Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 22

57K to 60K   out of 64.9K words

ta yi ba tun yanzu ba ta yi nadama
Ga duk abinda ta aikata sai dai ta san ba mai amincewa da nadamar tata.  Sai ki masa takatsantsan da cikinsa idan mun yi waya da shi zan sanar da shi kina da cikinsa kin san dai aurensa na nan a kan ki har sai kin haife cikin nan sannan iddarki ta cika ko? Najma ta  d aga kai tana jin wani sanyi a ranta jin abinda Umma ta ce wai da auren Jaheed a kanta, auren da ta Riga ta fitar da dai da shi ta zata ya mutu murus, idan kuwa haka ne zata yi duk mai yiwuwa ganin ta dawo da Jaheed cikin rayuwarta, zata bi duk hanyar da zata bi ta karkato da soyayyarsa gareta. Umma ta ce  Allah ya raba lafiya. Ta cigaba da tuk inta zuciyarta na ayyana mata abubuwa da da dama.




_______________



K arfe ukun dare daidai lokacin da agogon d akin Fulani Raheenan ya buga. Ta bu de idonta da ya fara mata nauyi sosai saboda matsanancin barcin da yake cikinsu. Bata samu barci ba a daren ko ta ce ma tsawon kwana uku da suka shige bata samun barci Saboda halin firgicin da take ciki. K afafunta ta ziro k asa ta taka tattausan carpet d in dake bakin gadon ta. Ta mik e tana tattare gashinta ta tufke waje guda. Tana mik ewa ta shiga toilet fitsari ta yi kafin ta fito ta zura wani zundumemen hijabinta da ya rufe duk jikinta ruf ta jawo nik ab ta saka ta rufe fuskarta da shi. Sannan ta  d au y ae jakar ta fata ta fita a hankali yarda ba wanda zai ji motsinta. Ta k ofar baya ta fita kamar yarda ta saba irin wannan fitar ta sirri. Shiru wajen baka jin kukan ko tsuntsu a wajen. Bata jin tsoro don zuciyarta ta bushe mafita kawai take nufi da rufin asirin ta. A hankali take taku zuwa inda suka yi za su ha du da mutanen.


Banda duhuwa ba abinda kake gani a wajen sai hasken farin wata da ya mama ye wajen, don hanya ce da sam mutane basa binta da rana ma balle da daddare. Haskota aka yi da torchlight hakan ne ya nuna mata inda suke. Ta isa wajen a hankali tana sakin ajiyar zuciya. Kamar koda wani lokaci Suna sanye cikin bak ak aen kaya baka ganin komai a tatttare da su suka mik a mata wani k ulli a leda  Dukka bayani yana ciki, abin buk ata ki yi takatsantsan baa son kuskure ko guda. A satin nan muke son ki kai buk atar ha da auren Murad da k anwarki gaban sarki. Ta karb i k ullin tana sakin ajiyar zuciya kafin ta ce  Kuna tunanin Sarki zai amince da buk atar auren Murad da k anwata? Dariya suka yi sosai suna furta  Da zarar kin saka wannan layar a k ark ashin harshenki kika furta masa k udirinki zai amince. Ta gyad a kai kafin ta furta  Ba zaku nuna min kan ku ba? Shekara nawa muna tare ban tab a ganin fuskarku ba? Tambaya ta gaba kune kuka samar da cikin Murad? Kuma wacece mahaifiyarsa? Kuma
Me yasa cikin bai zama tare da ni ba sai wata can? Dariya suka yi sosai kafin su ce  Lokaci na zuwa da zaki samu amsar duka wa dannan tambayoyin naki, ki je ki aikata abinda muka umarceki!
Suka fa da cikin daka tsawa
Kafin su umarceta ta bar wajen. Ta juya a hankali ta bar wajen zuciyarta cike da jin haushin rashin amsa mata tambayoyinta da ba su yi ba, su waye wa dan nan d in? Shine abinda bata sani ba.


Kashegari kuwa da k udirin hakan ta tashi a ranta. Ta yi duk abinda zata yi kafin isa turakar Sarki bisa jagorancin Jakadiya. Sai da ta gama hilace shi tas kafin ta bijiro masa da zancen ha da Murad da k anwarta. Abin mamaki ko ka dan Sarkin bai musa mata ba ya amince take ya kuma ce mata ta sanar da Murad d in shima kuma zai sanar masa ranar Sallah za a d aura auren da zarar an sakko daga Sallahr Idi shi kansa zaman Murad d in ba aure ya fara isarsa. Zallar farin
Ciki ya bayyana akan fuskarta ta fice daga d akin cikin farin
Ciki ta isa sashenta kafin ta dannawa mahaifiyarta kira ta bata kyakykyawan albishir. Ta Kuma ce ta turo mata Amran a yau akwai abinda zata bata ta je da shi har b angaren Murad da zarar ya sha ka zai ji duk duniya ba matar da yake son ya aura sama da ita.




_______


Da k ananan kayansa da ya je training da su ya yi hanyar da zata sadashi da b angaren matan Sarkin. Kai tsaye sashen Mammansa ya nufa. Bata d akinta kamar yarda ya saba ganinta a duk safiya don haka ya fito yana kallon su Mardiyya masu aikin b angaren nata.  Ina Mamma? Ya furta cikin murya mara sautin amo don a gajiye yake lik is. Mardiyya ta nuna masa kitchen. Har zai zauna ya ce ta kira masa Mammahn sai kuma ya fasa ya nufi kitchen d in da kansa. A tsaye ya samu Mamman da y ar bak ar yarinyar suna aiki tare don Mamman ta saba ko me take yi ita take masa abinci shi da Maimartaba a duk ranar girkinta. Ya ware ido ganin yarda yarinyar take aikin fere dankali.  Mammah me wannan take yi? Mamma ta juyo fuskarta a ha de ta ce abinda idanunka suka gane maka. Ta juya ta cigaba da aikinta Harara ya zubawa Najwa kafin ya fice daga kitchen d in duk yunwar da yake ji ba yarda zai yarda ya ci abincin da waccan yarinyar ta saka hannu.

Yana zaune a parlourn sa Hannunsa cushe cikin sumar kansa yana murzawa a hankali ransa ne a b ace ga yunwa da yake matuk ar ji ya ji an turo k ofar an shigo. Azababben k amshin da ya ji ne yasa shi bu de ido a hankali. Kyakykyawar budurwar da ta sha kwalliya sosai tana tsaye tana sakar masa murmushi ta zauna a gefensa ha de da d aukan pillow tana saka shi a cinyarta ta d ora hannayenta a kai, cikin murya mai cike da yanga ta ce  Barka da hutawa. Murad kasa d auke idanunsa ya yi a kanta wata irin soyayyarta mai zafi tana harbawa a zuciyarta ya lumshe ido a hankali yana furta  Barka dai Beauty!





JIKAR NASHE
'

KUDIRAR ALLAH

25.

NAZEEFAH SABO NASHE
'

08033748387.



Shi kansa da ya yi furucin sai da ya ji abin wani banbarakwai, abinda bai tab a yi ba a rayuwarsa son wata mace ko ya bawa halittarta. Ya d an furzar da hucin numfashi yana cigaba da kallon fuskarta da ta sha makeup. Da gaske kyakykyawa shi da kansa ya shaida haka. Yanayinta ya nuna gogewa da wayewa yarda take kallon cikin k wayar idanunsa tana jifansa da wani sihirtaccen murmushi mai sanya maza kasala. Layar hannunta ta cigaba da matsawa kafin ta sake jifansa da wani murmushin ta mik e tana taku ta nufi hanyar fita  Am sorry na for disturbing you Amrah by Name. Ta fice cikin takun yanga da take sarrafa jikinta yarda ta so duk da ba wata kyan sura ba ce da ita ta azo a gani. Murad ya lumshe idonsa yana jin wata irin kasala gaba d aya ta mamaye gabbansa abinda bai saba da shi bai kuma d aukeshi da mahimmanci ba tunanin aure da sha awa ma gaba d ayanta.


Amra na fita ta saki ajiyar zuciya ganin da gaske tarkonta ya kama Murad ita da kanta ta san ya yi mata kuma shine ya dace da zama Mijin Amra. Ta fa da tana murmushi ha de da fa din  Nagode Yaya Raheena kin biya ni. Daga haka ta nufi b angaren Fulani Raheenan tana tafe tana sauraran wak ok in da suke sanyata nisha di. Ta fuskarta Fulani Raheena ta hango alamun nasara. Murmushi ta sakar mata kafin ta furta  Bani Layar nan don itace makaman yak in, da alamu mun yi nasara. Amra ta saki murmushi tana furta  K warai kuwa, wallahi tarkon da kika d ana masa ya kama shi, Alllah ya nuna mana ranar auren Yaya, Murad ya yi ta ko ina ba shi da makusa shi ya dace da zama Miji na har na k agu lokacin ya zo ban san wani irin y ay a zan haifa masa& &   Ke! Fulani Raheena ta dakatar da ita a tsawace tana wurga mata wani irin kallo.  Wace irin banza ce ke? Daga ganin Sarkin fawa sai miya ta yi zak i? Ce miki aka yi nufina ki aure shi ki haifa masa yara? Ba don wannan na shiga na fita na samo miki zuciyarsa ba saboda nawa burin ne, ran Murad nake so so nake ki zame min tsani na shek a shi lahira, bana son ganinsa Abdul nake so ya mulki mutanen Gabas&  waro ido Amra ta yi tana kallonta cikin tsananin mamaki ta furta  Kisa kuma yaya?  Kisa Amra, ya kuma zama dole ki bi umarnina tunda kika ji sirrina idan ba haka ba kuma ki shirya tafiya lahira kema, zan iya kawar da ko waye don cikar burina. Ta fa da idanunta suna k afa fitowa suna nuna alamun b acin ranta da gaske. Amra tsorata ta yi da yanayin Yayarta ta ta kuma bata mamaki matuk a da gaske, bata yi tsammanin rashin Imanin nata har ya kai haka ba.  Zaki iya ko kuwa? Ta fa da tana sake tsareta da ido. Amra ta ha diye kakkauran yawun da ya taru a bakinta kafin cikin mutuwar jiki ta d aga kai  Zan iya.  Ashe kina son rayuwarki, banda abin ki ke Ai abin jin da dinki ne ace kece matar Yareeman gabas ko bakomai kema kin shiga tarihi, za kuma ki samu dukiya mai tarin yawa ta tumunin takaba, ki bu de kunne da kyau ki ji ni, duk abinda na umarceki shi zaki yi bana son musu. Ta sake d aga kanta a hankali. Tashi ki tafi ki bani waje. Tana tafiya Fulani Raheena ta bi bayanta da wani watsattstsen kallo kafin ta ciji leb enta tana furta da alamu kema sai an min aiki a kan ki yarinya, dole sai an min yarda zan dinga juya Ki son raina ki dinga bin umarnina ko ba kya so. Daga haka ta mik e zuwa cikin d akinta tana jin kamar duk wani burinta ya gama cika.



Da Magriba Murad na zaune a parlournsa hankalinsa duk yana kan kallon football sai ga Sak o daga sarki akan yana nemansa a Fada. Ba b ata lokaci ya mik e suka fita da bafaden zuwa ainahin k aramar Fadar gidan sarkin.

A zaune ya samu Sarkin gabas d in Fulani Raheena na zaune a gefensa hannunta d auke da plate d in apples tana yanka masa. Da murmushi fal fuskarta ta tari Murad  Din. Ya zauna a gefen kujerar Sarkin kansa a k asa yana matsa hannunsa. Maimartaba ya dubeshi yana murmushi bayan ya amsa sannu da shan ruwan da yake masa.  Mun sha ruwa lafiya Murad gwauro. Murmushi ya saki yana sosa kansa a hankali cikin nutsuwa ya furta  Lafiya k alau. Maimartaba ya mik a masa tray d in da yake d auke da peppe soup na cowtail.
Duk da a k oshe yake haka ya amshi peppe soup d in yana sha a hankali don ya san bai isa ya ce Ya k oshi ba Sarki ba ya kyauta ace ba a so, yana daga cikin abubuwan da baya so, kuma kowa ya sani. Sipping yake a hankali yana jin bugun zuciyarsa na k aruwa haka kawai tun yammacin ranar yake fama da bugun zuciya mai k arfin gaske.  Lokacin da ya kamata ka yi aure ya zo Murad! Ya jiyo maganar Sarki daga sama yana fa da a hankali cikin nitsatstsiyar murya. Da sauri ya d ago yana kallon Sarki. Shima dubansa yake yana murmushin da alamun rashin wasa a maganarsa.  Da gaske ya kamata ka yi aure Murad shekarunka sun tura, kana da wacce kake so ko mu maka zab i? Haka kawai sai hoton yarinyar d azu ya dinga fa do masa yana jin ita ya dace ya aura sai dai haka kawai ya dinga jin nauyin bakin furta hakan ga Sarki.  Na baka zab i. Ya fa da a hankali. Sai a lokacin Fulani Raheena ta saki ajiyar zuciya farin ciki ya cika ta, ta tabbata aikin Malamin ne ya ci.  Alhamdulillah! Tunda ka bamu zab i ba za mu maka zab in tumun dare ba, Dama yanzu Mamanka take ce min ta maka Mata ta baka k anwarta don haka In sha Allah ranar idi zata zama ranar aurenka ba don komai ba sai don kafa tarihi, shi yasa na zab i ranar idin k aramar sallah, ina fatan hakan ya maka? D aga kansa ya yi kawai yana ajiye plate d in hannunsa, sai ya ji yana fatan dama yarinyar da ya gani a d azu ita zata zama matarsa. Jikinsa a sanyaye ya mik e ya fita daga fadar, yana jin kamar bai yiwa kansa adalci ba da ya bada damar a zab a masa matar da zata zama maha din rayuwarsa, me yasa bai tsaya ya tantance da kansa ba duk da burin da ya ci na zab ar mata ta kerewa sa a da kowa zai jinjina masa. Tunda yake bai tab a ganin matar da take burgeshi ba shi yasa ba agenderr hakan a cikin ransa banda yarinyar da ya gani d azu bai tab a d arsa wata mata a ransa ba.


Haka ya dinga tafiya yana rangaji zuwa sashen Mammansa da yaji haka kawai k afafunsa na jansa zuwa can ba tare da ya san dalili ba. Ba kowa a Babban parlourn sai Hadimanta ya bi su da ido kawai kafin ya saka kansa d akin Mamman tana zaune idanunta akan t.v sai dai ba kallon take ba tunani ne ya cika mata zuciya. Shigowar Murad yasa ta d aga kai da sauri tana kallonsa. Damuwar da ta gani a idanunsa ya sata mayar da hankalinta kansa. Ta nuna masa gefen gadon tare da kashe t.vn tana furta  Me ya sameka haka? You looked worried. Ya sunkuyar da kansa kawai ya kasa magana. Mamma ta ja hannunsa tana kallonsa  Oya talk to me me ya sameka na ce? Ajiyar zuciya ya saki kafin ya furta  Na yanke hukunci without you Mamma shine abin ya dameni. Fa duwa gabanta ya yi sosai ta gyara zamanta ta ce  Hukuncin me ka yanke Murad?  Aure! Ya fa da idanunsa suna raunacewa cikin nata. Hannunta na rawa ta ce  Aure kuma? Wa zaka aura? Ya saki ajiyar zuciya yana fa din  Sisterr Umma.  What? Fulani ta fa da da sauri hannunta na saki gaba d aya ta zauna a hankali gefen gadon tana furta  Wa ka gayawa zaka aureta? Kuma me yasa baka nemi shawarata ba me yasa hakan ta faru ba tare da sani na ba? Ta fa da hankalinta a tashe duk ta d imauce.  Mai martaba na gayawa Ta sake zare ido hankalinta na sake tashi ta furta  Shikkenan ba ni da ta cewa, Murad me yasa kake son saka kanka a matsala? Ka san abinda ka aikata kuwa? Zaka saka kanka a matsala? Tashi mu je wajen mai martabar. Bin bayanta ya ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yi a hankali ta fice zuwa k ofar da Zata sadata da Parlourn Maimartabar. Fulani Raheena ta gani a zaune da maimartabar bayan Jakadiya ta yi mata umarni ta shiga. Yanayinta kawai Raheena ta gani ta saki murmushin mugunta don ta san abinda ya kawota. Kallo Saddik a ta watsa mata kafin ta gaishe da Sarkin da yake kallonta cikin mamakin yanayin da take ciki.  Wata magana Murad ya je min da ita, wacce zai yi wuya na amince da ita. Mai martaba ya gyara zamansa ganin da gaske maganar mai mahimmanci ce maganar da zata sa Saddik a ta taso da daddare ta zo turakarsa ba ranar girkinta ba.  Ina jin ki! Ta zauna tana fitar da hucin numfashi na alamar b acin rai.  Auren Murad da ake neman k aga masa ba Zan amince da shi ba! Mai martaba ya dinga kallonta cikin mamaki yana son karanto abinda yake ranta. Fulani Raheena kuwa gyara zama tayi tana sake matsa Layar hannunta cikin murmushin mugunta tace  Auren Murad da Amra kamar an yi an gama, ko da ke kika haifi Murad balle ba ke ce uwarsa ba!  Idan kuma ni d in ce Uwarsa fa? Ko kin gwada jininsa da nawa kin ga ba d ana bane? Shin kin gwada k wayoyin halittarsa da nawa kin ga ba nice Uwarsa ba? Ta fa da cikin furzar da numfashi tana jin kamar ta rufe Raheena da duka& & ..  Aure da k anwarki da Murad ba zai yiyu ba in dai ina numfashi!





JIKAR NASHE
'


A yi hak uri wayata ce ta lalace da ta aro na yi. >???
KUDIRAR ALLAH..


26.

NAZEEFAH SABO NASHE
'

08033748387.



Fulani Raheena ta sake dubanta sosai tana mamakin furucinta da tunanin yarda aka yi idanun Fulani Saddikan suka soye har suka daina tsoronta. Saddik a kuwa idanunta ta mayar cikin na sarki tana jiran jin abinda zai ce, ga mamakinta ba wani b acin rai a fuskarsa ya ce  Me yasa Saddik a ba kya son ha da auren? Ina ga ba wani aibu bane tunda har shi Murad d in

20 / 22