa a shagwaɓe. Daga Mommy har Ruƙayya ɗagowa suka yi suna kallon Shukura, ta fakaici idon Daddy ta sakar musu gwalo sai kuma ta sake fashewa da kuka.
"Ni ba zan rama miki ba, sai dai ki rama da kanki."
Daddy ya faɗa yana matsawa gefe. Babu ko kunya Shukura ta matso da niyyar yi wa Mommy mari a fuska. Ruƙayya ce ta sha gaban Mommy, fuska a haɗe tana wurgawa Shukura mugun kallo.
"Za ki matsa ta rama marin da uwarki ta yi mata ko sai ranki ya ɓaci?" Daddy ya buga wa Mami tsawa. Zuciya a ƙeƙashe ta ce.
"Duk wani hukunci da za ta yi ta sauke shi a kaina, amma idan ta sake ta ɗora hannu a jikin mahaifiyata wallahi za ta gane kurenta." Cikin zafin zuciya Daddy ya sake marin Ruayya ya ce.
"Haka Karima ta gurɓata tarbiyyarku ban sani ba? Ba za ki matsa ba sai na sumar da ke."
"Ko za ka kashe ni Daddy ba zan bari wannan matsiyarciyar ta mari mahaifiyata ba." Ruƙayya ta faɗa zuciyarta a dake, don a yadda take ji a ranta komai za ta iya aikatawa a kan mahaifiyarta. Tana nan tsaye Daddy ya rufe ta da duka, amma taurin kai irin na Ruƙayya ya sa ta ƙi motsawa daga wurin. Kuka Mommy ta saka, ta janye Ruƙayya ta ce.
"Ba sai ka illata mini yarinya ba, za mu tattara mu bar maka gidanka." Fisge Ruƙayya Daddy ya yi, a zuciye ya dubi Mommy kamar zai kai mata duka ya ce.
"Kada ki sake shiga tsakanina da 'yata idan ina hukuntata. Idan ba haka ba wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci." A daidai lokacin Haidar ya shiga, jin abin da ake tattaunawa ya sa ransa ɓaci. Shukura ta sake fasa wani sabon kukan ta ce.
"Yanzu shi kenan sun daki banza da wofi ko? Wallahi ba zan sake kwana a gidan nan ba, kuma wallahi idan ban rama ba sai ka sake ni" Da sauri Daddy ya janyo Shukura jikinsa ya ce, "Babu inda za ki je, kuma mari kamar kin rama kin gama." Shukura da ke gaban Mommy ta ɗaga hannu ta zabga mata mari a fuska, ko sauke hannu ba ta yi ba Haidar ya ɗauke fuskarta da mari. A zafafe Daddy shi ma ya sauke wa Haidar mari sannan ya ce.
"Ni za ka wulaƙanta ka tozarta Haidar? Ashe kai ma ba ka da mutumci?" Rai a ɓace Haidar ya ce, "Daddy ba ka ga abin da ta yi ba ne? Ni fa dama na jima ina tara yarinyar nan. Wallahi tuntuni darajarka take ci, da tuni na ɓarar da ita." A zafafe Daddy ya ce.
"Za ka gane ba ka da hankali kuwa, idan hauka ne a kanka zan sa a sauke maka shi." Yana gama faɗa ya zaro waya ya nemo wata lamba, yana jin an ɗauka ya ce.
"Hello officer, ina son ganinka yanzu. Please ka taho da yaranka." Daga haka ya katse wayar, da mamaki Mommy take kallonsa kamar za ta tanka masa sai kuma ta haƙura. Suna nan tsaye suka ga ya ja hannun Shukura yana lallashi suka fita. Daga Haidar har Ruƙayya rungume Mommy suka yi, Mommy da Mami sai kuka suke yi. Haidar ne ma yake iya lallashinsu, ba su ɗauki lokaci ba suka haɗa kaya a cikin akwatunansu. Gabaɗaya kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Suna gab da fitowa suka ji ƙarar motar 'yan sanda, babu jimawa suka ji muryar Daddy yana cewa.
"Ku shigo ga yaron nan, ku zo ku tafi da shi. Ba shi tarbiyya ko kaɗan yaron nan, duk wanda ya zo belinsa kada a bada shi sai saka hannuna. Ku hora shi yadda ya kamata." Mommy da su Haidar suna tsaye, suka ga 'yansanda biyu sun shiga falon Mommy. Nan take suka saka masa hangoff a hannu, Daddy ya ba su umarnin su tafi da shi. Mommy tana kuka tana riƙe shi haka suka tasa ƙeyarsa suka tafi da shi, da ƙyar Ruƙayya ta lallashi Mami ta tsagaita da hawaye. Sannan suka ɗauki jakunkunansu suka fito harabar gidan.
GIDAN HAFIZ
Wani dogon tsaki Bilkisu ta saki cikin jin haushi ta ce.
"Da ka san ba kai kaɗai ba ne ai da sai ka sanar da ni." Ajiye akwatin Amina ya yi ya rungumo ta jikinsa ya ce.
"Kafin a fara faɗan ya kamata a yi mini oyoyo ɗin tukunna." Ajiyar zuciya Bilkisu take saukewa akai-akai, saboda yadda ta ji zuciyarta tana harbawa kamar ta faɗo daga ƙirjinta. Amina ta taɓe baki ta ce.
"Sannu da gida Aunty."
A sheke Bilkisu ta dube ta, ta ce. "Ke zan yi wa sannu, ni da nake gidan mijna sannun me za ki yi mini." Amina ta fahimci maganarta, don haka ta ce.
"Ai da yake tare muke da Habibi, na san kuma kin sha aikin gida shi ya sa na miki sannu. Ga shi sai da na ce ya kira ki kafin mu ƙaraso amma ya ƙi."
Bilkisu ji ta yi kamar an zuba mata borkon, Hafiz da ke tsaye mamaki ya kama shi, don shi dai ya san bai yi haka da Amina ba. Yana shirin yin magana Amina ta yi gaba tana faɗin.
"Baby ka shigo mini da akwatin, kuma ni yau kwana za ka yi kana matsa mini ƙafa don ciwo take yi mini."
Bilkisu jin haka ya sake hargitsa ta, rai a ɓace ta saki hannun Hafiz ta wuce ɗaki fuuuu kamar za ta tashi sama. Amina tana ganin haka ta saki murmushi, a ranta ta ayyana.
'Ashe dama matar nan sakarya ta mayar da ni, shi ne take kunna ni ban sani ba. Ai kuwa da ni take zancen.'
Tana shiga ɗaki Hafiz ya shigar mata da akwatin, sannan ya fito ya nufi ɗakin Bilkisu. A kan kujera ya same ta, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce.
"Baby kin yi kyau sosai." A madadin ta ba shi amsa sai ta ce.
"Wato Hafiz ni ka so tozartawa ko? Saboda za ka dawo da matarka shi ne ba za ka sanar da ni ba. Na gode, ai yanzu amfanina ya ƙare tun da ta dawo." Zama Hafiz ya yi a gefenta ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa za ki ce haka? Ina kasuwa mahaifinta ya kira ni, amma don Allah ki yi haƙurin rashin kiranki." Yana rufe baki sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, janyo ta jikinsa ya yi ya shiga lallashinta. Sai da ta tsagaita da hawayen sannan ya ce.
"Ina abincina?"
"Yana kicin." Ta ba shi amsa a daƙile.
Har ya miƙe zai fita ya waigo ya ce.
"Am dama tun da Amina ta dawo, a ɗakinta zan kwana yau."
"To mene ne na faɗa mini Abban Sayyid, ai duk abin da ka yi ka isa ne. Da za ka dawo da ita ka faɗa mini? Sai don za ka je ka kwana a wurinta za ka yi mini 'yar murya, duk abin da mutum dai ya yi Allah Yana kallo." Murmushi kawai Hafiz ya yi ya fita, don ya fahimci rikici Bilkisu take ji, idan ya ce zai tanka mata sai ta mayar da abin ya zama babba.
A ranar kwanan farinciki suka yi tsakanin Hafiz da Amina, duk wani tabon da take kallon Hafiz da shi ya goge. Kuma tun daga wannan lokacin Amina ta sauya taku, duk wani motsi da furucin Bilkisu tana ganewa. Don haka koda ta yi wani abin Amina ba ta nuna mata ta damu, wannan dalilin ne ya sa Amina ta cigaba da zaman aurenta cikin kwanciyar hankali. Sai laulayin cikin da yake danunta, shi ma a lokacin da ya shiga wata huɗu sai laulayi ya yi mata sauƙi sosai. Don babu abin da ba ta ci sai wanda ba a rasa ba, haka kuna ta ɓangaren ciwo zazzaɓin dare da yawan ciwon kan da take yi duk ta daina.
Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri duk ranar da Hafiz yake ɗakinta, a ɓoye za ta aiki yaranta gidan wata ƙawarta Maman Siyama, da yake yaran Maman Siyama sun girmi su Sayyada sai su sayo mata Nama ko kifi a ɓoye. Sai ta yi girki da shi, ko kuma da safe ta sayo ƙwai tun da dare ta soya musu ita da yara. Haka wunin ranar Amina za ta yi ta cika tana batsewa, kuma sai abin ya haɗe mata ga saurin fushi irin na mai ciki ga kuma abin da Bilkisu take yi. A irin haka har faɗa suka taɓa yi da ita da Hafiz, ya yi mata rantsuwar duniya a kan ba shi yake saya wa Bilkisu ba ta ƙi yarda. Tun yana lallashinta har ya yi watsi da ita, sai watarana da ta jin sallamar yaro bayan ya shiga ɗakin Bilkisu har zai fita ta bi shi soro da sauri. Murmushi ta yi masa cikin bugar ciki ta ce.
"Ni kam kifin da kake sayo wa Maman Sayyada yana da arha kuwa? Naman da kifin wanne ya fi sauƙi ne?"
Yaron ya yi jim sannan ya ce. "Gaskiya kifin ya fi arha don Ummanmu ma shi take saya, amma na ga ita Maman su Sayyid ta fi son na sayo mata nama." Jinjijna kai ta yi ta ce.
"To je ka, na gode ka ji."
Ya amsa mata ya tafi.
Ɗaki ta koma tana nazari, sai kuwa ta ɗauko waya ta kira Hafiz sai da ta ji ya ɗauka sannan ta fita tsakar gida ta ce.
"Hello Habibi, ba na jinka ko network ne?" Bilkisu tana tsakar gida tana koyawa su Sayyada aikin makaranta, ta ji muryar Hafiz raɗau a kunnenta. Amina da ta tabbatar da Bilkisu ta ji, sai ta fakaici idonta ta katse kiran ta ce.
"Yawwa dama na ce, don Allah idan za ka taho ka biya gidan Aunty Nana ka ba ta kuɗin naman kai ƙafa, don gobe farfesunsu nake so kuma ba na son na yi wahalar dafa su." Sai ta shige ɗaki ta ce.
"Eh network ɗin ya dawo, to shi kenan Hubby Allah Ya bar mini kai." Amina ta leƙa ta windo ta ga Bilkisu ta yi kasaƙe har da sakin ƙwafa.
Tun a daren ranar ta kira yayarta Aunty Nana ta tura mata kuɗi, ta ce da safe ta aika yara a sayo naman kai ta yi mata farfesu, idan ya so da rana idan Hafiz ba ya gida sai ta aiko a kawo mata.
Kamar yadda suka tsara Amina tana zauna a tsakar gida washegari da rana, tana sai ga Usaina 'yar yayarta ta yi sallama. Da yake budurwa ce, kuma Amina ta kitsa mata komai tana shiga cikin ɗan ɗaga murya ta ce.
"Aunty ga farfesun naman kan, wai Umma ta ce ga canjin dubu ɗaya da ɗari biyar na Yaya Hafiz." Amina ta karɓa ta buɗe, take ƙamshin ya mamaye gidan har ta ji yana shirin saka ta amai. Gani suka yi Bilkisu ta fito, Amina ta ɗan yamutsa fuska saboda dama can naman kai bai wani dame ta ba ta ce.
"To ku kunci ne?" Yarinyar ta girgiza kai, sai ta ɗauko wata ƙaramar roba ta ɗauki ƙafa ɗaya ta ɗora a kai da romo ta ce a miƙa wa Bilkisu. Tun Usaina ba ta rife baki daga sallamar da ta yi wa Bilkisu ba, ta buga mata tsawa da cewar ba ta ci. Dariya Amina ta yi a ranta, ta dubi Usaina ta ce.
"Ungo canjin nan nasa je ki kanti ki sayo mini multina guda biyu, don wannan naman kan ba lallai na iya cinye shi ba sai dai ki tafi da shi."
Babu jimawa Usaina ta sayowa Amina, sai da suka shiga ɗaki sannan Amina ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Maza ki mayarwa da Aunty naman kan nan, don wallahi daurewa kawai nake yi ji nake kamar zan yi amai." Dariya Usaina ta yi, ta yi saurin fita daga gidan ba tare da Bilkisu ta ganta ba.
Tun bayan zuwan Usaina Bilkisu ta cika fam tana jiran dawowar Hafiz, yana dawowa da daddare ko mashin ɗinsa bai gama ajiyewa ba fuuu Bilkisu ta je ta same shi a wurin ta ce.
"Wallahi ka ji tsoron Allah Hafiz, don kuwa Allah sai ya tuhume ka a kan rashin adalcin da kake yi."
Da mamaki ya dube ta ya ce. "Rashin adalcin me na yi miki?" Takaici ya sa Bilkisu ta fashe da kuka ta ce.
"Yanzu don zalinci har naman kai za ka sa a dafowa Amina ni yarana muna zaune ko oho? Wallahi Allah ba zai barka ba, idan kuwa kana zalintata ban yafe maka ba." Rai a ɓace Hafiz ya ce.
"Ni kike faɗa wa haka?"
"An faɗa maka, mugu azzalumi. Wallahi ban yafe maka ba Hafiz." Har ya ɗaga hannu kamar zai mare ta sai ya sauke, bayan ya gyara mashin ɗinsa ya ce.
"Amina! Amina!"
Da sauri Amina ta ƙaraso ta ce.
"Gani baby, ashe ka dawo."
"Me yake faruwa? Na ji Bilkisu tana zancan naman kai?" Hafiza ya tambaya. Amina ta wara hannu ta ce.
"Ranka shi daɗe itaa za ka tambaya, ba ita ta yi maka maganar naman ba."
A ƙufule Bilkisu ta ce. "Ni za ku mayar mahaukaciya ko 'yar iska? Na ji kina waya kina cewa Hafiz ya biya ya kai kuɗin a saya miki naman kai, har a kawo ki kawo mini ɗazu shi ne za ki raina mini hankali?"
Amina ta zaro ido tana tafa hannuwa haɗe da salati ta ce.
"Aunty sharri za ki yi mini? Ni na ce Baby zai tura kuɗin naman kai?" Sai kawai Amina ta rushe da kuka.
Ummou Asalam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA ƊAYA
KU ZO KU SAYI MUSULMAN KAYANMU💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Assalamu Alaikum
Ina manyan mata yan gayu masu ji da kwalisa ...
Ina masoyan jakankuna da mayafai da kuma sarƙoƙi?
Ummee's Collection ta tanadar muku su kala kala acikin farashi mai sauki, lallai ku hanzarta