Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 22

24K to 27K   out of 64.9K words

ya b oye hakan saboda wani gagarumin laifi da suka masa, shima kuma ya rufa musu asiri ne saboda ba ya son a sake cewa ya yi wani auren ba tsarin sa bane auren Mata da yawa.


Da k yar ya saki ajiyar zuciya ya sake d agowa yana zubawa Murad da yake hannunsa ido, kamanninsa da yaron yana sake k arfafa irin kamannin nan da Hausawa sukewa Lak abi da kwabo da kwabo. Idanunsa a raunane ya d ago ya kalli jama ar Falon wanda duk jininsa ne da suke Uba d aya, shi ka dai ne bare a cikinsu y ar uwarsa d aya ce Mace kuma ta rasu shekara d aya da ta wuce a hatsarin Mota. Ya yi gyaran murya yana so ya fa di abinda yake ransa Amma yana nazarin fuskar y an uwansa da kai tsaye dama burinsu kenan su samu mummunan abu da zai zama bak in tabo gareshi su ya da shi a duniya don mutane su yi Allah wadarai da shi, so suke a dole sai mutane sun k i shi, Haushinsa suke ji sosai da ya zamo shine Sarkin gabas ba d aya daga cikinsu ba, duk da girman da ya bawa Yayansu bai wuce kwana ashirin da takwas ba, amma a tsari na Masarautar Gabas ko da kwana d aya ya girme shi shi zai gaji sarautar Ubansa don haka sarautar kai tsaye ta fa da kansa. Duk da Uwarsa itace ta uku a matan Sarkin Gabas Mai rasuwa Amma ita ta fara haihuwa don haka dole shine ya zama Sarki wannan ya d arsa tsana mai girma a zuk atan zuriyar Mahaifinsa Sarkin Gabas Abdallah.

Ya d inke fuskarsa tsaf ba ragowar d igon rahma so yake sai ya cirewa zuciyarsa Shakkarsu da tsoron cutarwarsa gare su.  Ba ni da wani abu da zance, sai dai ina ji a jikina koma daga ina wannan yaron yake na amince Jini na ne, zan kuma kira likitoci su zo su tabbatar da hakan, idan komai ya kasance kuma kuna da ikon zartar da hukuncin duk da ya dace gane da Mulki na, abu d aya na sani Ina son sa! So mai tsanani da zan iya rasa komai da kowa a duniya ciki kuwa har da Sarautar da ku kan ku, zan zab i kasancewata da shi na rabu da kowa saboda shi. Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke yana jin hukuncin da ya zartar a zuciyarsa shine daidai su suka damu da Mulki suke kuma d okinsa. Shi a yanzu Son da yake wa jaririn hannunsa ya fatattaki son da ya kewa Mulki dama shi ba ma abocin son Mulkin ba ne don dai jama ar Gabas sun nace sai shine, Business d in da yake yi a k asashe daban-daban ya ishe shi rayuwa don yana da ku di ba na wasa ba.


Gunguni da k ananan surutai ne suka dinga tashi a Babban Falon Fulanin kowa yana furta abinda yaga dama akan wannan maganar, Abu d aya fuskokinsu suke nunawa duk da basa son bayyanuwar hakan sai dai kallo d aya Sarki Mukhtar yake musu ya tabbatar da Burinsu ya cika! Haka dama suke so idan Jama a suka ji abin kunyar da ya aikata su masa tawaye su kuma yi tur da Allah wadarai da Mulkin nasa. Don zina A masarautar Gabas Babban laifi ne a zamanin da yake sawa har su jefe mutum ko kuma a masa d aurin talala. Balle Sarki da kansa? Da d an da suke tunanin d an shege ne a hannunsa. Fulani dai tana zaune tana jin zuciyarta ta yi wani irin nauyi sam maganar da Mijin nata ya yi bata mata da da di ba, sai dai ta san ko giyar wake ta sha ba yarda za a yi ta fuskanci Mukhtar da wannan zancen, duk da yake mutum mai sauk in hali gefe guda kuma yana da zafin zuciya a lokuta da dama kuma mutum ne shi Mai zurfin ciki. Ta ja bakinta ta tsuke ga wani irin ciwon baya da na mara da ya zo mata lokaci guda.


Da k yar k ananan maganganun suka lafa kafin kowa ya mik e suka fice d aya bayan d aya zuk atansu d auke da madaukakin farin ciki da ya kasa b oyuwa a saman fuskokin su, duk da k ok arin da suka yi wajen b oye hakan.

Shiru parlourn ya d auka, ba kowa daga Sarki sai Matansa guda hu du biyu ba gaske biyu kuma daga ciki sun san Matan Jabu ne, tunda ba aure a tsakaninsu. Sarki Mukhtar ya d ago a hankali yana nazarin fuskokin Matan nasa da kai tsaye zai iya hango matsananciyar damuwa da take kwance akan fuskokinsu musamman biyun Fulani Rahina da Fulani Saddik a su fi nuna matsanancin tashin hankali duk da na Rahina ka dan akan na Saddik a da bata ma da cikin ba kuma ta da alamar sa, gwara Rahina zata iya haihuwa nan kusa. Su kuwa sauran idan ya yi nazarin fuskokinsu zai iya d orasu a mizanin Kadaran kadahan duk inda ta kwana sha ce, tunda su da kansu sun san igiyoyin auren nasa a wajen Sarki Mukhtar sun mutu murus ba ko d aya. Ya saki sauk akkar a zuciya kafin murya a dake mai sautin Amon rashin tsoro ta daki dodon kunnensu.  Ku saka a ranku Murad d ana ne Jinina ne, kuma ina son kowa ta masa kallon hakan bana son wata magana bayan hakan, kuma ban ce kowa ta tambayeni dalili ba abu d aya na sani da Kuma shi zan gaya muku ba wata mu amalar banza da ta tab a ha da ni da wata Mace, ban san ta yarda aka samar da cikin ba kamar yarda ban san a yaushe na kusanci wata Macen na mata ciki ba, wanda ya aikata shi ya san ya ya samar da cikin ko shi ko Uwar yarinya, abu d aya da zan fa da idan likita ya tabbatar da Murad Jinina ne, zan rungumeshi zan nuna masa So ba Kuma zan laminci a nuna masa k yama ba zan iya rabuwa da kowa saboda Murad, dafatan kun fahimta? Ya fa da yana ware idanunsa masu tsananin kyau da kwarjini a kansu. D aga kai suka yi alamar sun gane sun kuma Fahimta. Ya dubi Fulani Saddik a Mace mai hak uri kawaici mara son tashin hankali sab anin Fulani Rahina da ta zama Mace mai fa da da masifa ga saurin fushi ya ce  Saddik a zo nan. Ta mik e jikinta a sanyaye ta isa wajensa.  Daga yau na baki Amanar Murad, Ina son ki saka a ransa ke ce Uwarsa ke kuma kika haifesa kada ki bar wani abin cutarwa ya rab esa zaki iya? Cikin wani irin tsananin farin ciki Fulani Saddik a ta d aga kai tana jin duk wani bak in cikinta ya yaye. Ta saka hannu biyu ta amshi Murad tana saka shi a jikinta ta rungume wata irin zazzafar k aunarsa tana bin sassan duka jikinta. Da gaske Sarki Mukhtar ya gama mata komai. Fulani Rahina kuwa hankalinta ne ya tashi jin hukuncin da Sarki ya zartar lokaci guda, idan har tana fahimta daidai shikkenan Fulani Saddik a ce zata zama Uwar Sarki mai jiran gado, duk da ta san Al ummar Garin Gabas ba za su amince D an Shege ya Mulkesu ba, duk da Haka bata so ba, bata so a bawa Saddika ba, me Yasa SARKI bai bata ba duk da Kowa a Gabas ya san itace MOWAR SARKI, ita Sarki ya fi so kamar yarda kowa ya shaida itace mai fa da a ji a Fadar Garin Gabas. Cikin fushi mabayyani ta kalli Sarkin da ya d auke fuskarsa tamau  Me yasa za a bawa Saddika alhali ni ce Uwargida? Sarki Mukhatr ya zuba mata ido kafin shima nasa ran a b ace cikin zafin murya ya ce  Haka na yi niyya. Ya juya ga Saddika da ta sake rungume shi tsam a jikinta ya ce  Ki je da shi Sassana a can na amince ki yi rainonsa saboda bana son a yi wasa da lafiyarsa idan komai ya kammala ma barin k asar za ku yi ke da shi za ku koma England har sai Ya girma sannan zaku dawo ni da kai na Zan dinga zuwa muku ziyara, abu d aya nake son sani yanzu likitoci su tabbatar Murad Jini na ne. Za a siyo Madara da duk abinda yake buk ata. Fulani Saddik a ta sake d aga kai kafin ta mik e rungume da Mukhtar a jikinta ta bi wata hanya da kai tsaye zata kai ta sassan Sarkin. Fulani Rahina ta bita da wani wulak antaccen kallo tsanarta da kishinta yana sake kambaba a zuciyarta ji take kamar ta je
Ta mak ureta da ita da Shegen jaririn su Mutu gaba d aya ko ta huta da ciwo da ra da din zuciya. Sarki da yake hankalce da ita bai mata magana ba, har sai da su Fulani Maimuna da Fulani Habiba suka fice sannan ya dawo da kallonsa gareta cikin muryar garga di ya ce  Ki aikata abinda yake ranki, tabbas kina son ki bi sahun su Maimunatu don zan iya aikata komai game da tsare rayuwar Murad.
Daga haka ya Mik e cike da taku mai nuna nagarta da k arfin Mulki ya bi bayan Fulani Saddika. Wannan furucin nasa shi ya sake gigita Rahina ta rasa natsuwarta gaba d aya ta san tunda ya furta tabbas yana nufin abinda yake cikin zuciyarsa ne kai tsaye.
Ta ciji yatsa a hankali tana sake jin azababben ciwon na sake dawo mata k ugunta kamar zai b alle.

(Ku cigaba da biya masoyana da din
Littafin na gaba wannan duk shimfi da ne. Kamar yarda na fa da In sha Allah. 500 zuwa asusun banki kamar haka 2118666253 UBA. Sai a tura shaidar biya ta numberr waya 08033748387.


JIKAR NASHE.
'

K UDIRAR ALLAH.

11.


NAZEEFAH SABO NASHE.
'
08033748387.




Yarda gumi ya jik a Fulani Saddik a zai tabbatar maka da nak uda ce take yi mai azabar gaske. Runtse ido take yi kawai tana cije bakinta kukan ma ya k i zuwa sai cizon leb enta take. Hakan ya janyo hankalin Barorinta ba shiri suka yi yo kanta da sauri da k ok arin son su taimaka mata. Zafin ciwon da take ji ne yasa tana ji tana gani suka kamata zuwa cikin d akin.
Kafin su juya sanar da Jakadiya ta yi wani irin k akkarfan nishin da yasa kan Babyn ya danno da
K arfin gaske. Ta saki hucin wahala a hankali tana duban abinda ta haifa, zuciyarta ce ta kusan bugawa ganin jaririyar yarinyar a gabanta. Da k yar ta ha diye yawun da ya tokare mata a mak oshi ta janye hannunta ta d au jaririyar a hannunta kamarsu guda da y ar ba abinda ta d auko na Ubanta. Hawaye ne ya so ya kece a idanunta sai dai ta yi k ok ari sosai ta danne abin a ranta ganin yardaddun barorinta a wajen.


Labari ya kara de masarautar gabas aka fara sanar da haihuwar Fulani Saddika kowa ya cika da al ajabi gefe guda kuma ana tunanin a ina aka samo wancan jaririn da aka tsinta? Sanda Sarki ya samu labarin bai ji komai a ransa ba kamar yarda ya samu farin ciki da aka kawo masa Murad a matsayin d ansa bai sani ba ko don Macece. Da kansa ya taso zuwa b angaren Fulani Saddik an don ganin lafiyar ta da ta jaririyar da ta haifa. Ido Fulani ta zuba masa lokaci guda kuma abinda yake ranta ya kasa b oyuwa a zuciyarta sai da ta bayyana kuka ta saka sosai kukan da ya raunata zuciyar Sarkin gabas bai san sanda ya k arasa wajenta ba da sauri ya fara tambayar ta lafiya? Hawayen ne ya fara zubo mata ba kakkautawa kafin ta sanar masa damuwarta na rashin samun muradinta Magajin Sarkin Gabas. Shiru ya yi yana zuba mata idanunsa masu cike da kyau da Haiba kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce  Ki k addara haka Allah ya so ki ma gode masa da ya baki d iya macen ki kuma yi fatan ta rayu&  Ta ha diye kukanta ta yi tunawa da budulcin da taso ta yiwa Allah da sauri ta ce  Astagfirullah. Ta kuma sake rungume jaririyar a
Jikinta cikin nutsuwa take sauke ajiyar zuciya. Sarkin Mukhtar ya saki murmushi a
Hankali shima. Yana cigaba da nazarin Saddik ar ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da bata iya b oye abinda yake ranta. Da kansa ya amshi yarinyar ya kuma yi mata hu duba Da Fateema.

Daga lokacin da visar su ta fito ya ha da Murad da Uwar rainonsa zuwa k asar England inda a can ya fara karatu ba kuma ya zuwa ko ina sai idan an yi hutu yake zuwa Nigeria, don haka mutane da yawa ba su san shi ba saboda rashin son hayaniyar sa da shiga mutane.


Sanda Sarki ya gama ba shi labarin tuni jijiyar kansa ta tashi ta yi ra da ra da, idanunsa sun sake girma kamar yarda suke kasancewa idan yana cikin b acin rai. Hannu kawai ya saka yana murza goshinsa da yake sara masa kamar zai dare. Ya
Lumshe idanunsa so yake
Hawayen su zuba sai dai juriyarsa da izzar sarauta ga allurar sojojinsa mai saka zuciyarsu dakiya sun hana shi zubar da hawayen.
Ya mik e yana furzar da huci a hankali, Sarki yana ji yana gani ya fice daga fadar duk da yanayin da yake ya ci a dakatar da shi sai dai ya san a wannan lokacin ba wanda ya isa ya dakatar da Murad. Nutsuwa yake so ya samarwa kansa kafin zafin zuciya ya saka shi ya Jirge fushinsa a kan duk wanda ya yi nufin shiga gonarsa.


Har ya isa b angarensa hucin yake furzarwa, jin alamun Hadimansa suna binsa ba tare da ya juyo ba ya dakatar da
Su ta hanyar d aga musu hannu. Yana shiga ya rufe k ofar da saurin gaske hannayensa duka biyun ya dinga dukan bangon d akin da su, tunani ne fal ya cika zuciyarsa so yake ya hango wacece mahaifiyarsa shin shi d in d an Sunna ne ko d an haram, dole ba zai zama d an Sunna ba tunda dai sarki da kansa ya san bai tab a kusantar wata mace ba sai Matansa hu du idan haka ne ya zama dole ya gano ta hanyar da aka samar da shi wacece kuma Uwarsa?





______________________



A gefen Baffa Jaheed yake zaune kansa a k asa zuciyarsa a raunace take sosai jin zantukan da Baffan yake yi.  Gobe zata tare a gidanta ba wata bidi a da za a yi don na ga Uwarta bata neman zaman lafiya da ni. Zuciyar Jaheed ta shiga wani irin bugu da da hali da kansa zai dakatar da Baffa daga wannan zancen don bai hango ta yarda zamansu da Najma zai yi tsawo ba. Amma kima da martabar Baffan ta hana shi furta komai illa ha diyar yawu mai kauri da ya yi ya d agawa Baffan kai murya can k asa Kuma ya yi furucin godiyar da ya san tabbas ba ta kai har zuciyarsa ba. Baffa ya d aga kai ya ce  Ni zan gode maka Mujaheed da aka amince da auren mara kunyar yarinya irin Najma sai dai ina son ka yi hak uri da duk abinda zai faru wata rana sai labari wata rana kuma da
Kan ka zaka gode min. Jaheed ya d aga kai duk da bai hango sanda ranar zata zo ba in dai har da Najma yake tare yarinyar da ta tashi da tsanarsa a zuciyarta tun k uriuciyatta. Jaheed yana fita Baffa ya mik e zuwa cikin gidan. Fuskarsa a d aure ya shiga sashen Mahmeey a parlour ya zauna kafin ya saka Nasma ta kira masa Najma. Fuskarta a ko de ta fito daga d akin da alama ranar ma yini ta yi tana kukan. A gaban Baffan ta zube idanunta suka cigaba da zubar hawayen da suke. Baffa ya bita da kallo mai cike da nuni da zallar jin haushi kafin cikin takaici ya kira sunanta murya a kaurare. Najma da sauri ta d ago kafin ta rusunar da k wayar idanunta tana jin ko kasheta Baffa zai yi ba zata amince ta zauna da d an mahaukaciya ba, da ta zauna da shi gwara ta gudu ta bar gidan.  Dole ne ki zauna da Jaheed in dai kina amsa sunana a matsayin mahaifi idan kuwa kin shirya goge sunana daga matsayin mahaifin Ki sai na ce Bissalam. Ya furta mata kai tsaye kamar ya san abinda yake ranta. K irjinta ne ya buga sosai murya a sark e ta ce  Baffa bana son shi na tsane shi kamar yarda na tsani mutuwata Wallahi zan iya kashe shi na kashe kai na a duk sanda ya amsa sunan Mijina&  wani irin Mari Baffa ya bata, kamar an cillo Mahmeey cikin tashin hankali ta janye ta tana furta  Kada ka sake dukar min y a akan wancan banzan shashashan&  Baffa ya d ago ransa a b ace yana kallonta ya furta  Idan kin ga bata amsa sunan Matar Jaheed ba sai dai idan na daina amsa sunan Ubanta& &  wani irin jan burki Mahmeey ta yi kafin ta ce  Akan d an mahaukaciyar? Baffa ya d aga mata kai cike da tabbatarwa. Mahmeey ta saki dariya kafin ta ce  Ai dama ni na san ba banza ka ke zaune da matar nan ba akwai wata a k asa&  wani kallo Baffan ya mata wanda ya sata shiru ba shiri shi kuma ya mik e yana nuna Najma ya ce  Ki shirya gobe kamar yanzu Mijinki zai d auke ki zuwa gidansa. Ba Najma ba harta Mahmeey sai da k afafunta suka kasa d aukarta suka zauna

9 / 22